Showing 204001 words to 207000 words out of 261165 words

Chapter 69 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1156

roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu harta birgeshi kaine silar komai..........”
        Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.
        Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.
         Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa. Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.
          Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.
      Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta mi

ƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace, “Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.
       Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.
        Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na kalli inda Aunty Aamilah take zanyi magana, wata muguwar harara ta watsomin tana jan tsaki da ɗauke kanta ta nufi ɗakinta. Duk da naji babu daɗi sai nai ɗan murmushi kawai najuya ga Yah Salman. Shima koda nai masa magana bai amsamin ba, haka na baro inda yake jiki a sanyaye naima Dad da duk abinda ke faruwa yana kallonmu sallama na fice.
            Fa kallo Dad yabi Bilkisu harta fice daga falon, ya sauke nannauyan numfashi yana gyara babbar rigarsa, kallon Aamilah da keta cika da batsewa yay ya ɗauke kansa, batare da yace mata komaiba ya haye sama abinsa. Ɗakinsa ya wuce, sai da ya rufe ƙofar sannan ya ciro wayarsa daga aljihu yay kiran Qaseem. Bugu biyu Qaseem ya ɗaga kuwa. Dad ya sauke numfashi yana cire hularsa ya zauna a bakin gadonsa, “Qaseem gasu nan sun fito, dan ALLAH ka danne ranka karka bari rigimar da kuka saba da yaron nan ta shiga tsakaninku, mu lallaɓasa musan inda Mamana take dan nasan wlhy shi kaɗaine keda masaniyar hakan”. “Karka damu Dad, namaka alƙawarin a daren yau sau Shahudah ta kwana gida, yanzun nan zan kirashi a waya nace masa yazo ya sameni muyu magana”. Qaseem ya faɗa yana danne ɓacin ransa da mugun tsanar Jay dake cimasa zuciya. Sallama sukai, Dad ya ajiye wayar yana sauke numfashi da haɗiye tsantsar damuwarsa akan rashin abar ƙaunarsa mafi soyuwa acikin ƴaƴansa. Qaseem kuwa daga can kiran Jay yayi duk da yana tunani da wahala ya ɗauka tunda bayin wayar sukeba, a yanzunma sai da Dad ya turo masa number Jay ɗin dan bashi da ita da.

         A cikin mota na iske boss yana waya, bayan na shiga Sadiq ya rufe ƙofar kamar yanda ya buɗemin na shiga. Har muka kusa isa gida yana waya, koda kuma ya kammala bai kulani ba har muka ƙarasa gidan, a ƙofar gida yace Sadiq yay parking. Batare da ya kalleni ba yace, “Kije ciki”. Kallonsa nai zanyi magana ya sake ɗaure fuska. Haɗiye maganar nai kawai na ɗauki ledar da Dad ya bani zan fita ya riƙe ledan. Sake kallonsa nai, sai kuma na sakar masa ledar batare da nace komaiba na ƙarasa ficewa dan tsagwaron masifa na hango cikin ƙwayoyin idanunsa.
           Duk yanda naso riƙe hawayena a yanzu kasawa nayi, haka na shiga cikin gidan inayinsu duk da nasan Nabeelah tana a gidan kuwa. Kwance na isketa a babban falo tana barci, dan haka na wuce bedroom ɗina kawai na faɗa saman gado ina fashewa da wani kukan. Kusan mintuna biyar ina kukana kafin ƙarar shigowar saƙo ta sakani dakatawa, ɗaukar wayar nayi ina share hawayen dan zatona ko boss ne, zumbur na miƙe cike da firgicin ganin yawan kuɗin da Dad ya turo min. A fili nace, ‘Tashin hankali, kodai Dad bai lura baneba?’. Bani da mai bani amsa dan haka nai saurin yin dialing Number sa. Bugu biyu kuwa ya ɗaga, cikin rawar murya nace, “Dad a......” “Banason kice komai ɗiyata, kin cancanci fiyema da haka daga gareni kinji, ke dai ALLAH yay miki albarka”. “Nagode Dad, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi mai albarka”. Na faɗa cikin kuka. Ina jiyo sautin murmushinsa daga can, ya sake kwantar da murya yana lallashina cike da kulawa har sai da na

yi shiru sannan mukai sallama.
          Jikina duk babu ƙwari na tashi na shiga bayi nai wanka da alwala, na idar da salla ina ƙoƙarin tashi dan naje na tado Nabeelah sai gata tama shigo da sallama. “Ai bansan kin shigoba, Sadiq ne da kulolin abinci inji Yayanmu”. “Abinci kuma?”. Na faɗa ina ajiye sallayar. Tare muka fita, da mamaki nakebin manyan kulolin da kallo, dan abincine na kusan mutane goma sha biyar ma. “Sadiq wannan fa?”. “Oga ne yace na kawosu, amma inagafa baƙi za'ayi dan naji yana waya akan nanda awa biyu da wasu mintuna ma zasu iso”. Bilkisu dake kallonsa kawai tace, “Yana ina shi?”. “Da muka saukeki Barrack mukaje, bayan mun baro can kuma na saukesa a General hospital sannan naje na amso wannan abincin, yanzu can zan koma na ɗakkosa dan yace dubiya zaiyi”. 
          Sallama yay mana ya fita, ni da Nabeelah kuma muka kwashe kulolin muka kaisu kicin inata tunanin baƙi kuma daga ina zasuzo haka to?. Bani da mai bani amsa, dan haka na koma ɗaki danna gyara jikina, Nabeelah kuma tai alwala itama.

JAWAAD
      
         Wayar da bily ta samu Jay nayi a mota wayace daga Qaseem dake a General hospital a killace, ya buƙaci ganin Jay ɗin da gaggawa, duk da hakan ya bama Jay mamaki baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen amsawa, shiyyasa suka ajiye Bilkisu a gida ita. Barrack suka fara zuwa wajen baba ƙaura da shima tun a safiyar yau ya saka aka kirashi a waya akan yana buƙatar ganinsa. yaso suje tare da bily ne dama, to sai kuma kiran da Qaseem yay masa ya shafe hakan. Kusan mintuna talatin ya ɗauka anan sannan suka fito.
         Likitoci basu bari Jawaad ya shiga wajen Qaseem ba kai tsaye sai da matakan tsaro na kare kai, ko ina na jikinsa sai da ya kasance a rufe ruf sannan aka kaisa inda Qaseem ya ke. Wajene na musamman.......

          Babu wanda yasan mi suka tattauna har na tsahon mintuna hamsin da uku sannan Jay ya fito, baka isa fahintar yanayinsa ba, dan kamilar fuskarsa ta shanye komai, sai dai kumafa jijiyar kansa tai masifar miƙewa ruɗu-ruɗu, hakama idanunsa jazur suke. Sadiq da tun da ya dawo yana zaune yana jiransa ya miƙe da sauri ya buɗe masa mota ya shiga, yana zama wayarsa nayin ring, daba dan yasan kirane mai muhimmanci ba bazai ɗaga ba, yay ƙoƙarin saisaita muryarsa suka gaisa da gambiya Munaya. Bansan mi tace masa daga canba, ya ɗan dai murmusa yana gyara zamansa da ƙyau. “Ina sake roƙon alfarma dai Ummu, Please a bani ƴar damarnan nima koda sau ɗaya ne”. Idanu ya lumshe a hankali yana cigaba da saurarenta, ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kansa kamar yana a gabanta, saida yay mata godiya sannan ya sauke wayar daga kunnensa yana cika bakinsa da iska ya fesar.

             Muna zaune a falo ni da Nabeelah ya shigo, sannu Nabeelah ta shiga jera masa, bai amsa mataba, sai dai ya ɗaga mata hannu kawai ya wuce abinsa. Da kallo muka bisa da gani har ita, na lumshe idanu da kwanciya jikin kujera ina sauke numfashi. “Shi dai Yayanmu kamar mai jinnu haka yake, yanzu zaki gansa a mutum anjima kaɗan ya koma dodo”. Nabeelah ce da wannan maganar cikin shagwaɓa, Bance da ita komaiba na miƙe, ruwa na ɗauka da kofi nabi bayansa.
          Ban samesa a faloba, hakan ya sakani binsa bedroom. A gaban mirror na iskesa yana waya da cire boturan shirt ɗinsa, ido muka haɗa ta cikin mirror'n kasancewar a bayansa na tsaya daf. Ni na fara janyewa, dan nikam banason ganinsa a cikin yanayin nan tsoro nakeji, cigaba yay da yin wayarsa tamkarma bai ganni ba. duk da hakan ya sosamin rai sai na nutsu ina saurarensa, mamaki ya kamani sosai dan fahimtar wayar yana yinta ne akan Aunty Shahudah, cikin tsoro-tsoro nake kallonsa lokacin daya ajiye wayar. “Boss wai kana nufin kasan inda aunty Shahudah take dama kenan?”. Rigarsa da ya gama cirewa ya jefa saman sofa, ya fara ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa batare da ya kalli sashenma da nakeba balle nai tunanin samun amsa. Sai da ya gama zame komai daga shi sai boxer sannan ya raɓani ya wuce abinsa. A take jikina ya fara rawa, na shiga ambaton innalillahi..... Ina kafe ƙofar bayin da kallo kamar zai fitone ya bani amsar da nake buƙata. Bansan sanda na zube a bakin gadonba na dafe kai, ts

ahon mintuna ina a haka wayarsa kuma nata faman ring a gefena amma banko kalleta ba. A haka ya fito ya sameni, yanzun ma dai ban ishesa kalloba, ya shirya a gaggauce cikin ƙananun kaya farin wando da farar riga, sai ya ɗaura baƙar jacket a sama mara hannu. Koba'a faɗaba yayi ƙyau sosai, dan shi mutum ne da koyaya ya saka sutura sai kaga ta zauna masa a jiki tsaf tamjar danshi akai. Tsabar wulaƙanci a gabana ya sake ficewa a ɗakin bayan ya zauna ya saka takalma a ƙafarsa, bansan sanda na fashe da kuka ba nai baya a saman gadon.

                 Gudu sosai Jawaad ya saka Sadiq shararawa dan jirgin su Umm-Anum harya sauka bisa ƙasa, duk da gimbiya ta sanar masa Takawa ya aika motocin da zasu tarosu hakan bai hanashi jin ɗokin son zuwa ya tarbo mahaifiyarsa da kansa ba, shi kaɗai yasan a yanayin da wannan ranar tazo masa, tazo masa da abubuwa kashi-kashi masu yawa, ruɗani daban al'ajabi da matsanancin farincikin dawowar mahaifiyarsa duniyarsa cikin ƙasar haihuwarta.
       Suna isowa su Umm-Anum na fitowa a jirgi Anuwar riƙe da hannunta. Da gudu Anum ta ƙaraso gaban Jay da tun tana sakkowa ta hangosa, jikinsa ta faɗa ta rungumesa. Duk da damuwar da yake ciki da yanayinsa na rashin son shiga harkar yara bai gaza karɓar ƴar ƙanwar tasaba kamar yanda taso, ya shafa kanta yana ɗan murmushi kafin ya janyeta a jikinsa ya nufi Umm-Anum. Haɗata yay ita da Anuwar ɗin ya rungumesu gaba ɗa yana maijin a yau babu tamkarsa duk faɗin duniyar nan. Kasan cewar yasan umm-Anum na fama da matsalar kafa bai tsaya ɓata lokaciba suka nufi inda Sadiq ya faka motarsa kusa da motocin masarauta guda uku da sukazo tarbarsu. “Ummuna Abbu fa?”. “Sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho suma insha ALLAHU, nima dan bazan iya haƙurin kaiwa goben bane shiyyasa”. Murmushi ya saki mai sanyi yana taimaka mata ta shiga motarsa da Sadig ya buɗe. Anuwar da Anum kuma suka shiga motar masarauta ɗaya badan sun so hakanba.
           Sai da ya tabbatar komai yayi dai-dai sannan ya zagaya inda Sadiq ya buɗe masa kusa da Umm-Anum shima ya shiga, ya riƙo hannunta ya sumbata, “Amsiyatul sa'iidah. Marhaban biki Ummuna”. Fuskarta ɗauke da murmushi da hawaye tace, “N: Kaifa anta Jay-p na”. Idanu ya lumshe a hankali yana haɗiye nauyin da ƙirjinsa yay masa da sake damƙe hannunta cikin nashi kamar mai gudun a ƙwace masa ita yace, “Ana bikhairin Ummuna”. Ta shafa kansa tana murmushi da faɗin, “Alhamdulillahi ala kulli halin Noorul Ayn”. Ɗagowa yay idanu jazur ya kalleta da sake sumbar hannunta ya ɗaura kansa saman kafadanrta yana sake lumshe idanu. “Ummuna nayi kewarki”. “Nima haka Muhammad Jawaad”. Ta faɗa tana sumbatar goshinsa.

           Cikin nutsuwa motocin suka fice daga airport ɗin, ta Jay ce gaba shi da Umm-Anum, sai kuma wadda su Anuwar ke ciki shi da Anum, sai ɗaya da babu kowa a ciki, ta ƙarshe kuma dogaraine.
   

___________________

            Daga kukan da ya barni inayi sai barci ya kwasheni, cikin barci naji ana knocking ƙofar, na buɗe ido a hankali da tashi zaune dan nasan bazai wuci Nabeelah bace, bayi na fara shiga na wanko fuskata da hawaye suka bushe, sannan na fita. Nabeelah tai saurin riƙo hannuna tana faɗin, “Baƙinfa sun iso inaga, dan naji ƙarar buɗe gate”. Bata jira amsata ba taja hannuna muka fito babban falo. Kiciɓis mukai da Anum data fara shigowa. Ta daka wani uban tsalle ta ɗareni, tuni naji duk wani ɓacin ran da Boss ya barni da shi ya gudu, na rungumeta nima cike da tsantsar farin ciki.
         Anuwar ne na biyun shigowa, ya fara sauke idanunsa akan Nabeelah da ke tsaye tana kallon su bily da dariya, kafin ya maida ga su Bilkisun yana ɗan ɓata fuska. “Lallaima Aunty, ni baki ganniba sai wannan yarinyar”.  “Tuba nake Yah Anuwar ” na faɗa ina sakin Anum.
         
          A waje kam Jay ya taimakama Umm-Anum ta fito daga motar, ƙafafunta duk sunyi fushi saboda zaman jirgi, ga kuma dama ƙafarta na mata ciwo. Wani irin kallo take bin gidan da shi dan bazata taɓa mantawa da shi ba koda a magagin mutuwa take, gidan da yazama tushen komai na maida mijinta wane, gidan da yazama harsashin ginin ɗaukaka ga abin sonta, gidan da zata iya a

mbatonsa da komai a ɓangaren farin cikin rayuwar aurensu da akasinsa, gidan data haifi gudan jininta bayan shafe shekaru tana kuka da fatan samu. kallon Jay tayi hawaye cike da idanunta. A hankali ya kaɗa mata nasa kan yana ɗan murmushi. Ta sake damƙe hannunsa cikin nashi tana haɗiye abubuwa masu yawan gaske dake yunƙuro mata tun daga ƙasan zuciya har saman harshe. A hankali ya fara takawa da ita suka nufi ƙofar da zata sadasu da cikin gidan, suna gab da isa ƙofar falon Bilkisu ta fito cikin matsanancin hanzari.
         Nai saurin ƙarasawa garesu batare dana tuna da wani matsayinta na surukata ba, ni kallon uwa nake mata, uwa ɗinma mai muhimmancin gaske ga ɗa. sakin Jawaad Umm-Anum tai itama da sauri ta buɗema bily hannayenta, aiko tazo ta shige jikinta. A take hawayen da Umm-Anum ke maƙalewa suka gangaro mata saman kumatu. Kauda kai Jay yayi daga kallonsu saboda ƙwallan da suka cika masa idanu, sai ya tura duka hannayensa cikin aljihun farin wandonsa ya ɗaga kansa sama ya maida hawayen. Sai da ya tabbatar hawayen sun koma sannan ya sauke fuskarsa a kansu. Yanzu kam Bilkisu ta ɗago daga jikin Umm-Anum, sai dai su duka hawaye suke tana jeramata sannu da zuwa. Umm-Anum ta shafa fuskar bilyn tana ƙare mata kallo sosai, wani sassanyan murmushi ta sake saki da jawota jikinta ta sake rungumeta, dan ita kaɗai tasan mita gano.
           “Ummuna kumuje ciki, sai ku cigaba da murnan”. Jay ya faɗa a hankali kamar bashine yay maganarba. Kallonsa tai shima ta riƙo hannunsa suka sakata tsakkiya shi da Bilkisu, a haka suka shiga falon inda Nabeelah da Anum ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login