Showing 126001 words to 129000 words out of 261165 words

Chapter 43 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1113

suka kawo matansu gidan Ummah babba, su kuma suka yada zango a masaukin da su Hafiz suka tanada musu.
        Ango kuwa yau alhamis yana zuwa office Sir Ahmad ya korosa akan ya tafi sun bashi hutu, karya ƙara ganin ƙafarsa sai nan da sati biyu ciff, shidai murmushi kawai yayi baice komaiba. Ƴan station ɗinsu ma dai zuwa yanzu sunsan boss ya auri Bilkisu, masu gulmar dama soyayya yake da ita sai bakuna suka buɗe aka samu nayi, yayinda masu goyama Rose baya suketa angizata da maganganun ɓatanci ga Bilkisu da Jay ɗin kansa, masoyansu na ƙwarai kuwa murna suke tayasu da ganin sun dace da juna.

    
MASARAUTA

           Tunda garin ALLAH ya waye an tashine cikin shirye-shiryen kamu da aka haɗashi da Hausa fulani day baki ɗaya, su Ummie, Nazifa, Zuhrah, Rebecca, Amina, Nabeelah, duk suna can suma tare dasu Amaturrahman, abin birgewa kuma duk ƙawayensu na Boarding skull sai da su Ummie suka gayyatosu suma duk sunata isowa masarauta a safiyar yau, hakan saiya saka Bilkisu hawaye da tuno iyayenta, inama da ransu wannan rana tazo mata, inama suna jingine da ita har zuwa yau ɗinta, ina firdausin ta, ƙawar amana ko tace ƴar uwa rabin jiki, kullum addu'arta ALLAH ya

sadata da Firdausi da iyayenta kafin tabar duniya.

  Tunda safe dama mai ƙunshi tazo muka shige cikin ɗaki daga ni sai ita ta shiga zanamin na nutsuwa, zuwa azhar ya bushe yay shar kamar ka cinye dan baƙi da jaa aka ɗaɗara mani, kasancewar fashin salla nike dama sai kawai aka shigamin gyaran kai a nan gida dan Gimbiya nada dukkan kayan gyaran kai a gida da takema kanta, bayan an kammala nai wanka lokacin ƙarfe kusan uku.
     Kasancewar ba sallah zanyi ba sai ban damu da kwalliyar da ake shirin tsaramin ba, ni kaina basai an faɗaba nasan ina tsaruwa dai-dai gwargwadon iko, duk da ba'aimin kwalliyar dana canja kamanni baneba amma nayi ƙyau fiye da zato. Bayan an kammala kwalliyar aka shiryani cikin atamfa lass ƴar ubansu datasha stones work ɗan gaske, sket da riga akai da suka fidda ainahin tsarin jikina dukda basu matseni tsam ba, sundai zaunamin a jiki ɗas har ni kaina ban gaji da kallon kaina ba. An min naɗin ɗan kwali mai tsari aka ƙawata adon nawa da sauran kayan ƙawata kwalliya irinsu sarƙa da sauransu. Ƙamshina kam ai har hawa kan mutane yakeyi, daka ganni kaga cikakkaiyar bahaushiya jinin Fulani, tabbas a yau na sake yarda da babu mummuna a duniya sai wanda ya munana kansa, idan har zaka tashi ka gyara kanka tofa ka wuce a kiraka mai muni, dama can rashin gata da kulawane suka dadushe sihirtaccen ƙyawuna mai cike da kwarjini.
      Taron iya matane, dan acikin masarauta ma za'a yisa, su Ummah da danginsu duk sun iso masarautar, hakama danginna na ɓangaren Uwa su Inna Zainabu dasu Momy harda Aamilah, Aunty Shahudah dai ban gantaba, ƴan gidansu Boss ma kam inada tabbacin ƙwai da kwarkwata ne a wajen nan. Babu abinda da dai za'a cema UBANGIJI sai godiya a wannan al'amari, amma tabbas Bilkisu tazo da farin jini mai ban mamaki da tarin alkairi. Iyayen ƙawayenta su Ummie, matansu Aliyu, abokan aikinsu ƴan station ɗinsu, ƙawayenta na makaranta harma da waɗanda sukazo dalilin wane da wane duk suna a wajen. Sai ƙarfe huɗu da rabi Gimbiya Sarauniyar gagara badau Munayatul-muna ta fito riƙe da hannun amarya Bilkisu mai gadon zinari.
     Ai a take wajen ya ɗauki ƙannan magana musamman ma ƴan gidansu Jawaad da ada suke ɗaukar Bilkisu ba komaiba saboda yanda su Momy ke munanata da ƙasƙantar da ita a garesu. Wasu sunɗan santa sama-sama wasuko sai a yau suke ganinta.
       Ganin yanda ɗunbin mutane suka taru danni sai kawai naji hawaye sun zubomin a kumatu, Zuhrah ce ta duƙa gabana inda ya kasance mazaunina ta shareminsu da handkherchief tana murmushi, “Haba amarsu ai lokacin kuka baiyiba kinji, sai gobe idan ALLAH ya kaimu kina kusa da Boss, da sun zubo ya lashe kayansa”. ta ƙare maganar da kashemin ido. Hararta nayi ban iya cewa komaiba, sai dai fa maganar datai sai da naji gabana yaɗan faɗi, dana tuna kuma ma ina period saina ɗanji sauƙi a raina.
           Ba'a ɓata lokaci wajen fara gudanar da abinda ya tara mutane ba, komai kuma a nutse babu wata hayaniya, koda aka fara kiɗan ƙwarya ma a nutse ƴammata da matan aurenma masu jini a jika keyin rawa, ina tsakkiya nikam anata zubamin liƙi, Anum na liƙe dani wai tana gwagwaɗamin wai itama idan ta tashi aure zamuje Saudiyya da masu kiɗan su mat. Murmushi kawai nayi mata dan ta bani dariya.
        komai ya tafi cikin burgewa da kwanciyar hankali, kafin a koma yin hotuna da kowa ke fatan yi da amarya da gimbiyar gagara badau. Zuwa magriba aka tashi.
    Ni dai tunma kafin magriban muka bar wajen tare da Ummu da akoda yaushe tana kusa dani idanunta akan kowa da zai iya raɓata. Dan tace itafa bata wani yarda da kowa dake wajenba.
        
    __________________

    A ɓangaren su Jay suma sunacan suna nasu shagalin, sai dai su nasu sai bayan sallar isha'i suka fara, suma iyasune maza zalla a wajen abokansa, su Aryaan duk suna can dan kuwa dai sa'annine, sudai su Abdur-raheem, dasu Anuwar basu jeba kasancewar su Jay yayunsune wannan shigar ba tasu bace, suna buƙatar sakewa kuma, sunama can gidan Mami Munubiya suna shan shaftarsu hankali kwance.

      Dauriya kawai Jay keyi, dan kansa ciwo yake masa matsanancin ciwo ma kuwa, amma kasancewar yasan duk ɗunbin mutanennan dan shi

suka taru sai ya daure har zuwa goma na dare kafin ya gudu ɗakin da zai kwana a hotel ɗin ya barsu, ko wanka baiyiba dan bai jima da yiba, kayansa kawai ya zame ya faɗa saman gadon ya kwanta yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, cikin ransa ko mamakin Bilkisu ya keyi, ƙaramar yarinya da ita sai shegen jan aji da miskilanci, tunda ta tafi bata nemsaba, ta dawo ma haka. Wani ɓangare na zuciyarsa yace, ‘Kaida haƙƙin sanin lafiyarta ke a kanka ka nemeta ne?’. Kansa ya dafe kawai da lumshe idanu, kafin ya buɗe a hankali ya jawo wayarsa dan tunawa da saƙwanin da yasa a turo masa. 
       Kasancewar datarsa a buɗe take duk sunma buɗe kansu da kansu, harda videos. Ya sauki wani lallausan murmushi maiban mamaki daya sakani tunanin wai shin mi yake kallo hakane?................✍

Jiya kun haɗan zafi yasin, waɗanda ban ɗaga kiransu ba suyi haƙuri man kaina ne ya tsiyaye😂🚴🏼.

BARKA DA JUMA'A.

Musha weekend lafiya

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭😭🙏🏻.[12/25/2020, 6:15 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 38

.................Tinda su gimbiya munaya suka isa gidan,banda yabawa da tsari,da kuma kokarin da jay yayi kan gidan,babu ajinda suke! sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta  daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a  itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
        A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
      Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
     Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
        Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
         Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”.  Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
          Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
             Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.

        A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
        Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

          Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita tace a bani wayar.  Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji, kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”. Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya nai mata mukai sallama.

            Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda haka Ummu ta tsara.
          Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
       Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho, dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
          Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.

     Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah su barni anan, hakan kuma na

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi, dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
     Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
     Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss, murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa tsakanin...........
          Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da ɗakuna biyu a ciki.
      Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login