Showing 66001 words to 69000 words out of 261165 words

Chapter 23 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1116

fahimcesuba yace shifa a haka aka kawo masa sunayen anguna da amaren da za'a ɗaurama aure a yau, kuma iyakarsu kenan ya kammala gama takardar. Yay maganar yana nuna musu.
     Ganinfa za'a iya bama hammata iska a massalacine ya saka ƴan agaji sallamar kowa akace su Dad su fito a shiga inda ya dace ayi magana, sannan ana neman dukkan angunan da aka ɗaura aurensu ba dai-dai ba.
           Yah Qaseem kawai aka gani a cikin anguna, amma babu Jawaad babu Habibu da aka ɗaurama Shahudah, kuma kowa yayi imanin yaga Jawaad a massallaci kafin a tada sallah, yanzukam an nemesa ƙasa da sama tamkar allurar mayya an rasa. Kowa ƙoƙarinsa ya kira wayar Jawaad amma sam taƙi shigama, gefe kuma ana jajen wanene habib ɗin da aka ɗaurama aure da Shahudah?.

       Lokacin da ake waccan dambarwar a lokacinne shikuma Salman ya kira Shahudah ya sanar mata komai, kafin ya kira Momy itama, yana tsaka da sanar mata abinda ke faruwa Shahudah ta nufi ɗakin Bilkisu da wuƙar data ɗakko daga kicin tsirara tana iƙirarin yaufa saita kasheta.

             A masallaci komai ya hargitse, imam ya tara dukkanin ƴan agajin massallacin dake da alhakin rubuta sunayen waɗanan anguna da amare anata jera musu tambayoyi, dan kuwa dai Dad da kansa shine ya kawo list ɗin farko kuma an tabbatar yanada banbanci da wanda yake a hannun imam a yanzu. Sudai ƴan agajin dakeda wannan alhaki sun tabbatar abinda suka gani kenan, sannan kuma ga takardar farko da Dad ya kawo an samo kuma bata da alaƙa data yanzun. Abun ya ɗaurema kowa kai hatta da imam ɗin kansa, dan shidai yanada yaƙinin babu yanda za'ai ƴan agajin su bada abinda ba haka yakeba, dan invitations ake kawo musu na ma'auratan da duk za'a ɗaurama aure a satin, sukuma saisu rubuta sunayensu a takarda gabaki ɗaya domin samun sauƙi, nasu Jawaad kuma a rubuce Dad ya kawo tunda ba'a buga invitation card ba abin yazo a ƙure. TO A INA MATSALAR TAKE?.
       Wannan itace tambayar dake a bakin kowa a wajen musamman lokacin da Yah Qaseem ya yanke jiki ya faɗi a sume shima. Dai-dai kuma da kiran da akaima Dad akan tashin hankalin dake faruwa a cikin gidansa. Abin tausayi sai kawai Dad ya fashe da kuka shima yana neman faɗuwar, cikin amincin ALLAH Uncle Sulaiman ya samu damar tarosa da faɗin, “Haba Alhaji Ali, ka kwantar da hankalinka mana, na tabbata saɓani aka samu ko kuskure, kuma abune mai sauƙi da nake ganin zamu warwaresa da gaggawa, Jawaad ya sakima Qaseem matarsa, haka shima wannan da bama asan ko wanenen ba ya sakema Jawaad matarsa”. Kasa magana Dad yayi, dan babu abinda yake fahimta daga kalaman Uncle Sulaiman, gaba ɗayama numfashinsa neman barin gangar jikinsa yakeyi.
         Shugabannin massallacin dai nata ƙoƙarin binciken tushen wannan matsala da basu taɓa cin karo da itaba a tsahon rayuwarsu, anɗaura auren da babu adadi a shekarun wanzuwar massallacin amma hakan bai taɓa faruwaba koda da kuskure kuwa, babban tashin hankalinsu ma shine wanene Habib da aka ɗaurama Shahudah aure dashi?, dan kuwa dai an nema wakilan nasama an rasa balleshi kansa, matsalar Qaseem da Jawaad kam kowa yana ganin tanada mafita tunda su an rigada an sansu gasu kuma ƴan uwan juna.
          Imam da kansa ya gama ɗaukar zafi gaba ɗaya ya cire rawanin kansa yana sharce gumi da faɗin, “Wannan wace irin matsalace haka? Tayaya za'ace an ɗaura auren da sam bashi da alaƙa da juna?”. Qaseem shi

ne mijin Bilkisu, an ɗaurama Jawaad, Shahudah itace matar Jawaad an bama Habib, Habib shine mijin Azeema, an bama Qaseem, Qaseem da Jawaad ahali ɗaya suka fito, a tare kuma aka kawo sunayensu, to yaya akai shi Habib mai mata azeema suka shiga cikin wannan sarƙaƙiyar? Idanma ance wajen haɗe sunayen waje ɗayane dan a sauƙaƙama liman wahala to tayaya abin ya kasance haka? Kenan suk yandama akai aka dawo akwai saka hanun hadiman masallacin kenan?. hakan bazai kasance mai yuwaba dan gashi dukkan bincike anyi babu wani baƙon al'amari daya shigo har aka bama imam ainahin takardar amare da angwayen wannan satin, wadda kuma kowane ɓangare suke nuna ba ita bace imam yay amfani da ita, kenan dukkan matsalar a yanzu tadawo ta tattarane gama shi imam ɗin dan kowa shi yake zargi.

★★★★★★

            Ganin babu wata mafita anan Alhaji baba ya shawarcesu da tafiya gida kawai aje a samu nustuwa kafin a fuskanci matsalar cikin kwanciyar hankali a nema masalaha a kanta.
       Kowa yay na'am da batun Alhaji baba, dan haka aka ɗunguma zuwa gidan Dad da tushen matsalar take.
     
        Isowar motocin su Dad yay dai-dai da isowar motar gidan Sarki Sameer Saifudden dake ɗauke da ƴaƴansa ƴanmata a ciki, waɗanda suke cikin farin cikin samun fita yawo a wajen da basu saniba. Babu wanda ya fahimci su wanene su ɗin?, saboda kowa baya cikin hayyacinsa, ga matsananciyar hayaniyar data fiddo ƴan anguwa gaba ɗaya dake tashi daga gidan Dad.
        Su Amaturrahman da kansu ke a kulle sunbi ayarin masu shiga gidan ganin shine gidan da Bilkisu ta tura musu address ɗinsa, sai dai gidan a harmutse yake har basu da damar fahimtar komaima. Isowar su Dad kuma ya sake harmutse gidan saboda ganin halin da Bilkisu da Shahudah ke ciki, ita kanta Momy bata cikin hayyacinta, ga Yah Qaseem can an wuce dashi asibiti shima, sai kawai Dad ya yanke jiki ya faɗi shima ganin ƴaƴan nasa biyu ga Qaseem kwance tamkar sun mutu.
        Tashin hankali wanda ba'a saka maka rana kenan ke wanzuwa a wannan lokaci, a take aka kwashesu su uku aka fita dasu daga gidan zuwa asibiti domin ceto rayukansu, tuni suma sauran jama'a suka bisu a motoci, ƴan anguwa kuma suka shiga tattaunawa, danma anguwace ta manya kowa yana harkar dake gabansa babu ruwan wani da wani, amma a yanda lamarin yazo duk rashin shiga harkar junansu yazama dole a tattauna.
        A wannan kace nace na ƴan anguwa su Amaturrahman suka fahimci wasu abubuwan, ciki kuwa harda fahimtar wadda sukazo gurintama tana cikin waɗanda aka fita dasu tamkar gawa daga gidan. Jikinsu a sanyaye suka koma mota driver ya jasu sukabar anguwar, Safah sai kuka take akan itafa subi suga wane asibiti aka kai Bilkisu, saida Amaturrahman tai kamar zata bugeta sannan ta nutsu tai musu shiru.

★★★★★

        A ɓangaren su Jabeer kuwa tun dambarwar farko ta massallaci suka shiga ayarin ƴan neman Jawaad, sai dai komai kama dashima basu ganiba, bayan kuma a tare suka shigo dashi massallacin har aka tada salla, bayan an idarne suka nemesa suka rasa gaba ɗaya, a lokacin basu kawo komai a ransuba saboda ba'akai ga ɗaura aurenba, sai bayan an ɗaurane tsoro ya kamasu da tunanin kodai yanada masaniyar komai, to amma mizaisa yayi hakan kuma? Tunda sunsan halinsa sarai, suk son da yakema Bilkisu inhar babu wani dalili bazai zama mai aikata wannan abunda dake faruwaba domin kawai ya aureta, dolene su nemesa domin jin minene ke faruwa? Shine? Kokuwa shima bai saniba.
         Sun fara da station, sai dai bai koma canɗinba kamar yanda kowa ya tabbatar, sannan gidansuma bai komaba, gidansa dake Abdul-aziz Yusif street nanma dai baima jeba, gaba ɗaya kuma sai kansu ya kulle ɓam akan komai.
      Suna tsaitsaye a ƙofar gidansa na A.Y street ɗin saƙo ya shigo a wayar Jabeer. Jikinsa har rawa yake ya buɗe saƙon ganin Jawaad ɗinne ya turo.
        “Kubar wahal da kanku wajen nemana, zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu zan bayyana, akwai aikin dana tafi yine, sannan karku zargeni akan abinda ya faru kamar yanda nasan rashin ganina anjima kaɗan zai ɗarsama wasu daga cikin ahalina, sam bani da hannu a ciki, akwai ɓoyayyen al'amarin danima ban sanshiba, lokacine ka

wai zai warwareshi. Inason kuyi duk yanda zakuyi kafin nan da awa uku a canjama Miemaa asibiti, dan nasamu labari yanzunan akwai matsalar data faru gidansu, karku barta ta kwana a asibitin da aka kaisu, karkuma wanda yasan kun ɗauketa daga asibitin har Alhaji baba”.
       Kallan kallo aka komayi tsakanin Jabeer da Hafiz da Aliyu akan wannan saƙo na Jawaad da ya kuma ɗaure kansu akan wannan al'marin............✍

Yau dai gashinan na muku words 3700😲 kuci ku ƙoshi har safiyar litinin.😉👌🏼

Barkanku da juma'a, kar a manta da saka bayin ALLAH a addu'a dan ALLAH.

Ƴan facebook kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi a gareku a duk duniyar da kuke.

Asha weekend lafiya my sweet fans, banda taƙaddama kuma.😂😂😘😘😘😍👍🏻👌🏼



ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[12/7/2020, 11:22 AM] HASNA✍🏻: Billyn Abdul:
Page 23

...............Tunkan su isa asibiti Dad ya farfaɗo, lokacin kuma da suka iso sun iske shima Qaseem ya farfaɗo, duk yanda Doctor yaso yayma Qaseem ɗin allurar barci danya huta yaƙi yarda, hakama Dad bai yarda ko dubashi ayiba, cayay babu damuwa su barshi. Bilkisu da Shahudah kawai aka shiga bama taimakon gaggawa, wanda daga farko Momy da catai baza'a duba Bilkisu ba, sai da Dad ya nuna mata ɓacin ransa a fili sannan ta nutsu, sai dai tanata ƙananun magana akan hakan.
     Haka suma sauran family dake harabar asibitin saboda yawan da suke dashi aka tsaidasu nan kowa nata tofa albarkacin bakinsa, saidai mafi yawan kalamansu suna ɗora laifinne akan Bilkisu ce tai asiri. Yanda suke jifanta da mugayen kalamai dolene kaji tausayin Bilkisu, dan zaka ɗauka akan wata uwar mata suke maida yanda akayin. Hayaniyarsu ce ta saka Uncle Nasir cewa duk su wuce gida domin zamansu anan ɗin bashi da wani amfani. Badan sunso hakanba sukabi umarninsa.

          Motocinsu na cikin fita su Jabeer suka iso asibitin suma domin cika umarnin Jawaad, mamakine yay masifar kamasu ganin wannan uwar gayya tamkar anan ake bikin. Shi Hafiz ma abin haushi ya bashi, ya buga tsaki cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Mutanen nan suna bani mamaki da al'amarinsu, to wannan gayyar kuma ta miye?”. Aliyu dake jinsa yace, “Kaima dai ka faɗa”.
     Fitowa sukai a motar suka isa inda su Uncle Nasir ke tsaitsaye shi da Dad, da Uncle Sulaiman, sai Qaseem dake zaune cikin mota, Salman kuma yana zaune a saman motarne yanata latse-latse a waya tamkar baida wata damuwa a duniya. Gaishesu suka shigayi cikin girmamawa, tare da musu jajen abinda ya faru. Cike da kulawa suma suka amsa musu, Uncle Sulaiman yace, “Ina Jawaad ɗin shi yake? Tun ɗazun sai neman wayarsa muke taƙi shiga”. Duk kasa cewa komai sukai, dan kuwa suma dai basusan amsar daya dace ace sun basuba akan inda Jay yake, tunda suma basu saniba.
      Uncle Nasir ya buɗe baki zaiyi magana ya fasa saboda shigowar motar Jawaad harabar asibitin, duk bin motar sukai da kallo harsu Jabeer, cike da mamaki suka tsatstsareshi da idanu lokacin daya fito a motar, yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda ƴar ubansu ruwan zuma, sai maiƙo take, sosai ɗinkin ya zauna masa a jiki cif. Kosu kansu su Uncle Nasir ɗin ya musu ƙyau, dan kafin kaga Jawaad da manyan kaya akan daɗe saboda yanayin aiki, shiyyasa idan ya saka ɗin sai ya zama na musamman. Nufowa yay inda suke fuskarsa sam babu walwala, Qaseem da babu wanda ya lura da fitowarsa a mota yasha gabansa.
          Kallonsa kawai Jay ya tsayayi batare daya iya cewa dashi komaiba, cike da ɓacin rai Qaseem yakai hannu zai shaƙosa, da sauri Jawaad ya ɗaga masa hannu, da watsa masa wani irin kallo mai razani dake gauraye da ɓacin rai, “Qaseem bani hanya”.      “Anƙi a baka ɗin” Qaseem ya faɗa a zafafe. Jawaad baice komaiba ya raɓashi zai wuce, sake shan gabansa Qaseem yayi, Jawaad yay wani murmushi mai ciwo idanunsa na sake ƙanƙancewa tsabar masifar dake cin zuciyarsa, cikin wata irin muryar data bama Qaseem mamaki Jawaad yace, “Qassem ka riƙe girmanka, banason ka kaini bangon da zan sakaka dana sani mara amfani”. Kafin Qaseem yace wani Abu Uncle Sadiq ya ƙaraso wajen. “Ku wane irin shashancine haka kukem mutane anan?”. Jawaad baice komaiba, sai Qaseem ne ya bama Uncle Sadiq amsa da, “Uncle bazaka ganeba, wannan yaron munafukine, wlhy ko rantsuwa nai babu kaffara nasan yanada hannu akan wannan abun daya faru, kuma wlhy dolene ka saki Bilkisu a yau ɗin nan basai gobeba”. Murmushi Jawaad yay cikin taɓe baki ya raɓasu ya wuce batare da yace komaiba.
       Ƙarasawa yay wajen su Uncle Nasir ya gaishesu, Uncle Nasir yace, “Kaikuwa ina kaje anta nemanka tun ɗazun Jawaad?”. “Amin afuwa Uncle, naje wani wajene”. “To amma saika kashe wayarka? Minene amfanin hakan?”. Jawaad dai baice komaiba.
            Uncle Uwaisu yace, “Amma dai kasan miya faru a wajen ɗaurin aure ko?”. Cikin nuna halin ko in kula Jawaad yace, “Uhmmm na sani”. Ran Uncle Nasir a ɓace yace, “Ka sani? Amma shine dan wulaƙanci katafi wani waje ka barmu da nemanka?”.
      Kafin Jawaad yace wani abu Uncle Sadiq yace, “Ya

ya nikam inaga wannan ba maganar nan bace, kamata yay muyi haƙuri yaranan su dawo cikin hayyacinsu sai ayi maganar a nutse a gida kamar zaifi, sannan kuma mu maida hankali wajen neman shi wancan angon da aka ɗaurama Shahudah aure dashi da ita Azeema take kowa”. Duk sunyi na'am da hakan, Jay ya kalli Uncle Nasir a wani yanayi, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru kawai.

           Bayan sallar la'asar su Uncle Nasir suka wuce gida harda Dad da Qaseem da aka tilastama dole akan yadace suje su watsa ruwa kodan suji ƙarfin jikinsu, anbar momy kawai wajen Shahudah, Ummie da maman Amina kuma suna tare da Bilkisu, Jawaad bai shiga duba kowaba a cikinsu.
      Suna isa gida ya shige sashensa, wanka yay yasha magani saboda kansa ciwo yake masa sosai, duk yanda yaso ya kwanta ya huta hakan ya gagara, ya shiga zagaye bedroom ɗinsa cikin faɗawa wani dogon tunani akan wannan dambarwar da suka wayi gari da ita yau, tabbas yasan kaso mafi yawa na abinda ya faru, musamman akan sarƙaƙiyar ɗaurin auren, sai dai akwai wani al'amarin daya ɗaure masa kai sam ya kasa samun amsa akai, kuma yazama dole ya nemo wannan amsar, Tabbas saiya nemota, itace zata zama tsanin buɗe masa hanyar fahimtar abinda ya kasa fahimta a yanzu da duk sauran jama'a ma. Ya sauke numfashi mai zafi tare da kwanciya a kan gadonsa ƙafafunsa a ƙasa.
        Shi da kansa shine ya canja list ɗin ɗaurin aure a masallaci, sai dai daliline mai ƙarfi ya sakashi aikata hakan, kuma duk wanda zaiji dalilinsa anan gaba zai tabbatar abinda yayi shine dai-dai kuma shine ya dace, to amma tayaya zai fahimtar da mutane sukuma su fahimta batare da ya fito da ainahin maganar filiba?. Wannan tambayar itace keta cin ransa da sukarsa a ƙahon zuciya. Barci ɓarawo shine ya sacesa a wannan lokacin batare daya shiryama hakanba, bai farkaba sai gab da magriba, wasu massallatanma har sun fara kiran sallar. Wanka yay a gaggauce yay shiri cikin ƙanan kaya ya fita riƙe da key ɗin mota da wayoyonsa, mota ya buɗe ya zubasu sannan ya nufi massallacin ƙofar gidansu sukai sallar magriba.
           Koda ya dawo bayan an idar mota ya shiga ya fice daga gidan.

★★★

MASARAUTAR GAGARA BADAU

              Koda su Amaturrahman suka iso masarauta sai suka iske gimbiya Munaya tana sashen mai martaba, haƙura sukai akan idan ta fito saisu sanar mata da duk abinda ke faruwa.  Safah dai batace komaiba, tana ganin yayun nata sun nufi ɗakinsu ta zare jiki zuwa sashen mai-martaban batare da sun saniba. Sai dai koda ta nema Jakadiya tai mata iso saitace mata gimbiya na tare da takawa, tasan kuma babu mai shiga ganinsa inhar yana tare da matansa. Tarbiyyar da su Safah suka tashi ciki akwai girmama hadiman gidan, dan koda wasa Gimbiya Munaya bata yarda yaranta suce zasu taka koda bawa na gidan yanda suke soba, tsaye take kan tarbiyyarsu daga ita har mai martaba da Mommah. Safah sai ta kwantar da kai cike da shagwaɓa tana lallaɓa jakadiya, harda bata ƙyautar dubu biyar. Baki Jakadiya ta washe, tace, “A uwar masu gida ai dolene nai miki iso, ammafa inhar basa falon farko to saidai kiyi haƙuri anjima saiki dawo.
      Safah tace, “Na yarda, amma dai ba falon farko kawai ba, dan ALLAH harna biyu, dan kinsan inhar Ummu na tare da Abbu bazasu zauna a falon farko ba, nikuma maganace mai muhimmanci zanma Ummu”. Rigimar Safah da Jakadiya ta sani yasa ta amince zataje har falo na biyun. Safah na nan tsaye a ƙofar ƙatafaren falon mai-martaba Jakadiya ta shiga domin mata iso. Iyakarta falon farko tai kira ta wayar landline kamar yanda tsarin Sarki Sameer yake. Munaya ce dake masa tausa ta ɗaga, cike da girmamawa Jakadiya ta isar da saƙon Safah. Daga can Munaya zata fara faɗa akan Safah ta jirata saita fito Sarki Sameer yaymata nuni data bari Safah'n tazo, badan tasoba tabi umarninsa.
        Cike da ɗoki Safah ta shiga kamar yanda Jakadiya ta sanar mata anbata izini, tun daga falon farko har zuwa na uku bata iske kowaba, hakan yasata wucewa ƙaramin falon da bakowa keda lasisin shigarsaba saisu da iyayensu. Tai sallama a bakin ƙofa suka amsa mata kafin a bata izinin shiga. Sarki Sameer na kishingiɗe a ƙasan lallausar daddumar da

aka ƙawata falon da ita, ya zubama ɗiyar tasa da bazata gaza shekaru sha uku ba ido yana murmushi, itama murmushi take masa tana satar kallon Ummu dake zuba mata harara ta gefen ido. Ganin tayi tsaye taƙi ƙarasowa garesu mai-martaba yakai dubansa ga gimbiya Munaya, hannu yakai yanda Safah bazata ganiba ya Mintsineta, gimbiya Munaya ta ɓata fuska irin taji zafinnan, gira ɗaya ya ɗaga mata yana murmushi da cewar, “Kin tsaremin yarinya da ido takasa ƙarasowa, Ummuna kinga zo naji mike tafe dake?”. Da sanɗa Safah ta raɓa gefe taje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login