Showing 63001 words to 66000 words out of 261165 words
Chapter 22 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
tsereminba, harke wacece da kika isa ruguzani? Nazo miki da lallami ranar amma kikaƙi saurarata, hhhhhh ke baki isa zama matar aureba yarinya saina karɓi abinda yake nawa, gashi kina a cikin yanayin danafi buƙata ma kina haila, kina bani shikenan, dan samunsa bada igiyar aure a kankiba shine yafi komai muhimmanci, bakuma zan sake bibiyarkiba dana samu cikar burina, hhhh bilkisu kece kammaluwar nasarata, kece ƙarashen nasarorina, da dukkan wahalhaluna na tsawon shekaru zan cika nasarata! Hhhh taya kike tunanin zan bari ki kufcemin, ɗaura miki igiyoyin aure tamkar ni aka ɗaure da igiyoyinne, taya zan bari hakan ta kasance ban amshi abinda yake cikamakin nasarorina ba?, abinda naketa bibiya tsahon shekaru kenan, karki yaudari kanki da tunanin ranar kin tsira yauma zaki tsiran, namiki shiri sosai a yau bilkisu, na shiryama wannan ranar, dan tana cikin damammakin da idan na rasasu babbar asarace a gareni, bana asara yarinya sai dai nasara! hhhhhhh!........”
Duk wannan maganganun da yakemin a cikin kunne na zama tamkar wata gawace a kwance, gangar jikina ne kawai a duniya amma numfashina da tunanina basa tare da duniyar, ba'a maganar zubar hawaye ma dan waɗanan dama ke sakasu fitowa, wata irin hasala zuciyata keyi da kumburar ɓacinrai irin wanda ban taɓa tunanin inada shiba, haka kawai yau nakejin zuciyata ta bushe dukda inajin tsoron ya samu nasarar da yake fatan kuwa, sai dai ban fasa gayama UBANGIJINA ba, addu'a nake kawai ina ƙiyasta tunanin shaidar dazan iya barma koma wanene wannan shaiɗanin, bazanyi sake irin na wancan darenba a yau insha ALLAHU, koda ace zaici galaba a kaina nima saina ribantu dashi da izinin UBANGIJINA.
Lokacin da naji ya sassauta min riƙon da yaymin yana shirin hawa kaina saina samu damar bada dukkan ƙarfina da yazomin daga mahaliccina wajen ƙoƙarin son tureshi, sam hakan bamai sauƙine a gareni, dan da alama ba ƙaramin mutum bane, danni sam kusani bana kawoshi a jerin aljanu, inada tabbacin mutum ne tamkar ni da rigar shaiɗanu. Wata sassanyar dariya maicin rai da nuna tsantsar mugunta da bushewar zuciya ya saki, tare da komawa gefena ya kwanta da faɗin, “Bara na baki damarki, kafin nai yaga-yaga dake yanda bazaki taɓa ganuwaba a safiyar gobe, na kula tausayin banza nake miki, tsaurin idonki yayi matuƙar yawa yarinyarnan”. Ya ƙare maganar da cire abinda ya ɗauremin bakina. Kukan zuci nake da babu hawaye ina kai masa du
ka ta ko ina da masa gargaɗi cikin zafin rai, “Karka cutar dani dan ALLAH, minai maka kake ƙoƙarin ɓatamin rayuwa?, kaji tausayin maraicina dan ALLAH, kobaka tsoron mahaliccinka ne? ina buƙatar zuwa da martabata gidan mijina tamkar kowacce mace mai mutunci, idan ka ketamin haddi wlhy ALLAH bazai barkaba, zan ƙare rayuwata ne wajen jifanka da munanan addu'oin da koka samu cikar burin naka saiya zame maka musiba, mugu azzalumi, ALLAH ya gagauta tona asirinka dama kosu waye kuke aikatama ƴaƴan mutane ɓarna, ALLAH ya ruguzaku sheɗanu, insha ALLAHU wutar jahannamace makomarku inhar baku tuba kun koma ga ALLAH ba tare da neman yafiyar bayin da kuke cutarwa, la'anannu masu ado da rigar musulunci suna cin dunduniyar bayin ALLAH, insha ALLAH bazaka cika burin nan nakaba koda kuwa kasamu nasara a kaina.........
Shiiiiii!!!! Ya faɗa yana dannemin baki tare da birkiceni ƙasa ya fallamin wani gigitaccen marin da komaina yay tsaye cak na wucin gadi kafin na ƙwalla ƙara, yasa hannu ya dannemin baki tare da kaina da azabar ƙarfi, kiciniya na fara dan harda hancina ya haɗa gaba ɗaya, tako ina yakushinsa nake dukda babu farce a hannuna sosai, hannunane ya sauka akan wuyansa, jin wani abu a ɗaure kamar sarƙan bit na samu damar fincikarsa da masifar ƙarfi saboda fita a hayyacina da nayi lokacin da numfashina ke gab da barin jikina................✍
Ƴan WhatsApp kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya. Saura kuma yau naji wani yacema Yah Qaseem ko Dad kwarto🙄🚴🏼🚴🏼😍😍😍😘😘😘😍😍.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[12/4/2020, 6:12 PM] HASNA✍🏻: Billyn Abdul:
Page 22
...............“Bazai yuwuba, Ka gaggauta fita!! Ka gaggauta fita!!!” na jiyo wata murya mai amo sama-sama tana amsa kuwwa a cikin ɗakin lokacin da numfashin ke gab da barin gangar jikina. Daga haka ban sake fahimtar komaiba dake a cikin duniya sai wayar gari nai na ganni kwance a ɗakin Momy.
A hankali na shiga buɗe idanuna da sukaimin nauyi, na shiga bin ɗakin da kallo daki-daki, dan bamma fahimci inda nakeba da farko saboda zan iya irga shigowata ɗakin Momy a tsawon zama gidan, da ƙyar na tashi zaune ina sake mamakin abinda ya kawo ni nan ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Momy ɗakin.
“Yauwa kin tashi Bilkisu?”. Kaina na ɗaga mata a hankali, saboda jikina yaymin wani masifar nauyo, na buɗe baki da ƙyar nace, “Momy miya faru na ganni anan?”. Hankalinta nakan ciro abu a cikin drawer ta bani amsa, “Za'a gaya miki daga baya, tashi kije ɗakinki kiyi wanka”. Da “to” kawai na amsa mata na sauka jikina duk yana wani masifar ciwo, ga tunani fal raina, wani abin mamakinma na sake tararwa a folon ƙasa, dan kuwa cike yake da dangin Momy, na gaisar da waɗanda zasu iya jina na wuce ɗaki kaina na kuma ɗaurewa. Akan gadona dake mugun yamutse na fara sauke ido, ‘Kowaye yay masa haka kuma?’ na ayyana a cikin raina, dukda banajin daɗin jikin sai nai tunani bara na fara share ɗakin, gadon na shiga kakkaɓewa, ƙarar faɗuwar abu naji kamar ƙwandala a ƙasa lokacin dana ɗaga zanin gadon, dube-dube na fara, sai dai banga komaiba, sharewa nai kawai na gyarashi tsaf, nakoma shara. A wajen shararne na sharo abinda ya faɗi ɗazun ashe wajen gado ya shige, Wuri ne kalar ja, sai dai wannan yafi wurin dana sani girma, haka kawai na samu kaina daƙin maidashi a sharar, saima na jefashi cikin jikkar islamiyya ta dake kusa dani, na cigaba da sharata. Da ƙyar na kammala aikin na lallaɓa bayi nai wanka, ganin baƙona ya tafi saina haɗa da wankan tsarki. Ina shiri ina mamakin barcin danai daga daren jiya zuwa safiyar yau ace bamma farkaba kamar yanda na saba a lokacin sallar asubahi dukda bana salla, yanzu hakafa sha biyu ma, ni saima yanzu maganar zuwa aiki tazomin a rai, gaba ɗaya wani iri nakejin kaina tamkar birkitacciya, wayata na shiga dubawa, sai dai kuma ban gantaba, ƙarasa shirin nai da tunanin naje ɗakin Momy na duba ko tana can idan na gama. Sallamar Momyn ce ta kacemin tunani na juya ina kallonta. taci kwalliya cikin rantsatstsen lase ɗan ubansu sai walƙiya yake, ga gwalagwalai ta zuba a wuya da hannu, taimin murmushi irin wanda tsahon zamana da ita ban taɓa cin karo da shiba sai yau, “Bilkisu irin wannan kallo haka” kunya naɗanji, dan haka na murmusa ina mai duƙar da kaina, nace, “Kinyi ƙyaune Momy”. “To nagode sosai” tafaɗa tana zama a bakin gadona da ajiye ledan data shigo dashi a hannu. takai dubanta gareni, “Kinga cire waɗannan kayan waɗanan zaki saka, nasan akwai tambayoyi fal ranki, karki damu zamu baki dukkan amsoshinsu zuwa dare idan baƙi sun tafi, fatanmu dai kizama maiyin biyayya a garemu kamar yanda kika saba, batun zuwa aiki kuma yau bazaki jeba”. Shiru nai kawai ina kallonta, sai kuma nace mata, “To momy, wayata fa?”. Miƙamin tayi tana faɗin “kin ganta nan, dama anata kirankima kuwa tun ɗazun”. Amsa nayi, itakuma ta miƙe ta fita. Da kallo na bita kaina na sake ɗaurewa da abubuwan da ban saba ganinsuba sai a mafarki, ganin ta ɓacema ganina saina sauke nannauyar ajiyar zuciya, wayar na duba, miss calls kam da yawa harma bansan dawa zan faraba, Yah Qaseem, Ummie, Amina, harma da Numbers ɗin da bansan na wanene ba, kafin nayi wani yunƙuri kira ya shigo, sunan Masarauta danai saving ne ya fito ɓaro-ɓaro a jiki, ɗagawa nai muka gaisa a mutunce kamar ranar, daga ƙarshe take sanarmin bayan an sakko massalaci zasuzo kawomin cards ɗina, murmushi nayi ina mata godiya, kafin mu yanke wayar. tunanin yaya zanyi na shigayi, dan yakamata ace koba komai nai musu tarba ta girmamawa ko badan gidan da suka fitoba, to amma yanda gidannan ke cike ta ina zanma fara nikam? Wlhy gaba ɗaya yau kaina ya ɗauki zafi, sam tunanina baya tafiya dai-dai dana sauran mutane. Kasa yin komai daya dace nayi, nai zaune a inda Momy ta barni, niba
n canja kayan datace ba, bankuma miƙe na nemawa baƙin abinda zasuciba idan sunzo balle kuma cikina dake Masifaffen ƙugin yunwa kamar zanci babu. Ina a wajen har ƙarfe ɗaya ta buga, tashi nai jiki a sanyaye na ɗauro alwala, gabana sai wata iriyar muguwar faɗuwa yake wadda ban taɓa jiba, idan girata ta haggu ta harba sai ta dama ma ta harba, sai kuma inji wata faɗuwar gaba ta biyo bayansu. Haka nai sallar azuhur batare dana fahimci abinda nama karanta a sallarba, dan wasu irin mugayen halittu na rinƙa gani suna zuwa gabana, haka dai na dake raina na cigaba da sallar inata faman kwarar da zufa tamkar wadda take a cikin ruwan zafi, a sujidar ƙarshema sai naji wata iriyar muguwar dariya a ɗakin tamkar za'a fasashi, sai kuma aka fashe da kuka, zuwa can aka kuma saka dariyar datafi ta farko. Na kasa ɗagowa daga sujidar ma gaba ɗaya tsahon lokaci, saida naji an taɓani ne a baya da magana kamar muryar Ummie sannan ALLAH ya bani ikon ɗagowa. Shiru naji ɗakin ya ɗauka sannan bana ganin komai a gabana harna kammala na shafa addu'a. Na sauke idanuna akan Ummie dake zaune da a bakin gadona tana latsa waya, sai dai na kasa cemata komai saboda wani irin yanayi da nakejin kaina mai masifar tashin hankali, jina nake tamkar ana kunnamin garwashin wuta a jiki........
“Bily! Bilyy!!” na tsinkayi muryar Ummie na faɗa tana girgizani. Kallonta nai na amsa da ƙyar, dan bansanma tazo kainaba, bana gane komai a yanzu bana kuma fahimtar komai hatta da kaina neman suɓucemin ya keyi. Tace, “Na shiga uku, Bilkisu lafiya kike kuwa? Wai mike faruwane haka?”. “Ban saniba nima Ummie” nai maganar hawaye na ziraromin akan kumatu. Kafin ta samu damar jehomin wata tambayar muka jiyo matsananciyar hayaniya ta kaure illahirin gidan tamkar ana faɗa. Mu duka kallon ƙofa mukai, hakan yay dai-dai da bugo ƙofar da aunty Shahudah tai hannunta ɗauke da wuƙa tana kuka.
A tare muka miƙe da Ummie, dan lokaci ɗaya wani ƙarfi yazomin da bansan daga inaba kuma, ganin kaina tayo da wuƙar saina zaro idanu waje ina faɗin, “Au...aunt...aunty Shahudah lafiya? kuw....” bankai ga ƙarasawaba ta kawomin suka tana faɗin, “Wlhy kasheki zanyi, tsinanniya jinin asara jinin masifa, jinin tsafi....” wani mugun tsalle nai na kauce mata, amma dukda haka saida taɗan yankeni a damtsen hannuna. Ɗakin ya cika sai ƙoƙarin janyeta ake tana ihu da tabbacin yaufa ita saita halakani.
Bansan hawaba bansan saukaba kawai naji aunty Aamilah da wasu ƴammata sun rufeni da duka sukuma, tun ina ƙoƙarin kare kaina harna gaza dan sunfini yawa, gashi kuma bayan Ummie babu mai yunƙurin karɓata.
Tun Bilkisu na fahimtar abinda ke faruwa harta sume, amma idanunsu ya rufe bama su fahimci bata numfashiba, haka suka jawota ƙiyyy!! waje har tsakar gida suna duka, abinda zai baka mamaki babu wanda ya hanasu acikin manyan iyaye irinsu Momy, suma kansu ruɗanin abinda yazo musu babu zato baisa sun kula da abin ƴaƴansu sukeba na yunƙurin kisan kai, Ummie ce kawai ke kuka da Amina da mama da suka shigo gidan saboda jin matsananciyar hayaniyar dake tashi.
Shahudah kuwa tun tana kuka da iƙirarin kashe Bilkisu har itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa babu numfashi, nanfa gidan ya kuma harmutsewa, babu mai iya fahimtar yaren wani balle ka samu tabbacin abinda ke faruwa dahar ya kawo wannan tashin hankalin.
____________________________
Abinda ya faru shine, a daren jiya su Mom sun dawo misalin ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna sai sukaci karo da wani irin ihu maiban tashin hankali da saka firgici a gidan, babu wanda bai tsoraba a cikinsu dan Aamilah harda fitsari ta jiƙe jikinta, sai bayan wasu mintuna komai ya lafa sannan suka fahimci daga ɗakin Bily wannan ƙara ta fito, sai dai a cikinsu babu wanda ya iya jarumtar shiga ɗakin. Mom ce ta ɗaga waya ta kira Dad hankalinta a tashe ta sanar masa komai, shima hankalin nasa a tashe ya tabbatar mata gashinan zuwa gidan dama ya fita rakkiyar su Alhaji baba ne da sukazo.
Duk wannan ihu yau Yah Qaseem bai jisaba sam, yana ɗakinsa yana barci, saida Shahudah taje ta tasoshi bisa umarnin Momy. Kafin isowar Dad Yah Qase
em ne ya fara shiga ɗakin, sai ya tadda bily a sume, ga ɗaki a hargitse tamkar anyi sukuwar salla a cikinsa. Babu wanda abun bai taɓa zuciyarsaba a gidan har Dad daya iso yanzun, sun shiga yayyafama Bilkisu ruwa amma ko motsi bataiba. sunkuma bi duk wasu dabaru shima bata farfaɗoba, hakan yasa Dad bada shawarar a maidata ɗakin Mom ta kwana a can, shikuma zuwa safiya zai ɗauki mataki akan wannan abun dake faruwa.
Daga Aamilah har Shahudah suma a ɗakin Mom suka kwana, da ita kanta Mom ɗin harma da Dad kansa saboda a firgice suke yaran da Mom. Har ALLAH ya wayi gari lafiya Bily kam bata dawo hayyacintaba sai kusan ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna ko nace sha biyu saura na rana.
Abinda ya farunne ya saka Dad yanke shawarar ɗaura auren Bily da Qaseem a wannan safiya ta juma'a dan kowa ya huta duk da basusan ainahin abindama ake bibiyar Bilkisu da shiba, ɗari bisa ɗari Mom ta bashi goyon baya. Ana idar da sallar asuba Dad ya nufi gidan Alhaji baba ya sanar masa halin da ake ciki tare da neman alfarmar haɗawa dana Shahudah da Jawaad, zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu a cewar Dad sai ayi biki su tare. Alhaji baba bai musaba, dan yana fatan jikan nasa matsalarsa ta zama babu aure tazo ƙarshe. Daga gidan Alhaji baba gidansu Jawaad Dad ya wuce, a canma sun tattauna dasu Uncle Nasir kafin ai kiran Jawaad dake shirin tafiya Office.
Koda suka sanar masa shirinsu shima babu musu ya amsa musu, harma amincewar tasa da gaggawa ya basu ɗunbin mamaki, amma shi saiya fuske abinsa tamkar baiga mamakin nasuba sam ko bai fahimtaba, ya kuma fiddo kuɗin sadaki a take ya direma Uncle Nasir har dubu ɗari biyar. Kasa haƙuri kam sukai saida suka tanka akan hakan, batare daya kallesuba yace ai Alhaji baba ne ya kirasa ya sanar masa kafin su sukirashi, cikin gamsuwa da maganarsa Dad yace to ya rage kuɗin sunyi yawa, dubu ɗari sun isa. Murmushi Jay yayi yana wani susar ƙeya, kansa a ƙasa yace, “Karka damu Dad nariga na fidda kuɗin matsayin sadakin, Uncle kuje dasu wajen ɗaurin auren kawai please. Albarka suka saka masa tare da sallamarsa, yay musu sallama ya tafi fuskarsa ɗauke da wani shegen murmushi daya tsayama Uncle Nasir da Dad a ƙahon zukata. Dad ya dawo gida, yayinda Jay yanufi office ya nema alfarma tare da gayama Sir Ahmad abinda ake ciki. Sannan ya sanarma su Hafiz ma, sunyi matuƙar mamaki, amma ganinsa a wani yanayin da suka kasa yima fassara sai basuja zancen da nisaba suka shiga faɗama mutanensu nanan office da waɗanda suke kusa irinsu Abbati ta waya.
Maza nata haramar tafiya massallaci, inda daga canne za'a ɗauro auren bayan idar da sallar juma'a, yayinda ahalin gidansu Momy keta tururuwar zuwa gidan harma da tsiraru na ɓangarensu Dad kamar su inna Zainabu. Duk wannan abunda ke faruwa babu sanin bily, tanacan tanata barci abinta.
Massallaci ya cika tab da al'ummar musulmi yara da manya da matasa da tsoffi harma da mata dakanje sallar juma'a kasancewar wannan ranar ranace ta musamman a garemu, bayan an idar da sallar juma'a kamar yanda aka saba akai sanarwar ɗaure-ɗauren aure daza'ayi daban-daban wanda harda nasu Qaseem a ciki. Duk wanda yaga Qaseem a yau zai tabbatar yana cikin farin ciki, dan kuwa yaci ado da wata ɗanyar shadda fara ƙal da Dad ya bashi ya sanya, sai walƙiya da walwalin angwanci yakeyi kamar ka sacesa ka gudu, ga haƙoransa farare tas sun kasa rufuwa. Sai dai nayi iya dubana da waige-waige bangano ko mai kama da Jawaad ba balle shiɗin kansa, saisu Aliyu da suma duk suke sanye da shaddoji a yau, da alama dai gida suka koma bayan zancen ya riskesu suka canja shiri.
An fara ɗaura aure guda biyu da baida alaƙa dasu Dady, kafin a ɗaura wani da yaso bama kowa mamaki, wato dai Sabira da wani waishi Habib, ankuma roƙi Uncle Nasir dake kusa ya zama wakilinsu saboda wai wakilan amarya masu isoba har lokacin, wannan shine ya gogema mutane da yawa abinda ya taɓa musu zukata, ɗaurin aure na huɗu daya biyo baya shima bashi da alaƙa dasu Qaseem ɗin, saida akai kusan na mutum uku kafin a ɗaura na Qaseem da Azeema, jikin Qaseem har rawa yake ya miƙe zaiyi magana amma sai Uncle Uwaisu ya maida
shi ya zaunar yana mai sanar masa bafashi ake nufiba maybe wasune daban, ajiyar zuciya Qaseem ya sauke dukda dai hankalinsa bai kwantaba, gashi iya dubansa baimaga Dad a wajenba, bayan kuma tare dashi sukazo masallaci, ɗaurin aure na ƙarshe baki ɗaya shine ya tada hankalin dukkan mai alaƙa dashi, wato Jawaad Abdul-aziz da amaryarsa Bilkisu Adam, Alhaji Baba wakilin amarya Uncle Nasir da yay zaton da Shahudah ya kasance wakilin Ango, saida aka ambatanefa yaji wasan ya canja salo. Qaseem yama manta a ina suke, take yanke yaci kwalar imam da masa tambayar yaya haka ta faru?. Da ƙyar ƴan agaji suka ɓanɓare imam a hannun Yah Qaseem, cikin tsagwaron tashin hankali Dad da Qaseem ya gaza gani ɗazun a masallacin ya shiga jeroma imam tambayoyi shima. imam da duk bai