Showing 105001 words to 108000 words out of 142169 words

Chapter 36 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

470

kyautata mishi ba dama, shima sai ta dauki duk wata tsanar duniya ta dora mishi. Ba damar taga ya tunkareta sai ta hau zaginshi da hantara da kyara, wani lokacin har da bugu.
Akwai wata rana data kamashi da duka saboda yace mata, 'Mama'
Ta daki yaron nan kamar wadda ta samu sa'anta tana bugu, zagi da alkaba'i kuwa iri-iri.
Ummah tana bayi tana wanka ta dinga jiyo kukanshi kamar wanda ake yankawa, babu shiri ta fito a sukwane, jiki duk kumfa taje ta kwaci yaron nan a hannunta. Ta daga hannu zata mareta, sai taga ma ai bata lokaci ne, halin Hadiza wanne ne bata sani ba? Kawai ta kama hannunshi suka wuce dakinta ta samu ta lallasheshi. Shima dai tun daga ranar nan da ya sha kashin wannan, sai ya fara baya-baya da ita, tsoronta ya shigeshi sosai da sosai.

Suka cigaba da lallaba rayuwa a haka, Ummah tana ta kara warwarewa jiki na kyau. Sumayya ta shiga aji na shida na sakandare zata zauna waec. Abdullahi da kanshi ya kaita ta cike Jamb, ta cike Medicine a Usman Danfodio University, babu yadda Ummah bata yi da ita ba akan ta cike makarantu na nan kusa dasu mana. Amma tace ita kawai Makarantar ce tayi mata. Don haka bata tsawwala ba, sai tayi mata fatan alkhairi kawai.

Suna nan ranar nan sai suka wayi gari ta dinga jiyo hayaniya kamar fada-fada a dakin Hadiza. Ta riga ta saba da hakan, don tunda aka maida Habibu wajenta bata tunanin an sake zaman lafiya tsakanin Hadizar da Abdullahi. Kullum cikin fada suke da tashin hankali. Don haka bata sanyasu a kanta ba.
Ta ci gaba da tatar kunun aya da take anan gidan, ana kai mata wani shago anan cikin unguwar, daga gidaje ma kuma ana aikawa a saya.

Sai ga shi ya fito daga dakin nata, ya gama shirin fita wajen aikinshi.
Ta biyo shi a sukwane, yadda taga Hadizar tayi wani firi-firi kamar mahaukaciya sabon kamu sai da hakan ya tsoratata. Ta dakata tana kallonsu cike da mamaki, a ranta tana tambayar me ke faruwa ne?

Hadiza ta sha gabanshi dai-dai zai sa kanshi a soro ya fita, "wai gidan wa zaka tafi Malam baka sallameni ba? Wallahi sai ka sakeni yau zaka bar gidan nan, idan kuma ba haka to ni da kai da duk jama'ar gidannan babu zaman lafiya!"

Tsaye take, amma ilahirin jikinta rawa yake yi gabadayanshi. Gashin kanta duk ya cuccure ya wani cukurkude, Ummah ta tsaya tana kare musu kallo jikinta itama yana dan rawa.

Ya kalleta yace, "wai ke wani irin bala'ine wannan da ba zaki bar ni in huta ba? Saki kike so ko? To ki je na sakeki saki daya!"

Amma maimakon tayi murna ko ta hakura, kawai sai ta kamo kwalar rigarshi, idanunta har wani tartsatsi suke yi, "Malam saki uku zaka yi min wallahi, sai ka karasa sakina!"
Abin nata sai kace mai fama da aljanu, shi kanshi kamar wanda ake tunkudawa. Bashi da niyar sakin mace idan ya aureta, shi yasa tun farko bai tashi yin aure ba sai daya ji cewa ehh lallai zuciyarshi ta nutsu da Ummah sosai. Itama kuma Hadiza din dalili kenan da yasa yake matukar yin hakuri da al'amuranta.
A ranar dai a haka ya furta mata ya saketa saki ukun da ta bukata. Ta sakeshi ta shige dakinta, kafin kace me! Ta zauna hade kan kayanta. Dama can ba wasu kaya bane na azo a gani, duk sun kare a yawon bin Malamai.

Kafin zuwan Azzuhur, Hadiza ta bar gidan kamar ba ta taba wanzuwa ba. Babu ko allurarta, ta kwashe komi.

Shima ya kada kai ya tafi aikinshi, Ummah ta tsaya nan tana ta rawar jiki. Jin furta kalmar saki ba karamin abu bane. Daga baya ta tabe baki itama ta cigaba da gudanar da harkokinta.

Tun bayan barin Hadiza gidannan sai rayuwa tayi musu dadi ta kara dadada a garesu.
Shekaru biyu bayan nan, ya biya musu aikin Hajji ita dashi, aka bar Habibu a wajen Inna. A dan tsakanin Allah Ya yiwa Malam Ibrahim rasuwa.

Suka je suka yi Hajjinsu suka sauke farali cikin dadin rai.
Kudi masu kauri ya bata domin tayi tsaraba dasu, itama kuma da nata kudin na sana'arta da take yi.

Kafin a fara aikin Hajji suka shiga kasuwa da niyar fara sayayyar tsaraba, kawai sai wata dabara ta fado mata.
Yana da aboki da yake Agent ne na Alhazawa anan garin Makkah din, sai kawai ta nemi shawararshi akan tana so ta sari kaya a auna mata su gida ta jirgin ruwa. Yace wannan ai karamin abu ne.

Sai kawai ta kwashi takalma, jakunkuna, turarukan wuta, kayan ado na mata da yara iri-iri. Aka kira yan dauri suka daure kayan nan, aka badasu aka kai aka dora a jirgi ta biya komi.

Suna komawa gida ba dadewa suma kayan suka sauka a Kano, Agent din ya hadata da wani anan Kano din yaje ya amso mata kayan aka yi clearing, aka doro mata su motar Kaduna.

Ta bude wannan kaya da wata irin nasara da sa'a mai ban mamaki. Aka yi dafifi akan wannan kaya kafin kace me! Sai ga kudadenta cas a hannu, ta samu riba mai matukar yawa.

Daga wannan lokaci sai ta fara wannan harka, a sayo mata kaya daga Makkah, a auno mata su. Idan an kawo gida Nigeria kuma taje ta amso ko kuma aje a amso mata, ta fasa ta sayar.
Cikin dan kankanin lokaci sai gashi ta zama Hajiya ta kanta, don kuwa ba karamin samu take yi ba.

Shi kanshi Abdullahin a cikin wannan shekarun ya samu karin matsayin fiye da biyu a wajen aikinshi. Don haka rayuwa tana mika musu cikin jin dadi da godiyar Allah. Har zuwa lokacin dai Ummah ko batan wata bata taba yi ba. A shekarun baya ta sanyawa ranta damuwar rashin haihuwa, shima kuma Abdullahi din duk da cewa dai yana matukar kokari wajen ganin bai nuna mata hakan ba. Ta ziyarci likitoci da dama domin son samun tabbaci akan rashin haihuwarta, kusan duk abu daya suke mata; Mahaifarta lafiyarta lau, rashin haihuwarta kuma baya da nasaba da faduwar data taba yi. Kawai dai Allah ne bai kawo haihuwar yanzu ba. Su dorata akan magunguna ta koma gida.
Don hakane ta sake kama Habibu da Sumayyah ta rike kakam.

A wani zuwa Birnin Lagos da tayi akan wata matsala da aka samu da kayan da aka aika mata daga China, ta ci karo da wani abu daya bata mamaki.

Kasancewar Hashim a Lagos din yake, Chief Superintendent Customs Officer ne a lokacin, a ofishinshi ta tsinci file mai dauke da takardun kayan Laminu Nalado. Ta yi matukar mamaki da ganin hakan, ta samu kanta da tambayarshi, "shin me wadannan kayan suke yi ne anan?
Sai yace mata, 'ai sun rike kwantainonin ne guda biyu wadanda ke dauke da kayan Laminun da na sauran mutane fiye da watanni uku da suka wuce, saboda basu cika ka'idar da aka bada ba. Kuma suna tunanin ana smuggling abubuwan da kasa bata yarda da shigarsu ba. Amma fa hakan ba matsala bane, idan ta san mai kayan zai iya musu hanya su amshi kayansu salin-alin! Tunda a yanzu haka wadanda suka san manyanshi da dama an riga an basu nasu kayan.'

Tayi dan murmushi, ranta na wani irin suya na bacin rai da bakinciki. Tace mishi, 'ban san ko wanene ba!'
Amma bacin ran dake kwance akan fuskarta ya nuna akasin hakan. Har tayi cike-ciken da zata yi ta gama, zuciyarta cikin sake-sake take. Zuciya da shaidan suna kara kissima mata bakinciki da bakin talauci da Lameen ya sanyasu a ciki bayan daya cucesu.

Da ta gama komi tsaf, sai ta juya ta kalli Hashim, tace mishi, "ni da zaka bi shawarata ma da ka kara rike wadannan kaya ka sanya musu tsauri da kyau. Ka min alfarmar kada su koma hannun mai shi!"
Da wannan ta kulla da Hashim, aka hana Lamin kayanshi.

Koda ta koma gida bata zauna ba, zuciya ta cigaba da auna mata da ta dauki fansa, ta rama abinda Lamin ya mata. Ta nuna mishi itama fa yanzu ta zama wani figure a duniya da zata iya taka wanda ta so, a kuma zauna lafiya.

Kai tsaye ta kira Uwargidan Sarkin Bornu ta wancan lokacin, kawarta ce wadda zumuncinsu ya dore har zuwa yau. Ta roki alfarmar ta sanya ayi mata bincike akan Lamin. Cikin yan kwanakin komi daya faru dashi sai da aka sanar mata, tun daga kan arzikinshi da kuma siyasa daya shiga kai tsaye da iftila'in daya auka mishi.

Amma maimakon zuciyarta tayi sanyi tunda ga shi nan Allah Ya nunawa Lamin karshenshi tun a duniya, amma ina! Zuciya da shaidan sun gama rinjayarta. So take yi kawai ta karasa shi, kai ba shi ba ma, har 'ya'yanshi da tattaba kunnenshi. So take yi suma ta dandana musu abinda Lamin ya dandana musu.
Don haka ta cigaba da bibiyarsu da rayuwarsu har zuwa lokacin da aka sanar da ita bikin Zahra'u.

A shekarar ne Sumayyah ta gama samun kwalinta na degree akan Psychology, aka tura gidansu neman aurenta daga wani wanda suka yi UDUS dashi, Engineering yayi. Cikin ikon Allah kuma ya samu aiki da kamfanin Jordan Petroleum Refinery a Jordan, yana rokon a daura musu aure ya tafi da ita, itama kuma za ta jona second degree dinta a can.

Ummah bata so wannan aure ba, amma ganin daga Sumayya din har Fahad suna son junansu, sai ta hakurarwa ranta. Aka daura aure suka tafi.

Ba ayi wata daya da bikin Sumayyah ba aka tashi yin na Zahra'u, ta shirya tsaf ta tafi. Yadda dangi suka dinga rawar jiki a kanta duk bai burgeta ba, hasalima haushi hakan ya dinga bata. Sai yake kawai data dinga yi, a ranta tana kiransu da 'munafukai'
Da ta shiga wajen Lamin sun gaisa dashi lafiya-lafiya, yana ta rokonta yafiya da neman gafara. Tana jin shi har ya gama, sannan ne ta sanar dashi cewa ita tayi sanadin da aka rike mishi kayanshi. Wannan kuma duk ba komi bane akan sauran abubuwan data shirya mishi, ta kakkabe zaninta ta barshi anan cikin tashin hankali, yana kiran sunanta da ihun ta mishi aikin gafara.

Ta koma gida cikin murnar wannan abu. Sai ta samu wani karin abin farincikin, an yiwa Abdullahi karin matsayi a wajen aiki, ya zama General. Ga kuma wawakeken fili da aka bashi sakamakon yabawa kwazonshi wajen kwantar da wata tarzoma da ta tashi anan tsakanin Kaduna da Abuja. Suka sha murnarsu sosai da sosai, ya yanki fili a ciki yayi musu tanfatsetsen gini, tsohon gidansu kuma ya gyarawa Innah ta koma da 'ya'yan yan uwa da take riko.

Suna cikin wannan rayuwa mai dadi da kololuwar daukaka da jindadi, Allah Ya yiwa Abdullahi rasuwa a hanyarshi ta dawowa daga Porthercourt. Sai gawarshi aka kaiwa iyaye da yan uwa da matarshi. Fadin irin gigitawar da mutuwar nan ta yiwa Ummah ma bata baki ne. Sai data susuce ta dinga sambatu.

Sumayyah ta zo wajen gaisuwar daga Jordan, saboda a gareta Abdullahi mahaifin da bata tashi a gabanshi bane. Suka sha kukansu suka koshi, kafin su fawwalawa Allah lamarinShi.

Anyi sati ana zaman makoki, kafin nan dangi duk sun watse. Sumayyah ta zauna da Yayar tata har ta gama takaba, da yake ta samu miji mai fahimta da kuma tayata son wanda take so, yasan duk duniya bata hada lamarin Yayarta da na kowa, don haka bai tsawwala ba. Shi kanshi yaje wajen gaisuwar ya musu kwana uku kafin ya juya.
A dan zaman ne Ummah take fadawa Sumayyah abinda tayi, amma maimakon taga tana murna sai taga akasin haka.

Tace, "Subhanallahi! Haba Yaya! Wannan abun ai bai dace dake ba sai sam, haba don Allah! Ni wallahi tuni na manta da duk abinda ya faru a raina, ni yanzu haka wannan zuwan ma da nayi ina so ne zan karasa har can ne. Yakamata zuwa yanzu duk mu hakura da abinda ya faru, mu manta baya. Kina kallon yadda ake komi namu wai ace babu dangin mahaifinmu a ciki? Abin fa babu dadi sam!"

Ummah ta harareta tace, "aikuwa idan kinga kinje wajensu Sumayyah, to sai bayan raina! Na rabaki da mutanen nan har abada, kuma idan har kina daukata a matsayin Uwa kamar yadda kike fadi, to ki dauki hakan a matsayin umarni. Kuma daga yau, kada in sake jin bakinki akan al'amurana. Idan ba zaki tayani ba, to kada ki kara sa min baki!"

Amma Sumayyah bata gaji ba, har zuwa lokacin da ta koma ga maigidanta, bakinta bai gaji da yiwa Ummah nasiha da kara nusar da ita ba akan rashin kyawun abinda ta aikata ba.
Maganganun nata kuma suka cigaba da yiwa Ummah kararrawa aka, suna nukurkusarta. Wani sashe na ranta dake da sauran taushi har a lokacin yana tuhumarta da anya, anya kuwa ta kyauta? Kamar fa yadda mai Hadisi, daga bakin Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace, 'ka so wa dan uwanka musulmi abinda kake so wa kanka!' Hakan fa kamar dai yana nufin, 'ka kuma ki mishi abinda zai cutar da shi kamar yadda zaka ki wa kanka ne!'
To ga shi kuma ita ta cutar da wani duk akan son kanta. Musamman da a dan lokacin aka aika musu da rasuwar Lamin din. Mutuwar ta daketa ba kadan ba, har hakan ya sanya ta kira Hashim ta roki ya saki kayan nan daya rike.
Yace mata ai a halin da ake ciki dai yanzu wannan al'amari ya girmeshi, saboda zancen da yake mata ma an nemi kayan an rasa, ana kuma zargin manyane suka sacesu.

Jikinta ya kara yin sanyi, wannan dalili yasa tasa aka mata kintacen yawan adadin kudin, ta turawa matar Sarkin Bornu wadda taje har gida ta kaiwa Dada mahaifiyarshi kudin, ta sanar da ita sakone daga Hajiya Ummah din kawai. Don haka duk da bata je wajen rashin ba, sun ji dadin wadannan kudade. Don kuwa da aka fara biyan tarin basussukan da Lamin ya bari, basu tsira da komi ba.

Aka zo aka yi rabon gadon abinda Abdullahi ya mutu ya bari, kowa aka bashi hakkinshi. Ita kanta ba karamin kadara da kudade aka bata ba na tumunin takaba kawai, balle ayi zancen Habib da ya kasance dan shi namiji kadai.
A lokacin yana ajinshi biyu a jami'a yana karantar Geography.

*

Tun bayan rabuwar Abdullahi da Hadiza, bata kara waiwayarsu ba ko da wasa. Itama kuma Ummah bata taba nemanta ba balle ta kai Habib wajenta ko na yan'uwanta. Amma duk da haka Ummah tana sane da abinda ke faruwa da Hadiza din. Don kuwa har gida ake zuwa ana bata labarin duk halin da take ciki.
Tayi aure har sau uku amma tana fitowa, a lokacin da Mahaifin Habib ya rasu tana auren wani tsohon ma'aikacin Gwamnati ne, wanda yake da mata biyu ita ta uku.

Matashi Habib sun samu hutun mid-term semester, ya taho gida cike da doki da jindadin kasancewa da Ummahn shi.
A duniya babu abinda yake tausayawa kamarta, hidima da dawainyar da take yi dashi kadai yana da tabbacin ko Mahaifiyarshi data haifeshi ba zata yi mishi hakan ba.

Da wayonshi sarai lokacin da abubuwan gidansu ke ta faruwa, har a yau kuma, bai manta dukan mutuwa da mahaifiyarshi ta mishi akan ya kirata da Mama ba. Tun daga wannan lokacin ya yanke shawarar ja da baya da ita.

Amma bayan rabuwarsu da mahaifinshi shi ya dinga zuwa inda take, ita ce dai bata son ganinshi har a lokacin. Ya rasa wani irin laifi ya aikata a gareta har haka? Abun kuma yana matukar yi mishi ciwo nesa ba kusa ba. Ya daukarwa kanshi duk lokacin da zai je wajenta zai samu wasu yan kudade ya tafar mata da su, musamman da yaga yanayin rayuwa da suke ciki ita da yan gidan da take zaune, don kuwa iyayenta sun jima da rasuwa.
Hakan ne kadai yake dan sanyawa yaga sakin fuska a wajenta, duk da cewa dai bata daina zaginshi da cewa shi sallamamme bane a yawancin lokuta.

Zuwa na karshe da yayi wajenta, gidan aurenta na biyu da yaje, lokacin ajinshi biyar a sakandare. Ta bukaci tarin kudi a hannunshi, wai jari take so ta tada saboda kishiyarta tana mata gorin bata da sana'a. Iyayen kudin data nema sai da suka yaji kanshi yana juyawa. Yace mata, 'q ina zan samo wadannan kudade? Nima fa har yanzu bani ake yi, ba kuma tarasu nake yi ba!'

Anan tayi mishi kora ta wulakanci, tace mishi, 'ita ai dama tuni da ta sallamawa Ummah shi, don kuwa yanzu bata ma sanyashi a cikin jerin wai 'ya'yanta, tuni da ta rufe babinshi. Kada kuma ya kara zuwa inda take, kudin ma da yake kai mata ya daina bata so daga ranar. Idan kuma ya sake komawa to wallahi sai ta tsine mishi. Ai duk da dai ta sallamawa Ummah shi, amma har yanzu tana da hakkin tsine mishi kuma tsinuwar ta bishi!'

Ya koma gidansu rai a matukar bace da wannan rashin adalci nata. Ya kuma yanke shawarar daga wannan rana, ya gama.

Yana sanya kai cikin falon gidansu, ya tsinci tashin muryoyin da ko a cikin maye yake, ba zai taba kasa shaidasu ba. Ummah ce da mahaifiyarshi Hadiza suke wasu maganganu da suka tayar mishi da hankali.


43.




Hadiza ce take cewa Ummah cikin daga murya, "tunda dai ba ke kika yi min nakudarshi ba, to ki tattaro min kudaden shi na gado da aka bashi kike neman yin ruf-da-ciki a kansu ki bani, idan kuma ba haka ba kotu ce zata rabani da ke!"

Hajiya Ummah kallonta ta dinga yi cikin mamakin irin wannan karfin hali nata, ta daga baki daga baya da kyar tace mata, "kin manta ke da bakinki kika sha fadin kin sallamawa Habib ni duniya da lahira? Ko kuwa kin manta cewa tun bayan tafiyarki baki taba waiwayarshi ba wai da sunan son jin abinda yake faruwa da shi? Sai yanzu kuma rana daya ki zo sama ta ka kice wai kinzo amsar rabon gadonshi? Ashe ma ba don shi ba kika zo nan kenan?"

Tace mata, "Duk abinki dai, baki isa ki raba hanta da jini ba wallahi. Habibun ai da na ne, ni na sha nakudarshi da wahalarshi da rainonshi, ke da kika tsinceshi daga sama? Ko wannan wahalar kadai ai ta isa zama hujja a kanki. Ki daina ganin wai na koma gefe na zuba muku ido kiyi zaton zan kyaleki ne ki bi ta kan kudin gadon yaro ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login