Showing 45001 words to 48000 words out of 142169 words

Chapter 16 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

447


Tun a wajen dinner din ta kula da yadda yake ta bibiyarta da kallo da magana, duk kuma yadda tayi kokarin yakiceshi wannan bawan Allah ya ki amincewa.

Sai daya samo lambar wayarta a wajen Rabi'ah, haka ko shigarsu cikin gidan ya dameta da nacin kira da tura sako, shi fa tsakaninshi da Allah sonta yake yi. Duk kuma yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita dai ba wannan ne a gabanta ba, ya ki saurarenta.

Haka washegari da safe yaje gidan ya kasa ya tsare, shi fa ala dole sai taje sunyi magana. Bata yi niyyar zuwan ba kuwa sai da Anty Jamilah taje ta furtomata sannan.
Ta dauki hijabi ta dora akan doguwar rigar material dake jikinta, ta tafi ta sameshi a falon farko.

Yana ganinta ya jimke hannu alamun gaisuwa, yace, "ranki ya dade! Barka da fitowa... Takawarki lafiya Hajiya Nadiya. Ina godiya da wannan karamci da aka min na bani damar ganin wannan kyakkyawar fuska taki a wannan hantsi mai albarka!"
Duk kinta sai da tayi dan murmushi. Ta fahimci mutum ne shi mai barkwanci da ban dariya. Ko a maganganunshi zaka fahimci hakan.

Ta zauna a kujerar dake fuskantarshi tace, "wannan kirari duk ni kadai dai?"
Yace, "ai kin cancanci fiye da hakan ne ma. Idan kina so in nuna miki kuma to mu fara."
Tayi gaggawar girgiza kai, "a'ah, hakan ma nagode... Ina kwana?"

Yace, "lafiya lau. Da fatan dai kin tashi lafiya? Allah dai Yasa su Rabiah sun bar kin ke kinyi barci da kyau. Don idan ba haka ba lallai fa zan shiga har gida in zanata!"
Yar dariya kawai tayi da jin haka.

Ya gyara zama yana kallonta a nutse, duk da haka fuskarshi a sake take babu daurewa.
Yace, "Malama Nadiya, kamar dai yadda kika sani, Sunana Abdullahi Aminu. Sannan ni likita ne, ina aiki a Aminu Kano Teaching Hospital. Shekaruna talatin da hudu yanzu a duniya, ba kuma zan boye miki ba, nayi aure amma mun rabu da matar. A zance na gaskiya kuma, da na ajiye auren ne a gefe, babu ranar sake wani, amma a yanzu dai har ga Allah na ganki ne, ina sonki, kuma in shaa Allah ina son hakan ya kaimu ga aure!"

Ta jinjina kai tana kare mishi kallo a hankali. Yanayin jikinshi dogo ne, bashi da kiba, yana da tsayinshi dai dai misali. Ba zaka kirashi baki ba, haka ma ba zaka kirashi fari ba. Sannan duba da shekarunshi daya fada mata, idan ba sani kayi ba sai kace shekarun nashi basu haura talatin ba.

Tayi tsai da ranta tana kara tunani. Zata iya cewa wannan shine karo na farko a shekaru fiye da biyu da wani namiji ya nuna sha'awar aurenta kai tsaye. Ta sha samun samari da magidanta da ke zuwa wajenta, wadanda tun kafin lokaci ya ja ma take fahimtar ba aure ya kaisu ba. Soyayya da holewa kawai suka je yi, ita kuwa ta zubar dasu a take ba tare da bata lokaci ba.
Taga shi auren kamar yadda suke fadi dace ne. Kuma zaman gida da take yi, ba zabar hakan tayi ba, ba kuma don tana jin dadinshi bane. Menene ma amfanin cigaba da zaman gidan da a kowace dakika nuna maka ake yi ba fa wajen zamanka bane na dindindin? Kuma ba a gajiya da goranta maka rashin aure kamar kai ka janyowa kanka?
Watakila idan ta nutsu, zata iya samun abinda take so a wajen Abdullahi din.

Tana daya daga cikin mutanen da suka yarda ba wai lallai dole sai anyi soyayya ba ake yin aure. Ta fi yarda da cewa kawai dai fahimtar juna ta fi taka rawa a wannan bangaren.

Don haka ta nisa ta kalleshi, tace mishi, "to Malam Abdullahi, naji duka kalamanka kuma na gamsu. Amma kayi hakuri ka bani wasu yan lokuta domin in tattauna da manyana, saboda kada in yanke hukunci ni kadai."

Ya gyada kai, "ehh, kwarai hakane, da gaskiyarki kam! To yanzu zuwa yaushe zan baki kenan? Yau ko gobe?"

Ta saki yar dariya a tausashe, tace, "a'ah Malam, me kake ci na baka na zuba ne haka? Ka dai bani yan kwanaki dai!"
Ya langwabar da kai gefe daya, "to ni dai ina rokon alfarmar a daure a tunana lamarin nan nawa da wuri. Saboda so nake as soon as possible inyi caraf dake, kafin inji ana min guda a tsakar kaina wani yayi awon gaba dake!"
Ta yi murmushi kawai tana girgiza kai.

Sun jima sosai suna hira da shi anan har sai da aka kira Azzuhur kafin suka rabu da shi.
Ko a yinin haka suka yini suna waya, motsi kadan ya kirata, a zauna ayi ta hira abin har ya fara gimsarta.

Da dare ta samu Anty Jamilah da zancen, ta tambayeta ko me take gani ya kamata tayi a shawarce?
Tace mata, "Abdul fa yana da hali na gari, gaskiya mawuyaci ne ki samu wani ya fada miki akasin haka. Sannan ko a yanayin mu'amala da mutane, mutum ne mai tausayi da tausasawa. Idan kina ganin hankalinki ya kwanta da shi, to ki bashi dama ki ga inda hakan zai kaiku. Amma dai kam babu wani mutum da nake ganin zai dace da ke kamar shi din!"

Hankalin nata bai kwanta dashi duka ba, amma a hankali a hankali watakila hankalin nata zai kwanta dashi dari bisa dari.

Don haka data koma daki ta kirashi ta sanar dashi abinda ta yanke. Irin murnar da yayi ba kadan bace, har hakan ya bata mamaki.
Tace, "sai dai wani hanzari ba gudu ba!"
Yace, "me fa?"
Tace, "to ina sa ran cigaba da karatuna saboda yanzu haka admission nake tsammani daga ABU Zaria daga nan zuwa ko wani lokaci. Ina fata hakan ba zai zama matsala ba?"
Yayi saurin cewa, "ko kadan! In shaa Allah hakan ba zai zama matsala ba!"
Tace, "to nagode!"

Haka suka kusan raba dare suna hira. Sai data gaji tace mishi kanta yana ciwo sannan ya mata sai da safe.

Washegari suka koma Kaduna. Kwanakin da suka biyo baya kuwa soyayya ake sha ita da Abdullahi din ba ta kadan ba. Ko kuwa ita a bangarenta hira zata ce? Gata nan dai. Ita dai duk wani dokin masoyi da kewa da shauki da ake ji na masoya, bata jin ko kadan a tattare da Abdullahin.
Sai dai har zuwa lokacin tana ba kanta uzirin zata so shi a hankali. Tunda dai shi ta tsayar a matsayin wanda zata aura.

19.


Ranar Alhamis basu bude shago da wuri ba saboda sun zauna meeting akan yadda yakamata su gudanar da tsarin azumi da ake sa ranshi kwanaki uku masu zuwa ko biyu.
Su duka sun fi ta'allaka akan a cigaba da tsare-tsaren da aka saba yi kamar dai sauran azumummuka da suka wuce. Wanda zasu dinga bude shagon da yamma, ana yin kayan ciye-ciye saboda masu son motsa baki bayan shan ruwa.
Sai kuma aka kara shawarar a dinga gashin kaza da kuma yin tatattun lemuka na kayan marmari don a dinga hadawa dashi. Da wannan shawarar duk suka yi amanna, aka ware mutane biyu da zasu dinga kula da wajen da dare din saboda daga Nadiyar har Aramide kowa kafin a sha ruwa yake tafiya gida, meeting din ya tashi.

Kasancewar ranar Aramide bata je wajen aikinta ba, sai duk suka hadu har ita aka cigaba da sallamar kwastomomi da gudanar da ayyuka kamar yadda aka saba.

Wajajen karfe hudu da rabi ne, Nadiya tana cikin decorating din wani 4 steps cake taji daya daga cikin ma'aikatan wajen tana nemanta.
Ta juya tana kallonta cike da alamun tambaya, sai tace mata, "wani yaro ne yazo yana nemanki!"
Tace, "ni kuma?" cike da mamaki.
Tace, "ehh! Kwatancen da yayi dai kamar na ki ne, kuma ya ambaci sunanki!"
Tace, "to shikenan!"

Dama saura kadan ta kammala abinda take yi, don haka tace mata taje tace mishi ya dan jirata.
Ta kammala touching din da take yi, tayi packaging din shi nan da nan, ta bada a kira masu kaiwa su kai, ita kuma ta fita wajen da ake jiranta.

A bangaren VIP aka ajiyeshi, can kuma aka nuna mata data tambayi wanda yake nemanta. Ta wuce can cike da mamakin wane yarone wanda zai je yana nemanta a dai dai wannan lokacin.

Zaune yake akan daya daga cikin kujerun dake wajen, da remote control na game dake wajen yana bugawa.
Yaron ne kuwa kamar yadda aka ce, bata tunanin shekarunshi zasu haura bakwai. Yana saye da wasu kyawawan cotton din sweat pants na yara na Nike ruwan toka, da farar vest. Ta kalleshi kamar ta sanshi, amma kuma ta kasa tunano a inda ta san shi din.

Ta matsa ta zauna a kusa dashi, shi kuma daya ganta sai ya ajiye abin wasan nashi ya juya yana kallonta da murmushi, "Anty Ina kwana?"
Ta murmusa itama sosai, Allah Yayi ta da son yara ita dai, tace, "lafiya lau boy. An ce kai ne kake nemana?"

Ya gyada mata kai, "Daddy ne ya kawoni nan yace in zauna a wajenki zai je ya dawo!"
Ta dan juya kanta cike da mamaki, tace, "Daddynka kuma? wanene shi?"

Yace, "Habib Abdullahi Makama?!" cikin sigar tambaya.
Jin sunanshi kadai ma sai daya sanya taji bugun zuciyarta ya canza. A duka kwanakin da suka wuce tun bayan daya ajiyeta a kofar gidansu ya wuce, karya take yi tace babu wata rana da zata fito ta koma ga mahaliccinta bata tunano wannan mutumin ba. Abin har ya kusa zame mata jiki, yin tunaninshi a lokacin da taje yin kwanciya barci. Da kuma yawan tunanoshi a cikin yini, randomly zata ji kawai ya fado mata a rai. Ko kuma ta tsinci kanta da tunanin ko me yake yi a daidai wannan lokacin? Wasu dararen kuwa har da mafarkinshi da tunanin wannan daddadan kamshin nashi, wanda ta samu ta lalubo turaren da yake amfani dashi cikin wadanda ya bata, itama ta mayar dashi nata turaren.

Yaudarar kanta take yi, da take cewa wai tuni ta manta da sha'aninshi da kurar data kwasoshi. Ita tasan karya take yiwa kanta.

Duk kuma yadda taso abinda ke tukarta a zuciya kada ya bayyana, sai daya bayyana din. Ta rasa fara'ar kirkirowa tayi ko da ta yake ce kuwa, haka bugun zuciyarta ya ki saisaituwa duk yadda taso ta saisaita shi din kuwa.
Ta daure dai da kyar tace, "ok, kwarai na ganeshi. Yana ina yanzu?"
Ya dan daga kafada, "ban sani ba nima. Kawai dai yace in zauna a wajenki zai dawo ya daukeni. Kuma bai ce ga lokaci ba."

Ita abin ma sai ya girmame mata, mamaki ya hanata motsi. To ita kuma a su wa? Da zai dauko danshi ya kai mata? Sai lokacin ta tunashi a matsayin yaron data gani tare dashi lokacin da suka ci karo a Makarfi. Ashe har d'a ma gareshi amma yake tata rashin kirki haka sai kace na wanda bashi da responsibility na Iyali. Koda yake ai dama Anty Lima tace yana da Mata, mutum kuwa mai mata ai ba zai rasa d'a ba ko ma 'ya'ya idan ba wani ikon Allah ba.
Tayi dan murmushi don kada yaron yaga kamar ba ta so zamanshi anan ba, tace, "to shikenan. Zaka iya zama anan kai kadai har zuwa lokacin da zan kammala abinda nake yi?"
Ya gyada mata kai.

Don haka ta barshi anan ya cigaba da wasanshi, amma sai data dauki kayan tabe-tabe ta kai mishi ya ci da lemu. Haka duk bayan yan lokuta zata leka ta inda yake ta ganoshi da abinda yake yi.
Data sake komawa a wani lokaci sai ta sameshi yana gyangyadi, don haka ta kama shi taje ta kwantar dashi a dakin hutunsu, ta koma ta cigaba da ayyukanta.

Da rana ta mishi take away din jollop din shinkafa aka kai mishi ya ci.
Yinin nan guda na ranar anan yayi shi. Yaron yana da wayo, kuma yana da saurin shiga rai. A hirarrakin da suka yi da shi taji cewa shi kadai ne a wajen mahaifin nashi. Kuma bata tunanin ma Mahaifiyarshi tana gidan saboda koda wasa baya ambatarta, sai dai Babanshi din, da Granny da tasan bata wuce Hajiya Umma, da Anty. Wannan kuma bata san ko wacece ba. Sai wajajen karfe hudu na yamma sannan security din wajen yaje yace Ammar yaje inji Babanshi.
Ta samu leda babba ta zuba mishi cima iri-iri na makulashe ta damka mishi a hannunshi.

Tayi tunanin ta barshi ya tafi shi kadai kamar yadda yazo, sai kuma tayi tsoron yanayi da ake ciki da kuma abinda kan iya zuwa ya zo idan aka samu matsala ta dalilin haka. Don haka ta kama hannunshi suka fita farfajiyar wajen inda security ya nuna musu wata farar Elantra, a gefenta kuma bakar Highlander ce.

Kafin ta karasa wajen motar, ya fito daga bayan Elantra din.
So tayi ta buga mishi warning din kada ya sake kai mata dan shi wajen aikinta, kai ko inda take ma kada ya sake tunkara. Don bata ga alakar da zata hadasu dashi ba. Sai kuma yayi mata wani irin kwarjini a ranar.
Farar shadda ce ya sha ta sha surfani baki, ya dora bakar hular Dara a kanshi, kafarshi ta sha takalmi sai ciki shima baki.

Kasancewarshi mutum mai dan gwabin jiki, da kuma kalar jikinshi da ta kasance mai dan duhu, sai shigar ta matukar haskashi, ta kuma fitar mishi da kamala da cikar haibarshi.

Ta kasa ko hada ido dashi balle ta samu bakin iya gaida shi. Shi kuwa hankalinshi yana ga dan shi, ya kama hannunshi yana tambayarshi 'ya yake?' da kuma 'ya ji dadin zamanshi anan?'
Shi kuwa yana ta amsa mishi da 'ehh!'
Ya juya yana kallonta a nutse, cikin tausassar murya yake ce mata, "nagode da kulawa da kika yi da shi Nadiya. It means a lot!"
Ta kasa cewa komi sai, "uhm!!"

Tana so ma ta daga baki ko yaya ne tace mishi wannan ya zama karo na karshe da zai mata haka, amma ta kasa. Shi kuwa yayi tsaye yana kallonta, ba tare da yace mata uffan ba.
Sai kuma ta juya da sassarfa ta koma cikin shagon babu ko waiwaye.

Tana lekensu ta cikin taga, tana kallo har suka fita daga wajen, bakar motar nan tana take musu baya. Ta saki ajiyar zuciya a hankali tare da sauke numfashi, tuhumar kanta take yi, anya ba nema take ta wuce makadi da rawa ba kuwa?
Zuciya cike da sake-sake ta gama ayyukan ranar ta wuce gida.

Washegari Juma'ah ta tashi da farinciki akan sakon samun gurbin karatun Masters data yi a jami'ar Ahmadu Bello Zaria. Wanda suka tura mata shi ta email dinta a ranar da safe.
Ranta fari tas, tuni ita har ta gama tsara yadda karatun nata zai tafi da kuma aikinta da take yi. Tunda saboda shagon ne ma yasa ta yanke shawarar tsayawa a kusa da gida, amma da ba don haka ba so tayi ta cilla can Kudancin Nigeria ma abinta.
Ta so su hadu da Abba ta sanar dashi da wuri tunda ana gama sallah zasu fara darasi, don cikin azumi ma zata je tayi registration. Sai bata samu haduwa dashi ba saboda ya fita.

Don haka ta bari sai da dare sai taje ita da Mama, ita ta mishi maganar karatun. Sai ta bar Mama ta mishi zancen Abdullahi da shima yake so a bada rana da lokaci magabatanshi su je. Saboda shima so yake yi da zarar anyi sallah a tado zancen biki gadan-gadan.

Sam ranar bata yi mata tsayi ba. Sai taga nan da nan kafin tace me har lokacin rufewa yayi, ta dauki hanyar komawa gida.

Haka kawai taji gabanta yana faduwa, wani irin abu ya danne mata kirji, gabadaya ta nemi sukuni da jindadi ta rasa. Yadda kasan wadda aka fadawa sakon mutuwa.

Cikin tsananin mutuwar jiki ta shiga dakin. Ga mamakinta sai ta tarar da gidan ra-rai, yadda kasan babu wani rai da ke ciki.
Duk da cewa girkin Mama ne ranar, tasan idan lafiya to da ka samu su Lantana suna abinda suka saba. Ko Mama din da Amarya suna aikinsu idan yayi musu dare. Amma babu kowa. A ranta tace ko lafiya?
Ta wuce daki abinta, sai ta hangi Lantana da Salame suna lekenta ta tagar dakin Lantana suna kus-kus. Tace, "to! Ashe dai suna gidan!"
Tayi wucewarta dakin Mama ta samu Amarya ma tana can, ta musu sannu da gida kafin ta rage kayan jikinta, ta watsa ruwa kafin ta nemi wajen yin sallah.

Bayan isha'i su dukansu suna falon Mama suna kallo, Mama din kuma tana dakin Abbansu. Duk da bata fadawa Nadiya ba, sai tayi tsammanin ko zancen Abdullahi din zata yi mishi. Tunda ita Mama din da kanta tace zata fadawa Abban nasu a maimakon Yaya AbdulHadi da ita Nadiya din tace a fadawa ya fada mishi.

Zuwa can sai ga Mamar da kanta ta leka tace Nadiya din taje.
Zuciya na dukan uku-uku, haka ta dauki hijabinta ta bi bayan Mama. A ranta tana saka da warwarar ko me yake faruwa? Tunda a tunaninta a sukwane Abban zai karbi zancen zuwan su Abdullahi tunda dai neman kai yake yi da ita. Tana da tabbacin da za a bi tashi ma, kila yace kawai a daura auren kafin azumin ta tare. Ita tasan zai iya aikata fiye da haka ma. To menene zai sa yace yana nemanta? A ranta tace kila nasabarshi yake son sani. Ta gyada kai cikin aminta da haka, sai ta kara samun kwarin gwiwar daga kafa ma ta bi bayan Mama din.

Sai dai shigarsu dakin Abban nasu sai ta ja tayi turus, ta kasa gaba ta kasa baya kamar wadda aka kafe a wajen.

20.


Kusan rabin dakin na shi shake yake da kaya data rasa gane ko na menene. Katan-katan na lemuka, kwalaye na alewa da cingam da biskit har basa kirguwa, ga huhu na goro. A sama kuma ga bandir din kudi yan dubu-dubu sabi gal a ajiye.

Ta lalubi kasan kujerar da Abbansu yake zaune ta durkusa ta gaisheshi.
Ya amsa mata da fara'a sosai, wadda tunda take rabon data ga irinta a fuskarshi har ta manta.

Mama yake kallo, don fara'a bakin nan nashi har kunne. Cewa yayi, "Zuwairah, kinga da gaske da ake cewa da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakkwara! Yau dai na yarda da hakan. Gashi yau ina zaune diyata zata yi silar zuwana Makkah!"

Ta hau kallonsu shi da Mama din cikin alamun daurewar kai. Kafin ta kai ga tambayar ainihin abinda yake faruwa, Abbansu ya yi mata nuni da kayan dake shake a dakin.
Yace, "ki kalli wannan tarin kaya na arziki da girmamawa haka, kayan na gani ina so din ki ne.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login