Showing 75001 words to 78000 words out of 142169 words

Chapter 26 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

454

tayi abinda za a ce tayi. Amma duk da haka sai da Shukurah din ta gogeta da kafadarta.
Wai kuma maimakon ta amsa gaisuwar da Nadiyar take mata, sai ta watsa mata wani sakaren kallo. Murya cike da hargagi take ce mata, "ke ni kike bangajewa?!"

Ita abin ma sai yaso ya bata dariya, ta nuna kanta da dan allinta, "ni kuma? To ki yi hakuri. Ina ga ban kula bane."
Maimakon amsar tata ta gamsheta kuma sai ta kara tunzurata, ta wani kama kugu tana nuna Nadiyar da dan yatsanta, "an ki ayi hakurin kinji? Bani son iskanci da rashin mutunci fa kina ji na? Wallahi ba karamin aikina bane in sameki anan inyi ta jibga, kuma wallahi na daki banza! Sakarai kawai wadda miji yake gudunta tana manne mai!"

Daga farko abubuwan da take fadi dariya ma suka dinga ba Nadiya saboda taga rigima ce take nema da ita haka kawai ba tare da ta yi mata wani abu ba. Amma yanzu kuma da taji abinda ta fadi, sai taji wani irin bacin rai ya ziyarceta. Wato ashe dai duk abinda ke faruwa ana kula da su?

Ta gyara tsayuwarta da kyau don ma kada Shukurah din taga alamar raini a tattare da ita, tace, "ba da kashi dai kam wannan kin ci uwar raini wallahi, don kaf duniya ban ga wanda ya isa ya daga hannu ya dakeni ba yace wai ya ci a bilis! Wallahi ba a haifeshi ba tukun. Shi kuwa miji da kike wani gori a kanshi da babatu da daga jijiyar wuya, ban sa a ka ba, don haka bai dameni ba. Ke din da ya dama har kike sanyawa rayuwar wasu ido, sai kije kiyi ta fama dashi!"

Kawai sai ta nufi Nadiya gadan-gadan, wai wallahi sai ta bata kashin tsiya taga shegen daya tsaye mata.
Ita kuwa ta kara gyara tsayuwarta tana jiran ko-ta-kwana. Don kuwa tasan a bugu dai, tsaf zata make Shukurah din ta barta anan. Ko a zubi da dirin halitta, ta ninka Shukurah din nesa ba kusa ba. Haka take yar yaloluwa da ita babu kiba sai tsayi, sai dai itama tana da nata zubi da dirin daidai-wa-daida. Kana ganinta kuma kasan ka ga yar gidan hutu. Irin sangartattun yaran masu kudin nan ne da suka tashi cikin kudi da wadata, suka kuma raina kurar data kwaso sauran mutane.

Gyaran muryar Ummah ne ya katse musu shagalin da suke yi, ta tsaya daga saman steps din bene tana kallonsu, "ku kuma lafiyarku, me yake faruwa ne?"

Nadiya ta daga baki za ta amsa mata, kawai sai Shukurah ta fashe da kuka. Ta ruga sama wajen Ummah ta rungumeta, wai fada mata take yi Nadiya ce ta bangajeta, kuma ma take cewa sai ta bata kashin tsiya.
Nadiya tayi saurin cewa, "wallahi Ummah karya take yi! Ita ce fa ta so bangajeni ma na matsa, amma kuma duk da hakan shine ta dinga zagina har da ce min banza."

Ummah ta kalleta fuska a hade, "wato zaman lafiya ne ba ki so ko? Haka kawai zata kama bangajeki da fadin maganganu ba tare da kin mata wani abu ba? Ai in bera da sata, to daddawa da warinta! Ke dai kika san me kika mata!"

Wasu hawayen takaici suka cika mata ido. Wannan fa shine a dakeka a hanaka kukan. Tace, "wallahi, wallahi Ummah ni ban san me na mata ba!"
Tace, "to tunda baki san me kika mata ba, da kika ga haka ba sai ki bata hakuri ba? Shukurah dai ta girmeki, anan gidan kuma matsayin babba take a wajenki. Dole ki bata girmanta yadda yakamata. Saboda haka nan gaba, kada ki kuskura inji abu makamancin hakan ya faru a tsakaninku. Kina ji na ko?"
Hawayen nata suka karasa dirowa kan kumatunta. Abu goma da ashirin ya mata rubdugu. Dannewa dai tayi ta gyada mata kai. Ta wuce ta fita daga wajen nasu jiki a sanyaye ko karyawa bata yi ba. Wannan tsagwaron rashin adalci har ina? Ga gaskiya kiri-kiri amma a danne don kawai ba a son mutum?
Haka ta koma sashenta tana ta wannan mitar a ranta. Sai da yunwa ta isheta ne sannan ta hada custard ta sha.

Da dare da kamar ba zata koma sashen na Ummah ba saboda har zuwa lokacin abinda ya faru dazun bata mata rai yake yi idan ta tuna. Ta dai daure ba don ranta ya so ba, ta tafi.
Tana kallon Shukurah akan dinning da ta sha kwalliya kamar zata je wajen gasar kyau, ita ala dole ga mai girki a ranar, ta ki gaisheta. Saboda dai ta mata magana ne ai har take binta da sharri ko? To babu kari. Nan gaba sai ta ga da abinda kuma zata kakaba mata wani abin.

Ta zuba abinci ta zauna tana ci, da wayarta a hannu tana chatting.
Data gama sai ta koma falo ta zauna tana kallo don ta rage dare. Ta shafa kan Ammar da yake faman yin assignment. Daga karshe ma sai ta buge da taya shi tunda taga yana kakarewa a wani wajen.

A haka gogan ya shiga ya samesu. Kai tsaye shima dinning din ya wuce ya zauna. Bata san ya aka yi ba, bayan wani dogon lokaci da ta kai kallonta wajen da yake, sai ta tsinci Shukurah kusan zaune akan cinyarshi. Tana ta wani kissa da abubuwa. Tayi saurin dauke kanta ta mayar gefe daya, tana kokarin dauke hankalin Ammar daga kallonsu don bata ga tsari a abin nasu ba.

Zuwa can kuma sai Shukurah din ta taso, ta wuceta tana wani taku dai-daya. Da taje dai-dai inda take sai ta juya tana ce mishi, "baby ina jiranka fa!" Ta karasa fita, takalmin kafarta yana 'kwaras-kwaras!' akan tiles din falon.
Ta kalli gogan ta ga ko waiwayenta bai yi ba, sai kawai ta girgiza kai abinta. Ta cigaba da taya Ammar da zanen gida da motoci da yake yi, don kuwa abin na Shukurah bai wani dadata da kasa ba.

Da ya gama cin abincin fita yayi daga sashen. Ita kam tana nan har sai da Ummah ta sauko kasa, ta gama cin abincinta ba tare da wata magana ta hadasu da ita ba bayan gaisuwar da ta mata.
Ammar da zai yi barci ta rakashi dakinshi da kanta, anan saman yake kusa da na Hajiya Ummah. Ta taimaka mishi ya wanke baki tare da canza kayan barci, ta mishi addu'ar kwanciya barci kafin ta sauka kasa. Ta yiwa Ummah sai da safe, ta koma sashenta itama tayi shirin barci.

Har karfe sha daya ta gota, lokacin shima ya gama tura wasu takardu can Kasar Indiya game da wani project da yake yi akan siyasa da kuma tsarkin muhalli, yana kokarin kwanciya sai ga kiran Ummah ya shiga wayarshi.
Wai tambayarshi take yi 'me ya hanashi zuwa dakin Shukurah?'

Yayi jim na wani lokaci mai dan tsayi. Ba ya so maganganu irin haka na ratsawa a tsakaninsu, shi yasa tun farko bai tsaya yin wani dogon jayayya da ita ba a game da hukuncin data zartar a tsakaninshi da Nadiya.
Yana da alkunya da girmamawa ga duk wani wanda zai mu'amalanta. Personal zance irin wannan ba da kowa yake yi ba.
Dalili kenan da yasa bai taba daga baki ya kai mata karar Shukurah ba, wadda ta maida kwanciyar aure da shi wani kasuwanci na musamman. Ba ta ba shi hakkinshi har sai ta san da akwai wani abu da zata samu a gareshi ko wata bukatarta ta kanta da zata biya sannan. Wai a hakanma kuma ba koda yaushe ba, ba kuma zama za tayi ta tarairayeshi ba kamar yadda yake so. Sai dai kawai ta mishi kim, ya gama kidanshi da rawarshi ya kara gaba. A hakanma sa'a ce ya ci idan bata ce mishi ta gaji ba ta tashi ta barshi.

Duk wannan abu, bai taba daga baki koda sau daya ya furtawa Hajiya Ummah ko wani na kusa da shi ba. Saboda a ganinshi zance irin haka yayi tsauri da nauyi a tsakaninshi da Ummah din. Amma sai yaga kuma ita tana nuna hakan ba komi bane a wajenta.

Duk da hakan, sai ya daga baki yace, "Ummah ita me ya hanata zuwa?"
Tace, "ka rufe min baki anan, bana son wata doguwar magana. Iyalinka ce ai, ita in bata zo inda kake ba kai sai ka je gareta ai. Ko baka san mata yan lallashi bane? Tana ganin yadda kayi mata kishiya dama ai dole ta ja baya da kai, kai ne zaka yi kokari har ka ja ta a jikinka!"
Yana so ya tambayeta, 'to ita kuma Nadiya ba Iyalina bace kenan da kike umartata da in gujeta?!' amma sai ya kame bakinshi.
Yace mata, "kiyi hakuri Ummah. Zan tafi yanzu in shaa Allah."
Tace, "yauwa!" tare da kashe wayar abinta.

Yayi jim zaune a gefen gado cikin zuzzurfan tunani. Bai manta abinda Shukurah din ta mishi ba kwanaki, shi yasa shima yayi niyar shareta. Tunda dai dama ba wani abu yake mata ba, haka itama ba wani abin kirkin take tsinana mishi ba.
Shi kanshi yayi mamakin tarairayar data dinga mishi dazu, sai da yayi tsam da ranshi sannan ya fahimci saboda ganin idon Nadiya ne take yin hakan. To ina amfanin abinda ba don yaji dadi aka yi ba sai don a kuntatawa wani?

Har ga Allah Ya so ace Ummah bata shiga cikin zancen ba. Don kuwa ya sha alwashin shi da Shukurah dai, sai dai idan ita ta je gareshi. Amma ba dai ya kai kanshi gareta ba.
Da kyar ya iya tashi ya wuce bangaren nata.

Wannan fita da yayi karaf a idon Nadiya kamar an ce ta daga kanta. Da yake tagar kicin dinta tana fuskantar bangaren Shukurah din da na Hajiya Ummah. Tana kallo ya bude kofar dakin ya shige. Tayi kwafa rai na suya. To! Ashe dai da gasken gudunta yake yi?

Shi kuwa Asubahin fari ya bar wajen. Bayan mita da yada kananun maganganu babu abinda ya tsinta a wajen Shukurah din. Ita ala dole ya ci zalinta tunda ya mata kishiya. Daga baya kuma ta koma nuna mishi tasan dai baya kwana tare da amarya har yanzu, idan ya yarda tafiyar tasu ta dore to zai iya duk abinda ya ga dama da ita. Wato dai har yanzu tana kan bakanta.
Ya kalleta a wulakance, yace, "me kike yi min ne wai? Me kuma kike bani wanda ba sai kin wulakanta ni ba? In dai don wannan ne, ki rike kayanki. Ki kwadashi kiyi duk abinda kika ga zaki iya Shukurah! Ba na so!"
Sai ta fashe mishi da kuka. Shi kuwa ya juya mata baya ya kyaleta tayi ta gama.


31.



Zuwan su Amarya ganin daki washegari shi ya dauke mata damuwa da ta kwana da ita. Don kuwa barci gagararta yayi a daren daya gabata. Ta kwana tana tunani da tambayar kanta, wai shin menene matsalar? Kuma ta ina za ta tattago wannan al'amari?
Suka mata yini guda ita da sauran yaran gidan da suka je. Amarya sai binta take da kallo tana murmushi, ce mata take yi tana karawa, 'ai lallai wannan amarci ya karbeta!' Nadiya dai dariya kawai take binta da ita. Sai zuwa can yamma suka shirya tafiya, da suka je yiwa Hajiya Ummah bankwana, haka ta musu sha tara ta arziki, ta kuma hadasu da direba tace ya mayarsu gida.

Amarya ta ja Nadiya gefe tana kara mata nasihar lallai ta kama Surukarta hannu bi-biyu, ta mata biyayya ta girmamata. Tunda tana sonta, itama ta kaunaceta don Allah. Nadiya ta yi shiru ita dai tana jinta, don kuwa bata tunanin shawarar da zata cigaba da bata kenan idan taji abinda ke faruwa a gidan. A haka dai direba ya ja su suka tafi tana daga musu hannu.

Da dare suka hadu da mutumin nata a wajen cin abinci, kasa ko daga ido ta kalleshi tayi a lokacin saboda tsabar yadda yake bata haushi. Ita kanta bata san tana da irin wannan kishin ba sai a yanzu. A da gani take yi ita Allah bai dora mata wannan abun ba, a da, gani take yi koda Allah zai sa ta shiga yanayi kamar wannan to ba zata taba damuwa ba. A yanzu kuma sai ga shi labari ya sha bambam. Kishin Habibun take ji yana nanikarta har a cikin kokon kanta, ta kasa daga ido ta kalleshi daga shi har Shukurah din saboda dukansu haushinsu ma take ji.
Ta gaisheshi a kaikaice, da ya zauna a kujerar kusa da ita kuma sai ta juya mishi baya. Ta dinga tura abincin ma da kyar saboda ji tayi cikinta ma ya cushe gabadaya.
Ai tana gamawa ta musu sai da safe ta tsere sashenta.

Abin daren jiya bata samu barci da yawa ba, tana kwanciya cikin ikon Allah sai barcin yayi awon gaba da ita. Shi yasa sanda ya bi sahunta ya buga mata kofar falo bata ji ba, waya kuma da yake a silent ta sanyata ko da ya kira bata ji ba.

Washegari shima tunda farar safiya ya bar gidan don haka basu hadu ba. Ita dadin hakan ma ta ji. Don kuwa duk da bata ga shigarshi bangaren Shukurah ba jiya, amma zuciya da sake-sake haka suka dinga auna mata ai a can dinma ya kwana. Yau ma haka ta tashi rai a cunkushe.

Taje ta gaida Hajiya Ummah wadda itama ta sameta tana shiri da alama dai fita zata yi. Shayi kadai ta iya hadawa mai dan kauri ta sha, ta wuce dakinta.
Kasancewar ranar Public Holiday ce, Ammar bai je makaranta ba. Sai Ummah ta fita da shi. Gida ya rage daga ita sai Shukurah kadai.

Wajajen karfe sha daya ta shiga kicin da niyar dora abinci saboda yunwar data fara nanikarta. Ta samu shinkafarta ta barza, ta dora rigana ta hau aikin dambun shinkafa.
Nan da nan gidan ya kacame da kamshi mai dadi. Kafin ta gama kuma sai ta dora farfesun kaji. Aikin da dan yawa tayi saboda yau ta kudurta har Ummah za ta kaiwa abincin. Ta ga abinda zata ce mata kafin kuma daga nan taga ko idan za ta cigaba da kai mata.

Da ta sauke dambun ta zuba cikin mazubai masu kyau guda biyu, sai ta bar farfesun under low heat don ya karasa dahuwa. Kunun ayar data hada kuma ta sanya a cikin firjin don ya kara sanyi kafin ta tashi sha.

Ta wuce dakinta ta fara watsa ruwa kafin ta dauro alwala ta je tayi sallar Azzuhur.
Tana tahiyar karshe taji alamun an bude kofa an shiga dakin tare da maidawa aka rufe. Kafin ta fara mamakin ko wanene kamshinshi ya bayyanashi.
Ta sallame sallar ta zauna tayi tasbihai da ladubban da take gudanarwa a duk sallar da ta yi. Ta mike tsaye tana nade abin sallar hannunta tana kallonshi yana zaune ta gefen gadonta yana latsa wayarshi. Tayi tsaye bayan nan tana kallonshi ba tare data cire doguwar hijabin jikinta ba. Don kuwa bayan wankan da tayi bata maida wasu kayan kirki jikinta ba. Karamar rigar shan iska ce a jikinta da bata gama rufe mata cinyoyinta ba, sai ta dora zani a kai. Ganin ita kadai ce a sashen nata ba wani yake je mata ba.

Ya bita da kallo tun daga sama har kasa yana lura da yadda take kaucewa hada ido da shi.
Yace, "wai ni wannan shan mur din da ake mun na menene? Na lura tun jiya kina wani jin haushina da kin yi mun magana. Akwai abinda na miki da ban sani ba ne?"

Ta dan tabe baki tana kallon can gefe daya, "ni kuwa me kayi mun? Yaushe ma muka hadu da kai da har za kayi mun abinda raina ba zai so ba?!"
Yayi murmushi yana kallonta kamar abinda tace din dadada mishi rai yake yi, yace, "to idan haka ne, zo nan ki zauna kiji wani abu."
Ya fadi hakan yana daddabar kusa da shi alamun nan za ta zauna.

Tayi tsaye cak tana kallonshi ta ki motsawa, maimakon ta je din sai tace mishi, "abinci nake son ci idan hakan babu damuwa."

Ba shi take kallo ba, shi yasa bata ma san lokacin daya tashi daga inda yake ba har ya karasa gabanta. Sai data ganshi gab da ita sannan tayi kokarin juyawa, ya kama gefen hijabin nata ya rike gam, ya hanata matsawa ko nan da can.

Yace, "to wai me yasa ne idan zaki yi magana ba za ki kalleni ba Nadiya? Kuma na tambayeki kin ce wai ba kya fushi da ni? A haka kike so in yarda dake?"
Kokarin ya sake mata hijabi take yi, "to tunda nace babu wani abu ka kyaleni mana! Nace maka yunwa nake ji!"

Ji tayi kawai ya zame mata hijabin ya yar, ta daga hannu a sukwane ta kare kirjinta tana kokarin durkusawa kasa. Ya sanya hannu ya jata cikin jikinshi ya rukunkume. Kanshi a cikin gashinta yake ce mata, "know what? Nima yunwar nake ji Nadiya, amma daga ni har ke yau ba zamu bar dakin wannan ba har sai kin fada min abinda na miki sannan!"

Ganin babu Sarki sai Allah yasa ta sauko daga tsinin data hau ba shiri, ta hau magiya da kankan da kai. "Na rantse da Allah babu abinda ka min. Ka wa girman Allah ka kyaleni, don Allah. Yau fa ranar girkin Anty Shukurah ne ko ka manta?!"

Ya kai hannu bayan wuyanta yana shafawa zuwa gadon bayanta, wasu abubuwa suka fara mata yawo a jiki da jijiyoyi. Jikin nata gabadaya sai ya dauki wata irin rawa kamar wadda lantarki take ja.
Idanunshi a rufe, tunaninshi da kwalwarshi ba lokaci daya suke tafiya ba, shi yasa ma ya fara rasa zaren tunaninshi gabadaya. Wasu abubuwan yi yake, amma shi kanshi ya fara rasa sanin abinda yake aikatawa din. Sunbatarta yake, shafata yake, komi ma yi mata yake, amma duk da haka ji yake yi it's not enough.

Cikin hakan yake ce mata, "kin manta cewa ku dukanku da zarar an gama karin safe shikenan kun gama fita daga girki? Yanzu kuwa lokacin Azzuhur ya shiga Nadiya, lokacinki ne. Don haka ki barni in fanshe takaicin kwanakin da na rasa na amarcina!"

Maganar tashi ta so ta bata haushi ma, ta bude baki tace, "to ni na hanaka cin amarcin? Ko kuma ni ce na sabbaba maka hakan?"

Sai ya dakata, ya kalleta da kyau da murmushi akan fatar bakinshi, "ai dama nace hakan yana damunki amma kika ce ba haka ba. Ana son mutum amma ana kaiwa kasuwa! Nadiya wannan hali naki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login