Showing 93001 words to 96000 words out of 261165 words

Chapter 32 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1141

tare da sojoji ukun nan yayi, cikin mutunta juna suka gaisa, wanda ya kasance babba a cikinsu mai yawan shekaru kuma ya kalli Jay yana faɗin, “Jejin nan jejine mai haɗari, Sojinmu sunsha wahala sosai a cikinsa kafin ALLAH ya kawo mana ɗauki ya haɗamu da Ƙaura na bakin kadarko, a bakin jajenin yake rayuwa shida iyalansa, sannan a cikin jajen yake farauta, sai dai wani babban al'amari ya faru a shekaru biyu da suka wuce wasu azzalumai suka tashi gidansa dukkan iyalansa babu wanda ya tsira sai shi, shima dai ya rasa hannunsa guda, daga nan ne muka ɗakkosa mukazo dashi nan yay jiyya har ALLAH yasa ya warke, yaso komawa jajenin saboda ya saba sosai dacan, yakan faɗa mana zama a cikin gari shi baya masa daɗi, to adai taƙaice har zuwa yanzu da nake muku magana bamu barsa ya komaba, dan yama tsufa kawai jarumtace irin ta mutan da da ALLAH ya azurta da sani.........” isowar ƙaura da wani soji wajen ya saka Lieutenant General Mubarak Kambawa yin shiru, ya zubama waje ɗaya ido. Duk juyawa su Jay sukai suma suna kallon inda yake kallo, tsohone mai shekaru da yawa wanda basusan adadiba, babu wani gashi a jikinsa da zaka iya gani baƙi sai wanda UBANGIJI ya ɓoye. Yana sanye cikin kayan fatu, ya ɗaura fatar zaki a ƙasa yay riga data damisa wadda take tamkar ƴar shara, dan kai kawai aka fitar sai gefe da gefe akai mata maɗauri, yana rataye da jikkar fatar kura a wuyansa, sai dai bashi da hannu guda. Daka gansa kaga ƙauran kuwa. Yanda sukaga lieut.. General na gaidashi cikin girmamawa yasa suma suka gaidashi da girmamawa, dan koba komai ya wuce uba sai dai kaka. Dattijo ƙaura dake amsa musu idanunsa kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa bayayi, ya saki murmushi yana kauda idonsa daga kallon Jay ɗin. babu wanda kallon bai bama mamakiba hatta lieut.. General, dan haka yaja Ƙaura gefe guda.
       “Baba nasan baƙwa kallon banza, akwai matsalane? Dan na lura ka kafe yaron can da kallo har  murmushin ka ya kasa ɓoyuwa” murmushin yanzuma Ƙaura ya sakeyi tare da juyawa ya kalli Jay da Jabeer ke taimakawa yana saka bullet proof jacket a jikinsa kafin ya sake maidowa ga lieut.. General yace, “Shima sojan kune yallaɓai?”. Lieut... General yace, “A'a baba, sune nai maka bayani ai zakuyi tafiyar”. “Oh na shafa'ane wlhy, kasan ƙwaƙwalwar yanzu sai a hankali takan manta wasu abubuwan”. L. General dai murmushi yayi kawai, dan yasan wanene baba ƙaura, yakuma tabbata akwai abinda ya gani tattare da Jawaad, amma tunda yake wani kakkaucewa bayason ya sanine, dan haka ya ture maganar Jawaad gefe ya shiga masa bayani akan taimakon da sukeso yayma su Jay saboda sanin sirrin jajen da yayi. Sunɗan tattauna sannan suka dawo inda su Jay da suka gama shiryawa tsaf suke harda Bilkisu data fito bisa umarnin Jawaad bayan yaje da kansa har cikin mota ya taimaka mata ta saka bullet proof jacket ɗin itama suka dawo wajen tanata sinne kai saboda kunya, yayinda Rose ta shaƙa tai fam da haushi tamkar zata f

ashe.
        A bazata sukaji Ƙaura yace, “Yarinya yaya sunanki?”. Duk juyowa sukai su duka suna kallonsa dason ganin dawa yake tsakanin bily da Rose?. Sai sukaga da Bilkisu yake dan itace gab dashi kuma itace ta gaidashi tunda sai yanzu ta ganshi, gashi ta kafeshi da idanu tamkar maison tuna inda ta sanshi. Tambayar da yaymatane yasata dawowa hayyacinta, tace, “Bilkisu”. “Balqeesa! mai gadon zinari kenan” baba ƙaura ya faɗa yana wani murmushi tamkar yanda yay ɗazun akan Jay. Jawaad zaiyi magana L. General ya riƙe masa hannu yana girgiza kai alamar kar yace komai. Komawa yay ya tsaya badan yasoba danshi al'amarin tsohon ya fara bashi haushi. Sarai ƙaura yaga abinda Jawaad yayi, danta wutsiyar ido yake kallon duk miotsinsa, amma sai yay kamar hankalinsa akan Bilkisun kawai yake. Har Lieut.. General ya basu Umarnin shiga Jirgin Ƙaura ya sake jefama Bily tambaya. “Balqeesa! yaya sunan mahaifinki?”.  Yanzunkam ba Jawaad kaɗaiba kowama abin yazo masa wuya banda Rose, ahaka zasuyi tafiyar da wannan mutumin mai shegen tambaya da bin ƙwaƙwƙwafin mutum?. A miskile Bilkisu ta amsa masa da “Adam makaho”. Duk ido suka zubama Ƙaura suji mizaice, amma sai ya ɗauke kansama gaba ɗaya kamar bashi yay tambayar aka bama amsa ba.
    Ganin yanda yay ɗin yasa L.. General cemusu su shiga. Haka duk suka fara shiga suna ƙunƙuni da hararar baba ƙaura daketa murmushin da basusan inda ya dosaba. Jay ya matsa ya kama hannun Bily dake tsaye tamkar wadda aka tsayar, ajiyar zuciya ta sauke dan tayi nisane a tuno mafarkinta na daren jiya wanda ayanzu ta tuna acan taga fuska wannan tsohon. Baba Ƙaura dake biye da bayansu ya ƙure hanunsu dake cikin na juna da ido yana murmushinsa har yanzu, sai da suka taka ƙafarsu zasu hau jirgin yace, “Sara da sassaƙa baya hana gamji tohowa”. Daga Jawaad har Bilkisu sunji furucin baba ƙaura sarai, harma Jay ya juyo zaiyi magana sai kuma ya fasa.
       “Karka damu yaro faɗi duk abinda ke ranka, nima nawa nake faɗa dan bana bari a ciki ta kasheni. Ƙwai cikin ƙaya na gani ajiyar ALLAH”. Karan farko da kalaman tsohon suka saka gaban Jawaad faɗuwa, kalmar Ƙwai cikin ƙaya idan bai mantaba ya taɓa jinta a cikin mafarkinsa mai Sarauniyar da har yau basan inda ya dosaba. Har suka zauna idonsa bai daina kallon baba ƙaura ba da yay biris da kowa tamkar bashi ya gama takale-takalen maganaba yanzun.
         Gaba ɗayansu duk da addu'a a bakinsu har jirgin ya ɗaga sararin subahana.
 
      Duk da wannan shine karona na farko a hawa jirgi abin mamaki babu wani tsoro ko ƙauyanci tattare dani, kodan helicopter ne oho, nasan dai lokacin da zamuyi sama na riƙo hanun wanda bansan wanene ba sai da muka dai-daita na fahimci Rose ce, aiko tacika tayi fam da haushi, har nai mamaki da bata turo hannunaba, sai daga baya na fahimci Boss dake facing ɗinmu ne yaymata shamaki da hakan dan duk abinda zamuyi zai iya gani.
         Haka mukai ninƙaya a tafiya idanuna sun gaza daina kallon tsoho mai kayan fatu, har jirginmu ya samu sauka. Jejine maiban mamaki da al'ajabi, bakajin komai sai kukan tsuntsaye da mabanbanta sauti da zuciya bazata iya hasaso minene ba. Kowa kagani hankalinsa a tashe yake da wannan jeji amma banda tsohon nan. Haka muka firfito kowa na karanta addu'ar da tazo masa a baki, wani irin makeken ruwane kwance ƙar-ƙar har haskensa na ɗaukar idanu a gabanmu, Oga Aliyu yace, “Ikon ALLAH, amma a taswurar jejin nan bamuga wannan ruwanba sam, ko masu zanen taswirar basu san da shi bane?”. “Wlhy Aliyu wannan shine abinda nake ayyanawa a raina yanzun” Jabeer ya faɗa murya a harɗe.
           Tsohon nan ya bimu da kallo ɗaya bayan ɗaya sai kuma ya girgiza kansa da faɗin, “Wannan ruwa zuwayyene ba zaunanne ba”. “Kamar ya?”. Suka kusan haɗa baki wajen tambaya.
     Ƙin basu amsa yay, saima kallonsa daya maido gareni, “Ɗiyata Balqeesa bismillah saka ƙafarki a ruwannan” sosai naji gabana ya faɗi, idanuna suka cika da ƙwalla, ganin babu wanda yay magana a cikinsu yasa na ɗaga ƙafa zan nufi ruwan. Caraf aka riƙomin hannu, basai na juyaba ƙamshinsa kawai ya bani amsar shine, murya a kausashe yace, “Baba ya zaka turata shiga wannan ruwan maikama

da ruwan tsafi?”. Mu duka kallonsa mukai, Jawaad da shima maganar ta suɓuce masane kawai babu shiri yay saurin dafe kai da faɗin, “Sorry, ina nufin ruwan daga gani yanada ban al'ajab, tunda nake ban taɓa ganin ruwa mai ƙyawunsa ba da ɗaukar ido irin haka”. Murmushi mai sauti mukaga Baba ƙaura yayi, cikin ɗauke kai daga garemu yace, “Dole saimun ƙetarashi zamu kai inda muke hari, anmana katanga da shine domin mu juya, kuma wlhy kunji na rantse wannan yarinyar kaɗaice zata ƙetarashi kafin mu sami hanya, dan tanada taurari masu ƙarfin gaske”. A take duk suka zubamin ido, ni kaina wata irin jarumta nakeji da dakiyar zuciya da bansan yaushe na sameta ba. Hafiz yace, “Kana nufin har kai da akai iƙirarin kasan ciki da bai ɗin jejin?”. “Yaro, baiwa kowa da irin tasa, wani har yabar duniya babu mai fahimtar tasa, wani ko harmutsin duniya ke bayyana tasa, waniko nasarorinsane, wani ko hatsabibancinsa ne, wannan idanun da kake gani ALLAH kaɗai yasan ajiyar da yay a cikinsu”.
       Kai kawai duk muka shiga jinjina masa, boss yace, “Inhar zata ƙetara ruwannan sai dai tare dani”. Murmushi baba ƙaura yay kawai ya nuna mana hanya.
   Sai da mukaje gab da ruwan yace, “ku tabbatar a tare ƙafafunku suka sauka, kuma da bismillah”. Umarninsa mukabi mukai yanda yace, ni dai harda ƙarama wata addu'ar nayi, wani irin azabar sanyi ne mai keta fata da tsoka ya shiga cikin jijiyoyi ya gauraye da jini ne ya riskemu lokacin da ƙafafunmu dake cikin takalma suka sauka cikin ruwan, atake muka fara rawar ɗari dagani har boss, maimakon muyi ƙoƙarin komawa baya sai naji ya fisgi hannuna mun sake saka ƙafafunmu na haggu suma, abin mamaki sai gamu mun jiƙe da zufa sharkaf dalilin zafin daya riskemu kuma a yanzu tamkar ana tafasamu a garwashi, zafin bashida maraba da wani zafi dana taɓaji kwanakin baya da bazan tuna dalilin jinsa ba. Sake fusgata Boss yay muka cigaba da tafiya dukda azabar dake ratsa jikkunanmu. Wani irin mahaukacin ihu ne mai ƙarfin gaske ta karaɗe jejin, gaba ɗaya ruwan da muke tsakkiya ya koma jini, da farko na tsorata, amma addu'ar da naji Boss ya kamo yanayi tuni nima na karɓa masa ina mamuƙeshi. Ɗaf ruwan ya ɗauke lokaci ɗaya tare da kukan, sai ƙarar iskar guguwa mai ƙarfin gaske da mukeji tana tinkaromu, a take muka daina ganin komai saboda guguwar tai mana ruf. Wata muguwar shaƙa naji anmin a wuya, nai ƙoƙarin fincike hannuna cikin na boss danna ƙwaci kaina amma hakan ya gagara, ashe shima shaƙesan akai,  da hannuna na haggu na shiga laluben abinda ya shaƙenin, dan idona a rufe yake saboda guguwar data lulluɓemu. Ɗumbin mamaki ya kamani jin jikin mutumne da gaske, jikin da ya taɓa riskata a cikin wasu darare da sam na mantasu a cikin ƙwaƙwalwata, cikin amincin UBANGIJI Hannuna ya sauka a nasa wuyan shima, na damƙi sarƙar dake wuyan na fincika da masifar ƙarfin dana san daga UBANGIJINA ne kawai. A take jejin yay wata irin girgiza tare da wasu irin gigitattun ƙararraki ta mabanbanta muryoyi. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba.

           Yanda aka shaƙe bilkisu haka shima Jawaad aka shaƙesa, sai dai shi saɓanin itane, maimakon ya samu nasarar fisgar sarƙar wuya sai yasamu nasarar ciran wani abu dake hanun wanda ya shaƙesan, danshi hanunsa yay ƙoƙarin cirewa daga wuyansa da aka shaƙe.
      Da sauri yay azamar taro Bilkisu jikinsa ya rungumeta da ƙyau yana cigaba da karanto addu'a, isakar data lulluɓesu ta fara washewa a hankali har suka bayyana filin subahana, babu wancan ruwan da suka riska a farko, hasalima wajen tsaunine.
        Su Hafiz da suka samu kariyar UBANGIJI daga wannan guguwa da basusan daga ina ta ɓulloba duk suka miƙe daga rumfar da Baba ƙaura yay musu da jikinsa. Dan ranƙwafe yake kansu ya baza hannayensa tamkar maison tattaro wani abu.
      Gaba ɗayansu kansu Jay dake durƙushe a ƙasa kan Bily bisa cinyarsa yana girgizata sukai, baba ƙaura yay murmushi yana mai ɗaga hannayensa sama da zuba kirari wa UBANGIJIN AL'ARSHI, idanunsa na zubda hawaye, sai yanzune ya fahimci ƙaddarar zamansa cikin gari na tsahon shekara biyu bayan halaka masa iyalinsa da akai, UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama, sarkin da baya

zalinci ya kuma haramtashi a tsakaninmu, sai da ya kammala miƙa godiyarsa ga ALLAH kafin ya nufi su Jay da duk suke kan Bilkisu kowa na ƙoƙarin faɗama Jawaad taimakon da zai bata kozata farfaɗo, masu cewa ya murza hannu nayi, masu cewa ya murza ƙafa nayi, masu jajen ina za'a samu ruwa a zuba mata nayi. Shikuma sai faman girgizata yake yana faɗin ainahin sunanta na yanka wato BILKEESU!!.
     Murmushi baba ƙaura yayi tare da katsesu baki ɗaya, “Bazata taɓa farfaɗowa a hakaba ko zaku kwana kanta”. Gaba ɗayansu shi suka juyo suna kallo, sai dai babu wanda ya iya cewa wani abu a cikinsu. Shima bai sake faɗar komanba, sai nuna musu su koma gefe da yay da hannunsa, babu musu sukabi umarninsa aka barshi daga shi sai su Jawaad ɗin. durƙusawa yay kusa da Jawaad murya ƙasa-ƙasa yace, “Iskar numfashinka ce kawai zai taimaki nata dawowa gangar jikinta ɗan saurayi, ka ɗaura bakinka kan nata ka zuƙo insha ALLAHU zata farfaɗo”.
        A hankali Jawaad ya lumshe idanunsa tare da ranƙwafawa bisa fiskar Bilkisu ya aza bakinsa saman tattausan lips ɗinta, numfashin dake fita ta hancinsa yana sauka akan fuskarta, ya tura harshensa cikin bakinta dake ɗan buɗe kaɗan ya shiga hura mata iska tare da  shanye yawun bakinta babu ko ƙyankyami, wani irin numfashi mai ƙarfi ta kawo tare da ƙanƙame hanunsa dake cikin nata ta damƙe laɓɓansa itama. Da sauri Baba Ƙaura yace ta farfaɗo?”. Yay maganar da bubbuga bayan Jawaad ƙaɗan.
         Jay ya janye bakinsa dake cikin na Bilkisu da ƙyar yana sauke numfargashi da sauri-sauri, wani irin tsitstsinkewa jinin jikinsa keyi, baba ƙaura yay murmushi tare da ɗora hanunsa akan na Jawaad da ƙofofin gashi duk suka buɗe. A hankali Jay ya buɗe lumsassun idanunsa yana kallon Baba ƙaura kamar yanda itama Bilkisu ta buɗe nata a hankali akan fuskar Jawaad. “Da bakajin sha'awarta a matsayin mata ko?”. Gaban Jawaad ya faɗi yana mai al'ajabin ya akai tsohon ya sani?. Murmushi baba ƙaura yay yana ɗauke kansa ya maida ga bilkisu, “Yanda bakajin sha'awarta itama haka batajin komai game dakai dama kowane namiji a duniya, sai wanda sukaso yimata wasa da hankali a kansa, ada ita kaɗaice da wannan matsalar, amma dalilin aurenku kaima hakan ta shafeka, sun riga sinci buri mai tsanani a kanta, wanda hakan bamai yuwuwa bane a garesu cikin sauki sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan, akwai al'amari mai sarƙaƙiyar gaske tsakaninku, sai dai inaji a jikina komai yana gab da warwarewa dalilin abu uku wanda nima ALLAH bai bani ikon saniba, ka jajurce wajen tsananta bincike zaka fahimci komai da yake komai dangane daku. Bazan ɓoye makaba, wanda kukazo nema a wannan Jejin baya raye, sai dai jininsa shine jini mafi haɗari dazai zamarma duk wanda tsiyayar dashi tauraruwa mai wutsiya, ki adana wannan tsintuwar ta hannunki tamkar yanda kika adana ta farko, sai dai zasu cigaba da tsorataki domin bibiyar kayansu dan kin raunanasu sosai, duk randa ta uku tazo gareki suka zama huɗu dana hannun mijinki komai zai buɗe”. Baba ƙaura ya miƙe yana ɗan murmushi da binsu da kallo tamkar yanda suma suke kallonsa har Bilkisu, ya sake cewa “ƘWI CIKIN ƘAYA AJIYAR ALLAH”. ya juya ya barsu.
        Da ƙyar Jawaad ya iya maida kallonsa ga Bilkisu, ya kamo hannunta dake rumtse ya buɗe a cikin nashi, Wurine baƙi mai girma tamkar wanda ta taɓa tsinta a ɗakinta. Zumbur ta tashi zaune jikinta har yana rawa, dan sai yanzu ta fargafa a jikin boss take kwance. Wasu hawaye masu zafi suka fara zirara a kumatunta suna sauka bisa fuskarta.
         Shidai Jay kallonta kawai yakeyi,  ɓullowar su baba ƙaura ya sashi faɗin. “Shiii!!!”  yana mai ɗora yatsansa akan bakinsa. Saurin kallon inda yake kallo tayi itama, su Jabeer ne ɗau da mutum bisa buzu. Atare suka miƙe ita da Jay harsu Hafiz suka iso inda suke suka ajiye gawar Gimba da duk fuskarsa tai kaca-kaca da raunuka tamkar yakushi. Durƙushewa Jawaad ya koma yayi gaban gawar, hanunsa na rawa yakai kan fuskar Gimba ya shafa, idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar yin jazurr, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Su Hafiz sai sharar ƙwalla sukeyi suma.
     Ɗagowa Jay yay yana kallonsu, dagani kasan shima kukan zuci yakeyi, ya maida duba

nsa ga Baba ƙaura dake riƙe da farin ƙyalle a hannu. Baba ƙaura ya girgiza masa kai da lumshe ido alamar ban haƙuri. Juyawa yay yana kallon Bilkisu dake  kusa dashi tsaye tana kuka iya ƙarfinta. Ya dafe goshinsa yana murzashi da ƙarfin gaske, soyake yayi hawaye tamkar yanda suma sukeyi kozaiji daɗi, sai dai sunƙi fitowa, sai zuciyarsa dake wani irin zafi mai azabartar da gangar jiki da ƙwaƙwalwa. Miƙewa yay daga gaban gawar ya kamo Bilkisu dake tsaye. Jikinsa ta faɗa tare da sake fashewa da kuka mai huda zuciyar mai sauraro.
        Baba ƙaura sai basu baki yake da nuna musu muhimmancin ƙaddara da karɓarta a duk yanda tazoma bawa, sannan mutuwa alƙawarin ALLAH ce ga kowane mai rai dake doron ƙasa, shi da ya tafi ba gaggawa yayba, mu da muke raye bamuyi jinkiriba, ALLAH yay alƙawarin kwanansa ya ƙare, waɗanda suka kashesha sanadi suka zama, da sunyi haƙuri ma aranar zai bar musu duniyar dama. Da waɗan nan kalaman hikima Baba ƙaura ya shawo kansu har suka ɗakko ledan da sojoji kan saka gawa kafin a kaita inda ya dace idan har basu da damar binneta a wajen yaƙi. Haka aka saka gawar Gimba da cikin hikimar UBANGIJI babu abinda tayi tamkar yanzune ya rasu.
        Bily bata iya shiga cikin jirginba saida taimakon Jawaad, yanzunkam kusa dashi ya zaunar da ita, dan shima yana buƙatar jin ɗuminta.
      Dukda halin da ake ciki hakan ba ƙaramin zafi yayma Rose ba, har cewa Jay take munafuki a cikin zuciya, a ganinta shida yake gudun taɓa macen daba matarsa ba yau wane gulma ta kaisa mamuƙar wannan yarinyar kuma? Taja tsaki a cikin ranta tana ɗauke kai, ta tsani yarinyarnan wlhy, kuma itama tana gab da salwantar mata da rayuwa inhar bata fita rayuwar boss na, yarinya ƙarama sai baƙin karuwanci?.
        Wannan zantuntuka sune Rose taita tattaunawa da zuciyarta har jirginsu mai saukar angulu ya sauka a garin su gimba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login