Showing 132001 words to 135000 words out of 142169 words

Chapter 45 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

455

aika mata. Sun samu damar hayewa kan karagar mulki su ma.
So take yi Nadiya ta amsa tayin gayyatarta, tana so ta nadata shugabar gidauniyar tallafawa mata da yara ta Nigeria baki daya.
Akwai manyan mutane da dama da suke harin kujerar, wadanda suke da matakin ilimi wanda ya fi na Nadiya din nesa ba kusa ba. Sai dai basu da zarra da tsayawa tsayin daka akan abu kamar na Nadiya din.

Hajiya Badariyya tana sane da cewa duk wani taimako da zai fita daga ofishin First Lady din, Nadiya ce a????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? bayanshi. Don kuwa ita ce take ba Shukurah shawarar ga abinda yakamata ayi, ita take binciko da zakulo mutanen da suke taimakawa. A takaice dai Shukurah ce ke da alkalamin zartar da hukunci, amma Nadiya ita ce bango kuma mai shan wahalar aikin.
Tace me zai hana ta fito domin a taka rawar da ita? Kuma tayi aikin a inda ya dace, mutane zasu sani kuma su gode mata?
Abinda tace mata a lokacin shine a isar mata da sakon godiyar wannan karramawa da aka mata, kuma a sanar da Her Excellency, tayi hakuri ta bata lokaci tayi shawara da Maigidanta wanda yayi tafiya a halin yanzu. Da zarar ya dawo sun tattauna, zasu sanar da su shawarar da suka yanke. Suna cikin yin sallama ne Shukurah din ta dawo.

Ta tsaya suka gaisa da bakuwar, Nadiya kuma ta rakata zuwa bakin kofa inda security dake tsaye ya bude mata kofar, suka sake yin sallama.

Ta koma falon ta sameta tana ciro takardu daga jakarta, ta zauna a gefenta tana daukar Abul da daya daga cikin ma'aikatan gidan dake kula da yaran ta kai mata.

Shukurah ta mika mata wata takarda, tace, "wannan dazu aka turota ofishinmu. Sai dai ina tunanin kina bukatar ki gani ko menene ta kunsa."

Ta karbi takardar tana dubawa cikin daurewar kai. Mamaki yasa ta hangame baki tana kara duban takardar.
Request ne Madam ta aika da kanta ba sako ba, wani wawakeken waje ne da yake fuskantar Arena dinta take so ta saya. Taje ofishin sayar da filaye an ce mata waje na Gwamnati ne, ita kuma filin take so sosai domin ta hadeshi da nata ta kara fadada wajen. Duk da cewa ta fada musu ko ita wacece da kuma matsayinta a wajen Mai Girma Gwamna, amma sun kekashe kasa sun ce basu san wannan zance ba. Idan ba sanya hannun Gwamna suka gani ba ba fa zasu bata damar sayen fili ba.

Shine ta tura wannan request wajen Shukurah. Dama tun farkon cin zaben sai data yiwa Nadiya maganar wannan fili tace tana so ya zamana aikinta na farko da zata yi idan ta shiga ofis, to ta mallaka mata wannan filin. Bayan da suka yanke shawarar Shukurah ce zata shiga ofis ba karamin fada da bacin rai Madam ta haddasawa Nadiya ba.
Kiranta tayi musamman ta zazzageta fiye da kima, akan me zata ce ba zata karbi matsayin First Lady ba? Kuma akan wane dalili zata ki shiga ofis?
"...kenan kina nufin duk wahalar da na sha zata tashi ta tafi ne a banza ko? Duk irin kudaden dana kashe don ki kai matsayin da nake son ki kai a banza kike so su tafi kenan? To wallahi kinji na rantse miki, kinyi kadan Nadiya! Kada ma ki kuskura ki bari wata rana tazo in nemi wani abu daga Gwamnatin Kaduna in samu wani tsaiko, na rantse da Allah sai kin ga irin bacin rai wanda baki taba ganin irinshi ba a duniyar nan. Sakaryar yarinya kawai, banda tsabar bakin ciki da son kai ma irin naki, ana kokarin a rufa miki asiri amma ke baki sani ba ko? Tunda kin ga yanzu ke kin zama matar Gwamna wato ni zaki ajiyeni a gefe kenan, ga yar iska ko?!..."
Ire-iren fadan nata kenan data dinga yi, ya zamana tun Nadiya din tana kokarin bata hakuri don su rabu lafiya, har ta tsaya kawai tana sauraron fadan nata har ta gama ta kashe wayar tana jan tsaki kala-kala. Ta dafe kai tana girgiza kanta hawaye na mata ambaliya a fuska. Zagin da Madam din ta mata don taba rai ya taba ranta, amma gorin data dinga mata ne yafi dagula mata lissafi.
Ya zata ce wai don ta shiga cikin daula shine take so tayi mata tawaye? Bayan dama can ba ita ta daga baki tace tana so ba? Hasalima tun farko ba kushewa ta dinga yi ba saboda gudun faruwar irin hakan? Tana kuma sane ta ki karbar shiga ofis din, ta koma ta bayan fage tana taimakawa masu bukata. Saboda har da tsoron irin abin da Madam zata iya daukowa ne ta dora mata. To gashi tun ba aje ko'ina ba ma kuwa ta dauko musu gingimemen aikin da yafi dala girma, babu kuma gammon dorawa.

Ita yanzu me ya kamata tayi? Damka wannan fili a hannun Madam daidai yake da daukarwa kansu wani jan aiki ba karami ba, dama tuni har abokan gaba sun fara cece-ku-kuce akan shi. Tun a tsohuwar Gwamnati ake rigimar abinda yakamata ayi dashi saboda manyan mutane da dama suna kai mishi hari, wasu na so su yi hotel wasu na so su gina wani wajen shakatawar, Gwamnatin ta sanya hannu da cewa zata gina asibitin yara masu lalurar shan Inna da kuma mata masu lalurar yoyon fitsari ne. Wannan abu bai yiwa mutane da dama dadi ba.

To kuma har Gwamnatin ta sauka basu kai ga fara yin aikin ba, duk da cewa an fitar da budget din komi da komi. Kuma cikin yarjejeniyar da suka yi da tsohon Gwamna din kafin ya marawa Habibu baya a matsayin magaji, har da alkawarin zai dora daga inda Gwamnan ya tsaya ne. Kuma yanzu kawai sai su zo su damkawa Madam shi saboda tana takamar ta taya shi kamfen? Ita bata yin abu don Allah ne? Kuma duk alfarmar da itama aka yi mata a baya bata isheta ba sai ta dora da neman wani abu dai?
Ta duba dai ta ko'ina taga babu ta yadda ma za ayi su aikata wannan danyen aiki. Don haka ta daga kai ta kalli Shukurah, tace mata ta manta da maganar kawai. Koda ma an sake turawa da maganar tace Maigirma Gwamna ya hana.

Itama Shukurah din sanin rashin yiwuwar hakan yasa bata ja maganar da tsayi ba, ta tashi ta wuce dakinta a ranta tana cewa 'sun fi kusa!'
Yanzu kam ta daina tsanar Nadiya, duk da cewa dai har lokacin basu gama sakin jiki da juna ba can-can, amma taimakon da Nadiya take mata wajen zakulo ayyukan alkhairi suna yiwa mutane da sunan ita Shukurah din da ofishinta ne suke hakan, ya matukar sayo mata mutunci da daraja a idonta sosai. Tunda itama yanzu mutane sun santa sosai, ana ta yaba mata da sanya alkhairi. Don haka take kara lallaba Nadiya din tana binta a hankali.


53.


Nadiya ta tattare takardu ta kaisu can cikin kaya ta musu boyo na musamman.
Har Maigidan ya dawo daga tafiyarshi bata sanar dashi halin da ake ciki ba.
Ta sanya dai amintacciyar security dinta, Hannatu Bishir, ta fara duba mata possible wajaje a kusa da inda Madam din take wanda za a iya saya a madadin waccan din.

Madam da bata san abinda yake faruwa ba kuwa tana can tana ta kara hawa da kumbura cikin bacin rai.
Ta sake kiran Nadiya a karo na biyu ta mata tatas, tace mata wallahi idan bata yi wasa ba akan wannan maganar sai ta yafewa duniya ita tunda ita ta zaba akan ta. Banda tsabar butulci da cin mutunci irin nata, har ita zata yiwa haka? Ta hana a bata fili? Ita Madam?!

Nadiya tayi mata bayani iyaka bakin kokarinta, amma Madam din ta ki ta saurareta balle ta fahimta. Da ta fada mata cewa ta sanya a duba mata wani filin, sai ta katseta ta hanyar cewa, "idan ba wanda nake so zaku bani ba, ku rike abinku bana so! Nadiya ni ai na fi karfin in nemi alfarma a wajenki wallahi, sai dai in baki umarni. Tunda kuma kin rainani, kije zaki gani. In dai nice, zaki zo har inda nake ki sameni!"
Ta katse wayar da wannan kalamai nata masu razana kwalwa.

Ita kanta Nadiya sai data dimauce da jin hakan, tayi ta kiran Madam din hankali a tashe amma ta ki dagawa.
Ta rasa yadda zata yi da ranta, kuka ta zauna tana yi wiwi, Madam tana nema ta mata baki akan abinda bai taka-kara-ya-karya ba.
Tana so ta yiwa Habib magana amma tana jin kunyar da irin idanun da zai kalli Madam, saboda shi mutum ne strict akan duk wani abu daya taba mulkinshi, baya cutar da talakawa kamar yadda baya saba alkawari. Tana da tabbacin akan Madam ba zai canza ra'ayi ba. Yadda kuma yake ganinta da mutunci da girmamawa, bai kamata ta zubar mata dasu ba wajenshi. Don haka tayi ta jinjina abin a cikin ranta ita kadai kwana da kwanaki.

Kusan kwana biyar da yin zancen kenan, ta tashi da safe wata bakuwar lamba tana danna mata kira a wayarta. Tana da wata wayar ta musamman don amsa kiran daya danganci wani lamari na siyasarsu, amma wannan ta wareta ne musamman saboda yan uwa, kuma su kadai suke kira.

Tayi kamar ba zata daga ba, sai kuma ta daga tana cewa watakila emergency ne. Tayi sallama tare da daga kiran, sai ta jiyo muryar Madam kasa-kasa tana amsawa kamar wata barauniya, ta gyara zama tana gaidata cikin taraddadin yau kuma da me taje mata?
"Mommy, ina kwana, kun tashi lafiya?"
Madam tayi wata irin doguwar atishawa yadda kasan wani dan tsako ne zai fita daga hancin nata, ta ja hanci alamun mura take yi, tace mata, "Nadiya, ki taimakeni ki rufa min asiri, ki zo ki ceceni don Allah!"

Nadiya ta tashi tsaye a sukwane, hannu dafe da kirji tana tambayarta, "Subhanallahi, Mommy lafiya?"
Don kuwa daga yadda taji muryar Madam din ta tabbata akwai matsala. Matar da duka-duka kwanaki biyar kenan data gama ihu da bugun kirjin babu wanda ya isa ta nemi taimako a wajenshi, ita ce take kuka da neman taimakon kuma? Ai da babbar magana ba ma karama ba!

Madam sai ta fashe da kuka, tace, "kin ganni nan kwanana biyar a cell yau Nadiya, azaba kawai ake gana min ban ma san me na aikata ba wallahi. Don Allah ku zo ku ceceni. Sun hanani kiran kowa balle a san halin da nake ciki, kuma sun ki fada min laifin nawa. Yanzu ma wata constable ce na samu ta bani aron wayarta da kyar da magiya..."

Nadiya ta fara rarumar gyale cikin dimaucewa, Madam a cell kuma? Wannan tashin hankali da me yayi kama?!
Tace mata, "kina ina ne? Kin san inda aka kaiki?"
Tace, "muna Lagos. Ina gama waya dake ranar nan dama ina kan hanyar airport ne zan je Lagos, ina dira suka kamani a filin jirgin, amma ban san ina suka kaini ba. Sun amshe kayana da komi nawa a can, kuma sun hana ni magana da kowa!"

Kafin Nadiya ta sake yi mata wata tambayar, taji wani yana magana cikin hargowa. Kafin kuma taji kit! An kashe wayar.

Fadar irin tashin hankalin data shiga ma ba karami bane ba a wannan rana.
Duk wanda ya kamata ta kira, ta kira, amma babu labarin Madam babu alamarta.
Sai da aka kwana biyu, shima da taimakon wani mai bincike na musamman da Babangida ya ba aikin, sannan suka samo labarin inda take.

Washegari Nadiya din da Anty Hauwa da taje Kaduna din jiya, suka dauki hanyar Lagos. Tare da Lauya da securities biyu da Gwamna ya hadasu da su.
Tafiya suka yi cikin badda kama, saboda sun san idan yan adawa suka samu labarin halin da suke ciki ko kuma yan jarida, ba karamin matsala za iya samu ba.

A Area C Command Police Station aka riketa, wanda yake a Herbert Macaulay Way, dake a Sabo, Yaba anan Lagos din.
Suna zuwa suka samu ganin DPO da taimakon Lauyan da suka je dashi.
Bayan sun zauna a gabanshi, suka sanar da shi abinda ya kaisu da kuma tambayar me yasa aka kamata ba tare da takardar data bada umarnin a kamata din ba da kuma laifukan da ake tuhumarta dasu? (wato warrant?)

Ya gyara zama yace musu su kansu dokar daga sama taje musu, directly daga ofishin Brigadier General Abdussalam Oluwalu (CON) ta je. Suna zarginta ne da safarar miyagun kwayoyi. Duk da ba a kamata da kayan ba kai tsaye, amma an kama mutane da dama wadanda suke distributing kwayoyin anan cikin Lagos da Kaduna, wadanda duk suka bada tabbacin kayan daga hannunta suka fita. Sannan an samu waje na musamman a cikin Arena dinta ta Kaduna, inda suka samu stock-stock na kwayoyi, wadanda zasu yi kimanin miliyoyin kudi.

Nadiya ta dafe kanta daya fara wata irin sarawa tana jin kamar zai balle. Tashin hankali wanda ba a sa maka rana! Neman kudin Madam din kuma yanzu har ya fara kaucewa ka'ida?
Suka bukaci son ganin Madam din amma yace ina, a dokar da aka basu na su ci gaba da riketa ne kawai har zuwa lokacin da za a shiga kotu da ita. Daga nan kuma sai dai zancen yanke hukunci. Suka kada, suka raya, yace ai kaf cikin ofishin nan babu wanda ya isa yayi jayayya da ofishin Brigadier Janar.
Hankalinsu duk ya tashi ya dugunzuma, lallai fa gaba da gabanta, wai aljani ya taka wuta.

Anty Hauwa ta fita tana kiraye-kirayen waya don a samu wanda zai iya yi musu wannan taimakon. Itama sai ta lalubo Habib ta sanar da shi.

Ba su samu ganin Madam ba sai can da yamma tare da taimakon Habibun wanda ya san wani dake tare da Brigadier din, aka yi musu izinin ganawa da ita.

Yadda suka ganta abin tausayi kamar su zubar mata da hawaye. An kulleta a wani dan akurkin daki mai dan banzan duhu da sauro, ga doyi. Bugunta kawai ake yi kamar jaka, babu dare babu rana.
Tayi wani irin baki na ban mamaki, fuska duk sai tarin kuraje. Kayan jikinta sunyi raga-raga, daga ganinta fatar jikinta bata ga ruwa ba tun lokacin da aka kai ta wajen.

Tana ganinsu ta rushe da kuka, su kansu matsar hawayen suke yi cike da tausayinta daya cika musu rai.
Wadda ta rakata wajen nasu ta cire mata ankwar da aka sanya mata, ta dangwarar da ita a wajen, ta juya ta tafi tana kara nanata musu mintuna sha biyar kadai aka bata.

Suna zama akan kujera Anty Hauwa ta matsa tana tambayarta, "Zahra'u, me ya hadoki da Brigadier ne haka har zai sanya a daureki? Me ya kaiki?"
Ta kai hannu ta share hawayen fuskarta. Tace, "wallahi bani da gami da shi ko kadan, amma akwai matarshi da muke huldar kasuwanci da ita. Tana son shiga cikin kasuwancina ne ni kuma na hanata, nace itama taje tayi nata. Shine ta bi min ta karkashin kasa, ta sanya aka kamani akan laifin da ban san na aikata ba!"

Nadiya ta gyara zama da kyau tana kallonta, don taga alamun kamar ma bata san me suke zarginta da shi ba, tace, "to ina zancen miyagun kwayoyi kuma da ake yi? Akan hakane fa aka kamaki."
Ta dafe baki, "kwayoyi kuma? Ni?!"
Tace, "baki san zancen ba? Saboda sun ce an kama wasu zasu yi safarar kwayoyin nade cikin lemukan energy drinks daga Kaduna zuwa nan Lagos din don har sun samu sun shigo da shi ma. Kuma da aka tambayesu suka ce daga Arena dinki suka daukosu, sannan anyi bincike a wajen an samu kwayoyi da dama wadanda za su iya cin miliyoyin kudi!"

Madam ta dora hannu aka ta saki wani irin ihun kuka kamar wadda zata hau bori. Sai kuma ta hau zage-zage kamar wadda ta fita daga hayyacinta. "Ni za su yiwa haka? Ni za a ciwa mutunci a min zamba cikin aminci? To wallahi-Tallahi ba zan yarda ba, duk wanda yake shirin wulakantani wallahi sai na ga bayanshi!"

Anty Hauwa da Nadiya suka kalleta cikin alamun tambaya, Anty tace, "su wa kenan? Me kike fada ne? Don kuwa dolene sai kin fada mana abinda yake faruwa mun fahimta, sannan ne za mu iya taimakonki Zahra'u."

Ta share hanci tana jan majina, kafin ta fara zuba musu bayanin yadda Mijinta Alhaji Shehu Balogun, ya yaudareta ta hanyar hada hannu da ita wajen bude Arena dinta lokacin da take neman masu sanya hannun jari, shi kuma yayi amfani da hakan wajen yin yarjejeniya da ita kan cewa zai dinga sana'ar sabon lemun energy drinks daya fara yi a wajen, amma kuma sai da yayi mata alkawarin cewa ba zai dinga gudanar da cinikayyar kwayoyi da yake yi ba a can, ya kuma ce ya yarda. Ashe yaudararta yake yi, zuwa lokacin data fahimci cewa yana sayar da kwayoyine kawai da sunan energy drinks, kuma a cikin arena din nata yake yin hakan ba a ko'ina ba, harkar tasu ta riga tayi nisa.

Da tayi confronting dinshi sai yace mata ai ba wai jimawa zai yi ba, kawai zai dinga sayarwa dinne na dan lokaci kafin ya samu zaunannen waje. Amma har aka dauki lokaci mai tsayi ba ya da niyar fasawa, hasalima sai kara yawan kayan suke yi. Ita kuma da taji tsoron kada ta kai maganar wajen yan sanda, yan sandanmu na Najeriya da basa tsoron Allah, tunda da yawansu ma manyan yan sandan duk abokan cinikayyarshi ne, sai ta tuntubi aminiyarta wato Hajiya Zainab Oluwatolu, matar Brigadier General Oluwatolu, kuma distant cousin din Alhaji Shehu din ce wadda dama can ta sanadinta ne suka hadu da shi. Sannan kuma yana dan jin maganarta.
Akan ta taimaka mata, ta bata shawarar yadda za ayi su rabu da shi Shehu Balogun din salin-alin ba tare da hukuma ta shiga zancen ba. Saboda in hukuma ta shiga sunanta zai baci, kuma zasu iya cin ta tarar kudade da yawa.

Ita kuma budar bakinta sai ce mata tayi, me zai hana ta mata hanyar da itama zata shiga cikin wannan sana'a?
Tace mata, "ke baki da wayo ne? Baki san babu abinda ke kawo kudade manya-manya a wannan zamani wanda ya kai wannan harkar ba? To ni idan ba zaki shiga ayi da ke ba, ki hadani da su ni ina so in shiga. Na miki alkawarin babu abinda zai samu wajen sana'arki, not even the President will dare to touch you. Saboda Ubangidanshi na yanzu wanda ya tsaya mishi, Kawu na ne!"

Madam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login