Showing 6001 words to 9000 words out of 142169 words

Chapter 3 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

436

gidan, ta shiga falon farko na gidan.
Babban falone sosai. An sanya kujeru manya-manya na leather sai babban center table, rabin bangon dakin wata katuwar plasma ce yayinda rabin kuma show glass ce mai girma da fadi da aka zuba abubuwan ado na tangaran da gilashi a ciki. Dim lights masu kyau suna ta sheki a ciki suna kara kawatata. Falon an fi amfani dashi saboda manyan bakin Daddy, amma su ma mutan gidan su kan fita su sha iska a wasu lokutan.

Tana bin wata kofa sai gata a tsakar gidan. Dakuna ne a jejjere daga kowacce kusurwa, Yayinda sauran tsakiyar gidan kuma aka shuka wata bishiya babba wadda ta bude daga sama ta saki rassai duk sai ta lullube gidan. All in all dai, gidan Anty Jamila gida ne wanda tsarinshi yayi matukar burge Nadiya. Domin gidane da daga gani kwalwa da dukiya suka jajirce wajen ganin an samar dashi. Kuma yanayin tsarin yana nuna rayuwa ta wayewa da kuma sanin darajar kai, ba irin ta gidansu ba.

Bangaren yaran gidan daban yake, duk da cewa dai a waje daya suke, amma kuma kowa bangarenshi daban yake.

Kana shiga daga bangarenka na dama, nan ne dakin yara mata yake. Idan kuma ka mike straight, nan zai kaika turakar mai gidan. Bangaren hagu kuma wanda ya dan shiga ciki nan ne bangaren maza.

Kai tsaye dakinsu Rabi'ah ta wuce. Tayi knocking kafin ta tura kofar dakin ta shiga. Dakin nasu yana da fadi matuka. Gadaje uku ne a dakin, guda biyu wadanda suka kasance bunk, a hade, suna daga jikin bangon kofar dakin, sai dayan kuma daya kasance single a daya bangon. Daya bangon kuma gabadayanshi wardrobe ce ta jikin bango, sai daya gefen da aka zuba desks na karatu, kowanne makale da laptop dinshi da sauran essentials, sai kuma karamar tv da aka manna. A tsakiyar dakin kuma an shimfida kafet mai taushi an zuba tuntu da wasu abin zama da hutawa masu kyau.
Rabi'ar tana zaune akan desk dinta tana rubuce-rubuce lokacin data shiga. Tana daga kai ta ganta, tayi tsalle ta wancakalar da abubuwan hannunta ta nufeta a sukwane tana ihun murna. Murmushi tayi itama ta rungumeta, nan suka hau juyi a tsakiyar dakin har dai suka dangane da gado suka zube a kai.

Sai data gama murnar tata sannan ta saketa, ta zauna a gefen gadon tana kallonta, "wai! Gaskiya sannunki da zuwa Anty, ya hanya?"
Tace, "hanya Alhamdulillahi, gamu mun iso ai!"
Rabi'ah tace, "sannu da hanya to. Mommy tace idan kin iso a miki sannu da zuwa zaku hadu da safe saboda tuni suka shige turaka ita da Daddy!"

Dan murmushi ta saki a tausashe, sanin halin Anty Jamilar sarai da yadda bata hada harkokin mijinta da komi yasa bata ji komi ba, sai kai data daga, tace, "to Allah Ya kaimu goben lafiya. A gajiye nake ai dama, ruwa kawai zan watsa in kwanta."

Tace, "to ki shiga kiyi, ga kayan barci da Mommy ta shigo miki dasu."
Tayi godiya tare da amsar kayan ta fita daga dakin ta fada toilet da yake fuskantar dakin. Shower stall ta shiga ta saki ruwa mai dumi a jikinta sosai, ta jima a ciki kafin ta fita tana jin yadda jikinta ya fara saki, gajiyar itama ta fara barinta.
Ta tsaya gaban karamar mirror dake makale a bandakin tana goge jikinta da tawul. Data gama ta dauki spray na CC mai sanyin kamshi ta fesa a jikinta kafin ta fasa ledar kayan ta sanya, dogayen riguna ne guda biyu na barci a ciki. Dayar bata da tsayi sosai da kadan ta sauka gwiwarta, kuma hannunta siriri ne haka kuma bata da nauyi. Dayar kuwa doguwa ce har kasa kuma tana da dan kauri haka hannunta dogo ne, tana da madauri a jiki kamar bath robe. Ganin su kadai ne a dakin kuma yanayine na zafi, sai bata dora ta saman ba, ta barta.

Tana komawa daki ta tarar har Rabi'ah ta baza mata kayan abinci duk da dai marassa nauyi ne. Dambun cous-cous ne da yaji hadin kayan lambu sai kuma yankakkun kayan marmari da madarar hollandia yoghurt ta strawberry. Ta zauna tana ci suna taba hira da Rabi'ah, gajiyar tafiya yasa ta kasa cin abincin da kyau sai fruits din data sha sosai, ta kuma sha yoghurt din. Data gama sai ta rufe komi, Rabi'ah ta wuce ta kai kayan kicin ita kuma sai ta koma bayi ta wanke bakinta ta dawo daki ta kwanta. Rabi'ah tana sama ita kuma tana na kasa, ta kira Mama ta shaida mata sun sauka lafiya, ta hadata dasu Maryam suka mata sannu da hanya kafin su yi sallama.
Daga nan ta yada kai akan filo babu jimawa barci yayi awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai da alarm ya tashesu sallar Asubahi. Bayan sun yi sallar, suka yi azkar, sake komawa suka yi suka kwanta abinsu.

Karfe tara da rabi ta farka. Jikinta ya saki sosai, babu kuma gajiya a tattare da ita sai rashin karfin jiki da kasala.
Ta sauka daga kan gadon ta fita tare da shiga toilet, baki ta wanke kawai. Ta bi dogon corridor din gidan ta shiga kicin. Ko'ina na gidan a gyare yake tas-tas, babu hayaniya wadda ta sanya mata natsuwa. Tana son rashin hayaniya da tsafta ita kam.

Yunwa take ji sosai, kuma ita ta tasheta. Ta fara bude-buden fridge da cupboards tana neman wani abu da zata fara dashi kafin ta yi abin kari, saboda tasan mutanen gidan zasu iya kaiwa sha daya ma basu tashi ba. Tasan kuma abu mai dan nauyi zasu bukata.

Freezer ta bude ta ciro kaza guda, ta fara wanketa ta dora akan wuta bayan ta yanka wadatacciyar albasa ta zuba kayan kamshi.
Sai ta dama quicker oats ta hada ta sha kafin kazar ta gama dahuwa.

Ta fara fito da abubuwan da zata bukata tana warewa. Kafin kace me, ta hargitsa gidan da tattausan kamshin girki mai dadi.
Dage-dagen kaza tayi da kayan lambu, sai ta soya kwai, ta yi toasting din biredi, sai shayi mai kamshi data hada. Ta riga ta gama sanin tsarin gidan, don haka tana gamawa ta samu flask da warmers ta zubawa Anty Jamila nata da na mai gidan, ta debar musu ita da Rabi'ah, sauran kuma ta ajiyesu a wani mazubin na daban. Duk mai so daga cikin mazan gidan wadanda kannen maigidan ne dake karatu a BUK, sai yazo ya dauka duk da cewa bata ji motsin kowa ba yau.

Tana cikin wanke-wanke Anty Jamila ta shiga kicin din. Doguwar macece mai dan jiki, baka ce amma kuma kalar fatarta mai kyau ce da sheki saboda tana bata kulawar data dace. Saye take da doguwar rigar barci cotton, sai ta dora hijabi karama a sama wadda ta tsaya mata a kugu, kafarta saye da takalmin silifas mai taushi.

Nadiya ta juya tana kallonta lokacin data shiga kicin din, fuskarta dauke da murmushi. Durkusawa tayi tana gaidata, Anty Jamila ta jata jikinta tana dariya, "ai tunda naji gida ya karade da kamshi nace lallai Nadiya ta dira gidana!"
Dariya ta sake a tausashe, tace, "haba dai Anty! Ke ma fa bangaren girkinnan ba daga nan ba. Ni ai nawa sharar fage ne!"
Anty Jamila tace, "ba wani nan. Ke kanki ai kin san kafin a kamo kafarki a bangaren girki, za a jima gaskiya!"
Murmushi ta sake yi tana girgiza kai kawai.

Tray din data shirya musu kaya da maigidanta ta nuna mata, tace, "ga abin karinku na hada muku, Rabi'ah bata tashi ba shi yasa bata kai muku ba!"
Saboda ita bata shiga bangaren Maigidan. Bakin iyakarta dashi idan sun hadu a falo ta gaisheshi, ko kuma tayi dakonshi da safe idan tana kicin tana aikin girki.
Anty tace, "da kyau Nadiyata! Wallahi kamar kin san ina kewar girkinki dama. Bari idan Daddy ya fita, zamu shiga kasuwa anjima muyi siyayyar spices don gashin kazar nan da kike mana da kuma local mac-D dinki nake son ci."
Tayi murmushi tana gyada kai, "to shikenan Anty, Allah Ya kaimu!"
Anty ta dauki farantin ta fita, ita kuma ta cigaba da aikinta.

Data gama ta dauki nasu abincin ta kai daki. Sai lokacin Rabi'ah ta tashi, ta shiga bayi. Kafin ta fito har Nadiya ta gyara dakin, ta hada musu shayi. Suka zauna suna kari. Mama ta kira suka gaisa, ta hadata dasu Rabi'ah suka gaisa, kafin hira ta kacame musu ita da su Maryam. Nan ta barsu suna ta yi, ta kwashe kayan abincin nasu ta kai kicin.

Dakin ta koma ta fara tsifar kanta saboda ya fara datti, a gida kuma bata cika samun lokacin yin tsifar ba. Tana jin sanda Rabi'ah ta kashe wayar tazo tana tayata itama. Tana son irin gashin Nadiya wanda ya kasance baki, sassalaka kuma mai tsayi sosai. Ba kamar irin nata ba wanda yake mai tauri sosai duk da cewa itama ba laifi tana da tsayin gashin da kuma baki.

Bayan nan dakin Anty Jamila suka je suka gyara mata, daga nan suka shiga dakin mazan gidan don su gyara. 'Ya'yan Anty Jamila hudu, danta na farko Auwal da suke cewa Yaya, shekarunshi sha bakwai, yana Sudan wajen Yayan Babansu, sai Rabi'ah yar kimanin shekaru sha biyar, sai mai bi mata Abubakar Sadeeq shekarunshi goma, dai autanta Haroun, suna ce mishi Haneep, shekarunshi biyar.
Da yake tana da abokiyar zama, wani lokacin yaran su kan je gidanta suyi weekend ko hutu, ko kuma ita nata yaran guda uku su zo nan gidan nata. Da alama wannan satin suna can.

Da rana ta mulmula musu tuwon semovita da miyar yauki, suka ci suka yi nak kafin Anty ta daukesu a motarta suka fita. Shagon saloon dinta dake nan cikin Nasarawa gra din suka fara tsayawa, aka wankewa Nadiya kai aka kuma yi mata kalba saboda ta fi sonta akan kitso. Daga nan suka shiga kasuwa ta taya Antyn hado kayan kamshi na abinci saboda a cewar Antyn ta ma fi son hadin spices din Nadiya akan ta siya na kanti.
Sai yamma likis suka koma gida.

Da dare tayi musu gashin nama mai ruwa, ta hada musu da taliyar indomie noodles wadda tayi steaming dinta sai ta soyata a cikin kwai sama-sama bayan ta wadatata da kayan lambu da taruhu daya sa tayi dan yaji-yaji.

Bayan sun gama cin abincin sun jima suna hira a falon Anty. Sai wajen karfe goma saura kafin suka yi mata sai da safe. A dakin ma koda suka gama shirin barci, wata sabuwar hirar suka dasa. Bata ma san lokacin da barci ya kwasheta ba sai can wajen karfe hudu ta farka. Da taga alamun barcin ba daukarta zai yi ba, sai kawai tayi alwala ta fara nafila.
Da aka yi Asubahi ta tashi Rabi'ah itama tayi, sannan ta sake komawa barci.
Ranar ita da Rabi'ah suka hada abin kari. Lokaci yana ta karatowa, don a yadda ta saba, ana yin Azuhur take yin haramar tafiya gida yadda zata isa da wuri. Ji ta dinga yi dama kada ta koma. Idan ta tuno irin tsarabe-tsaraben dake jiranta sai taji inama... inama. Inama ba zata koma wannan gidan ba.

Da zata tafi Anty ta hadata da tsaraba mai yawa. Ta dauki dubu goma ta bata tayi kudin mota, dubu goma ta kaiwa Mama, dubu ashirin kuma ta kaiwa Abbansu. Ta mata godiya sosai da sosai.
Har tasha suka kaita ita da Rabi'ah. Sai da suka tabbatar ta samu mota kafin suka yi sallama da ita cike da shauki. Babu jimawa mota ta tashi suka dauki hanya.

Sun isa Makarfi, direban ya tsaya a wani babban gidan mai domin su sha mai. Da wannan damar fasinjoji suka sauka domin su gudanar da wasu bukatunsu.
Nadiya ta bi bayansu itama ta fitan. Shago ta shiga ta amshi gorar madarar Dudu mai sanyi ta samu gefe daya ta zauna a cikin shagon tana sha, idanunta akan motar tasu har zuwa lokacin da fasinjojin suka fara komawa. Ta tashi tsaye tare da jefar da robar lemun a cikin kwandon shara. Yunwa ce tayi guzurinta sosai, saboda tun karin safe babu abinda ta ci. Anty Jamila babu yadda bata yi da ita ba amma tace mata ba zata ci komi ba. Wani lokacin dama haka take, idan a halin tafiya take bata cika cin abinci mai nauyi ba saboda hakan ya kan zame mata matsala a yawancin lokuta.

Dai-dai lokacin da zata fita daga shagon, su kuma sun kawo kai. Karo suka gabza ba tare da saninsu ba. Abu biyu zuwa uku taji a lokacin, farko wani irin daddada kuma sansanyan kamshi mai kwantar da rai. Tana da son kamshi, tana kuma girmama mutumin da yasan kamshi da kuma darajarshi. Ita fa sau tari, tana gwada halayen mutane da irin kamshin da take ji a tattare da su ne.
Abu na biyu kuma shine yadda kanta ya bugi kirjin wanda suka yi karon. Hakan ya nuna mata cewa mutum ne mai tsayi, saboda itama babu laifi tana da tsayi gaskiya.
Na uku kuma, wani abu mai sanyi daya tsiyaya yana kwaranya a cikin jikinta, wanda ta fuskanci lemun Five Alive ne, Pulp, dake hannun mutumin ya tsiyaye a jikinta.

Kafin ma ta gama tantance wadannan abubuwan, taji an sanya hannu an yakiceta anyi baya da ita. Tayi ido hudu da abu, halittar data sanya taji wani abu game da wani da namiji, da bata taba ji ba a tarihin rayuwarta.
Fari ne, dogo kamar yadda tayi kintace, mai cikar jiki da cikar kamala. Akwai alamun hutu sosai a tattare dashi, bashi da rama duk da tsayin da yake dashi, hasalima yana da dan nama a jikinshi. Kalmar 'giant' ita kadai ta iya je mata kwalwa a wannan lokacin. Saboda duk inda za a nemi mutane giants, to mutumin ya kai sahu na farko.
Fuskarshi cike take da gargasa wadda ta kwanta mishi luf a fuska ta kuma kara kawata fuskar tashi.

Lebbanshi take kallo wadanda suka saki wani irin siririn tsaki, suna motsewa da tankwashewa zuwa alamun bata fuska, "baki kallon gabanki ne idan kina tafiya ko me?!"
Ya watsa mata tambayar cikin fusata da bacin rai. Nan da nan itama sai taji nata ran ya baci. Abinka da mai zuciya a makoshi, kiris take jira.

Tace, "ban gane ba Malam! Idan ban manta ba ina ga ai kaine ka kawo min karon! Tunda kai ne ya kamata ka kalli gabanka kai da zaka shawo kwana! Kuma kai ka zubar min da abu a jiki ko?!" Ta fada tana nuna mishi ta'adin daya mata.

Amma ko a kwalar rigarshi, ya sake jan wani tsakin ya zagayeta yana jefa mata harara, Hannunshi jaye da wani yaro, magana yake yi kasa-kasa wadda ta tsinci kalmar 'sai kace makauniya' da 'rashin tunani' a ciki. Ta bishi da kallo baki hangangan cikin tsananin mamaki. Wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama. A dakeka kuma a hanaka kuka? Ai ba ma zata sabu bane!
Tana shirin bin bayanshi ta danna mishi rashin kirkin da ba zai manta ba, direba ya fara danna mata horn. Wasu daga cikin fasinjoji ma masu gajen hakuri har sun fara lekowa ta taga suna mata magana da masifa. Ta kara juyawa tana harararshi, cikin sa'a lokacin shima ya juya. Ta kuwa kara kaifafa zafin hararar tata kafin ta wuce dakinta sassarfa, jikinta a jike, ta shige mota.
Hankicin hannunta ta jika da ruwa tana goge jikinta kafin lemun ya bushe mata a jiki. Tsinuwa kuwa da Allah Ya isa tafi cikin kwando wadda ta ja tun ma kafin su kai ga barin gidan man.

Ranta bai kara dagulewa ba sai da suka tarar da wani babban hold up a Rigachikum. Motar mai ce ta fadi a wajen, don ma Allah Yasa rayuka basu salwanta ba amma dai hanya ta samu matsala saboda ta dalilin hakan, gada ta lalace. Don haka hannu daya ake bi, ga shi ranar Lahadi ce.
Zafi da gajiya suka mata rubdugu, tun suna zaman jin dadi har suka fara na wahala. Sai suyi zaman fiye da minti ashirin a waje daya babu alamun zasu motsa, idan kuma suka dan matsa, bai bi su yi kamar taku hudu zuwa biyar ba sai a sake tsayar dasu.

Suna nan fiye da awa biyu cikin wannan yanayin, har ta fara tunanin ko itama zamewa zata yi kawai ta sauka daga motar, idan ta taka da kafarta ta fita daga cikin hold up din sai ta samu abinda zai karasa da ita gida kamar yadda taga sauran fasinjojin suna yi.

Motocin sojoji suka wuce ta gabansu, maimakon suyi gaba sai suka fara kokarin bude hanya, da alama wani ne zai wuce. Hakan kuma ya faru yafi sau a kirga a gabansu. Farko dan gidan Sarkin Zazzau ne ya wuce, na biyu kuma Kwamandan sojawan ne gabadaya, na uku da na hudu bama ta tsaya jin ko su waye ba saboda ita abin takaici ma yake bata. Yanzu kuma ko wanene? Ta tabe baki tana jan dan siririn tsaki.

Manyan motoci ne bakake guda biyu suke kokarin wucewa cike da securities, sai wata farar BMW a tsakaninsu.
Motar take kallo saboda ta burgeta sosai. Daga gani sabuwa ce, ko kuma ba a cika amfani da ita ba. Hankalinta ya nutsa wajen tunani da lissafin lokacin da itama watarana zata mallaki mota mallakin kanta. Bata kula da gilasan gidan baya da ake budewa ba sai da suka hada idanu biyu da wannan mutumin na dazu.
Ita yake kallo, ta kula. Da wani murmushin gefen baki yake kallonta, cike da arrogance daya matukar kara kona mata rai. Wato saboda yana ji da kudi da mulki shine har yake wulakanta mutane son ranshi? Bata ma san lokacin data saki wani dogon tsaki ba, tana jin yanda ranta yake kara baci. Ita fa bata kaunar mutum marar kirki, taga alamun wannan mutumin kuwa ya hardace rashin kirki babi-babi a kanshi. Da taga tsakin ma bai mata ba, sai ta kara da harara da murguda baki. Tayi gefe daya da kanta don ma kada ta tsayar da kanta anan tana kallonshi har ya kara bata mata rai. Bata san lokacin da suka wuce ba. Su kuma suka cigaba da zaman jiransu anan.

Ana kwala kiran sallar magariba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login