Showing 9001 words to 12000 words out of 142169 words

Chapter 4 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

439

a wasu masallatan, ta tura kai cikin gidansu ta shiga. Ace ma ta gaji fiye da kima, bata baki ne.
Gidan kwalam kamar babu mutane a ciki, in banda karar TV dake fita daga dakin Abbansu.

Taja tayi turus a bakin kofar dakinta, zuciyarta na harbawa da bugawa cikin wani yanayi marar dadi da taraddadi.
Kofar dakin take gani a bude, babu alamun kayanta a wajen ko a alama. Idan ma ba sani kayi ba, ba zaka taba cewa wani ya taba wanzuwa a wajen ba. An fara buge wani bangare na dakin, tare da kicin da Salame tasa aka ware mata lokacin da ake kan gyaran gidan. A maimakon kuma ta zuba kayan kicin din, sai ta kulleshi kawai tana zuba tarkacen kaya, da kayan sana'arta na kayan masarufi da take yi lokaci zuwa lokaci idan ta samu kudin yi.

Da alama mutanen gidan sun ji sallamar data kwala, saboda taga wasu sun fara lekowa ta bayan labule suna kallonta. Da alama akwai abinda suke tsammani.
Tsabar gajiyar dake cinta, bata iya amsa sannu da zuwa din da Maryam take mata ba, sai bin ta da kallo data yi, kafin ta kara kallon kofar dakin nata, ta sake maida kallonta ga Maryam din. Tace mata, "me ke faruwa ne a gidan haka naga an buge dakina?"

Mama ta fito daga daki da hijabi a jikinta, da alama sallah ta gama yi.
Tace, "Nadiya kece da wannan magribar?"
Sai ta kalleta kawai ta kasa mayar mata da amsa.
Mama ta cewa Maryam, "amso kayan hannunta mana ki kaisu dakina. Nadiya, shigo nan kinji?"
Sai dai duk yadda ta kai ga son ta motsa kafafunta ta kasa, yadda kasan wadda aka kafe a wajen.

Tace, "Mama ina zan je bayan kuma nan shine dakina? Menene yake faruwa wai? Ban gane ba!"
Kamar kuwa wadda take jira, Lantana tayi caraf tace, "me kuwa ke faruwa? Mai gidan yake bukatar wajenshi. Amaryarshi yake gyarawa wajen zama!"

Sai ta rasa me ma zata ji a lokacin. Kuka zata yi na wannan rashin adalci, ko kuma murnar karuwar da zasu samu zata yi? A gefe guda kuma tunanin matsayin da take dashi a wajen mahaifin nata take yi. Tana ganin ko rikonta ake yi, ai tana da hakkin a sanar da ita, a bata notice, ba wai kawai tazo ta samu dakinta a balle ba.

Abbansu ya bude kofar dakinshi ya leko, "wai lafiya? Hayaniyar me nake ji ne haka da wannan magribar?"
Ta juya tana kallonshi tare da dan rusunawa, "babu komi Abba. Kawai dai na ga dakina a bude shine nake tambayar lafiya?"

Ya gyara tsayuwa yana kallonta fuska a cune cike da alamun ko ta kwana, "ehh! Dakin nake bukata saboda aure ya taso min na gaggawa, akwai matsala ne?"
Ta girgiza kai a hankali, kunar zuciyar ma ta kasa ji, bata jin komi. Tace, "ni kuma ina zan zauna?"
Yace, "ki samu dakin daya daga cikin iyayenki mana ki zauna? Dama ai ba zaman gidan kike yi ba, kwanciya kawai kike yi a ciki. Kinga ai gwanda a amfaneshi da kyau. Kuma dama can ai na fada miki cewa wajene na wucin gadi, saboda ke dai matafiya ce, don haka ban ga dalilin ware miki daki a gidana ba!"

Ta jinjina kai a hankali, idanunta kyas hawayen ma sun ki fita. Wannan ba komi bane cikin halayen Abbanta. Wannan ba komi bane cikin dubannin abubuwan daya aikata a gareta. Ta kalleshi a nutse, tace, "hakane. Allah Ya bada zaman lafiya to!"
Ta juya tana kallon Maryam da suka yi tsaye cirko-cirko, ta umarcesu dasu dauke kayan su kai dakin Mama kamar yadda tace.
Shi kanshi sai yaji alamun rashin dadi a ranshi, amma ya fuske. Fitowa yayi da niyar idan ta kama har korarta yayi don yasan Nadiya da kafiya da taurin kai, bai taba tsammanin zata bari su wanye lafiya ba.
Yace, "ki zauna anan ki dan yi maleji, idan an gama bikin, zan sa a tada miki wancan wajen na kusa da kicin kafin lokacin barinki gidan yayi!"
Tayi dan murmushi kawai, saboda tasan karshen maganar kenan. Bata da wannan matsayin da zai batar da kudin da zai gina mata daki, ita ta sani. "To shikenan, Allah Yasa!" ta furta a sanyaye.
Da wannan ya koma dakinshi ya maida kofar ya rufe, har da murda sakata.
Sauran matan nashi suka kwashi jikkuna a sanyaye suka koma daki, har da mai jan tsaki. Saboda duk ba haka suka so lamarin ya kasance ba. Itama kuma ta san hakan, shi yasa yau dai taki biyewa zuciyarta balle a kai ga yin batacciya.

Ta shiga dakin Mama ta tarar da kayanta a gefe guda, dama ba wasu tarkace ne da ita ba na a zo a gani. Don haka ita da su Amina suka sama musu waje suka ajiye.
Ta samu ruwan zafi a flask din Mama, tayi amfani dashi tayi wanka, tayi sallah, ta dan fara samun natsuwar da take bukata.

Mama tana kan kujera a zaune da carbi a hannunta tana ja, ta kalli Nadiya data gama waya da Rabi'ah.
Tace, "yau dai kinyi kyan kai da baki bari zancen dakin nan yayi tsawo ba."

Tace, "ai gani nayi idan ma na biye mishi ba ribar abun zan ci ba, zai iya ma cewa in bar mishi gidan. Shi kuwa mutum da gidanshi ai ba zaka mishi takama ba, sai ka barshi yayi duk abinda yake so dashi."
Mama ta girgiza kai, "ke dai kawai kin san halin mahaifinku sai shi. Amma in banda haka, yanda yake takamar yana da hakkin ya umarceki ki mishi biyayya, kema fa kina da hakkin idan abu irin haka ta taso ya sanar dake, idan ma ta kama ya lalubar miki mafitar inda zaki koma da sauransu."

Nadiya tayi dan murmushi, "Abba ne fa muke magana a kanshi. Ke kinsan ai wadannan abubuwa ba damunshi suka yi ba!"

Gidan tsit kamar babu mutane idan ka debe hayaniyar yaran su Salamen dake wasanninsu a tsakar gida. Da alama yau Abba ya tabo ran matan gidan, don kuwa da ana zaune lafiya ne da yanzu suna dakinshi suna ta hira da shewa abinsu. Dan murmushi tayi tana girgiza kai, tasan sarai maganar auren ce ta girgizasu, amma na dan lokaci ne. Ai yanzu ne sabuwar riritawa da kulawa zata fara.
In dai auren Abbansu ne, su kansu yaran gidan sun saba balle matan.
Ita a karan kanta, da wayonta dai, ba zata iya cewa ga iya adadin matan da Abban nasu ya auro ba. 'Ya'ya ma kuwa kusan hakan take. Idan aka zauna lissafi akan jima kafin a kai karshensu.

Bayan tayi sallar isha'i, ta zauna ta warware jakar tsarabarta. Mama taji dadin kudin da Anty Jamila ta bata, saboda dama suna cikin rububin yadda za a biyawa Maryam kudin jamb ne duk da Nadiya din tace ita zata biya mata.
Kudin Abbansu kuwa sai Mama ta damkawa a hannu ta kai mishi, shima kuma yayi godiyar sosai da sosai.

Amina ta kai mata abincin da aka yi da dare, shinkafa ce da miya. Miyar yadda kasan a lokacin aka markada kayan miyar saboda bata soyu ba ko kadan, shinkafar kuwa ita da tuwo bambancinsu kadan ne.
Da kyar ta iya cokali biyu, ta ajiye ta ture kwanon gefe guda. Dole sai lekawa tayi kofar gida ta samu wani matashin saurayi data saba aike, AbdulGaniyyu, yaje bakin titi ya samo mata shayi da biredi da wainar kwai, saboda bata so ta kwanta bata ci komi ba tunda da Azumi take da niyar tashi.

Tare suka ci abincin da su Amina. Fatima, yarinyar da take hannun Lantana, rikonta take yi saboda mahaifiyarta bata gidan, taje domin Amina ta tayata home work dinta na makaranta, ta zauna itama aka ci da ita.

Suna kallo da hira tayi shirin barcinta. Ta fito da katifarta da aka kai kuryar dakin Mama, ta shimfida a falon kusa da kofa. Mama taso taje su dinga kwana akan gadonta tunda su Amina katifa suke shimfidawa a kasar gadonta, amma ta ki. Saboda ba zata iya hada wajen kwana da Maman ba.

Tayi kwanciyarta tana sauraren hirar da suke yi, har da karin ya'yan Salame da na Lantana da suka bi sahun Fatima.
Lokaci zuwa lokaci idan iyayen basu hana ba, yaran su kan leka dakin Mama ko suyi kallo ko kuma don su Amina su yi musu assignment.
Bata san lokacin da suka bar dakin ba saboda barci daya dauketa.

Ranar kwana tayi tana mafarkin daddadan turaren data shaka a jikin wannan mutumin da kuma yadda fuskarshi take cunewa lokacin da yake yi mata fadan ta dinga kallon inda zata.
******
Kwanaki biyu da yin haka, amma har an gama gyaran dakin da amarya zata tare fenti kadai ya rage. A cikin satin kuma aka daura musu aure. Saboda daurewa karya wani gu, Abbansu har Kamu ya hadawa amaryar tashi. Can aka tsinto bidiyo din yadda ya dinga barin kudin liki a wajen kamun a wajen yan ba-ni-na-iya din yan unguwarsu.
Don kuwa har gida suka yi sallama suka kaiwa matan. Mama data gani baki ta tabe tace 'Allah Ya kyauta.' Nadiya ma haka.

Don kuwa abin ya girmame mata. A ranar da safe ya gama tijara da ihun ba shi da kudin da zai biyawa yaran gidan na makarantar boko da islamiya. 'Amma da yake amarya ce, ita ai gata can yana mata barin kudi da na jiki a banza.'
Irin maganganun da taji su Lantana sun hade kawuna a kofar kicin suna ta furtawa kenan cike da bacin rai. Lokacin kuwa taje wucewa zata fita waje da safiyar Alhamis, tayi dan murmushi, tace, "a dai juri zuwa rafi, saboda watarana tulun zai fashe!"

Salame ta zaburo mata, "ke karamar yar iska! Allah dai Yasa ba dani kike ba don naji me kike cewa sarai!!"
Tayi banza ta kyaleta ta kara gaba abinta tana dariyar mugunta.
Yadda taga maganar bikin ta gigitasu gabadaya abin dariya yake bata. Ko kuwa dai don Abban ya jima bai yi auren bane shi yasa suka fara mantawa har suka saki jiki suna tunanin ko shikenan? Ta tare abin hawa ta tafi wajen aikinta abinta.

A shago ta tarar da Aramide. Tayi mamakin hakan saboda ranar aiki ce, koda zata je bata cika zuwa da safe ba sai can yamma idan ta tashi daga aikin. Kuma mafi yawanci ta kan je ne kawai don ta karbi wasu abubuwan ko kuma kudi idan bata da su a hannu.

Ta shiga dakin da take canji ta rataya Apron a saman doguwar rigar jikinta.
Yadda taga dakin a hargitse ya tabbatar mata da cewa lallai Aramide anan ta kwana. Tayi tsaye cikin mamaki tana kallon Aramide din da tayi zaune akan arm chair, sai lokacin ta kula da yadda tayi wani jugum-jugum kamar wadda aka yiwa mutuwa. Gefen fuskarta daya yana can gefe guda ta ki yarda su hada ido da Nadiya.

Ta taka ta matsa gabanta cikin nuna alamun damuwa, tace, "Ara, me yake damunki ne wai? Lafiya?"
Kai kawai ta iya girgiza mata bata ce komi ba. Ganin haka sai ta dafa kafadarta tare da juyota ta kalleta, ai bata san lokacin data ja da baya ba hannu dafe da kirji tana zare ido a kidime. Gefen fuskarta ya hau yayi wani irin kumburi, idonta a rufe yake ma ruf da kyar take iya daga shi.
Tace, "innalillahi wa Inna ilaihi raji'un! Aramide me ya sameki ne haka? Waye yayi miki haka?"

Dama mai neman kuka ne aka jefeshi da dunkulen kashin awaki, tana jin haka sai kawai ta dargwaje da kuka. Tayi-tayi har ya isheta, Nadiya ta kasa ce mata komi sai ban baki da kokarin tausarta da kalamai masu dadi. Zuwa lokacin data gama kukan, fuskarta ta gama baci da hawaye da majina. Ta dauki tissue tana goge fuskarta tare da fyace majina.
Cikin murya data gama dusashewa da kuka take cewa Nadiya, "wallahi na gaji da wannan cin kashin da ake yi min Nadiya, na gaji! It's either in kai mutum kara ko kuma in kai kararshi wajen iyayenshi!"

Nadiya sai tayi sakato! tana kallonta cike da daurewar kai, tace, "wa ke nan? Ba dai maigidanki ba ko?"
Ta jefa mata harara cike da kulewa, "idan ba shi ba ta ya kike tunanin zan bari wani gardin yayi min wannan danyen aiki?"
Ta daga kafada tana dan tabe baki, "na sani?!"

Tayi kwafa tare da yin tsaki, "ban taba fadawa kowa halin da nake ciki ba har iyayena kuwa. Amma yanzu tura ta kai bango, na gama gajiya. Nadiya mutum ya mayar da ni kamar jakka, abu da wanda ya kai da wanda bai kai ba kawai sai kiga mutum wai ya hau ni da bugu babu gaira babu dalili? Ina dannewa ne ina cijewa saboda bana so a ga kamar na cika korafi ne, kuma bani da isasshiyar shaida saboda sau tari yana yin bugun nashi ne a inda mutane ba zasu gani ba balle a zargeshi da wani abu. Amma wallahi yau ya tsokanowa kanshi! Ke wallahi kotu kawai zan maka dan iska fakat babu wani jan dogon zance!"

Nadiya dai ta baza kunne tana sauraronta, ranta rabi cike da tausayi rabi kuwa dariya ce take tuketa tana dannewa.
Tace mata, "ba haka ya kamata ayi ba saboda komi na duniyar nan fa da kike gani dan hakuri ne. Idan kika kaishi kara yanzu saboda kina cikin fushi, kuma nan gaba kuka shirya to da wane ido zaki kalleshi da yan'uwanshi?"

Tace, "ai dama tsakanina dashi kotu zata shiga ba wani abu ba, don wallahi ba zan zauna ya nakastani a banza ba! Wai ma kinsan ko saboda me yayi min wannan mahangurbar?"
Nadiya ta girgiza kai.
Tace, "kawai saboda ya tambayeni ina links din hannun rigarshi nace ya duba cikin kayanshi. Kawai sai ji nayi ya kai min naushi a gefen ido! Ya kuma hau ni da jibga kamar wata jakar gidansu! Wai na raina mishi wayo saboda yana min magana ina maida mishi amsa gatsar babu ladabi! Nadiya mutum ga gori, ga shi da dan karen rashin mutunci. Duk wasu abokaina ya rabani da su saboda rashin mutuncin da yake musu idan sun zo inda nake. Yanzu abin ya tashi a kansu ya koma kan yan'uwana da dangina. Shikenan ranar nan har jaka yace min saboda na cinye malmalar amala hudu a gabanshi!..."

Nadiya kuwa me zata yi ba dariya ba. Ta dinga kyakyatawa har tana tuntsurawa.
Aramide ta tsaya tana kallonta cike da takaici. Sai da taga bata da alamun dakatawa sannan ta dada mata duka a cinya, tace, "baki da kirki wallahi Nadiya. Wato ma maimakon ki tausaya min shine zaki sanyani a gaba kina min dariya ko?"

Ta kai hannu tana goge hawayen da suka cika mata ido saboda dariya. Tace, "abin naku ne ai gwanin ban dariya. Kinga nan gaba sai ki dinga ba mutane shawara, a dinga hurawa kafin a ciza!"
Sai tayi turus tana kallonta. Ta yada kai gefe guda, tace, "ashe maganar nan ba zata taba wucewa a wajenki ba?"

Nadiya tayi saurin girgiza kai, "a'ah wallahi, ke kin fi kowa sanin cewa tuni data gama wucewa a wajena, kawai dai wata magana da kika taba fada min ne na tuna shine ta bani dariya..."

Sun hadu da Aramide a ABU Zaria, Division of Agriculture (DAG) inda duk suke karantar Home Economics. Itama Aramide haifaffiyar Kaduna ce amma iyayenta dukansu yarbawa ne, aiki ne ya kaisu Kaduna. Idan kaji Hausa a wajenta kuwa yadda kasan jakar Kano. Tasu tazo daya sosai da Nadiya, suka kulla kawance sosai.
A shekararsu ta karshe dai suka koma cikin ABU da zama sai suka hada suka kama gida off-campus.

A shekarar ne Allah Ya hada Nadiya da wani saurayi AbdulGaniyyu, shima Yoruba ne amma mahaifiyarshi bahaushiya ce. Yana da iliminshi babu laifi kuma yana aiki a Kaduna a hukumar NNPC. Babban mutum ne ba laifi, don ya ba shekaru talatin baya amma bai taba aure ba.
Yana da yawan hidima sosai, ga kyauta. Don kuwa kullum tafe yake da abubuwa iri-iri, kayan makulashe da tande-tande, kayan kawa da ado, har waya yaso ya canza mata a lokacin amma ta ki saboda ita har ga Allah bata da kudirin aurenshi saboda sam-sam bata jin auren nashi a cikin ranta ko kadan.

Bata san ya aka yi ba, ko cikakken watanni hudu basu yi da haduwa ba don har ya fara zancen idan suka je gida hutu wannan karon zai tura gidansu a tambayi aurenta. Kawai sai taga mutum ya janye mata rana daya. Sai ga Aramide ta fara fantamawa iyaka son ranta, tayi sabon saurayin dake mata hidima yana mata kashe-kashen kudi. Tun tana jin wai-wai a gari har dai ta gansu da idanunta, ya dai tabbata lallai Aramide ta mata snatching din sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?urayi. Tace umma ta gaida aysha don kuwa dama bata cikin yan kayan. Ta zuba mata ido tayi ta boye-boyenta, daga baya dai da kanta taje tana mata kame-kamen zance, wai wallahi kai tsaye gidansu ya aika yace yana sonta kuma iyayenta suka amsa da sun yarda shi yasa ita kuma bata zauna yin musu da su ba saboda ba zata iya bijire musu ba duk da tasan cewa hakan bai dace ba.

Nadiya dariya tayi sosai a lokacin, tace mata kada ta damu don kuwa ita har ga Allah abin bai dameta ba don dama bata sa a ka ba. Ta kuma yi musu fatan alkhairi, tace in dai namiji ne taje gashi ga ta nan.
Daga haka basu kara tada maganar ba. Suna gama makaranta kuma aka daura musu aure. Nadiya tayi musu kara sosai wajen halartar bikin da hidimtawa sosai a matsayinta na babbar kawa. Shima kuma AbdulGaniyyu din har aka yi aka gama bai taba nuna mata wani abu ba ko a fuska, don haka itama bata taba nuna mishi wani abun ba.

Biki aka yi gagarumi, irin nairar da aka barar abin sai ya baka mamaki. Amarya ta tare a gidanta dake Korau road, ita dai Nadiya tun washegari da suka koma suka kammala gyara mata gida, bata kara waiwayarsu ba.

Tare suka shiga camp da Aramide, da Allah Yasa itama tayi marriage certificate sai aka barta anan Kaduna.
Bayan sunyi service dinsu, Aramide din ta bata shawarar mai zai hana su kama hayar wajen da zasu bude shago na kayan ciye-ciye? Tunda ita Aramide din ta samu aiki a kamfanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login