Showing 123001 words to 126000 words out of 261165 words
Chapter 42 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
sai kuma ya shafa kansa, “Sorry Mami ai wlhy ni duk ɗaukata Ummu ce, bansan ita ƴan biyu baneba nasan dai tanada yaya mace”. “Karka damu ƙanina, Gida yay ƙyau masha ALLAH, ALLAH yasa rai akaimawa, ALLAH yasa a cika manashi taf da ƴaƴa ko jikoki zance”. Cikin murna su Safah suka shiga faɗin, “Amin”. Shidai a saman laɓɓa ya amsa nasa amin ɗin.
Kasa jurewa Mami Munubiya tai ta koma gefe tai kiran Munaya, tana ɗagawa tace, “Sweetheart kingako mina gani ga angon nan?”. Daga can murmushi gimbiya Munaya tai tana gyara kanta a kafaɗar takawa, tace, “Nasan ina kika dosa sweetheart, tun randa na fara ganinsa nima naga abinda kika gani, wannan ne dalilin tura matarsa can ta ɗan zauna, sai dai bamu da tabbas, amma muna fatan ALLAH yasa ta kasance hakanne”. “Kai to amin kuwa, al'amarin akwai ruɗarwa, amma gaskiya bana tantamar alaƙa a tsakaninsa da Umm-Anum Sweetheart, nifa da farko na zata Anuwar ne wlhy, sai da nai masa kallon nutsuwa na fahimci yafi Anuwar cikar zati, Anuwar kuma ya fisa haske, hatta da maganarsu kumafa babu banbanci, bara sai dai mun dawo ma tattauna”. Daga haka Mami Munubiya ta yanke wayar ta koma ciki dan baƙin da suke jira har sun iso.
Sai da suka gama zagaye gidan tsaf kafin su basu hotunan kayan ɗakin da zasu dace da tsarin gidan akan su zaɓa. Shi dai Jawaad bai saka musu bakiba, Mami dai ta tambayesa kalar da yafi so, ya sanar musu, daga haka ya cigaba da danne-dannen waya Safah na gefensa tana zuba masa surutu, shidai nasa saurarenta dayin murmushi, sai jefi-jefi yake bata amsar wani abun koyay mata tamba
ya.
Kusan awa guda suka kammala komai dangane da zaɓin kayan, a take Mami ta kira Ummu ta sanar mata kuɗin da suka cajesu. Kafin kuwa subar gidan har ƙuɗaɗensu sun shiga accaunt. daga haka suka bar gidan akan sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu zasu dawo suga yanda kamfanin suka shirya gidan. Jay yaymusu rakkiya har mota yanama Mami godiya, sai da suka wuce sannan shima ya shiga mota suka bar gidan.
Office Jay ya koma domin cigaba da tarin ayyukan dake gabansa, dama yana tsaka da aikinne Ummu ta kirasa akan yaje can gidan yanada baƙi, dole ya ajiye ya tashi ya tafi. Fatansa ya rage ayyukan sosai, gashi yanason ɗaukar hutu kona sati ɗayane, duk da dai Sir Ahmad yace bai isaba na sati biyu zai ɗauka shima yaje yasha angwanci da ƙyau.
Zamansa baifi da mintuna talatinba baƙon da yake jira ya iso, sai da akai masa iso sannan ya bada izinin a shigo dashi, ba kowa bane baƙon face Sulaiman yayan Amina, Jay ya ɗago daga abinda yake fuskarsa a sake dukda dai ba murmushi yake ba. hannu ya bashi suka gaisa kafin ya miƙe ya kawo masa abinsha baya. ya nuna masa wajen zama, yah Sule yay godiya. Ɗan murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sai da ya ɗan sha ruwa sannan Jay yace, “Yaya ake ciki Sulaiman? ka gano ina yake?”. Numfashi yaya sule ya sauke yana gyara zama, “Wato ni abin nasu yanzu ya fara ruɗar dani oga, nama rasa wanene mara gaskiyar tsakanin Alhaji Alin da Hajiya Humairan? A yanda bincikena ya nunafa Qaseem baya ƙasarnan”. “Baya ƙasar kuma?” Jawaad ya faɗa yana tamke fuska cike da ɗunbin mamaki kuma. “Ƙwarai kuwa wannan itace magana ta gaskiya, saura kwana ɗaya a ɗauki azumi ya tafi, kuma abinda na fahimta lafiyarsa ƙalau ba kamar yanda ku anan office yace zaiyi zaman ganin likita a gidaba”. Shiru Jay yayi yana juya al'amarin a ransa, tun randa ya fiddo Qaseem a cell bai sake ganinsa ba, sai ana gobe za'a fara azumi, ya shigo station amma baifi awa uku ba ya tafi, Jawaad bai kawo komai a ransaba sai da aka sake ɗaukar tsahon sati ɗaya baiga yazo aikiba, shinefa yay bincike ya fahimci Qaseem ɗin hutu ya ɗauka akan baida lafiya zaiyi zaman ganin likita a gida. Aranar bai ƙasa a gwiwa ba ya nufi gidan Qaseem, amma sai ya iske bayanan daga bakin maigadinsa, yayi tunanin yana gidansu ne, saiya saka a bincika masa can, nanma an tabbatar masa baya nan, tunda yayma gidan yajin aiki ma bai sake waiwayensa ba. Shinefa yasa yaya Sule ya bincika masa.
Huci mai zafi Jay ya furzar daga bakinsa yana danna ƙasan pen ɗin hannunsa da ƙarfin gaske, ya ɗan kalli yaya Sule ya ɗauke kansa daɗan duka table ɗin, “Tabbas yanzu na sake fahimtar akwai abinda suke ɓoyewa, in babu rami miya kawo maganar rami? Sun fahimci ina bibiyar Qaseem shiyyasa suka turashi can, ammafa sunyi abanza, sugama zagaye-zagayensu saina gano komai, da izinin ALLAH sai na bankaɗo komai, idan nace ina nufin komaima Sulaiman!!”. Ya ƙare maganar cikin fushi da dukan tebirin da masifar ƙarfi. Shidai Yaya Sule har sai da yaɗan rumtse ido. Jay yace, “Wace ƙasa suka kaisa?”. Yaya Sule da yay ɗan shiru alamar tunani yace, “Idan dai ban mantaba China naji”. Karan farko Jay ya saki murmushi mai ma'anoni da dama, yaɗan ɗage kafaɗarsa da taɓe baki.
★★★★★
Da daddare bayan Jawaad ya koma gida ya samu kira daga su Uncle Nasir, saida ya kammala shirin barcinsa sannan ya nufi sashen mama Atika inda suke jiransa. Bai wani nuna mamakin ganinsuba gaba ɗaya ya gaishesu cikin girmamawa kamar yanda ya saba.
Uncle Nasir yace, “Alhaji Ali ya kirani jiya akan ankirashi daga gidan sarki za'a kai lefenka gidansa, Jawaad kana ganin kuwa wannan hanyar daka biyo mai ɓillewace? Karfa ka manta a yanda kasa akai ɗaurin aurannan?”. Shidai Jay baice komaiba kuma bai ɗago ya kallesa ba. Cikin fushi Uncle Uwaisu yace, “Wato ga ƴan iska na magana kayi kunnen uwar shegu damu ko?” Murmushi Jawaad yayi yaɗan girgiza kansa batare daya ɗago ɗinba, yace, “Uncle to nikam mi kukeso nace, idan maganar yanda aure ta kasancene tun a wancan karon na bada amsar da duk ake buƙata, a tunanina yanzun mun wuce wannan wajen, kai lefe kuwa daga can masarauta ne sukai t
unain akai lefen can saboda koba komai ubane shi ga yarinyar shine kuma mariƙinta har a yanzun..........”
“A wannan ganganne Jawaad, Shine mariƙinta ko kai daka ɗauketa ka maida gidan sarki saboda ka isa, karkuma a taɓa maka ƴar gwal?”. Uncle Bashir ne yay maganar a fusace. Jawaad da har yanzu yaƙi kallon kowa a cikinsu yace, “Nidai duk abinda kuke ganin na mukushi ba daidaiba akan wannan aure kuyi haƙuri ku kuma gafarceni”. Uncle Sulaiman da tun ɗazun baice komaiba yace, “Nima dai a ganina maimaita maganar baida amfani tunda abinda ya faru ya rigada ya faru, haka kuma ALLAH ya tsara dama zata kasance, kunga kenan bamu isa canja wannan ƙaddarar ba. Yanzu Jawaad ina zaka ajiye matarka? Dan bamuga kana ƙoƙarin gyara ɓangaren nakaba”. Karon farko Jay ya ɗago daɗan murmushi ya kalli Uncle Sulaiman, “Uncle ba anan zan ajiyeta ba, A.Y street zata zauna har an kammala gyaran”. Uncle Nasir yace, “A.Y kuma? Saboda karmu cinyeta anan?”. Jay da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ba haka bane Uncle...........”
Da sauri Mama Atika ta ƙatseshi da faɗin, “Inma haka ɗinne kaidai ka sani fitsararre mai shegen taurin kai da raini, hakan dakai ni bai dameniba, dan ko kaƙi ko kaso dolene a maida aurenka da Sabira, dama shirin maka tsinannen mijin daka aura mata muke a kotu, sai gashi ya matu kuɗinmu sun huta, to wlhy kama tabbata aure kamar mun maidashi ne kai da Sabira”. Cikin fushi Jay ya kalleta zaiyi magana Uncle Sulaiman ya girgiza masa kai. Shiru yay ya maida kansa ƙasa, har sukaci jarabarsu suka tsire bai sake tankawaba, taron dai ya watse da sharaɗin sai ya maida aurensa da Shahudah.
Shidai bai tanka musuba tunda yasan ɗan fir'auna bai mutuba.
______________________________
SAUDIA
Gaba ɗaya wannan yinin na yau Umm-Anum ta yisane cikin yimin nasihohi da haɗamin kayan gyaran jiki da wasu littatafai masu muhimmanci kamar yanda tace, sai faifan cds da tace na kasance cikin kallonsu duk randa nake da lokaci zasumin amfani.
Gaba ɗaya raina a ɓace yake banason tafiya, basan yanda zan musalta muku yanda nakejinta a rainaba, tunda tafiyarnan ta gabato har kuka nakeyi idan na tuna zan tafi, baƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninmu ba a kwanaki sha biyun nan, kodan ta jani jikintane oho.
A ɓangaren Umm-Anum ma dai cike take da damuwa, haka kawai takejin batason Bilkisu ta tafi, yinin yau komanta sukuku zaka gansa, da daddare tare suka dawo gida da bilkisu, anan zata kwana yau gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce ita da Aunty Mahfuzah da Anum sai Anuwar daya dage shima zaije, da farko Umm-Anum catai bazaijeba, sai da Abie yasa baki sannan da ƙyar ta amince, dan haka kawai takeji batason suje da ga shi har Anum ɗin.
Abie bai taɓa ganin bilkisu ba sai yau bayan sun dawo, itama kuma yauɗin ta taɓa ganinsa, amma yanda ya karɓeta abin har mamaki ya bata, shikansa mamakin yanda yarinyar ta shiga ransa yakeyi, sannan badan kar ace yay ƙaryaba wasu abubuwa nata suna ɗan masa kama dana Umm-Anum ɗin, musamman tafiya da dai wasu ƙananun abubuwa da saika nutsu sosai kake fahimtarsu.
Sai da su Bilkisu suka shige suka kwanta sannan ya fuskanci matarsa, dan yanda take komai rai ɓace ne ya sakashi jinsa shima a damuwa. cike da kulawa yake tambayarta mike damunta?. Hawayen da taketa riƙewane suka zubo mata. Sake rikicewa yay ya jawota jikinsa, dan yanason wannan baiwar ALLAH shidai a rayuwarsa, dukda ba ita kaɗaice matarsaba kuwa, amma yanda take ƙyautata masa yasa tazama tauraruwa a garesa. Yanda yaketa jero mata tambaya wata kan watane ya sakata sakin murmushin ƙarfin hali, idonta a kansa tace, “Bafa komai baneba, yarinyarnan banason ta tafi wlhy, jinta nake cikin jinina fiye da yanda kake zato, ina mata ƙauna maiban mamaki har a ƙarƙashin zuciya, sannan sunanta duk sanda na ambacesa ko wani ya ambata sai naji matsananciyar faɗuwar gaba, bansan miya saba”. Abie dai kallonta ya keyi cike da nazari, sai da tagama ya sauke ajiyar zuciya tare da sake rungumeta, maganganunta na buƙatar ayi musu zama na musamman domin yin nazari, amma duk da haka bara ya gwadata ya gani, ko lokacin da suke fata
ne yazo. “To kodai zamu shirya muma muje bikin nata ne?”. da sauri Umm-Anum ta tashi daga jikin mijin nata tana girgiza kanta, fuskarta harta nuna ɓacin rai, tace, “Babu inda zani Annur, badanma ka takuraba kosu Anum bazasu jeba”. Da kallo shidai kawai yake binta, amma baice komaiba, baikuma sake cewa uffanba game da tafiyar har gari ya waye su Bilkisu suka tashi da shiri.
★★★★
Yau ta kasance ranar da zan koma ƙasata ta haihuwa tare da tarin alkairan Umm-Anum da mijinta da Aunty Mahfuzah, sai su Anum da nakejin ƙololuwar farin cikin tafiya tare da su, gefe guda kuma na zuciyata najin ɗacin rabuwa da Umm-Anum tare da matsananciyar kewa. Munfi awa uku zaune da ita tana sake tisamin abubuwa masu dama, daga ƙarshe ta roƙeni akan karna manta da ita, zata kuma ringa kirana akai-akai, idan kuma nasamu lokaci na daure muzo gareta wataran tare da mijina, haka kawai takeji a ranta tanason ganin mijin ƴarta. Murmushi kawai na iyayi ina share hawayena kaina a risine, ta rungumeni a jikinta tana jeromin addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya a gidan aurena. Da ƙyar ta barni na fito, tana kuka nima inayi tamkar zan shiɗe, da ƙyar Aunty Mahfuzah taja hannuna ita da Anum.
Har jirginmu ya ɗaga ban daina kukan kewar Umm-Anum ba, ina ƙaunar matarnan matuƙa a cikin jinina da tsokar zuciya harma da ruhi.
Kasancewar tafiyar yamma mukayo dukda ba time ɗinmu ɗaya da nanba munyi saukar dare ne, inda mukaci karo dasu Amaturrahman ƴan tarba, sosai muke murnar ganin juna, sai santi suke wai na canja matuƙa, sunata zubamin shaƙiyanci nadaiƙi kulasu, dan bana cikin mood ɗin farin ciki sam.
Koda muka isa masarauta Ummu ma rungumeni tayi, sai taɓani take tana jerama Umm-Anum addu'oi na musamman, ga daɗin da taji na barin su Anuwar da akai suka biyomu. A ƙasan raina inata mamakin ganin yanda suketa shirye-shiryen bikin tamkar zasu aurar da ƴarsu ne ta cikinsu ko ƴar uwa ta jini, kai waɗanan mutane sun cancanci zama shugabbani, domin duk mai fuskantar al'umma da maida al'amarinsu nasa to lallai shine shugaban da yafi cancantar zama shugaba.
Ɗaki guda aka waremin dan Ummu tace bazan zauna ɗakinsu Amaturrahman ba wannan karon, akwaima sauran kayan gyara da Umm-Anum ta bayar a ƙarasa min a kwanaki biyun da suka rage mana. Babu wanda yaymin maganar Boss nima kuma bamma kowa ba, da yake darene bayan anɗan gaggaisa duk muka kwanta.
WASHE GARI.
A safiyar yau nakejin wai za'a kai lefena gidan Dad ne, haka kawai naji gabana ya faɗi, amma sai na danne zuciyata na cigaba da addu'oi, har yanzu Yah Qaseem na ƙasan raina, inason nasan halin da ya ke ciki shi da Dad fiye da kowa a gidanmu, sai dai hakan ta gagara dan boss ya toshe ko ina da ina da zan iya jinsu. Su Amaturrahman sunata shirin tafiya can gidan domin amsar lefen suma, sai a yau naga sauran manyan ƴaƴan Ummu ƴan uwan tagwaicin Amaturrahman. Abdul-Raheem da Abdur-rahman, sai Ameen ɗan uwan tagwaicin Meenal, sai Uncles ɗinsu huɗu, Sauban da matarsa ƙyaƙyƙyawa mai kirki da yaransu huɗu masha ALLAH, sai Aryaan shima da matarsa da yara biyu, Aiyaan ma matarsa da yarinyarsu ɗaya sai ciki ƙarami da matarsa keda shi, sai Khalil shima da tasa matar da yara biyu, dukansu suma a jiya suka iso daga India. Gida ya cika yanda akeso tamkar bikine daya shafesu na jini, washe gari sai ga wadda naji suna kira Aunty Samha itama da nata ƴaƴan, sai kuma babbar mace suna kiranta Aunty Mimi. Wlhy bansan sanda hawaye suka faramin gudu a kumatuba, duk wani kewar ahali sun toshemin ita ta ko ina, sun mayemin gurbin dangin da suka nisanceni.
A wajen Amaturrahman nakejin wai Boss yazo masarauta wajen Ummu yau da safe, bai nemi inda nakeba har ya wuce, banji komai a rainaba game da hakan, sai daga baya suke bani labarin Ummu ce tace an daina ganina har da shi kansa bazai ganniba. Ni saida abinma yaso bani dariya amma na kanne.
_______________
A gidan Dad kam shirye-shiryen karɓar lefe suke, duk da dai ran Momy a ɓace yake matuƙa tana dai ƙoƙarin dannewane, shi dai Dad baka gane yanayinsa, dan yamafi maida hankali ga lallashin ƴar lelensa da suka cikama zuciya
da alƙawarin komawarta gidan Jay nan bada jimawaba.
Kusan sha biyun rana su Amaturrahman suka iso gidansu Hudah, Hudah dai bata fitoba zamanta tai cikin ɗakinta, Aamilah kuma an fito ayi rainin wayo saita iske waɗanan sunci uwarta aduk iskancin da take taƙamar ta tara kota iya. Dole fa ta nutsu waje guda ta kama kanta, harta je ta ƙwanƙwasama Shahudah dake ɗaki gulma da cewar lallai Bily ta shahara a asirin nata har ƴan gidan sarki taimawa. Cikin takaici Shahudah tace, “Tsinanniya jikar matsafa, ai nayi alƙawarin randa na koma gidan Bb wlhy bazata kwana a gidanba, shi kansa saina sakashi yin nadama wlhy, kuma a banza zata shiga ta fito Hajiya (mama Atika) tamin alƙawarin ko hannunta bazai riƙeba dan Uban da ya haifeta”. Dariya Aamilah ta sanya da sake tunzurata akan hakan da zatai shine dai-dai, kuma taji daɗin matakin da mama Atika tace zata ɗauka akan kar Bilkisu ta raɓu Jawaad, (dan sufa har iyanzu tunaninsu nakan asiri Bilkisu taima Jay bawai sonta yakeba😂). “Mtsooww kamar kin manta da aikin matsafa kenan” cewar Shahudah cike da takaici. Haka dai sukaita aikin zagin Bilkisu da Alhaji Babba harda su Ummah basu tsiraba, kai gidan sarki ma saida suka samu rabonsu😂.
Oho su bama susan da zaman wata Hudah ba a duniya balle a cikin gidan, sun ɓararraje abinsu sunata harkokinsu tamkar gidansu (😂Wani aiki saisu Samha) hankalinsu kwancefa yake a gidan Dad dukda sunga cika da batsewar da Momy keyi basu nuna ta damesuba.
Ƙarfe biyu da wasu mintuna na rana matan Uncles ɗin Jawaad dasu Ummah suka iso da lefen Bilkisu. Kayane gwargwadon iko na gani na faɗa babu fariyya a ciki balle nuna anfi kowa. Sai dai fa tsarin kayan da nagartarsu dolene ta girgiza zukatan mahassada da masu ganin wadda akai dominta bata cancancesu ba. Inna zainabu sai haɗiyar zuciya akeyi, hatta da Lawisa da ayanzun basa faɗa da bilkisun kuma itama mijinta Alhmdllh sun sami sauyi saida taji ɗaci a ranta, hakama sauran dangin kowa dai ta ciki na ciki, su kansu matan Uncles ɗin Jawaad da suka kawo kayan kowa dai sai murmushin saman fuska tunda suma sai yaune suke ganin kayan tunda su Ummah ne suka haɗa abinsu. To kowa dai ya danne an gama komai lafiya, an kuma bar kayan anan sai Dad ya gani sai a kaisu masarauta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suma su Gimbiya su gani.
Tukuyci mai tsoka ƴan masarauta suka saukema su Ummah, wanda ya girgiza kowa hatta momy da take ganin wanda Dad ya bada a bayar yayi yawa da.
Aikam tunda su Safah suka koma masarauta babu abinda suke sai labarin lefe, suka addabama Bilkisu da tsokana musamman su Amaturrahman da matansu Aryaan da suke biye musu suma dayake mashiriritan ne. Sai da gimbiya ta fito da kanta ta korasu daga kan Bilkisu sannan suka sama mata lafiya.
_____________
Gayya taban mamaki su Jabeer sukayo a wannan biki, al'amarin har ba'a cewa komai, tun a yau baƙin nesa kuwa suka fara sauka, irin su Abbati ma duk yau