Showing 27001 words to 30000 words out of 142169 words

Chapter 10 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

437

sallah ba, Nadiya bata kawo komi ba kawai sai tayi tunanin ko bata yin sallar ne.
Sai can an gama komi bayan isha'i ta sameta a dakinta tana ta jera sallah a gaggauce, kai idan ka gani hankalinka ma baya iya dauka. Ta sanyata a gaba zata fara mata nasiha, aikuwa ta wanketa tas da zagi har da la'adar mari, babu shiri ta bar mata dakin.

Ba a jima da yin hakan ba kuma ta sake komawa gidan hutu. Wannan zuwan da tayi ta fara fahimtar sauyi a tattare da Irfaan. Shekarunta sun shiga na goma sha biyar, don haka halittunta sun fara bayyana sosai da sosai. Ga yanayin kayanta dake gidan Madam din duk kananu ne, sau tari haka take yini da hijabi a jikinta saboda kayan suna fitar mata da surarta sosai.

Ranar da dare suna tare da Irfan a falon Madam ne, littafine a hannunta yana fada mata kalmomin turanci da fassararsu tana rubutawa. Bata san ya aka yi ya karasa kusa da ita ba tunda akwai tazara a tsakaninsu, sai da taji shi ya kama gefen hijabinta yana kokarin cirewa.

Ta ja baya da sauri tana watsa mishi wani irin kallo, fuska a hade take tambayarshi, "meye haka kake yi?!"
Wani sakaren murmushi ya saki, "ni? Me nake yi? Taimaka miki zanyi ki dan ji sanyin jikinki haka nan, naga alamun hijabin tana takura miki!"

Ta hade fuska, "to bana so! Kada kuma ka sake yi mun hakan gaskiya, bana so!!"
Ta fara hada kayanta jiki na rawa zata bar mishi wajen. Dama zancen gaskiya ta fara takura da irin kallon kurillar da yake mata, da wasu maganganun banza da yake mata wadanda take nuna kamar bata ji ba. Kawai fita zata yi daga harkarshi tunda abin haka ne.

Tana ta wannan sakar zucin bata san ya aka yi ba sai jinta tayi a jikin mutum. Ya kama fuskarta yana kokarin hade bakinsu. Kici-kici suka fara kokowa dashi, ala dole sai ya cire mata hijabi.
Ta kuwa kware baki ta kwala ihu. Sai ga mutanen gidan sun fito a sukwane, Madam Zahra da wata bakuwa da tayi abokiyarta, sai Nanny din Safiya da Safiyar biye da ita hannu rike da kayan wasa.

Suka samesu sunyi cirgai-cirgai a tsaye, Madam ta tafa hannu, tace, "ke lafiyarki kike yiwa mutane wannan ihu?"

Tana haki da shessheka ta zayyane mata abinda ya faru. Tana rufe baki Irfan yayi caraf ya fara korawa Madam nashi bayanin, "A'ah Mommy! Ni fa wasa ne nake mata, nace ta cire hijabinta ta sha iska, shikenan kawai sai ta hau kwala ihu. Ni ko tabata ma fa ban yi ba!"

Nadiya baki ta saki cike da mamaki tana kallonshi. Madam kuwa tsaki ta saki tana hararar Nadiya, "dalilin da yasa kike kwalawa mutane wannan ihun kenan? Wallahi nayi zaton ma macijine kika gani ko wani abu! Ni kaina so nawa ina fada miki ki daina yawo da hijabi a gida sai kace wata matar Limami amma kin ki? Shi ba Yayane a wajenki ba? Ashe bai isa ya yanke hukunci a kanki ki bi ba? To daga yau na hanaki sanya hijabin a cikin gida. Allah kuma yasa ki kara sanyawa kiga abinda zai biyo baya! Stupid yarinya kawai ta tsoratani a banza!"

Kawar tata ta kalleta da mamaki, tace, "haba ke kuwa Madam. Irin haka tsayawa kake yi ai ka bincika komi a sannu musamman tunda ta fito ta fadi ga abinda ya faru, ba wai ki bita da fada ba. Musamman ma ni ban ga laifinta ba. Tunda kema kin san gidanki gidane na jama'a, bai dace ma wadanda ba muharramanki ba su dinga kara-kaina a sashenki ba!"

Aikuwa sai Madam din ta juya kanta, ta rufe ido ta zuba mata rashin mutunci. Daga karshe ma tace ta fita ta bar mata gida tunda ita munafuka ce.

Jiki a sanyaye Nadiya ta ja kafafu ta koma dakinta.

Kwana tayi tana canki-cankar ko dai ta tafi gida ne. To tasan da tayi maganar Madam zata ce saboda abinda ya faru jiya ne.

Ta ja jiki ta shiga wanka a bandakin dake hade da dakinta. Tana tsakiyar shafa mai bayan ta fito daga wankan kawai sai ji tayi an turo kofa, ta juya haka sai suka hada ido da Irfan. Yayi tsaye yana mata wani kallo na yan iska da murmushi akan fuskarshi, yace, "Baby Nadiya, Mommy tace ki fito mu karya!"
Ya kuma yi tsaye yana kallonta ido cikin ido kamar dai ba zuwa yayi ya sameta ba daga ita sai tawul daure a jikinta ba.

Kasa mishi magana tayi har ya gama kare mata kallo ya juya ya tafi. Ta hadiye wani tukukin bacin rai a cikin ranta, zuciya na mata suya cike da takaici da bacin rai. Ji take kamar ta yi me. Haka dai ta shirya ta fita wajen karin.
Suna gama karyawa Madam ta suri jaka, dama a shiryenta take cikin wani pencil skirt dinkin atamfa da rigar bubu wadda ta tsaya mata a gwiwa, dankwali kawai ta kashewa dauri ta fita haka nan sangam-sangam wai taje ta gano shagunanta. Ta bar Safiya a wajen mai rainonta saboda sun samu hutun Prenursery da ake kaita, Madam kuwa dama bata cika daukarta ba.

Su uku kadai suka yi karin, daga ita sai Madam da Safiya. Bata ga Irfan ba tun bayan shiga dakinta din da yayi. Don haka sai ta dan saki jikinta, suka zauna ita da Habiba da Safiya suna wasa har Safiyar tayi barci, Habiba ta dauketa don taje ta kwantar da ita.

Ta shiga kicin ta bude firjin ta dauki ruwa zata sha. Kashedin Madam da taji na sanya hijabi yasa ta saka gown mai dan matsakaicin gyale, amma da yake gown din ba mai fadi bace, sai ta bi shape din jikinta ta zauna sosai. Kawai ji tayi an kama mata mazaunanta da hannu biyu ana murzawa, ta zabura tayi tsalle bakinta dauke da bismillah, ruwan da take sha duk ya bi ya zube a tsakiyar kicin din, robar ruwan ma tayi nata wajen.

Irfan ya bi bayanta yana kokarin rungumota, sai ga su suna kokawa da juna.
Ya kamo kirjinta yana damka, yana sakar mata wasu maganganu da tsabar rikicewar data yi ta kasa fahimtar ko me yake cewa ma. Da Allah Ya bata sa'a ta daga kafa ta harbeshi a tsakanin cimyoyinshi, sai ta kwasa tayi dakinta a guje ta barshi anan a kasar kicin a kwance yana malelekuwa dafe da mararshi.

12.

Bata tsaya dogon tunani ba , ta hade kan kayanta ta kimtsa. Babu wanda ya sani, ta fita ta nufi tashar mota sai Kaduna. Kudaden da suke a hannunta ba masu yawa bane, da kyar da magiya direban ya iya yarda ya kaita Kaduna da cewar in sun je za ta cika mishi. Suna isa kuwa da bayan la'asar ta samu mai mashin shima ta mishi magiya ya ara mata kudi ta biya direban, shi kuma yana kaita gida ta shiga ta amsa wajen Mama ta kai mishi.

Mama ta kama baki ganin Nadiyar duk a firgice, daga ganinta kasan tafiyar ba ta dadi bace. Saboda ba haka ta saba dawowa ba. Yawanci idan zata dawo direba ake hadota dashi, ya kaita ya juya. Sannan zata je musu da tsaraba iri-iri da aike cike da bayan booth din mota. Amma ranar sai gata zikal dinta. Sai bata ce mata komi ba.

Sai data bari ta nutsu, ta tada kwanan abinci guda, yadda take cin abincin ma hannu baka hannu kwarya, sai kayi tunanin ko ta kwana ne bata ci abinci ba.
Mama ta zauna cike da sigar jan zance, take tambayarta yau ko direban dake kaita baya nan ne? Sai lokacin ta dargwaje mata da kuka. Tayi zaune tana kallonta cike da mamaki har tayi ya isheta, kafin ta fede mata zani har bindi.
Abin kam bai yiwa Mama dadi ba sam, ta kuma so ta kira Madam din ta mata zancen ba haka ya dace ba, kuma ba haka ake yi ba, sai Nadiyar ta dakatar da ita. Don kuwa tasan ko tayi mata maganar ma ba lallai hakan ya haifar da d'a mai ido ba.

Dare yana yi ta lallaba dakinsu inda suke zaune ita da Haulatu da Zainab, dukansu kusan sa'anninta ne, sai Basira kanwar Zainab, mahaifiyarsu daya, da Abban ya aurota a can Mallawa, sai da Basirar ta girma ma ta tasa kafin a ka maidasu gidan.

Gidan ba wani mai fadi bane, ga su kansu dakunan ba wasu masu yawa bane. A da ma gabadaya yaran gidan daga mazan har matan a daki daya suke kwana. Sai da Yaya Saminu yaje gidan watarana yaga hakan, sannan ya yiwa Abban maganar rashin dacewar hakan. Sannan ne fa shi Yaya Saminu din yayi kokari aka fitar da dakin soro inda mazan suka koma can da zama. Su kuma matan aka bar musu wannan.

Washagari kuwa tunda safe sai ga wayar Madam. Fada ta dinga yi tun karfinta, ita fa ala dole Nadiya ta mata rashin kirki ta gudo daga gidanta akan abinda bai taka kara ya karya ba. Tace tunda kuma abin haka ne, to kada ta kara je mata gida, ta mata iyaka. Ita kuwa ta doki cinya tace ta fi nono fari.

Ta cigaba da zuwa makaranta abinta. Lokaci zuwa lokaci Mama ta kan bata kudin mota taje Maiduguri idan aka yi hutu, ta musu yan kwanaki kafin ta koma. A haka sai aka wayi gari ta kwashi shekaru da dama basu hadu da Madam ba.
Ita da kanta ta nemeta lokacin data shiga sakandare, suka cigaba da gaisawa. Amma bata kara zuwa Jos ba. Sai dai idan sun hadu a Maiduguri, ko kuma idan wani abu ya kaita nan Kaduna ta je inda take su gaisa.

Tun tana yar kankanuwarta babu abinda yake burgeta irin girke-girke da kuma baking. Wannan dalilin yasa koda taje cike jamb ta cike Home Economics kawai.

Duk gidansu ita kadai ce mace wadda tayi karatu wanda ya wuce na sakandare. To ba ma kowa yake zuwa makarantar ba sai yan kananun yara. Ita kanta da ba don jajircewarta ba da naci, da babu inda karatun nata zai je. Suna ss2 ita da su Haulatu aka musu aure ita da Zainab, ita Haulat mijin a Bauchi yake, Zainab kuma a garin mahaifiyarsu ta samu mijin auren. Da Abban ma cewa yayi itama Nadiyar ta fitar da mijin, a lokacin ita ko tsayuwa da samarin ma bata yi ba. To wane miji zata fitar?
A kuma lokacin ne Anty Jamila da Yayanta suka nemesu da kansu, suka je gidan suka ga juna.

Ganin matakin da karatun boko ya kai Anty Jamila da Yayanta, ya kara karfafa mata gwiwar kara tsayawa tayi karatu. Ita Anty Jamilar tana koyarwa a BUK ne, mijinta kuma yana aiki da In Land Revenue anan Kano. Yayinda Yayanta Abdur-Razak yake aiki da kamfanin Riyadh Airline, a can kuma yake da zama shi da iyalanshi.
Zuwan Anty Jamila gidansu shi ya kara gyara musu rayuwar gidansu nesa ba kusa ba. Kusan hidimar auren su Haulatu duk su suka yi ta, da Yaya Saminu da Yaya AbdulHadi. Shi kanshi Abbansu sai da suka saya mishi motar hawa saboda mashin dinshi ya samu matsala a lokacin. Kuma Anty Jamilar ce ta hana Abbansu hada auren Nadiya da wani dan gidan abokinshi da yaso a sanya ranar auren ranar da aka daura auren su Haulatu. Ita kuma Basira da yake ta fitar da nata mijin, sai aka sanya nata auren.

A kuma cikin yan shekarun ne ta fara fahimtar wai sautukan da take jiyowa a dakin Babansu cikin dare na menene? Ta sha jin su Haulatu suna tambayar Mama wai cikin dare suna jin wasu abubuwa na fita daga dakin Babansu na menene? Sai Mamar tace musu tari ne, ko kila bashi da lafiya ne, ko wani abu mai kamar da haka. Suna yarda a da din, amma kasancewarsu yara masu yawan shige-shigen abokai da kuma yawan karance-karance, yasa kafin a kai ko'ina ma suka fahimci zancen ba haka yake ba.

Ta taba jin Zainab tana fadawa Haulatu ai wannan sautin fa idan Ma'aurata suna tarawa ne suke yinsu. Tafi-tafiya kuma da shekarunsu suka kara tasawa, watarana sai taji Haulatu tana cewa ita fa wannan sauti yana daga cikin dalilan da yasa take so tayi aure, wai itama taje taji me ake ji.
Tayi tsaki a lokacin tana jinjina kai, don kuwa ita bata ga abin burgewa da sha'awa anan ba.

Mahaifinta ne fa. Ace kuma duk lokacin da zai kebance da matanshi sai kowa na gidan ya sani? Ina dalili. Musamman da a dan takin ta samu labarin wai a can bayan unguwarsu wata yarinya tayi cikin shege, da aka matsa mata da tambaya tace wai ai iyayenta ta gani suna yi, shine suke gwadawa da wani yaro dan unguwarsu sai wannan tsautsayi kuma ya auku.

Ga shi tun suna ma kokarin bari sai cikin dare idan sawu ya daga, har abin ya kai sun ma daina damuwa. Musamman bayan auren su Haulatu da suka hade a daki daya da su Maryam ga su Fatima, zaka ga gari ya waye tangaran amma suna yi kowa na jiyosu. Kuma mace ta fito tsakar gida tana juya mazaunai kai a sama ta shiga dakinta babu kunya, gabadaya rayuwar gidan sai ta gama fita a ranta.

Shi yasa tana samu da Allah Ya bata sa'a Anty Jamila da kanta ta bada aka cika mata jamb. WAEC dinta da NECO duka sunyi kyau, sai ga shi DAG sun bata admission.
Ta samu Abbanta da murnarta ta fada mishi, sai ya karkace baki yace sai taje wadda ta daure mata wani gu din ta biya mata kudin makarantar, don kuwa shi dai ba da yawunshi ba. Sai jikinta yayi sanyi. Idan da abinda ta tsana a rayuwarta to bai wuce roko ba. Kwata-kwata bata son shi, abubuwa da dama idan ba karfinta suka fi ba, bata cika daga baki ta roki ayi mata abu ba. Mace ce ita mai kokarin tsayawa a kan kafafunta, tun tana yar yarinyarta kuwa. Don kuwa koda tana gida a lokacin, tana yin kananun sana'o'i na hannu, kuma da su take toshe kofofin matsaloli idan sun taso mata.

Ta samu waya ta kira Madam ta sanar mata da yadda suka yi. Tace ta kwantar da hankalinta, in dai karatu ne ta mata alkawarin har sai ta gaji da yi. Sai hankalinta ya nutsa.

Kuma kamar yadda tayi alkawarin, haka aka yi. Ita ta biya mata kudin registration, ta bada aka mata komi daya kamata har gidan da suka zauna da Aramide ita ta kama musu, ta mata provision da duk wani abu daya kamata. Da lokacin tafiyarta kuma yayi, ta sa aka bude mata account wanda take sanya mata kudin da zata dinga bukata a duk karshen wata.

To cikin ikon Allah ma da yake ko a makarantar bata yi kasa a gwiwa ba, aiki ta dinga yi a kananun restaurants da kuma amsar kwangilar birthday cakes da sauransu, sai ya zamana bata zauna haka nan ba hannu babu komi.
Madam ita ta tsaye mata akan abinda ya shafi registration da accommodation, sannan lokaci zuwa lokaci ta kan aika mata na provision da kuma na batarwa. Anty Jamila ma da Yaya Saminu suna yin wannan kokarin. Don haka abin sai yaje mata da sauki sosai fiye da yadda tayi tsammani.

Tana makarantar Mama take bata labarin Anty Jamila da Yaya AbdulHadi sun sayi wani gida anan bayansu za a hade da gidan da suke ciki don a kara fadada shi. Abu na farko da tayi shine ta tuntubi Yaya Saminu da zancen ya taimaka a samu a cire mata dakinta daban. Saboda dama hada daki da su Fatima da sauran yaran gidan ya fara damunta. Dauke-dauke ake mata, sai daya zamana ma kayanta gabadaya a dakin Mama suke don bata isa tace an taba mata kaya ba sai su Salame su yi ruwa da tsaki su ce sharri take yiwa yaransu.

To kuma sai ware mata dakin ma ya zama dama ba ayi hakan ba. Aka ware dakin kusa dana Abbansu, gashi dan karami wanda ya kasa kwashe tarkacen kayanta.
Bugu da kari kuma da Salame ta fahimci alakarsu tana takurata, sai ta kara kaimin bada himma. Sau tari Nadiya tasan da gayya take wasu abubuwan, ko in suna hira da Abban a dakinshi kaji tana ta kara sauti da bude murya duk dai don Nadiya ta ji ta din. Abin ya bata takaici watarana ya bata dariya. Ta ga ita dai ba kishiyarta ba, balle tace idan tayi hakan zata ji haushinta ko kishinta.

Bata sani ba ko wannan dalilin ne yasa gabadaya taji maza basa kanta? Ta kasa tsayawa ta saurari wani namiji da kunne mai kyau balle har ta iya bashi damar aikawa gidansu. Saboda gabadaya ji take yi an cire mata son auren a cikin ranta. Bata tashi taga mu'amalar aure mai kyau a inda take ba a tsakanin ma'aurata. Bata ga ana mutunta mace a inda ta tashi ba. Bata ga ana bada hakkin aure yadda yakamata ba. Sai ta hada duka mazan tayi musu daurin goro. A wajenta su dukansu halinsu daya. A gareta kam, su duka mazan basu da bambanci. Ita kam da za a barta ma, tana da tabbacin zata iya dawwama a haka ba tare da tayi auren ba.
Wannan kenan!!



&&&&&

Sun gama hada abin da za ayi kari dashi, ta koma dakinta tayi wanka ta shirya cikin wata Arabian gown purple color mai adon duwatsu. Ta nannade gashinta a cikin ribbon, a ranta tana raya yakamata ta samu ta wanke kanta ko kuma ayi mata kitso.

Tana fita falo ta samu Dada da Aysha a zaune suna hira. Sai karin bakuwar fuska data gani. Daga ganinta kasan yar gida ce saboda tana yanayi da su Aysha amma bata tunanin ta san fuskar.

Ta zauna a gefen Dada ta gaisheta, kafin ta mayar da hankalinta kan bakuwar itama ta gaidata. Ta amsa mata fuskarta dauke da murmushi.
Lokaci guda ta fahimci irin mutanen nan ne da murmushi baya barin fuskarsu. Doguwa ce sambal, don zata iya fin Nadiyar a tsayi. Sai dai hasken fatarta bai kai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na Nadiya din yawa ba duk da dai itama tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login