Showing 123001 words to 126000 words out of 142169 words

Chapter 42 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

753

wadda a lokacin tana Lokoja.

Haka Ummah ta fito ta samesu. Ta zauna a kan kujerar data saba zama, Nadiya ta zame tana gaisheta. Itama Shukurah sai ga ta ta zube har kasa din tana gaidata. Hakan ya matukar ba Nadiya mamaki kam har ta kasa boyewa, don kuwa tun zuwanta gidan wannan ne karo na farko data dukawa Ummah lokacin da take gaisheta. Kullum a tsaye take ko daga zaune bata ko dan rankwafawa.

A kwanakin da suka biyo baya haka zaman nasu ya cigaba da gudana. Shukurah bata tsokanarta da magana kamar da, sai dai kuma bata shiga sha'aninta, itama kuma bata shiga nata. Iyakarsu dai idan sun hadu a falon Ummah su gaisa, daga wannan shikenan.
Amma mu'amalarta da Ummah da ta Habibu din tana matukar bakin kokari wajen ganin cewa ta gyarata, tana kuma kokarin jan Ammar jikinta. Sai dai ta fahimci ba karamin jan aiki bane a gabanta. Don kuwa daga Ammar din har Babanshi suna da wani hali na wuyar sabo, musamman idan suka saba da halin mutum, suna da wahalar canza yanda suke kallonshi a cikin ransu.

Amma da yake da gaske din shirin take so, ba don komi ba sai don fahimtar da tayi Habibun ba ta tatan yake yi ba, ta Nadiya da abinda ke cikinta yake yi. Sai ta samu kanta da damuwa da fatan inama ace ita ce take samun wannan kulawar? Sai ta cigaba da zage dantse kamar yadda Anty Hadiza tace mata. Ta kuma dage da addu'ar Allah Ya tsari zuciyarta da kishi marar misali, da bakin ciki da hassada ga kowa. Wannan duk shawarwarin Anty Hadiza dinne, kuma cikin ikon Allah ita kanta tana jin dadin yadda yanzu duk bata jin wannan haushin Nadiya da take ji a da.

Sai yanzu take da na sanin rashin haihuwa da wuri, watakila da ko don saboda danta ko diyarta Habibu ya dinga ganinta da mutunci. Tana sane ta dinga afa contraceptives don kada ta haihu da wuri kada jikinta ya sakwarkware. Shawarar mahaifiyarta da sauran yan'uwanta. Gashi yanzu haihuwar take nema ido rufe amma shiru kake ji kamar an shuka dusa.

***

Wata uku da dawowar Shukurah din aka kira Nadiya gida, Abbansu bai da lafiya sosai suna asibiti a yanzu haka. Lokacin cikinta har ya shiga wata na shida. Ta tafi hankali a tashe.
Asibitin da aka kwantar da shi suka wuce kai tsaye ita da direba.

Ta samu wajen dankare da matanshi da yayan duk sunyi wani wujiga-wujiga. Lallai maigida duk rashin kirkinshi dai maigida ne babu zancen musu.

Ta shiga wajenshi ta sameshi a kwance ana mishi karin ruwa. Bayan sun gaisa da matan ta tambayesu ya mai jiki? Aka kaita wajen likitan daya duba shi tana tambayarshi me ke damun mahaifinsu?
Ya ciro wasu charts na gwaje-gwaje da aka yi mishi yana nuna mata tare da yi mata karin bayani.

Abban ciwon mara yake damunshi da kuma matsalar rashin yin fitsari. Idan ya tashi yin fitsarin musamman cikin dare ko da safe, baya iya yin da yawa sai dai yayi dan kadan. Kuma yana samun matsalar iya rike fitsari, musamman idan ya kwanta da dare sai dai yaji ya tashi cikin fitsari, ko kuma bayan ya yi fitsarin sai ya dawo yana diga kadan-kadan. Ga shi duk ya kumbura, kafafunshi da fuskarshi sunyi suntum.
Sun yi mishi gwaje-gwaje da dama, a awon PSA da suka mishi, ya tabbatar musu yana dauke da cutar Benign Prostatic Hyperplasia (BPH). Common cuta ce wadda aka fi samunta a dattijai maza wadanda suka haura shekaru arba'in a duniya, kuma ta fi yin kamari ga irin masu yawan aure-aure dinnan ko yawan neman mata. Bayan matsalar fitsari ma suna tunanin kodarshi ta dan tabu amma ba da yawa ba, akwai kuma yiwuwar yana fama da matsalar low sperm count. Don haka zuwa gobe zasu kara yin wasu gwaje-gwaje don su tabbatar da zarginsu.
Zasu dorashi akan magunguna, zuwa nan da sati biyu idan basu gamsu da aikin magungunan ba to sai sun kai ga yi mishi aiki gaskiya.

Tayi shiru tana sauraren bayanin da yake yi mata har gama, ta mishi godiya tare da tashi tsaye. Sai data tsaya ta fara biyan duk wani abu da aka biyosu ta sayi magungunan da duk abinda za a bukata kafin ta koma dakin da aka kwantar da shi.
Ta zauna anan tare da matan tana kara yi musu maimaicin bayanin da likita yayi mata har zuwa lokacin daya farfado. Suka dukufa a kanshi suna tambayarshi ya jiki?

Sai zuwa yamma sannan Babangida yaje da kanshi ya dauketa bayan ya shiga har dakin da aka kwantar da Abban ya gaidashi ya mishi ya jiki. Shima sai daya sake ganawa da likitan da case din Abban yake hannunshi. Likita daya fahimci ko surukin wanene yake kulawa nan da nan ya kara shiga cikin hankalinshi, kulawa sama da kasa ya sake daukowa ya dora akan Abba.
Suka rabu dashi akan cewa daga yanzu komi na kulawar Abba din yana hannun Habibun, don haka duk wani abu daya taso ya fara sanar dashi. Sannan koda aikin ne ya taso, to shi zai dauki dawainiyar aikin.

Yana komawa dakin ta tashi ta fara gyara lullubin jikinta don tasan karshen zancen. Mama ce da Lantana a wajen lokacin da yaje, ya duka yana yi musu sallama tare da sanya hannu a babbar rigarshi ya ciro sabin kudi wrapper na dari biyar ya mikawa Nadiya data karasa wajenshi, yace a ba Mama an siyawa Baba magani.
Ta mikawa Mama kudin wadda ta sanya hannu biyu ta amsa tana musu godiya tare da fatan Allah maidasu gida lafiya.

Suna bada baya Lantana ta kaiwa kudin nan damka tana lalasu a hannu baki har kunne, cewa take, "kai! Auren 'ya mace mai dadi idan aka dace! Don Allah kiga irin wannan abin alheri da Malam yake gani iri-iri daga aurar da mace daya kadai!"
Mama ta kalleta cike da takaicinta amma bata ce mata komi ba. Ta raba kudin nan gida biyu ta soke a zaninta, ta mikawa Mama daya rabin tana ce mata, "gwanda ki boye wadannan kafin sauran su zo su ga ni su sanya miki wawa. Allah na tuba kuma me za a siyawa Malam yanzu? Duk wani abu da za a bukata sun kawo sun ajiye mana fa!"
Tsabar haushi Mama kasa ce mata komi tayi, ta cigaba da jan carbinta tana lazumi abinta, ta bar Lantana na cigaba da santinta da zubawa Nadiya da mijinta Habibu godiya.

****

Cikin satin suna ta kaiwa da kawowa wajen duba jikin Abban wanda aka sallamo daga asibiti bayan kwana uku. Yara ana ta shiga da fita kullum kaje gidan kusan a cike yake da yaya da jikoki yan dubiya.
Bayan kwanaki sha hudu suka sake komawa, likita yace dole sai sunyi mishi tiyata saboda abun ya riga ya taba mafitsararshi ga kuma koda da take kokarin tabuwa.
Aka sanya ranar aiki, aka yi cikin ikon Allah aka yi lafiya aka gama.
Sai dai likita yace akwai yiwuwar ba lallai ya sake haihuwa ba. Kai auratayya din ma gaskiya zai iya daukar lokaci mai dan tsayi kafin ya iya.

Suna komawa gida bayan an sallamesu ya tara matan duka, ya yi musu bayanin abinda likita yace. Ya fada musu su dukansu ya basu zabin duk wadda taga zata rabu dashi ko kuma zata cutu saboda haka ta fada mishi, gwara kawai ya sallameta akan ya dinga shiga hakkinta. Suka yi shiru su duka suna kallonshi, Mama dai tashi tayi ta fita ma daga dakin abinta ta cigaba da ayyukanta da take yi. Yaya AbdulHadi ya sake siya mata firjin babba ta hada da dayan da take da shi, don haka abubuwan sanyi da take yi ana saida mata yanzu ta kara yawansu. Don kuwa yanzu har daga gidajen biki da suna aikawa ake ana yi a kai musu.

Suma sauran duk sai suka tashi suka fita alamun dai babu mai niyar rabuwar. Duk da haka sai ya kara tsayar da amarya, yace mata ita ce karama a cikinsu, wadda ko haihuwar fari bata yi ba. Ba zai iya cigaba da zama da ita ba bayan shi babu tabbacin zai iya ma tsinana mata wani abun nan gaba. Don haka tayi hakuri amma ya sauwake mata igiyarshi dake kanta biyu. Ta kuma yi hakuri ta yafe mishi idan ya taba yi mata wani laifi.

Daga Mama har Nadiya babu wanda yaji dadin wannan hukunci daya yanke, sai dai su dukansu sun san cewa hukuncin daya yanke shine dai-dai. Sai kawai suka yi mata fatan Allah Yasa hakan ya zame mata alkhairi kawai. Zumunci kam ai sun riga sun daura shi da yardar Allah, za kuma su ci gaba da yi koda bata gidan.
Ta je ta kwashe kayanta tayi sallama da mutanen gidan.

Su kuma matan suka rukufa a kan maigida ana ta aikin jinya. Wannan zaman jinyar da yayi duk shi ya kara tsayar da duk wani samu nashi, ragamar kulawa da gida ta koma hannun Mama da Nadiya. Don ma su Anty Jamilah da sauran Yayunsu suna nasu iyaka bakin kokarin.
Tuni su Salame aka dawo cikin hayyaci don sun gane dai babu fa wani Sarki sai Allah. Ranar nan Nadiya taje gidan duba Abban sai ta tsinto Salame a kofar dakin Mama tana tayata zuba kunun tsamiya da zobo a cikin jarkoki suna jerawa a firjin ita da su Maryam. Lantana din kuma tana bakin kofar kicin tana aikin taya Mama din dahuwar abinci.
Ta kama baki cikin mamakin wannan abu, a ranta tace, 'lallai dai wato in da ranka zaka sha kallo har ka gaji! Dama wannan rana zata zo?!'


7'7'7'7'


Watanni uku ne bayan hakan, suka nabba'a a falon Ummah su dukansu family din a ranar wata Juma'ah da dare a cikin watan Afrilu, inda ake fadin sakamakon zaben da aka gama gabatarwa a ranar Alhamis, jiya kenan. Kasancewar an daga zaben da kusan watanni biyu sakamakon wani canji da Gwamnati tayi na tsare-tsaren zaben, amma da tuni an yi an gama ma.

Tana zaune da rindimemen cikinta Tubarkallah, wani lokacin har rinjayarta yake yi idan zata tashi. Hannunta damke cikin na Babangida, bakinta dauke da Bismillah. Ji take yi kamar ta fada cikin Talabijin din ta dubo rahotannin da kanta.
A gefe daya Ummah ce da Shukurah da Mami da itama taje cikin satin da kuma babban danta Ma'aruf, wannan shekarar ya hada degree dinshi akan Social Work, a University of Washington Zarqa (Zarqa shine babban gari na biyu a cikin Kasar Jordan). Farida da Yayanta Fu'ad suna tare da mahaifinsu da bai samu damar zuwa ba saboda karatun yaran da kuma wajen aikinshi da ba a jima da yi mishi karin matsayi ba.
Ga sauran amintattun mutanensu duk suna warwatse a zaune a falon suna zaman jiran jin sakamakon in a bated breath.
Duk da cewa daga yadda ake fadin irin nasarorin da suka samu a wurare da dama, suna da tabbacin suna da jagorancin tafiyar, amma duk da haka basu sakankance ba.

Har zuwa lokacin da mai gabatarwar yace, "sai kuma gari na karshe wato nan cikin Katsina City, an samu kuri'a dubu arba'in ga jam'iyyar BOP, kuri'u dubu hamsin da biyu ga jam'iyyar CPA, da kuma kuri'u dubu tamanin da dari hudu da takwas ga jam'iyyar New Hope Party..."
Ya dakata da maganar na dan lokaci, Nadiya ta ja numfashi sama, "....Da wannan muke cewa Jam'iyyar New Hope Party ita ce ta lashe zaben wannan karon a jahar Katsina da rinjaye ga sauran jam'iyu da kuri'u har dubu goma sha biyu. Don haka muke cewa congratulations to our new Governor, Alhaji Habib Abdullahi Makam tare da shi da mataimakinshi Malam. Abubakar Khamis. Allah Ya baku ikon sauke wannan nauyi da ya rataya a kanku, Allah Ya tayaku riko!"

Falon gabaday sai ya dauki Kabbara da shewar murna da farinciki, aka shiga yiwa juna barka.
Ta rungumoshi cike da tsananin farinciki da murna, tace, "Congratulations Habibi!"
Murmushi yake sosai lokacin daya rungumeta shima, yace mata, "I know we will make it dama, Alhamdulillah!"
Ya duka ya tafi yayi sujjada anan wajen, ita da su Ummah duk sai suka rufa mishi baya. Suka kai goshinsu kasa suna yiwa Allah godiya da wannan nasara da suka samu.

Falo ya rincabe da murna da farinciki, wannan ya rungume wannan, wancan ya rungumi wancan, sai ga su ita da Shukurah sun rungume juna cikin rashin sani. Suka yi kokarin janyewa, Nadiya tayi karfin halin rike hannunta tana kallonta fuska cike da farinciki. Tace, "ina tayamu murna Anty Shukurah, Allah Ya bamu ikon taya mijinmu sauke nauyi da hakkin daya hau kanshi."
Sai tayi dan murmushi, tace mata, "ameen ameen Nadiya!"
Zuwa lokacin kam duk wani abu dake ranta ta saukeshi. Sai dai ta kasa sakin jiki da Nadiya ko kadan, sai ita din take kokarin shiga jikinta tunda dai ta kula ta sauko. Ko babu komi, tana son kwanciyar hankalin mijinsu. Bata son abinda zai raba mishi hankali ko kadan, shi yasa take kauna da kwadayin su hade kansu da ita. Bata kuma son abinda zai taba tarbiyar yaransu, tana so ne su tashi su dukansu cikin farinciki da kaunar juna, wanda hakan ba zai taba samuwa ba matukar suka tashi suka ga iyayensu kansu a rarrabe.

Ita din ai victim ce na irin tsarin wannan gidaje, ga gidansu nan kowa wanda suka fita ciki daya ta sani da kuma uwashi. Musamman kannensu dake tasowa a yanzu, zaka yi mamaki idan kaga karamin yaro na nunawa dan wani dakin yan ubanci tsantsa. Babu kuma yadda za ayi dasu tunda tushen matsalar daga iyayensu yake.

Mutane suka fara yi musu sallama suna tafiya tare da kara tayasu murna.
Zuwa karfe goma sha daya duk an watse sai su ne kadai a falon suna cigaba da maida yadda aka yi.
Ya dubi yadda ta kwanta tayi lamo a kusa dashi, ya kalleta cike da kulawa, "baby lafiya?"
Ta girgiza kai a hankali tana dan yin hamma, "babu komi, barci kawai nake ji."

Sai ya tashi tare da kama hannunta, yace, "to muje mu kwanta. Ai kin ma yi kokari yau. Ke da kike kwantawa tun karfe tara."
Babu musu ta mike, suka yiwa su Ummah sai da safe. Shukurah itama ta bi bayansu tana cewa itama kwanciyar zata je tayi.

Suna zuwa sashenshi wanka tayi, ta yi shirin kwanciya ta kwanta. Babu jimawa shima yaje ya bi bayanta ya kwanta.
Cikinta yayi wani irin girma mai ban mamaki, gashi har ta shiga cikin watan haihuwarta, duk scanning din da ake yi mata tace kada su duba mata gender ko wani abu. Tunda dai abinda ke cikin yana lafiya, idan ya fito sun gani da idonsu. Don haka yanzu bata iya aikata mishi komi. Duk da cewa yana mata matukar kara da kawaici, haka zasu kwanta da shi su tashi baya taba neman komai a wajenta duk kuwa da cewa tana ganin yadda haka din yake damunshi. Ta kuma yi suggesting ko ya dinga kai kwanan nata wajen Shukurah a lokacin da yaga ba zai iya jurewa ba? Yayi kici-kici da fuska a lokacin yace mata kada ta sake mishi wannan zancen baya so. Don haka bata kara tada mishi zancen ba.

Yadda taji yana shigewa jikinta da shafarta yasa taji ta fara shan jininta.
Yace, "celebrating nake yi Nadiya kada ki hanani, ai nayi kokari ko? Yakamata ace har award din Sarkin hakuri da dagawa matarshi kafa kika bani."
Ta dai san bata da bakin hanashi, don haka ta kyaleshi ya dinga juyata son ranshi. Har zuwa lokacin daya samu abinda yake so din, ya ja ta cikin jikinshi ya rungume tsamtsan kamar ya tsaga kirjinshi ya maidata ciki.


50.



An sanya ranar handing over wato ranar da za a rantsar dasu kwanaki arba'in masu zuwa. Ana sanya ran azumi nan da kwanaki uku, don haka a kiyasce dai bayan sallar azumi da sati daya kenan.

Duk cikin satin basu samu zama ba, suna ta karbar baki iri-iri yan taya murna da kuma shirye-shiryen karbar mulki da Habibu yake yi, don haka ba yawan zaman gidan ba ma yake yi.

Mami tana nan anan zata yi azumi, tace sai an shiga gidan Gwamnati da ita sanna zata juya ta tafi, saboda hutu ta dauka a wajen aikinta mai tsayi. Sessions da take yi da patients dinta kuma yawanci suna yi through Google Meet, don haka bata da matsala.

Suna ta shirye-shiryensu da tsara yadda suke ganin zasu tafiyar da mulkinsu, ita Nadiya ba ta wannan take yi ba. Don kuwa cikin kwanakin duk a tsaitsaye take, ita kanta tasan bata jin dadi amma kuma ta ma rasa me ke damunta. Shi yasa ma bata fadawa kowa ba kawai ta daure tana cigaba da al'amuranta.

Sun kai azumi na takwas, ta tashi cikin dare zata yi fitsari. Ita kadai ce a sashen nata saboda Habibu yana wajen Shukurah.
Tayi fitsarin ta koma ta kwanta, sai kuma barci ya gagareta. Zuwa can kuma sai wani fitsarin ya taho. Tun safiyar ranar dama ta tashi tana zubar da wani ruwa mai kala kadan-kadan. Ganin bata jin ciwon komi kuma EDD dinta sai nan da sati daya ma zai cika, sai bata kawo komi a ranta ba.

Wasa-wasa sai gashi ta fara zaryar zuwa bandaki. Tun tana yin fitsarin har abu yazo ya gagara, sai dai kawai ta tsuguna ta tashi. Tafi-tafiya ma sai tafiyar ta fara gagararta. Nan dai tasan abin ba na wasa bane. Sai ta lalubo waya ta kira Babangida, amma wayar tashi a kashe. Ta manta idan zai kwanta barci wayarshi a flight mode yake sanyata, ta sake kiran ta Mami itama din dai a kashe. Ta cije lebe, a ranta tace bari kawai ta lallaba ta tafi sashen nasu da kanta. Cikin ikon Allah kuma duk ba wani ciwo ne take ji na azo a gani ba, wani barci ma yake janta, don haka sai kawai ta koma ta kwanta.
Can taji kamar an mintsineta, ta fara jin ciwo a mararta da kwankwasonta sama-sama, nan ta sake tashi ta nufi bandaki. Kafin ta karasa sai jin wani abu ya fashe tayi, sai ga ruwa yana bin kafafunta.

Bata san lokacin data durkushe a inda take ba saboda wani gigitaccen ciwo daya riketa a take. Ta dafe baya tana murkususu har dai ta samu ciwon ya lafa.
Ta sake lalubo wayarta a sukwane tana bin jerin contacts dinta har idanunta dake wani dishi-dishi suka dira akan sunan Shukurah, ta danna mata kira cikin fatan Allah Yasa ta daga.
Sai data kusa katsewa sannan ta daga muryarta cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login