Showing 135001 words to 138000 words out of 142169 words

Chapter 46 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

474

da jin haka sai jikinta ya fara rawa, ita tana neman mafitar da zata fissheta ashe shuka ce tayi a idon makwarwa! Ta fara lallashinta tana kokarin ta samu su rabu lafiya, amma matar nan fir ta ki.
Ransu ya hadu ya baci a lokacin, sai ga shi sun fara sa-in-sa da musayar kalamai ta cikin wayar har da gore-gore. Hajiya Zainab tayi rantsuwa ta maya kan cewa idan har ba zata mata hanyar nan ba, ita kuma tayi alkawarin sai ta fallasata.
Ta fusata ta kwaso wani mahaukacin zagi ta laulaya mata, tace, tayi duk abinda zata yi. Tunda dai bata ga laifin da ta aikata ba ai babu dan iskan daya isa yace zai kamata. Wannan waya haka suka rabu dai baran-baram.

Washagarine ta sake kiran Hajiya Zainab da niyar su yi sulhu, don kuwa ita ce kadai take ganin tsayayya ta fanninta da idan ta samu matsala da ita to tana ruwa.
Sai tace mata taje Lagos ta sameta kawai su tattauna a nutse saboda maganar ta fi karfin ayi ta waya. Bata san da abinda ta shuka mata ba ta amince mata a take, ta shirya ta tafi. A shirinta idan sun gama shiryawa da ita, ta sa Balogun ya rabu da harkarta, to zata yi kamun kafa da ita, ko da cin hancine ta bada don a bata wannan fili data sanyawa ido. Ita kuma Nadiya zata ci kaniyarta ne. Idan ma ta bata haushi to wallahi zata iya yin abinda tayi aka tuge Habibun a kan mulki ko kuma ta hanashi yin ta-zarce. Da wannan niyar ta hau jirgin Lagos ta tafi.

Ashe ita Hajiya Zainab ta gama shaka da abinda Madam din ta mata. Dama abotace suke yi ta cudeni in cudeka, babu Allah babu kauna ta fisabilillahi a cikinta. Kuma dama dai ita Zainab din ta jima tana bakin ciki da hassadar halin fantamawa da Madam din ke ciki. Saboda Madam ta kasance mai matukar tutiya da tinkaho, duk wani hali da take ciki na nasara to kawayenta sai sun ji, ta dinga fadi musu kenan tana nanatawa, ga shi kuma matakan nasara tana ta hawansu, kasuwancinta yana buduwa a kullum, bata kuma kunya ko shayin goranta musu hakan da musu burga. Wannan yasa da damansu kawai suna zaune da ita ne saboda abinda tare da ita zai musu, amma ba don suna sonta ba ko suna jindadin zama da ita din ba.

Hajiya Zainab tace dai ita ta gaji da wannan rashin mutuncin, kwanton bauna ta mata, tana jiran samun weakness dinta ko daya ne wanda zata yi amfani da shi ta janyota kasa daga matakalar data haye, to da yake Madam din tana da kaffa-kaffa, kuma tana kokarin gudanar da kasuwancinta bisa bin doka da ka'ida na kasa, sai bata samu komi a kanta ba sai yanzu.
Kai tsaye ta kira yan hukumar kula da safarar miyagun kwayoyi a Nigeria wato NDLEA ta fada musu Madam din tana safara. Su kuwa dama zaman jira suke yi, kuma a sace sun jima suna bibiyar Alhaji Shehu Balogun din da wannan zargin amma da yake mutum ne mai dan banzan wayo da kuma cewa yana da hadin baki da manyan kasa a cikin maganar, sai hakansu bata cimma ruwa ba. Don haka suna jin cewa matarshi ce, sai kawai suka bankado tsofin files dinsu, suka yi ram da Madam a airport ba tare da ta kai ga haduwa da ita Hajiya Zainab din ba. Suka kuma gudanar da bincike a Kaduna inda suka samu wadannan kwayoyi a wani daki can da aka boye a kasan store din da suke ajiye energy drinks dinsu a Arena din Madam. Da kuma suka bibiyi lamarin, sai aka kama mota shake da wadannan lemuka, a karkashin kwalayen kuma hodojin iblis ne. Suka kuma bada shaidar daga can suka daukosu. To a rubuce a jikin takarda dai Arena mallakin Madam din ce da duk abubuwan dake cikinta, don haka ita suka sani, kuma ita suka kama.

To ga wannan manyan shaidu dake hannunsu, ga kuma matar Brigadier data bada ajiyar Madam din. Kowa kuwa yasan Brigadier din shi yake rike da Lagos a wannan lokacin, har ya ma fi Gwamnati fada-a-ji. Don haka babu zancen sakin Madam.


54.



Su duka saurarenta suke yi cike da tsananin mamakin jin wannan abu.
Nadiya ta kalli Madam din jikinta a sanyaye, tana jin wani abu mai kama da bacin rai na shiga jikinta. Tace, "yanzu Mommy kina son cewa mijinki dealer ne na kwayoyi, kin kuma san da haka din amma kike zaune da shi? Har ma kike kokarin kin sanar da hukuma hakan duk da cewa ana gudanar da cinikayyarta a kan idonki?!"

Madam tace, "to ni ina ruwana Nadiya? Yayi harkarshi inyi tawa, as long as bai ja ni cikin matsalar data sameshi ba game da hakan ni ai bani da wata matsala da shi. Shekara da shekaru kuma a haka din muke, babu abinda ya taba faruwa sai yanzu."

Kawai gani suka yi Anty Hauwa ta mike tsam, zata fita tana share hawaye. Nadiya ta rikota tana rokon tayi hakuri ta koma ta zauna, don ita kanta bata tunanin zata iya zama ta cigaba da sauraron abinda ke fita daga bakin Madam. Da kyar ta koma din ta zauna, amma ranta ya gama baci, hakan kuma bai boyu ba akan kyakkyawar fuskarta.

Ta kalli Madam tace, "ke yanzu ko kunyar kanki baki ji ba, ki kallemu wai kina fada mana kin san mijinki ba mai halastacciyar sana'a bane amma kike zaune da shi a haka? Zahra'u ina zaki kai son duniya ne wai da mukami da son arziki? Muna kallonki a matsayin wadda tayi fice da zarra a cikinmu muna jin dadi da godewa Allah, ashe ba ta hanyar halali kike samun kudin ba?"

Ta bata fuska itama tana kallon Anty Hauwa din, "a'ah, ni fa ki daina hadani da wannan harkar tunda dai ba yin ta nake yi ba. Ni wai ina ruwana da abinda yake yi ne kam? Ni dai nasan kasuwancina na halaline, kuma ban yarda ya gauraya min kasuwanci da nashi ba, to ni ina laifina anan?"

Anty Hauwa tace, "aikuwa ke ma kina da naki kason laifin, har ma fiye da nashi din. Don me yasa ba zaki kai kararshi ba? Don me yasa kike boye laifinshi? Bugu da kari kuma da kike cewa wai kudinki na halal ne kema, how sure are you ba da kudin haram din kika fara kasuwancin ba tunda tun asali da kudinshi kika fara?"
Tace, "ai lokacin bai fara wannan sana'ar ba, sai bayan ma dana maida mishi kudin dana ranta na fara kasuwancin nawa sannan!"

Anty Hauwa ta kalleta kamar ta bugeta don takaici, tace, "to me kenan kika yi? Hakan dai ai ba shi zai wankeki daga cewa kina sane da shi ba kika kyaleshi ko?"

Ganin maganar tasu ta ki mutuwa, kuma ga lokacin da aka basu yana gudu, sai Nadiya ta dakatar dasu.
Ta kallesu duka tace, "Mommy, wadannan duk uzirirrika ne kawai kike badawa amma ba zasu taba wankeki daga zargin da kike ciki ba. Saboda a tsari da doka ta kasa ma, idan kasan mutum yana aikata wani laifi, to koda kaima din baka aikatawa matukar dai ka sani din, kuma wai har kokarin kare mutum kake daga sanin hukuma, to kuwa daurin kudin goro ake muku, don haka kema kina da naki laifin. Ban kuma taba zaton cewa zaki iya aikata irin hakan ba sam. Kina sane da diya a tsakaninku, yanzu idan kika janyo Safiya cikin zancenku fa? Ki ce mata me idan ta ji wannan abin kunyar?"

Madam tayi kasa da kanta tana muzurai. Ta share hawayen fuskarta tana kallonsu dai-dai lokacin da constable din data kai Madam ta koma daukarta, tace, "yanzu mafita zamu tsaya mu nema. Me ya kamata mu yi? Kuma ta yaya zamu shawo kan wannan matsalar?"

To amma har aka dauke Madam din a gabansu tana kara rokonsu da kuma yin magiyar su taimaka su dauketa daga wannan azababben waje, basu gama sanin takamaiman abinda yakamata su yi ba.

Wasa-wasa sai karamar magana ta zama babba, sai ga shi sun share kwanaki uku a nan suna ta buga-buga da neman yadda zasu yi. Sun samu ganin har Commissioner of Police, amma abinda ya fada musu shine case din gabadaya ba a hannun yan sanda yake ba yanzu, a hannun NDLEA yake don haka babu abinda zasu iya yi a kai.
Sai gashi connections din Madam da take tutiya dasu sun kasa tsinana mata komi. Duk wanda yaji a irin halin da take, sai ya hau mata yan kame-kame da zamiya, daga karshe dai babu wanda za su sake ji daga gareshi.

Abin sai data kai har shi da kanshi Habibu yayi tattaki yaje Lagos din, sannan ne suka samu da kyar aka bada belinta. Case din su an mayar dashi can Abuja, zamansu a kotun zai kasance sati mai zuwa. Haka suka tattara suka dawo Kaduna jikkunansu a sanyaye.
Duk wannan abin da ake yi, an nemi Alhaji Shehu Balogun da amintaccen na hannun damanshi a Nigeria an rasa. Tuni suka daga kasar waje.
Amma da Madam ta tsananta bincike, sai aka tabbatar mata da cewa yana Nigeria, a Porthercourt gidan wani amininshi da yake tsohon soja ne da yayi ritaya, yana bashi tsaro.

A wuya take da shi kwarai, kai da kowa ma na duniyar nan. Taga tana zamanta kalau yaje ya janyo mata wahala, ya kuma koma gefe ya boye abinshi saboda tsabar rashin kirki. Tace ashe har yanzu bai gama saninta ba!
Allah kadai Yasan yadda aka yi, a zaman kotu na farko da aka yi sai ganin Alhaji Shehu Balogun suka yi ya bayyana a kotu. Ana zaune kafin shigowar Alkali, wasu samudawan kattai guda biyu suka shiga dashi kotun rike da hannunshi, daga gani dai ba shi da niyar zuwa, suka ajiyeshi a can benci na karshe suka kuma zauna a gefenshi don tsaronshi kada yayi yunkurin guduwa.

Madam tana sahun gaba a zaune ta maka wani dankareren bakin gilashi, ta juya tana kallonshi tare da zame gilas din fuskar tata yadda zai kalli tsakiyar idanunta da kyau, sai ya kawar da kai gefe daya a muzance.
Nadiya da Anty Hauwa da Uncle Yasir duk suna zaune a gefenta har zuwa lokacin da Alkali ya shiga, bayan sun zauna aka kira shari'ar ta su. Madam ta tashi taje gaban alkali ta durkufa. Bayan an gama bayanin abinda ake zarginta dashi, aka tambayeta shin da gaske hakane? Tace 'a'ah'. Ta yiwa alkali bayanin duk wani abu data sani akan harkokin Alhaji Shehu din, ta kuma gabatar da takardun harkokinshi na kwayoyi da yake boyewa a cikin safe dinshi, yayi zaton bata san pin dinshi ba. Lauyan data dauka ya kara gabatar da wasu shaidun wadanda ma'aikatanta ne da kuma wadanda aka zakulo cikin wadanda suke taya Alhaji Shehu din safarar miyagun kwayoyin.

Ta ko'ina an yi mishi kawanya, saboda sun gabatar da duk wasu shaidu da takardu a gaban Alkali wadanda ya yarda da amincinsu ya kuma karbesu a take.

Ya daga kai daga kan takardun da magatakarda ya mika mishi, "kotu tana bukatar ganin Alhaji Shehu Balogun idan yana kusa. Idan kuma baya kusa ta bada awa biyu kacal a zo mata da shi gabanta a duk inda yake!"
Wadannan kattin maza da yan sanda haka suka tisa keyar Alhaji Shehu Balogun zuwa gaban Alkali manta sabo. Sanin cewa an riga an daureshi da jiniyoyin jikinshi yasa bai yi wasa da hankalin hukuma ba, ya amsa laifinshi a take. Ya kuma fadi sunayen abokan kasuwancinshi da kotu ta bada dokar tana bukatar a gurfanar dasu a gabanta su dinma nan da kwana uku.

Bayan shaidun da aka gabatar a gaban Alkali da wadanda hukumar NDLEA itama ta hada, Alkali ya fadi sakamakonshi. An yankewa wadanda aka kama da kwayoyin suna rabawa shekaru goma sha biyar a gidan yari da aiki mai tsanani. Alhaji Shehu Balogun da yake shine mai distributing da kuma sayenta da sayarwa da safararta, an yanke mishi shekaru ashirin da biyar a gidan yari da tara mai tsanani. Madam kuwa duk da cewa kotu ta wanketa daga laifin da ake zarginta da shi, to amma kotu din bata manta da cewa Madam din tana sane da ayyukan maigidanta ba kuma maimakon ta sadashi da hukuma sai ma take kokarin boye laifin nashi, tana da zabin zuwa gidan yari na tsayin watanni goma sha biyar ko kuma a ci ta tarar kudade masu dimbin yawa. A take tace da Alkali taji ta amince zata biya tara. A haka wannan taro ya watse.

Suka tsaya a kofar wajen suna taya juna murna da son barka. Jindadinsu su duka shine yadda aka gudanar da komi ba tare da wani dan jarida ya samu labarin abinda ke faruwa ba. Akwai rumors dake tashi sama-sama, amma kuma babu mai labarin abinda ke faruwa takamaima face shakikansu. Hakan ba shi ya hana jikin Madam yin sanyi ba sosai da sosai. Wai dama haka mutane suke da duniyar baki daya? Yanzu-yanzu mutum yana kaunarka amma kuma jimawa kadan bashi da makiyi kamar ka? Babu ma ya Mijinta Alhaji Shehu Balogun, ta ga ita har ga Allah bata nufinshi da cuta, tunda da tana da niyar hakan da tuni tayi. Tana sane kwarai da bibiyar matan da yake yi kamar wani dan bunsuru, bata taba nuna mishi hakan ba duk wai don a zauna lafiya ne, su taru su duka su rufawa juna asiri. Ashe shi a ranshi ba haka bane?

Suna nan tsaye aka fito da su za a wuce dasu zuwa gidan gyaran hali, hannu daure da ankwa.
Ta roki dan sandan daya rikoshi daya bata yan mintuna tayi magana da shi. Babu musu ya dan ja gefe daya yana fada mata ya basu minti biyu.

Ta kalleshi sama da kasa, wani murmushi na takaici akan fatar bakinta, "ba haka kaso lamarin ya kasance ba ko Shehu? Sai kuma da yake Allah Ya fika, kuma Shi ba azzalumin bawa bane sai gashi reshe ya juye da mujiya!"
Ya saki wata yar dariya, "kada kiyi tunanin wai kin ci nasara Zahra, kada fa ki manta da cewa kada mage ba yanka bane. Don kuwa abinda kike so ba zai taba faruwa ba, nan da dan lokaci zaki ganni na fito na cigaba da harkokina. Ba dai Nigeria ba ce?"

Ta tabe baki, "wannan kuma matsakarka ce Malam. Za ka bani takardata ta saki ko kuwa sai mun sake durkufa a gaban Alkali a karo na biyu?"
Ya jefa mata wani irin kallo kamar wata wadda ciwon hauka ya kama, "saki kuma? Ai ni da ke babu wannan abun wallahi. Kuma ko shekara dari zan yi a gidan yarin wannan, to ba zan taba sakinki ba. Sai dai mu mutu daga ni har ke a haka!"
Ta saki wani dan murmushi mai ciwo, "zamu gani ne ai!"
Ta wuce ta barshi a nan.

Masauki suka koma su dukansu suka huta daga wannan kujiba-kujiba da suka sha. Washegari duk suka tafi suka bar Madam anan. Don kuwa tace ba zata bar Abuja ba sai ta tabbatar da cewa babu auren Alhaji Shehu a kanta.

Nadiya ta koma Kaduna. Bayan sun zauna da Habibu ta mishi bayanin abinda Maidakin Shugaban Kasa take bidarta dashi, ya bata goyon bayanshi dari-bisa-dari. Don kuwa cewa yayi, 'bai ga wanda yayi deserving hakan ba kamarta'
Don haka da karfin gwiwarta ta mayarwa First Lady da amsar cewa ta amsa tayin gayyatarta.

Bayan wannan abu na farko da tayi shine kokarin samo gurbin karatun 'Communication and Public Relations' a Jami'ar Washington DC, ta online. Domin ta samu ta kara karfafa sanayyarta akan al'amuran da suka shafi mutane don gudanar da aikinta cikin dadin rai.
Itama Shukurah ta samu Malama ta musamman data kware akan Politics tana zuwa har gida tana yi mata tambihi akan siyasa da abinda ya danganceta. Don haka ta kowane bangare dai, His Excellency Alhaji Habib Abdullahi Makama, da iyalanshi suna kokarin rike amanar da Allah da Talakawa suka dora a hannunsu.

Madam dai tunda ta samu da kyar da jibin goshi aka raba aurenta da Alhaji Shehu a kotu, ta tsallaka itama ta bar Nigeria. Don kuwa sai a lokacin ne yan jarida suka samu labarin abinda ke faruwa. Nan suka yi mata caaa, kamar zasu cinyeta danya. Wayarta ma sai kasheta tayi gaba daya saboda yawan kira data dinga samu.
Ummah tace mata taje ta sameta a Saudiyyah suyi Umarah, in taga zata iya zama to ta zauna a can har kura ta lafa sai su koma tare. Don haka ta yiwa garin Makkah tsinke.

Tunda ta sauka a masaukin Ummah wanda ya kasance gidane irin na baki (Guest Inn) a madadin hotel, babu abinda suke yi sai ziyartar ka'abah da masallacin Harami. Su yi sallah, su yi dawafi, su bada sadaka, su koma masaukinsu. Wasu ranakun su tafi Madina, wasu ranakun kuma su shiga kasuwanni ko kuwa su je kananun garuruwa wajen abokan cinkayyar Ummah wanda Madam din ta fahimci tana da jama'a da dama a nan.

Ummah kullum cikin yiwa Madam fada take da nasiha a hankali cikin hilata don kada ta ji kamar fada take yi mata. Ta kan ce mata, 'kin dauki rayuwa da girma kwarai da gaske Zahra'u, shi yasa kike da yawan buri. Son abin duniya ya na neman ya miki yawa, hakan kuma shi ya sanya idanunki suke rufewa ki kasa bambance tsakanin fari da baki, d'a da bako, yan'uwa da makiya. A ta haka ne watarana ke da kanki sai kin nemi kanki kin rasa. Ki sassautawa kanki, ki dan dagawa duniya da neman kudi kafa, ki kama Allah da iyayenki da 'yan'uwanki, ki kuma zama mai kyautatawa duk wani wanda zaki zauna dashi koda kuwa baki sanshi ba. Saboda ita duniyar nan da kike gani ba madawwama bace, kuma bata da tabbas. Yanzu a duniya kin taba zaton mijinki da aminiyarki zasu taba aikata miki kwatankwacin abinda suka aikata miki? Amma sai gashi sun aikata din, kinga wannan kadai shi zai nuna miki ainihin ko wanene mutum? Wani kwayar halitta wanda bashi da tabbas koda na dakika daya ne. Yanzun nan yana sonka, amma anjima kadan kuma baya sonka. Don haka ki kama Allah kawai, ki nemi lahirarki tun kafin lokaci ya kure miki."

Ta karbi maganganun Ummah da gaske, ta kuma daura aniyar gyara halinta da dawo da rayuwarta bisa kan tsari da ka'ida.
Abu na farko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login