Showing 51001 words to 54000 words out of 142169 words

Chapter 18 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

446

nasu yaso yayi yawa, amma tsabar taurin rai ta ki ta matsa ta ja da baya. Ta kama kugu tana kallonshi ido cikin ido fuska a cune tana harararshi.
Da ta san yadda hakan yake kara kayatata a cikin ranshi, kila da bata yi hakan ba.

Ya daga baki yana mata magana, kamshin mouthwash mai citrus yana bugunta a fuska. Yace, "zuwa nayi kiyi min list abubuwan da kike bukata. Zan je Umarah cikin wannan satin, so daga can nake so in sayo duk abinda ya dace. Ina son sanin size din takalminki, maybe har tsayinki saboda dogayen riguna ko? Da kuma irin kalolin da zaki fi so... Sai kuma me ma...?" ya dakata da lissafin da yake yi cikin alamun tunani. Ita kuwa ta saki baki da hanci tana kallonshi, bakinta ya ma kasa motsawa balle ta katseshi.

Yace, "yauwa, an ce har da size din undies da kuma....!"
Ta daga hannu cikin karaji, "dakata Malam! Dakata nace!!"
Ya kuwa yi shiru yana kallonta, idanunta har wani ruwa suka samu kawowa na tsabar bakin ciki da takaici.

Tace, "wai baka ji me nake cewa bane? Aure na ce bana yi, ba zan yi ba. Don haka a matsa gaba. Kada ka sake yi mun wannan zancen, tam!"
Yace, "idan kuma na ki fa?!"

Tace, "sai ka san wadda zaka yi zaman auren da ita, Amma ba da ni ba. Ban da ma tsabar rashin zuciya an ce maka ba a sonka Amma sai ka nacewa mutane? Ina dalili!"

Yayi maza ya hade fuskarshi, dan murmushin dake kai ya bace bat! Yace, "ki daina ganin fa ina zaune kina dankara min magana son ranki Nadiya, idan nace zan baki amsa ba dadinta zaki ji ba. Aure kuma da kike cewa na dole ne, ai ba ni ne na tilasta miki ba ko? Kuma ba ni ne na karbi kudin auren naki ba. Yadda kike ihu da ikirarin auren dole nima ai auren dolen ne, ba cewa nayi na gani ina so ba, amma duk da haka ai baki ganni ina ihun ba zan aureki ba ko?"

Bata san ya aka yi maganar tashi ta bata mata rai sosai da sosai ba. Sai kawai ta saki wani irin tsaki, tace, "kada ka raina min wayau mana! To waye yace yana so ka so shi dama? Sonka din banza! Auren kuma da ba da zuciya daya za a yi shi ba menene amfaninshi?"
Yace, "hala ke ce zaki yi shi ba da zuciya daya ba ko? Ni dai nasan da tsarkakkiyar zuciya zan yi shi"
Tayi mici-mici da idanu, "Allah sa ma da daudaddiyar zuciya zaka yi shi, ni meye nawa a ciki? Ni dai na fada aure ne ba zan yi ba!"

Hannu ya sa ya murde mata baki, duk dauriyarta sai da taji kamar ta saki fitsari a wajen saboda azaba. Ya jefa mata wani wulakantaccen kallo, yace, "believe me Nadiya, idan da ba don umarnin mahaifiya ba, ko a kafa aka daura min ke zan kunceki ne in ruga nima. Aure kuma, sai anyi shi ko kin ki Allah. Don Allah idan an daura mana auren kiyi abinda zaki kinji? Magana kuma da kike yi duk yadda ta zo bakinki ki cigaba, but consider yourself warned Nadiya. Nan gaba zan miki abinda ya fi murde baki ma!"
Ya zagayeta ya fita daga shagon ba tare daya kara kallonta ba.

Ya bar ta nan tana ta aikin tsiyayar da hawaye, rannan bakikkirin. Ji take kamar ta dinga kwala ihu saboda takaici. Waye shi? Me yake takama da shi? Shi har ya isa ya zo inda take ya dinga zabga mata maganganu marassa dadin ji ma kamar haka? Amma ta kasa daga kafa ta bi bayanshi kamar yadda zuciyarta take umartarta da tayi hakan.

Nan ta kara jimawa tana shakar kuka, da kyar ta iya hada nata-i-nata ta wuce gida.
Ranar sai wajen karfe tara ta koma.
Tana dira kuma Abba ya tareta da nashi fadan, Aiken data dinga mishi na mutane akan maganar ya janye aure. Ya zageta tas, yace aure kuma babu fashi tunda ya karbi kudi. Don kaniyarta ta kashe kanta in taga dama ma karewa.

Ta koma daki nan ma Mama da Amarya suka sanyata a gaba da nasu kalar wa'azin da nasiha, ita dai kam ji take yi duniyar ma gabadaya tana wani juya mata. Ji take kamar duka mutanen duniyar sun hade bakine sun juya mata baya.
Da abin ya isheta Sai ta dargwaje musu da kuka, amarya ta fara aikin lallashinta Mama kuwa sai ta saki tsaki, tace, "don Allah kyaleta taje tayi duk abinda taga dama kuma tunda dai ta ki jin lallashin. Yarinya a dinga dama da ke amma kiyi biris da mutane saboda kunnen kashi ne da ke? Sai kiyi duk abinda kike ganin daidai ne a wajenki tunda mu ba zaki ji maganarmu ba."
Ta karkade zaninta ta barsu anan amarya na kara bata baki.

Aka kai mata abincin dare, ta samu ta tsakura haka nan ta barshi anan. Wayarta ta kashe gabadaya saboda taga Anty Lima na ta danna mata kira, ga Abdullahi da shima har ya gaji da kiran ya koma aika sakonni. ita kuma bata son takura ko kadan.
Saboda ciwon da kanta yake mata sai data sha magani sannan ta kwanta. Ko a cikin barcin ma, tufka kawai take yi da warwara, yadda zata samu ta bulle daga wannan aure. Shi yasa barcin bai haifar mata da komi ba sai tarin ciwon kai da ciwon jiki daya bar mata.

Da kyar ta iya tashi can wajen karfe biyun dare, ta dauro alwala mai kyau ta je ta fuskanci alkibla ta fara sallah. Koda ta daga hannunta sama, bakinta dauke yake da addu'ar Allah Ya hana yiwuwar wannan aure ta huta.
Bata samu ta kwanta ba sai da suka yi sahur sannan. Wannan karon kam barcin mai nauyi tayi sosai, don bata tashi ba sai can wajen karfe goma sannan.

Shima vibrating din wayarta ne ya tasheta. Ta zauna da kyar har wani jiri-jiri take gani ta daga wayar. Tayi tunanin Anty Lima ce ko Abdullahi, amma ga mamakinta sai taga Safiya ce.
Tayi dan murmushi, a ranta tana cewa yau watarana? Watakila itama ta kira ne ta mata tsiya kamar yadda jiya su Aysha suka dameta da Rabi'ah.

Ta daga murya a shake mai cike da barci, "Hello, Sophie manyan kasa. Ya kike?"
Shiru ta ji tayi kamar babu kowa ma akan wayar. Ta fara "Hello... Hello?! Kina ji na?!"
Zuwa can kuma sai taji kamar ana shesshekar kuka. Sai jikinta yayi sanyi, tace, "Safiya? Lafiya, me yake faruwa?"

Cikin rishin kuka tace, "har kina da bakin tambayata lafiya bayan abinda kika yi mun?"
Kanta ya daure da mamakin wannan abu, tace, "ban gane ba, me kike nufi Safiya? Me nayi miki kuma?"

Tace, "in case baki sani ba, Habib was meant to be mine, ba naki ba! Anyi mun alkawarin aurenshi tun ba yau ba, na gama tsara yadda rayuwata zata tafi a matsayin matarshi tun kafin ki san da zamanshi. Me yasa zaki zo ki wargaza min shirina? Me yasa zaki shiga cikin rayuwata? Me na miki?!"
Ta dargwaje da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Nadiya ta kasa cewa komi. Ta rasa abinda zata ce. Sai da kyar ta iya daga baki tace, "ban san me kike cewa ba Safiya, Amma ina mai tabbatar miki da cewa ko ma menene, ban san komi akai ba. Yadda kika ji maganar auren nan sama-ta-ka, nima haka na ji ta. Ni wallahi neman ma yadda za ayi in rabu da wannan karangiyar auren nake yi amma na rasa ta yaya zan yi hakan!"
Safiya ta ja hanci, tace, "kada kiyi gaggawar bari kanki ya fasu don kinga an zabeki a kaina. You don't know half of what's awaiting you a cikin wannan auren. Ki kula!"
Da wannan gargadi mai girgiza rai ta kashe wayar.

Nadiya ta bi wayar da kallo ranta a jagule, har ga Allah ranta bai yi mata dadi ba. Yadda taji Safiya tana kuka ya sanyayar mata da jiki, daga jin yadda take yin kukan kai da kanka kasan cewa da gasken yi take yi, da gaske son Habibun take yi. To ita kuwa me zata iya yi akan haka? Wannan abu ne wanda ya fi karfin tunaninta.

Ta kira Anty Lima, saboda ita kadai ce wadda ta fi kusa da duka Madam da Safiya. Tana da tabbacin zata iya sanin ko ma menene yake wanzuwa.

Anty Lima ta ja numfashi ta aje bayan da Nadiya ta gama kora mata bayanin abinda ya wanzu. Tace mata, "tabbas, wannan zance haka yake. Tun farko, Madam ita zabinta shine Safiya ta auri Habib. Naji ita kanta ta gama tsara komi, har yadda karatun Safiya din zai kasance bayan auren nasu. To kuma abinda duk basu yi tsammani ba shine da aka zabe ki a madadin Safiya din. Babu wata amsa da suka bayar wadda ta wuce cewa kin girmi Safiya, kuma kin fi ta sanin rayuwa. Don haka ne sai itama Madam din ta ajiye zancen auren su Safiyar a gefe. Ita kuma tun bayan da Madam ta bata tabbacin cewa Habib nata ne, saboda tana da tabbacin cewa za a zabeta, sai kawai ta ba ranta cewa ya zama mijin nata. Kawai ta fara son shi abinta da tsara abinda zai faru idan ta aureshi. Nima ta kirani dazu tana kuka ta ce min Madam bata kyauta mata ba."

Nadiya ta dafe gefen kanta da yake matukar sarawa, tace, "me zan yi Anty Lima? Yaya zanyi? Bana son abinda zai sa in shiga hakkin wani ko kadan Anty Lima. Bana so in zalunci rayuwar Safiya!"

Anty Lima tayi kasa da murya cike da lallashi, tace, "Nadiya, babu zancen cin zali a cikin wannan magana. Ba ke kika ga Habibu kika ce kina son shi ba, ba kuma ke ce kika ce kina son shi ba. Me yasa ba zaki zauna kiyi tunanin watakila alkhairin a tattare da ke yake ba da Safiya ba shi yasa aka zabeki a madadinta? Kada kiyi butulci da ni'imar Allah Nadiya. Ke da bakinki kike fada min addu'ar da kike yi akan Allah Ya kawo miki miji kiyi aure, me yasa kuma yanzu kin samu damar hakan kike neman butulcewa Allah? Sai me don manufar Hajja Umma da Madam ta daban ce game da auren? Ke ki yi shi don Allah mana, ki yi shi don saboda raya sunnar Ma'aiki Sallalahu Alaihi Wa Sallam!"

Nadiya tayi shiru hawaye suna tsiyaya daga idanunta, maganganun Anty Lima din suna ratsata.
Tace, "to Safiya fa? Kinji fa cewa tayi...!"
Anty Lima tace, "ki manta da zancen Safiya Nadiya. Ki duba gabanki ke dai. Safiya a yanzu take kan ganiyar yammatancinta. Ina kuma kara tabbatar miki da cewa, ba son Habibullahi take yi ba, son irin rayuwar da zata yi a matsayin matar Habibullahi dinne take yi. Saboda tun farko da irin wannan tunanin Madam tayi galaba a kanta ta shuka mata irin wadannan tunane-tunanen. Don haka ki kwantar da hankalinki, Safiya is an adult, ki barta tayi dealing da matsalar da ita ta janyowa kanta ba ke ba!"

Ta gyada kai a sanyaye, "nagode Anty Lima!"
Tayi dan murmushi, "anytime Nadiya, anytime!"
Ta kashe wayar itama tana dan murmushi. Sai taji ranta ya dan yi mata dadi. Magana da ita ya sanya taji wata natsuwa tana shigarta a hankali.
Mama da take sauraren hirar tasu, tayi dan murmushi itama a hankali. Ta cigaba da jan carbinta tana hailala da salati.

22.


Karfe bakwai saura, ya shiga gidan nasu. Daga Masallaci yake, hannunshi rike da hannun Ammar da ke ta bashi labarin irin abubuwan da suka faru a makarantarsu yau.

Kai tsaye bangaren Hajiya Ummah ya wuce kamar yadda al'adar gidan nasu take. Duk azumin duniya a can suke shan ruwa. Haka karin safe da abincin dare kullum a can suke haduwa da duka iyalan gidan su ci.

Ya samu Shukurah zaune a tsakiyar hadadden falon na Hajiya Ummah. Tsarinshi da komi na falon idan ka gani sai kayi tunanin ko wani gidan sarauta ne ka shiga.

Ta dan kalleshi a kaikaice lokacin daya shiga, ta mayar da kanta kan tarkacen kayan shan ruwa da ke gabanta, har ta rasa wane abu ma zata ci daga ciki.

Hajiya Ummah kuma tana kan dinning a zaune, da alama itama sai lokacin take buda baki. Ya wuce wajenta kai tsaye shima ba tare daya kara kallon inda Shukurah din take ba.
Ammar ya karasa wajen Hajiya Ummah da sauri, ya zauna akan kujerar dake kusa da tata. Babu bata lokaci ya sanya hannu cikin fruits da aka yanyanka ya dauki tuffa ya kai baki. Daga Habibun har ita, murmushi kawai suka yi a tausashe.

Ya karasa haye matakalar da zata sadashi da teburin, shima ya ja kujera dake fuskantarsu ya zauna. Ya bude baki yana gaishe da Ummah din tare da yi mata barka da buda baki.
Ya dauki faranti yana kokarin zubawa kanshi abinda zai ci, yayinda ita kuma Hajiya Ummah ke bude baki tana kiran mai mata girki, Lailah. Nan da nan sai gata ta fito daga kicin kamar dama jiran kiran take yi.

Tace mata, "zubawa Babangida abinci."
Ko kafin ma ta kai ga daga kafa ta karasa kusa dashi, ya dakatar da ita. Yace, "bar shi kawai, zan zuba da kaina."
Don haka ta juya ta koma inda ta fito. Shi kuma ya zuba kayan marmari da kunun tsamiya a cikin kofi ya koma ya zauna. Yawancin lokuta bai cika cin abinci ba idan yayi azumi har sai bayan yayi sallar isha'i.

Ummah ke jan shi da hira game da tafiyarshi Umarah tunda shi zai rigasu tafiya ita da Shukurah, da abubuwan daya kamata ya duba game da kayan lefe da za a hada.

Shukurah da take jin maganganun da suke tattaunawa, ta ture kwanon Sultan chips dake gabanta, ta tashi tana kokarin fita daga falon.
Ummah ta daga murya tana kwala mata kira, "Shukurah ina zaki je ne haka bayan ko sallah baki yi ba?!"
Bata amsa ba, ta bude kofa tayi fitarta tare da maida kofar ta rufe da karfi kamar zata babbagota daga jikin ginin.

Ya kawar da kanshi kamar bai san abinda suke yi ba, Ummah kuma ta dan girgiza kai. Itama bata sake mishi maganar ba sai ta cigaba da zana mishi lissafin abubuwan da take yi.

*

Karfe tara ya koma cikin falon bayan da suka gama sallar isha'i da kuma Tarawihi. Wannan karon Ammar kadai ya samu akan kujera yana barci. Ya gyara mishi kwanciya kafin ya wuce kan dinning kai tsaye. Ya zuba soyayyiyar shinkafa data sha naman sa zako-zako, ya hada da zobo ya zauna ya fara ci. Hankalinshi na kan TV inda ake hasko labaran duniya.

Anan Hajiya Ummah ta sauko kasa daga dakinta ta zauna itama tana kallon labaran da yake ma'abociyar kallonsu ce.

Ya ture kwanon abincin gefe guda, ko rabi bai samu ya iya ci ba. Ranshi a jagule yake kwarai da gaske, akwai wani abu dake mintsininshi a can kasan ranshi a cikin yan kwanakin. Ran nashi ya ki yi mishi dadi sam.

Ya taka a nutse ya karasa inda Ummah take, kafafunshi suna nutsewa cikin tattausan carpet da aka lullube tsakiyar falon da shi. Ya zauna a kasan carpet din kusa da kujerar Umman.
Haka suka cigaba da kallon, jifa-jifa su kan tattauna wani abu idan aka fada a cikin TV din, har dai aka gama shirin.

Ummah ta kira Lailah taje ta dauke Ammar ta kwantar da shi a dakinshi da yake anan bangaren Hajiya Ummah din yake da zama.
Shi kuma sai ya juya yana kallonta a nutse, yayi kasa da murya, yace, "Ummah dama cewa nayi ko wannan azumin a kai Ammar wajen Yadikko ne? Rashida tace tana son ganinshi saboda wancan zuwan da muka yi tana makaranta."

Nan da nan kuma sai tayi kici-kici da fuska, tace, "wani irin zuwa Makarfi kuma? Duka-duka kuma yaushe ne kuka je Makarfin har kuka kwana? Ina ce ko watanni biyu cikakku ba a rufa ba?"
Yayi kasa da kanshi yana jinjinawa, "haka ne Ummah. To zan fada musu hakan. In yaso ita Rashidar sai ta zo nan din, bayan sallah sai ta koma ko?"

Nan ma fuska babu walwala tace, "Allah Ya kawota lafiya!"
Daga haka suka dan yi shiru su dukansu. Zuwa can kuma ta kalleshi a tausashe, tace, "ka tashi kaje ka kwanta haka nan ko? Karfe nawa ne kace jirgin naku zai tashi?"
Yace, "sai jibi in Allah Ya kaimu, karfe goma na safe."
Tace, "ai nayi zaton gobene tafiyar. Allah Ya kaimu jibi din. Nima kwanciya zan je inyi."

Don haka yayi mata sai da safe. Ya jira har sai data haye sama kafin ya leka dakin Ammar ya samu yana barcinshi sosai, ya mishi addu'ar kwanciya barci kafin ya wuce sashenshi.

Ruwa ya watsa, ya fito daure da bathrobe ya tsaya a gaban mirror yana goge jikinshi. Bayan ya gama al'adar shafe-shafenshi daya saba, ya lalubi pyjamas ruwan madara masu taushi ya sanya. Ya sake bin jikinshi da turarenshi ya fesa.

Har ya nufi kan gado, sai kuma ya juya. Ya dauki wayarshi dake kan bedside drawer, ya fita daga bangaren nashi.

Gidan nasu babban gidane, an ginashi tun lokacin Mahaifinshi yana matsayin General ne. Wajene wanda yayi gadonshi tun Iyaye da Kakanni, daga baya kuma bayan rasuwarshi aka fadadashi aka hadeshi da wasu filaye. A yanzu kuma ya zama gida wanda za a iya cewa gari guda. Estate ce babba, wadda ta kunshi gidaje part-parts. Akwai bangarenshi, ga bangaren Ummah, ga bangaren Shukurah, bayan su ma akwai wasu parts din fiye da uku. Akwai waje na musamman da aka ware na motsa jiki, akwai wajen wasan yara, akwai babban garden da wajen shakatawa da shan iska, akwai madaidaicin masallaci a cikin gidan. Ga ma'aikata bila adadin da ko wane lokaci zaka samesu suna ta kaiwa da kawowa abinsu.

Ya wuce bangaren dake kusa da nashi, wanda kuma nan ne za a sauki Nadiya a cikinshi, ya shiga na kusa dana Ummah wanda na Shukurah ne.

Yanayin tsarin gine-ginen kusan duk daya ne da na sauran idan ka debe nashi da na Hajiya Umma.
Falon nata sai kamshin turaren wuta yake ga AC dake kara sanyaya dakin. Ya duba falon yaga bata nan, kai tsaye sai ya wuce dakinta.
Ya sameta tsaye tana kokarin ninke abin sallah, da alama sallah ta gama yi.

Ya wuce ciki kai tsaye ya zauna a gefen gado yana kallonta har ta gama ninkin, ta cire hijabin jikinta. Itama kayan barcin ne a jikinta, da alama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login