Showing 147001 words to 150000 words out of 261165 words

Chapter 50 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1155

bai shiga da ita gida ba ya shiga ya bar anguwar, kai tsaye address ɗin da dattijon nan ya bashi ya nufa, anguwace irin sabuwar anguwarnan da uncompleted building sukama fi yawa, sai dai inda gidan drama'n yake anɗan gaggama wasu gidajen dan wajen harya fidda santa ɗoɗar, bakajin hayaniyar komai saina Genretor ɗin da suka kunna da ƴar hayaniyarsu alamar basu gama zuwa ba, akwai ƙwayayen wuta a waje da suka haska kusan rabin layin, sai mai Nama daketa faman haɗa wuta, gefensa mutum biyune ɗaya mai ruwa ɗa kayan drinks, sai saurayi da budurwa dake can gefe suna hira, sai kuma masu shiga da fita cikin gidan ɗai-ɗai dan yanzu suke kan zuwa. Waya ya ɗauka yay kiran wani abokinsa da ya kasance ainahin police, saida suka gaisa ya gama tsokanarsa da ango-ango, sannan Jay yace, “Auwal kuna garin nan amma tsageru har suke da lasisin buɗe wuraren iskanci irin haka?”. Daga can Auwal yace, “Haba dai Jay, kaima kasan hakan bazai kasanceba”. “Gashi kuwa na gani da idona, akwai wani gidan Drama a sabuwar anguwar nan data kusa haɗewa da jan-ɓauna, inason ƙarfe goma da rabi kuzo wajen kuyi kamen kan mai uwa da wabi”. Bai jira cewar Auwal ba yace, “Mu kwana lafiya” ya yanke wayar. facemask ya ɗauka ya saka tare da facing cap,  kallon kasan yayi a madubi ya tabbatar komai yayi kafin ya fito bayan ya kashe motar. Sai da ya tabbatar babu wanda yaga fitowarsa sannan ya nufi gidan.

★★★★★★

         Ina idar da salla na koma bakin gado nai zaman jiransa, ganin shiru-shiru sai kawai nahau yin game a waya, hamma na farayi ɗai-ɗai alamun inajin barci, nayi guntun tsaki da kallon agogon ɗakin, tara saura minti ashirin, zamewa nai na kwanta tare da jan filo na ɗaura kaina na cigaba da game ɗin, tun ina ƙoƙarin damƙe wayar dake neman suɓuce min harna yaddata batare dana saniba.
              A firgice na farka jikina na wani irin ƙyarma, ‘innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ na shiga ambata ganin ɗakin dunɗum da duhu bayan kuma nasan fitilar a kunne take, dariyar da aka tuntsure da ita ta sakani sake firgicewa nahau laluben gadon.....
        “Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya tsere minne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.................✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gama
[1/4, 2:46 PM] HASNA✍🏻: Page 42

..................Inda mai naman nan yake ya tsaya, batare da yayi magana ba ya miƙama mai-naman 1k tare da nuna masa naman. Kallonsa yay a ƙufule, “Haba malam, ya zakazo waje babu ko sallama ka miƙomin dubu wai na baka nama? An faɗa maka ni irin sakarkarun masu saida naman nan ne da kuke rainama hankali, nibanma taɓa ganinka a gidannan ba, kai wane?”. Jay ya danne takaicinsa cikin salon maganar kurame yay masa nuni wai shi bebe ne”. Mai nama yace, “Oh to yanzu naji batu, kasan rainin tsagerun gidannan ne bazan iya ɗaukaba shiyyasa kaima nai zaton kalarsu ne, na duka kake so?”. Kai Jay ya jinjina masa. Mai nama ya fara yankowa yana sawa a takarda da raira ƴar waƙarsa ta shata mai taken “Natsaya ga annabi Muhammadu.......” Jay dai kallonsa yake da nazarin wajen harya kammala yanka masa, amsa yay da masa godiya ya juya zai tafi, sai kuma ya juyo da sauri irin kamar yayi mantuwar nan. Ƴar takarda ya ciro a aljihun wandonsa ya miƙama mai nama. Mai nama ya amsa da faɗin, “Miye kuma wannan? Nifa kunsan ba wani boko nayiba amma kuyitamin wani lagude-laguden jaraba. Kai Hamusu zo duba mi ya keso kuma?”. Wanda aka kira Hamisu dake gaban lemuka ya amsa da “To baba”. Takardar ya amsa ya duba sannan ya kalli mai naman, “Baba wai gidan Ɗan Alhaji ya keson a nuna masa”. Shiru mai naman yay yana kallon Jawaad, mikuma ya tuna oho masa sai ya washe baki, “Af to inaga irin abokansa ne daya ɗan gayyato, kasan yau zaiyi ajo”. Jinjina da hannu Jay yayma Mai nama irin ka gane ɗinan. Mai-nama ya sake washe baki da nunama Jawaad wani gida dake can kusan ƙarshen layin. Cikin alamar maganar kurame yayma Jay yay masa godiya da nufar inda aka nuna masan.
          Rufe gidan yake dan haka ya ƙwanƙwasa, sai da yay sau kusan baƙwai sannan akazo aka ɓuɗe cike da masifa.
      “Wai wane shegene yake bugama mutane gida haka? Sai kace ya bada ajiya ko an ci masa bashi, idan akai haƙuri dai ai zan fito ba sai ansama lokacina ido b.....” hankaɗa shin da Jawaad yay ya koma baya ya hanashi ƙarasa maganar, zai sake magana Jay ya ɗaura hannunsa saman baki yace, “Shiiiiii”. yana ɗaga rigarsa bindiga ta bayyana, jiki na rawa ɓaleru ya saka hannu ya toshe bakinsa yana faman zare idanu. Ƙofar Jay ya maida ya kulle bayan yay wurgi da ledar naman daya shigo da ita, ya sake kaima ɓaleru wani bahagon bugu tare da damƙo wuyan rigarsa ya miƙar dashi tsaye. Batare da yay magana ba ya nuna masa hanyar cikin gidan. Jikin ɓaleru na rawa ya shiga kaɗa kai tamkar wani ƙadangare.
    Gidane madaidai ci yasha tiles har a jikin bango, ga hasken wutar Genretor da alamu suka nuna na gidan drama ɗinne aka jawo masa har nan, ƙofar dake buɗe suka shiga, budurwar dake kwance saman katifa tsirara ta miƙe da sauri zaune tana jan bedsheet ɗin saman katifar ta ƙudundune kanta ciki zata zabga ihu.......
          “Idan baki rufemin shegen bakin kiba saina ragargaza ƙasusuwanki wlhy!!”. Jay yay magana cikin kaushin muryar da ta saka budurwar cusama bakinta bedsheet ɗin tana zare idanu hawaye na ƙwarara, jikinta sai rawa yake.
     Jawaad ya maida kallonsa ga ɓaleru da duk hankalinsa ke kan wayoyinsu dake zube a ɗan table na glass ƙarami dake gefe. Ƙafa Jawaad yasa ya taɗesa ya faɗi ƙasa tim, cikin zafin nama ya shiga sauke masa maruka a fuska da hannu bibbiyu. A take ji da ganin ɓaleru suka gushe, gashi babu damar yin ihu yana tsoron bindiga. Sai da Jay ya jigatashi da maruka ya tabbatar ya fita hayyacinsa sannan ya barshi. Budurwar daketa gunjun kuka da faman ɓoye fuska ya kalla, “K zoki kashemin duk wayoyin nan....”. Kafinma yakai ƙarshe harta miƙe zaram tana damƙe bedsheet ɗin da ƙyau jikinta na rawa, wayoyin uku manya ta kashe sai ƙarama ɗaya. Yace, “Ina taki?”. Nuna masa ɗaya daga cikin manyan tayi, ukun kuma tace, “N..na nashi ne sauran”. Ɗauke kai Jay yay batare da ya sake cemata uffan ba, ya ɗauki Coc dake ajiye yanata raɓar sanyi ya ɓalle murfin, saman fuskar ɓaleru daya suma ya juyeshi, a take ɓaleru ya kawo numfashi. Wani marin Jay ya sake sauke masa a fuska. Take ya dawo hayyacinsa ya fashe da kuka  yana share jinin da yake fita daga hancinsa yana sauka masa kan baki, “Dan ALLAH malam minai maka kake min irin wannan dukan? Idan kuɗi kakeso ko nawane zan baka, nidai  karka kasheni dan girman ALLAH, kag.....” sake wanka masa wani marin Jawaad ya ƙarayi tare da ɗora ƙafarsa ɗaya kan katifar ya ranƙwafo kansa da nuna masa fuskar wayarsa. “Wanene wannan?”. Ɓaleru da jikinsa ke rawa ga jini nata fita masa ta hanci da gefen baki yace, “Ni...ni ban sanshi ba wlhy”.  “Baka sanshi ba! Kace baka sanshi ba?!!”. “Eh wlhy oga bamma taɓa ganinsa ba”. “Yayi ƙyau” Jay ya faɗa yana miƙewa da tattare hannun rigarsa sosai yay sama. Har Ɓaleru ya fara murna an barsa sai kawai ji yay Jay ya cakumo masa wuya ya miƙar dashi tsaye da ƙyau. Mahaukacin duka ya shiga masa da babu algus, yanda yake bugun nasa zai tabbatar maka zuciyar ƴan mazan a wuya take. Sam baya sauraren roƙon da ɓaleru ke masa da kukan karuwarsa. Saida yay masa lilis sannan ya hankaɗashi ya faɗa saman katifar kansa ya daki bango Ƙummm!!!!. Dafe kan Ɓaleru yay da sakin wata wahalalliyar ƙara, saiga jini sharrrr. Jay ya sake cakumo wuyansa ya shaƙesa da ƙyau da hannu guda, ɗayan kuma ya sake nuna masa hoton Gimba dake tare dashi da suka ɗauka a gidan gonarsa wani zuwa da suka taɓayi tare. Yace, “Har yanzu dai baka sanshin ba?!”. “Dan ALLAH ka tausayamin oga  ka daina dukana karka halakani na sanshi, Abokina ne sunanasa Gimba garinmu ɗaya”. Ɗauke fuskarsa Jay ya sakeyi da mari yana faɗin, “Ɗan iska  kake son maidanine da?”. “Na tuba dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake maka ƙarya ba”. Miƙewa Jay yay tsaye ya kaima Ɓaleru harbi a ƙafa da tofa masa yawu, sai faman huci yake, jiyake tamkar ya kashe banzan nan ko zaiji sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.

________________________

             Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya tsere min ne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.
         Hannu nasa na toshe kunnuwana domin nisanta jina daga shaiɗaniyar dariyarsa, na fashe da kuka ina jan jikina baya, “Kaji tsoron ALLAH bawan ALLAH, koda kai aljanine na tabbata kasan akwai hisabi tsakaninmu ƴan adam da ku, minai maka ne kakeson ganin bayana? Ka tunafa ni matar aurrece yanzun, dan ALLAH na roƙeka karka wulaƙantani, ka barni da mutuncina.............”
       “Kima daina ɓata yawun bakinki madam, babu wani roƙonki dazan taɓa saurara, keɗin kaddarace mai girma a gareni, makullin cikar dukkanin burkana. Kinsan illa nawa kikaimin ne?!!” yay ƙare maganar a tsawace da cafke wuyana ya shaƙe. A take jikina ya fara rawa na fara ƙoƙarin fisgo numfashi cikin kakari. Hankaɗani yay na bigi fuskar gadon. Azaba ta sakani fashewa da kuka na riƙe wuyana da duka hannu biyu. Wani irin matsanancin fushine ya tasomin jin dariyar da yake sake ɓaɓɓakawa yanzu ma, nace, “Ƙarya kake azzalumi, idan ka isa ka daina ɓoyemin kanka, matsoracin banza da wofi kawai, Bazan sake roƙoka ka barni ba koda hakan na nufin zakai nasara a kaina ɗin, sai dai na ɗauki alwashin in ALLAH ya yarda, inhar ƙazamin jikinka ya kasance shine ƙaddarata, nima nice zan zama ƙaddarar mutuwarka, dan da hannuna zan kasheka a ɗakin nan, a wannan daren la'ananne ALLAH fasiƙi kawai!!!”.
          “Hhhhhhh!!” ya shiga sake ɓaɓɓaka dariyarsa mara daɗin ji da tafa hannayensa. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sauti hakan yasa na kasa fahimtar taka maimai inda yake. “Da ƙyau Bilkisu, da ƙyau!, ashe kema kin fara koyon jarumtar mijin naki?, nine zaki kashe, ni ni ninan kikejin zaki iya ki kashe.....?!!!” naji an sake damƙar wuyana an shaƙe.
        A take jikina ya fara rawa, nasa hannu na daki cikinsa cikin gushewar hankali, dukda alamu sun nuna yaji zafi bai sakeni ba, sai ma dannani da yay baya ya maƙureni jikin fuskar gadon ya haye kaina. “Zanyi abinda ya kawonin, ada nayi niyyar barinki a raye tamkar sauran kicigaba da rayuwa kema, to amma tunda kince ke tsagerace saina shayar dake gidauniyar azabar mutuwa, k har wacece? Nawa kike? Da zaki zamewa rayuwata matsala.......”
    Yanda naima Jazuga ne ya shiga dawomin a rai, duk da shaƙar da yaymin cikin rahamar UBANGIJI na samu damar lalubar bed side drawer da naji a kusa da hannuna, kofin da boss yasha ruwa ban fiddaba yana a kai na jiyo, ALLAH ya bani sa'a fisgosa na ɗaga hannuna dake rawa da ƙyar na maka masa a gefen kunnensa. A take ya sakarmin wuya yana huci na shigar zafi..... Kafin ya dawo hayyacinsa na caka masa sauran kofin dake riƙe a hannun nawa, sai dai bansa a inane ba dan a kwai duhu a ɗakin har yanzun. ƙara ya saki yana sake kaimin wawura sai dai na zille harma na dire a gadon. Cafkoni yay cikin zafin nama ya maidoni baya kan gadon har saida nai ƙara dan azaba nima. Na gallama hannunsa cizo tare da halbinsa da ƙafa cikin salon trianing ɗin da muka samu duk da ba ganinsa nake ba. kokawa ce ta kaure a tsakanina da shi dukda yafi ƙarfina nesa ba kusaba. Amma kasancewar akwai taimakon UBANGIJI da kuma kowa yasan mata ALLAH kan bamu ƙarfi a irin wannan yanayin koda ace bazamu iya ƙwatar kanmuba kuwa. Kokawa muke bil haƙƙi da gaskiya dukda nice keshan wahala ban yarda ya kaini ƙasa ba. Cikin sa'a na kama ɗan yatsan hannunsa da yake neman sake kaiwa wuyana na murɗesa da azabar ƙarfi nai baya dashi. Jikake ƙaraƙassss ƙasss ƙasss ƙashin na bada sauti. Wahalalliyar ƙarar daya saki yay baya ta bani damar jan hannuna baya nima, sai na saɓulo da zoben dake jikin yatsan.
     A take Ɗakin ya ɗauki sautin wata murya mai ban tsoro da saka firgici, aka shiga faman faɗin, “Barmata shine kuskure mafi girma, ka karɓa maza ka fita karka tsaya akwai matsala!!”.
       Wani irin ɗagowa yay a zabure ya fisgoni muka tafi ƙasa tare ya murɗe hannuna da zoben ke a ciki zai ƙwace. Hakan yasa na shiga ambaton,
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
      (ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro).
اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
     (Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so).
اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
         (Ya ALLAH! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki).
        Ƙarar da aka ƙwallah ta sakashi Hankaɗani kaina ya daki gadon, ya fita da gudu, na fasa wani irin gigitaccen ihu jikina na ɗaukar wani irin rawa, a take komai yay min ɗifff.......
        Fasa ƙarar Bilkisu tai dai-dai da ƙarasowar Jay jikin ƙofar falon zai buɗe dan isowarsa gidan kenan bayan yakai Ɓaleru ya ajiye a wani ɓoyayyen waje. cikin zafin nama ya faɗa falon batare da ya rufe ƙofar ba. Ledar dake hannunsa ma sakinta yay a falon. A gigice ya danna makunnar fitilar ɗakin ta kawo haske. Ya daka wani uban tsalle sai gashi gaban Bilkisu data sume. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunanta jikinsa na rawa dan har yanzu yana tattare da fushin ɓaleru ne, yay saurin maidata ya kwantar jin kamar gudun mutum ta bayan Windown ɗakin. Fita yay da gudu yana ƙwalama maigadi kira cikin matsanancin hargagi akan ya rufe masa gate. sosai maigadi dahar ya shiga ɗakinsa zai kwanta ya fito a gigice shima jin wannan mafaraucin kira, baƙaramin tashin hankali ya shigaba ganin yanda Jawaad yake nufosa tamkar mahaukacin zakin dake a yunwace. Ɗaukesa Jay yay da mahaukacin mari, “Waye ya shigomin gida? Ka gayamin wa kabama damar ya shigomin gida!!?”.
        Maigadi daya gama ruɗewa da marin da yasha yace, “Wlhy oga babu wanda ya shigo gidannan tunda ka fita, narantse maka babu wanda ya shig........” bai gama saurarensaba ya bar wajen, ta bayan Windows ɗinsu ya nufa kasancewar akwai wuta ko ina da haske. Take masa baya mai gadi yay da sauri shima dan bai fahimci abinda ke faruwa ba. Jay yaja wani mahaukacin birki yana kallon tsanin dake tsaye jikin katanga alamar koma wanene tanan ya shigo, kuma tanan ya fita. Naushi ya kaima bango da azabar ƙarfi yana faɗin, “Noooo!!”. Da sauri maigadi dake cikin tsoro ya riƙe masa hannu, “Oga dan ALLAH karka jima kanka ciwo”. Fisge hannunsa yayi dayin wani Uban tsalle ya ɗane katangar cikin ƙwarewar training da suka samu batare da ya kalli inda tsanin ya keba. Dirarsa can baya kawai maigadin yaji. “Na shiga uku ni gambo, mike faruwa a gidan wai?” mai gadi ya faɗa hankali tashe.    
       Babu abinda Jay ya gani sai sayin takalmi kawai da wani tsanin a baya, wajen siririyar hanyace data fita ɗoɗar har babban titi, hanyar tana taimakawa ƴan anguwarne wajen fita titi basai sunbi ta titin layinba dake da nisa da babban titi, ya dafe kansa dake wani irin masifar sara masa. Halin daya bar bilkisu a cikine ya faɗo masa a rai. Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga haske-haske harya zagaya ta ƙofar gate yay knocking. Koda aka buɗe baiko kalli maigadi dake neman ƙarin bayani ba ya nufi cikin gidan.
      Yanda ya barta haka ya Koma ya sameta babu alamar numfashi tattare da ita. Tsugunnawa yay gabanta ya Rungumota da ƙarfi cikin ƙirjinsa jikinsa na wani irin tsuma na tsananin ɓacin rai, “Ubanwaye ya shigomin gida? Miyay miki?”. Yay maganar cikin raunin murya da ɗaci, jijiyoyin kansa na miƙewa ruɗu-ruɗu, zafafan hawayene ke kwarara a cikin zuciyarsa, a zahiri kam babu ko ɗigonsu sai idonsa daya kaɗa yay jazur. Ɗagata yay gaba ɗayanta ya ɗaura a kujerar dake ɗakin guda ɗaya ƴar doguwa, sai da ya gama bin ɗakin da kallo tsaf, ɗigon jini har a kan gadon ya gani, sai fasashen glass aƙasa zuwa gadon dake a yamutse alamar ansha dabbe a kansa. Kauda kansa yay yana rumtse ido da danne abinda ke yinƙuro masa tamkar zai faso ƙirjinsa ya fito mai alaƙa da Masifaffen kishi, sauran ruwan daya bari dake yashe a ƙasa ya ɗauka, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. A take ta kawo wani nannauyan numfashi tare da miƙewa zumbur cikin zafin nama tana faɗin, “Saina kasheka, bazan barkaba yau, kasheka zanyi wlhy......” Saurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login