Showing 117001 words to 120000 words out of 142169 words

Chapter 40 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

462

da matsanancin farinciki irin wanda ba a kwatantawa. Aka kira Abba yaje ya ga dan'uwan Mama. Yana fita sai ga kaji manya-manya guda biyu an kai, aka gyarasu nan da nan Amarya ta dora sanwa. Yadda take murna da taya Mama farinciki kamar wata diyarta.
Su kansu su Lantana da Salame sai gasu suna rakube-rakuben zuwa gayar da Yayan Mama. Abin ya so ya bawa Nadiya dariya, lallai da gaske da ake cewa wai duniya rawar yanmata.

Mami ta wuce gida ta bar Nadiya anan don tace sai yamma zata koma.
Sun samu labarin tuni Baban su Mama da Innarta suka rasu, amma sun fada sun nanata kafin rasuwarsu, sun jima da yafe mata, itama kuma suna rokon data yafe musu. Baiwar Allah ranar tayi kuka har ta godewa Allah dai.
Da Alhaji Ja'afar ya fada mata gadonta na wajen iyayensu dake hannunshi, sai da yawan kudaden suka tsoratata. Tace mishi ita me zata yi da kudi yanzu? Ganinshi ma kadai da Iyalinshi ya wadatar. Yace a'ah, ba za ayi haka ba. Dole ta amshi hakkinta. Don haka suka yanke shawarar AbdulHadi zai amshi kudin, zai duba abinda za a dinga yi mata da kudin ta yadda duk karshen wata kawai sai dai a aika mata da ribar abinda aka samu.

Gabannin Magriba Mr. Hassan ya koma daukar Nadiya. Tayi sallama da mutanen gidan cike da kawa zuci, don bata da tabbacin ranar da zata sake fitowa. Suka dauki hanyar komawa gida.

Kai tsaye bangaren Hajiya Ummah ta wuce ta gaidata. Ta tareta cikin farincikinta har da rungumota, ta kuma tayata murna da nuna jindadinta na haduwa da Mama da tayi da danginta. Don cewa tayi ma zata samu lokaci taje gidan da kanta su gaisa, tunda tun bayan auren basu samu damar gaisawa ba dama properly.
Nadiya ta ji dadin jin hakan kwarai. Tana nan sashen taji dawowar Babangida, amma basu hadu dashi ba saboda bangarenshi ya wuce kai tsaye.

Itama da aka kira sallah sai ta koma bangaren nata. Tayi wanka, tayi sallah tare da gudanar da wasu abubuwa na musamman. Duk cikin shirin ziyartar Babangidan ne a turakarshi. Wanda ya dauki fushi ya kakaba, yau ko waya bai yarda sunyi da ita ba.

Bayan ta yi isha'i kicin ta shiga ta jefa danwake don shi kadai take son ci da man kuli, ta yanka kabeji da albasa da cucumber da tarkacen vegetables, ta zabga yaji kamar na kamun maye, ta zauna ta ci tayi nak, ta dora da lemon tea data zame mata ka'ida yanzu.

Zuwa karfe tara, ta kulle sashenta ta fita. Wani irin asirtaccen kamshi take ta kowane bangare na jikinta, duk inda ka taba da irin kamshin da yake yi.
Yana uwar dakinshi zaune akan sofa, desk ne a kusa dashi ya dora laptop dinshi yana aiki, fuskarshi saye da farin gilashi wanda ya kayatata sosai, ya kuma kara fitar mishi da kamalarshi da cikar haiba.

Ya daga kai ya kalleta lokacin data shiga dakin bakinta dauke da siririyar sallama. Ya amsa daga can kasan makoshi, don kuwa irin cika da kyawun data kara a cikin yan kwanakin ba karami bane, ko kuwa don ya kwana biyu bai ganta bane? Kokari yake ya danne duk wani kewa da jindadin ganinta da yake ji a lokacin, ko ba don komi ba don tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Idan ya tashi ya sabeta kamar yadda zuciyarshi ke raya mishi ai maza sun fadi, kuma ba zai isar da sakon haushin take dokar shi da tayi ba.
Amma sai hakan yake nema ya gagara, musamman da ta bi ta gefenshi ta wuce, wani irin kamshi da bai taba ji a tattare da ita ba yana surnanawa daga jikinta yana shiga hancinshi. Ya saci kallonta har ta wuceshi, taje gefen gado ta zare hijabin jikinta. Ai sai yayi suman zauna. Wasu arnun nighties data sanya ranar suka tafi da hankalinshi kai tsaye.

Yana yawan fada mata rashin sakewa da shi da bata yi balle har ta dinga yi mishi shiga irin wannan, wanda shi kuma ba abinda yake so ga matarshi irin shiga ta kananun kaya. Abinda bai sani ba ita bayan kunya, har da tsoron irin kwarzabar da taga yana yawan yi mata idan ta sanya kananun kayan. Shi yasa wai take kokarin takaitawa musamman idan taga ranar girkinta ne. Amma a yau, tana so ta yaye wannan hijabi dake tsakaninsu. Ta bi duka kalaman Mami daya bayan daya ta tsinci wadanda zasu mata amfani, a haka kuma sai ta hango wani abu da a da, bata bashi muhimmanci ba. Da gaske akwai tsoro a tattare da ita, tsoron ta mallakawa Babangida zuciyarta da jiki, shi kuma ya wancakalar da ita ya rabu da ita. Musamman a yadda taga Hajiya Ummah bata yi na'am da ita ba, shi kuwa baya tsallake umarninta.

Sai ta yanke shawarar bari ta dauki risk din kawai, ta so shi gabadayanshi ta kaunaceshi da duk wani flaws nashi da imperfections. Zuciyarta na fada mata da kara fada mata, he's worth it!

Ta fara takawa cikin taku na daukar hankali, har ta karasa wajenshi ta zauna a kusa dashi. Gashin kanta ta gyarashi ya sauko har kirjinta, yana ta sheki da kamshi. Ta janye laptop din daya kurawa ido kur yana kallo, amma a lokacin ko bindiga aka dora mishi a ka ba zai taba cewa ga abinda yake yo ba. Don kuwa tuni daya daina fahimtar komi.

Tace, "Habibina, shine ko sannu da hanya ba zaka ce min ba?" Cikin wata murya mai lankwashe da shagwaba da salo na jan hankali.
Ya watsa mata wani irin kallo, bakinshi a mace murus. Yau Nadiya mamaki kawai take bashi tana kara kasheshi da mamaki. Musamman data lallaba ta hade bakinsu waje daya ta bashi peck, ta janye tana kallonshi tana wani murmushi, "I miss you wallahi!"
Ai sai ya mance da wani zancen fushi da komi, ya wartota kamar wadda za a kwace mishi ita. Ya hadata da jikinshi.
Yace, "har kika fi ni Nadiya? Kwanaki dai-daya har goma sha biyu fa!"
Ta rada mishi a kunne, "then show me!"
Sai ya dagata camak gabadayanta yayi kan gado da ita.

Kewa dai kam, ya nuna mata yayi, itama kuma a yau ta dage ta nuna mishi ainihin so da kauna da take mishi. Abinda ya dadada wannan dare kenan, aka raba dare tsakanin ma'auratan kowa yana kokarin nunawa dan'uwanshi yadda yake jinshi a cikin ranshi.

Sun gama sallar Asubahi, ta kamo hannunshi ta dora mishi wani abu a tafin hannunshi.

Ya kurawa na'urar idanu mai kama da hand thermometer idanu yana kokarin tantance menene? Zabgegen jajayen layuka biyu daya gani, da sign din '+' a samanta yasa ya daga idanu ya kalleta a wani irin gigice. Fuskarshi na bayyana tsananin shock da yake ciki. Ta kai tafin hannu ta rufe fuskarta tana dan murmushi a kunyace, sai ya bi bayan hannun nata da sumba iri-iri.
Yace, "na rantse idan kika kara bani wani surprise din a yau Nadiya, zuciyata sai ta buga!"
Ta saki kayataccen murmushi tana kallonshi cike da jindadi lokacin daya maida goshinshi akan abin sallah yana mai godewa Allah Buwayi Gagara Misali, a fili da kuma boye.

Ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye, hannunshi na laluben cikinta da yaji shi shafal a shafe. Yace mata, "kin bani komi a yau Nadiya, bani da wani baki da zan taba iya bayyana miki farincikin da nake ciki a wannan lokacin. Allah Yayi miki albarka, yadda kike faranta min kema Allah Ya baki masu faranta miki!"
Tace, "ameen!"

Barci suka koma, sai can wajen karfe tara suka tashi. Cikinta kamar an yashe mata shi haka take ji saboda yunwa.
Ya tambayeta me take son ci?
Tace, "ita komai ma yau tana jin zata iya ci."
Amma da suka je bangaren Ummah da niyar yin karin, loma daya tayi ta hadadden cous-cous da aka yi da ya sha veggies da kwai yayi sharr, ta kasa ta biyu. Dole sai dan wake Laylah ta sake dafa mata.


47.



Yadda taga Hajiya Ummah da Mami suna tattalinta ne yasa ta sha jinin jikinta cewa sun san da zancen cikin, duk da dama ta dade tana zargin tuni Mami din ta gane, tasan kuma ita zata fadawa Ummah. Don haka fadar irin kulawa da take samu a cikin gidan a wannan lokacin ma bata baki ne. Motsi kadan idan tayi, sai duk sun zabura sun tambayeta, 'lafiya?'
Tun tana jin kunyar hakan ma har ta saki jikinta abinta.

Tun komawarsu gidan bata ga motsin Shukurah ba. Babu kuma wanda ya fada mata abinda ke faruwa, don haka itama bata tambaya ba.

Sunyi hakan da kwana biyu, da dare tana dakinta tana shirin kwanciya. Babangidan nata ya tura kofar dakin ya shiga. Cikin jallabiya yake ruwan toka, yana ta zubda kamshinshi na ka'ida.
Ya karasa shiga cikin closet dinta inda take zaune gaban madubi tana goga humra a wuyanta da gabobin hannunta.

Suka kalli juna ta cikin madubin suka yi musayar murmushi. Ya karasa ya tsaya a bayanta, yace, "mai ciki, ya ne ake kallona haka?"
Sai ta dan turo baki, "don Allah ka daina kirana da mai ciki dinnan haka. Wai sai kowa yasan matarka tana da ciki ne?"
Yayi dan murmushi, "ba zaki fahimci yadda sunan nan ke dadada min rai bane idan na fada shi yasa!"
Ta yada kai gefe daya, "to ai shikenan Habibi, na kyaleka kayi ta fadi tunda dai kana jin dadin hakan!"

Yayi murmushi yana ciro wani abu daga cikin aljihunshi. Kallonshi take yi in curiosity har ya ciro wani dan madaidaicin kwali, ya bude shi. Ya ciro wata irin siririyar sarka mai fararen stones, a tsakiyarta kwalliya ce kamar ganyayyaki na bishiya, an musu ado da wani stone din shi kuma green. Ya sanya mata a wuyanta. Tayi zaune tana kallonshi da mamaki har ya makala mata dan kunnen sarkar da abin hannu da zobe.

Ta kurawa zoben idanu tana jinta kamar wadda aka nutsa a cikin ruwa. Wasu irin emotions data rasa ko na menene suka lullubeta, sai taji hawaye suna diga akan fatar hannun nata.
Ko bata san duwatsu masu muhimmanci ba da ake kayan ado da su, ranta da jikinta sun bata wannan ba kananun abubuwa bane.

Ta karbi kwalin a hannunshi tare da zare takardar rasiti dake makale a jiki wadda take dauke da bayanin abubuwan da sarkar take da su. Sarka ce ta gwal wadda aka yi mata ado da kananun diamonds, tsakiyarta kuma wani diamond dinne shine mai kalar green din. Tsayawa fadin darajar sarkar wannan ma ba karamin bata baki bane.
Wai yau Nadiya ita ta mallakesu. Mijinta, abin alfaharinta ya mallaka mata su.

Ta kalleshi ta cikin madubin cikin karyewar murya, tace, "ban san me nayi na cancanci wannan ba, but thank you so much!"
Ta tashi ta rungumeshi. Shima ya sanya hannu ya kara riketa a jikinshi, "kin cancanci fiye da hakan Nadiya. Ai ni zan miki godiya, bayan kyauta kan kyauta da kika dinga yi mun da ba kowa ne yake da gatan samun ta ba?!"

Tayi murmushi amidst her tears, "kana dai fadin hakane kawai, kaima ka sani. Amma don me ake auren idan ba don wadannan ba!"
Sai kawai ya nutsa kanshi a wuyanta, yana ce mata, "Nya Raakna!"
(Ina son ki) da yarensu na Kanuri.


****

Anyi kwana biyu da yin haka din, Hajiya Ummah ta hadasu a falonta da dare. Tace musu akwai wani program da aka gayyacesu, 'Feed the Needy'
Wani ciyarwa ne ake yi ga marassa karfi da mabukata wanda gidauniyar "Helping Hand Foundation" take gudanarwa a garuruwa da dama. Wannan karon zasu yi ne a Kaduna, sannan salon nasu zai bambanta d sauran lokuta.
A maimakon a samu wani da zai bada taimakon kayan abinci, sai su gidauniyar su ba da kwangilar a dafa abincin a kuma raba da sunanshi, wannan karon suna so ne a samu wanda zai jagoranci gudanar da komi na wajen tun daga kan girkin har zuwa ga rabon abincin. Hajiya Ummah din tana kyautata zaton hakan zai basu exposure mai kyau, hakan kuma zai kara basu damar kara karbuwa a wajen talakawa. Amma ya suke ganin hakan? Zasu iya amsar wannan gayyata ko kuwa kawai a bari ta wucesu?
Yace mata, "to ni Ummah ga ki ga mai aikin dahuwar abincin nan, ni dai ta bangarena ai ban ga abinda zan iya cewa ba anan!"
Nadiya ta amsa a take cewa bata ga matsalar hakan ba. Zata bada duk taimakon da ake bukatar ta bayar.
Don haka suka fara shirin gudanar da wannan gagarumin shiri a cikin satin.

Kamar kuma yadda aka ce haka tsarin ya tafi. Ta nemi taimakon rakiya a wajen kawarta Aramide tunda an ce zata iya tafiya da wani, ita kuma bata bata lokaci ba ta amsa. A cewarta wa yake kin amsar gayyatar First Lady ta gobe? Sai kawai tayi dariya tace mata, "first Lady a ina?! Rufa min asiri in mutu maza su kaini ba mata ba."

Ranar tunda suka bar gida tunda safe suka yiwa wajen da za ayi aikin tsinke, suka hadu da Ara din a can tana jiransu. Sun samu yan jarida da masu aikin daukar vidiyo da hotuna ana ta yi. Hakan bai sanyaya gwiwar Nadiya ba, wadda tana haduwa da Manager din wajen itama gabadaya ta tafi ta dauko tsohuwar rigar manajanta ta sanya. Nan da nan sai ta karbe akalar aikin komi na wajen, suka hadu da sauran masu aikin dafe-dafe a wajen. Wasu ta bada umarnin abinda za ayi da yadda za ayi komi, wani kuma da kanta ma take yi. Aramide itama ta kama nata aikin suka hau yi gadan-gadan. Haka ta yini a tsaye akan duga-duginta suna gudanar da girke-girke daban-daban na gida Nigeria da kuma waje. Suka yi lemuka da snacks da dama, ga masu daukar vidiyo da mai gudanar da shirin suna aikin dauka da kuma yi mata tambayoyi iri-iri tana amsawa cikin nutsuwa da kwarewa a aikinta.
Abincin da suka yi suka dinga wrapping a take away ana lodawa a motoci ana tafiya gidajen marayu da su da kuma wani kebantaccen waje da aka tara mabukata suma ana kai musu.

Da suka gama komi, aka gabatar da ita a matsayin matar dan takarar Gwamnan Kaduna na wannan zabe da shi kanshi Habib din a matsayin wadanda suka dauki nauyin wannan aiki. Aka yi wata hira din dasu ta mintuna talatin, akan irin canji da cigaba da suke son kaiwa garin Kaduna idan Allah Ya basu damar samun wannan mulkin. Suka yi bayani na hankali, na ilimi, ba wanda ke dauke da alkawarin bogi da zantukan iska ba, akan yadda suke son kyautatawa manoma da kai cigaba a kauyuka da kuma kara kai cigaba cikin Jihar Kaduna.
Anan Nadiya tayi wata magana da ta ja hankalin su kansu masu daukar shirin, yadda take ganin yakamata ace shuwagabanni sun hada karfi da karfe wajen tallafawa mata da kananun yara musamman wadanda ake rabosu da iyayensu domin yawon almajirci. Ta kuma ce da ikon Allah, za su yi iyaka kokarinsu wajen ganin cewa sun inganta rayuwar yara kanana marassa galihu, tunda sune manyan gobe.

Yadda take maganar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, babu iko babu jin izza da ji da kai, ya ja hankalin mutane da dama a lokacin da aka saki vidiyon hirar tasu a daren ranar.

Kafin wayewar gari gabadaya social media ta dauka, Hajiya Nadiya matar Habibu Abdullahi Gwamnan Kaduna na gobe! Yadda kasan an jima da saninta.
Sai gashi an fara citing kalamanta da tayi a interview din.

Da misalin karfe goma na safiyar washegarin ranar duk sun nabba'a a falon Hajiya Ummah suna kallon shirin, Ummah ta dauki remote ta rage sautin karar talabijin din lokacin da aka karkare shirin. Murmushine sosai akan fuskarta, ta kalli Nadiya din dake aikin gyangyadi daga zaune don kuwa har lokacin gajiyar da tayi bata gama sakinta ba. Duk da tausa ta musamman da Habibin nata ya raba dare yana mata.
Ta kalli Babangida da yake satar kallonta, fuskarshi ta gaza boye jindadin yadda shirin ya karbu sosai da sosai a wajen mutane.
Tace mishi, "Alhamdulillah, ina ga mun kai matakin karshe a bangarenmu, wannan karon dai Nadiya ita ta kai mu ga wannan matakin nasarar. She did well, fiye da tunanina gaskiya. Babangida ka riki yarinyar nan da mutunci, ita tana yin duk iyaka kokarinta saboda taimaka maka ne kai kadai ba don wani abu ba, saboda ta dauki nasararka a matsayin tata, ba don tayi suna ko shura bane."
Ya lumshe idanu a tausashe yana dan jinjina kai.

Ummah a ranta take cewa, 'yanzu na kara gane bambancin dake tsakaninku da Shukurah. Ko da ace ta fiki shekaru da yanayin wayewa, sai dai a zahirance Nadiya ta fi Shukurah din exposure da iya bi da mutane sosai da sosai. Abinda tun farko yakamata in duba kenan kafin in ja Shukurah cikin harkokina. Amma son zuciya ya hanani."

Duk da haka tana godiya da Allah bai sa idanunta sun rufe gabadaya har ta kasa ganin hakan da wuri ba. Ga shi yanzu daga ziyartar show daya da Nadiya tayi a kwana daya, sun ga canji da tunda Shukurah take tata fitar basu ga kwatankwacin shi ba.
Saboda ita Shukurah tana da wani hali na nuna isa da izza da ji da kai, tana kuma amfani da kudi ta ce zata sayi mutane ba wai tayi amfani da halinta ba. Mutane da dama kuma a harkar siyasa ba kudi suke so ba, loyalty suke bukata. Suna so su samu assurance din cewa koda ka hau mulki, ba zaka juya musu baya ba idan ka samu abinda kake so. Hali na nagarta da girmamawa da kamala suna matukar jan hankalin mutane. Nadiya kuma tayi amfani da wadannan a jiyan, abinda Shukurah bata taba gwadawa masu bibiyarta da take mata baya ba.

Abin kamar wasa, cikin dan kankanin lokaci sai ga sunanta ya karade ciki da wajen Kaduna, fiye da na Shukurah. Wasu ma sai suka fara shiga social media da kansu suna yabawa halin Nadiya da irin yadda suke girmamata da maigidanta, abinda a da basu samu hakan ba.

Kasancewar gidauniyar Helping Hand Foundation babbar kungiya ce wadda tayi shura a cikin Nigeria da kewayenta wajen taimakawa marayu da marassa karfi, wadda kuma tayi fice kwarai da gaske ba ga talakawa kadai ba, har ma da manyan kasar. Haskasu Nadiya da aka yi daga bangarensu ba karamin cigaba ya kai musu ba, bugu da kari rawar ganin da Nadiya ta taka wajen gudanar da ayyukanta sun matukar taimakawa wajen kama zukatan duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login