Showing 84001 words to 87000 words out of 142169 words

Chapter 29 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

471

kauracewa abincin restaurants koda ya fita. Ita kuma sai take hada mishi snacks na ciye-ciye wadanda tasan zai ji dadinshi kuma zasu cika mishi ciki, idan zai fita sai yayi guzirinsu.

Ta cika musu leda taf tace sun ci a hanya. Haka ta rakasu har wajen motar da direba ya tuko Yakumbo a cikinta. Da zata shiga mota ta juya tana kallon Nadiya, ta kama hannunta ta rike tana murmushi wanda ya ke nuna wani abu na bacin rai dake dankara a can cikin ranta wanda take kokarin dannewa. Tace, "nagode sosai da sosai 'ya ta, Allah Yayi miki albarka. Allah baku zaman lafiya a cikin rayuwar aurenku. Don Allah a gaishe min da Ammar, hopefully shima idan sun samu hutu a kawo min shi. Shima Baban nashi a mika min sakon gaisuwata izuwa gareshi."

Tayi murmushi na yake tana jinjina kai, "in shaa Allah duk zasu ji Yakumbo. Ku gaida gida. Kuma in shaa Allahu ni da kaina zan kawo miki Ammar din idan sun samu hutu."
Ta sake yin murmushi wannan karon mai nuna jindadinta, tace, "to Allah Ya amince Nadiya!"
Ta shiga mota direba ya ja suka tafi.

Ta juya ta wuce sashen Hajiya Ummah da niyar dauke abubuwan data jera akan dinning kafin masu shirya abincin dare su kai ga zuwa. A ranta tana ta saka da warwarar wannan abu dake faruwa mai daure kai.

Sai ta samu Hajiya Ummah tana falon har a lokacin, tana shiga ta ambaci sunanta cikin wata murya dake nuna koma menene zata fada ba wanda Nadiya zata ji dadinshi bane.
Tace mata, "gargadi daya ne zan yi miki a yanzu wanda nake so ya zama na karshe a wajenki, kina ji na?"
Nadiya ta gyada kai da sauri, tana kallonta gabanta na faduwa, a ranta take tambayar me ya faru ne yanzu-yanzu ba tare data sani ba?

Hajiya Ummah tace, "kada ki kuskura, in sake yin baki a cikin gidannan ki shiga cikin ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?harkarsu ba tare da ni na bada wannan izinin ba. Nan din gidana ne, ni kadai nake da hurumin tarar wani idan yazo nan gidan da mutuntawa ko akasin haka, babu ruwanki, babu abinda ya hadaki da kowa da zaki dinga wani bare-bare da rawar jiki akan wasu daban. Wannan shine gargadi na farko da karshe, kada ki kara maimaita min hakan!"

Kanta ya daure da wannan abu, ta daga kai tana kallon Ummah din da mamakin kalaman dake fita daga bakinta, tace, "amma Ummah.... Yakumbo fa mahaifiyar Baban Ammar ce!!"

Ta daga kafada, "and? Sai me? Hakan ba shi ya goge cewar nan gidana ne inda nake da iko dashi, nake da damar yin duk abinda naga dama ba. Tana amsa sunan mahaifiyarshi ne kawai, amma ba wai tana da wannan girma da kimar bane ko iko. Don haka idan zaki sauke wannan giringidishin dake kanki tun wuri ma ki sauke saboda wannan hanyar da kika dauko ba zata bullar dake hanya mai kyau ba! Ki kwashe min wadancan kayan da kika baza min a kan teburi ki san inda zaki yi dasu." Ta haye sama ta bar Nadiya anan.

Ta jima anan tana sakar zuci, kafin dai daga karshe ta ja kafafunta ta wuce ta kwashe kayan ta kai kicin, ta koma bangarenta jikinta kamar an watsa ruwa.
Ta kasa ganewa kanta abinda ke faruwa, sai dai ko kusa bata tunanin zata iya biyewa umarnin Hajiya Ummah a wannan karon. Wace riba ce ma ita Ummah din zata ci idan ta raba 'da da Uwa? Kuma menene ribarta idan ta hana Nadiya bata girman daya dace? Ta sanya a ranta, idan har ta samu hali, ita kam sai ta kusanta Habibu da mahaifiyarshi.


34.



Ranar da girki ya juya kanta, ta tareshi kamar yadda ta saba a sauran ranaku. Ranar da wuri ya shiga bangaren nata, yana ta wani irin rawar jiki da bare-baren jiki yadda kasan dai shekara ce yayi rabonshi da ita. Har kullum hakan bai daina ba Nadiya mamaki ba, rawar jikin nashi tana yin yawa a lokuta da dama da har baya iya boyewa a gaban Ummah yanzu. Tana tsoron ranar da Ummah din kuma za tayi magana a kan haka don ga dukkan alamu idanu ne ta zuba mishi don taga iyaka gudun ruwanshi.

Duk da dai a kullum kuma sai ya mata korafin., 'ban san me zan miki ki saki jiki da ni ba Nadiya. Har yau kina boye min kanki, har yanzu baki gama mallaka min kanki ba Nadiya. Ban kuma san me zan yi ba, for you to give me all of you. Heart, body and soul!"
Ko a daren yau abinda ya gama fada mata kenan cikin yanayi na contentment da yake a ciki. Shi kanshi yasan cewa yana korafi da yawa da neman takura mata, but he can't help it. Daga yanayin da take karbarshi kadai, yasan cewa ba wai don ta bashi kanta bane dari bisa dari yasa take ziyartar shimfidarshi, sai don kawai sauke hakki wanda ya rataya a kanta. To in banda abinshi ma, har yaushe ne yake da wani iko ko katabus a kan matarshi? A tsayin shekarunsu na uku da aure shi da Shukurah, ba zai ce ga rana daya wadda ya gayyaceta zuwa shimfidarshi ba taje kai tsaye ba tare da korafi ko ta kai mishi wani excuse ba na daban. Sai ita Nadiya din mai kokarin yi zai takurawa? Wani lokaci haka zai zauna yana tuhumar kanshi.

Rayuwar aurenshi da Hidaya mahaifiyar Ammar rayuwace ta mutunta juna da kaunar juna mai tsafta wadda suka jima suna shimfidata tun kafin auransu, sun hadu da ita ne a Jami'ar Ahmadu Bello University dake Zariya, lokacin yana kokarin hada degree dinshi na farko. Babu jimawa da kammala karatun nashi aka daura musu aure da ita, da niyar bayan auren nasu zata karasa nata karatun saboda ita a lokacin tana shekara ta biyu ne kawai. Haifaffiyar cikin Zariya ce a unguwar Palladan.
Ba wani cin amarci suka yi ba na azo a gani, saboda ana yin auren Allah Ya hadata da wani irin ciki mai zafin laulayi. Ya zamana bata ko son ya kusanci inda take ma balle zancen auratayya ya shiga. Shi kuwa kasancewarshi mutum mai hakuri da tausayawa, yayi kokari sosai ya danne urges dinshi har zuwa lokacin da cikin nata yayi kwari da girma sosai. Ba jimawa da samun wannan lafiyar kuma ta haihu, cikin ikon Allah kuma tun bayan haihuwar bata samu wata cikakkiyar lafiya ba. Watanta uku da haihuwar Ammar Allah Yayi mata rasuwa. Mutuwar ta bugeshi kwarai da gaske, ya dauki son duniya ya dorawa Ammar. Bai kara bibiyar lamarin aure ba bayan nan har sai da Ummah da kanta taga dacewar ta shiga cikin zancen sannan.

Bayan kuma bin dogon layin yanmata da dama da suka wucewa tantacewar Ummah, rabon ya fada kan Shukurah. Sai gashi a wajenta bai samu abinda yake so din ba.
A yanzu daya samu Nadiya din gabadaya sai ya juye ya koma phase din cin amarcin sabon aure wanda bai ci ba a wancan lokacin. Amarcin da ko a wancan lokacin baya yi mishi wannan rawar kan da giringidishi.

Wani abu ne a tattare da Nadiya din na musamman, wanda shi kadai yasan irin halin da yake tsintar kanshi a ciki idan yana tare da ita. Shi yasa zuciya da sake-sake suke saka mishi, wai a hakan ma bata gama sakar mishi jiki ba. Me zai faru kenan idan ta mallaka mishi kanta dari bisa dari? Watakila dai ranar sai ya kai ga shidewa.
Shi yasa ya takura din, ba kuma wai don ta gaza mishi a komi ba. Wani lokacin shi da kanshi zai dawo daga baya yace mata ai ko a haka ta barshi, shi kam hakan ya isheshi.

Ta gama sauraronshi yana ta zuba korafinshi, idan ta itane ta riga ta gama sabawa da hakan. Ita dai kam, iyaka tunani da wasa kwakwalwa, tayi akan ta gano me Habibun ke nufi da kin mallaka mishi jiki amma ta kasa fahimta. Shi yasa ta ke kyaleshi kawai yayi ya gama. At the end of the day dai, a hakan zai sake dawo mata.

Ta kalleshi a nutse ta cikin dan hasken dake ratsawa dakin, tace mishi, "Ummansu Rashida ta zo ranar nan. Nasan kila ma kunyi magana da ita ko Rashida din, amma dai na ari bakinka na ci maka albasa. Nace mata idan su Ammar sun samu hutu zan kai mata shi har gida su gaisa. Don Allah kada kace min a'ah! Ka bari in cika wannan alkawarin."

Yayi shiru a kwance kamar bai ji abinda tace ba. Lokacin yana rigingine ne a kwance, ita kuma ta dan kishingida tana kallonshi. Sai ta dora tafin hannunta a saman kirjinshi wanda babu riga a jiki, ita a karan kanta ba zata ce ga lokaci na karshe da ta kai hannu ta taba jikinshi ba willingly, watakila ma zata iya cewa hakan shine na farko.

Ta kara yin kasa da murya cikin son janyo hankalinshi, tace, "Daddyn Ammar magana fa nake yi maka, kaji?!"
Ya dan bude idanu yana kallonta da idanu kasa-kasa, tsigar jikinshi har tashi take yi. Kamar dai ba yanzu bane babu dadewa ya gama sauke mata tarin rigingimunshi ba.
Yace, "to me kike so in ce miki ne Nadiya? Tunda kin gama are min baki kin ci albasa?"
Tayi dan murmushi a tausashe, "to kayi hakuri idan hakan ya bata maka rai."

Ya kai hannu ya dora saman nata inda take wasa dashi a kirjinshi ba tare da tasan tana yi ba, yace, "babu laifin da kika yi Nadiya. Sai dai wannan karon tuni an yiwa Kakanninshi dake Zaria alkawarin kaishi yayi musu hutunshi. Kinga babu dadi kai tsaye kuma ace musu an fasa ko? Amma mu jira zuwa lokacin sai mu ga idan hutun nasu da tsayi, daga can sai a kaishi Makarfi din. Hakan yayi?"

Tayi murmushi sosai cike da jindadin abinda yace, ko babu komi dai ai ta samu positive reaction. Tace, "to amma dai har da ni din za a je ko? Kuma dai kaga bikin Anty Lima ma nan da sati uku ne fa, ina so in je in tafi a week to bikin saboda bana so inyi missing din komi. Ka dai san yadda muke da ita."

Ya kalleta da baki a dage kamar wadda ta tsiro da wani sabon kai daga jikinta, yace, "ke yanzu idan nace miki ki tafi a week to bikin kuma sai ki tafi? Kusan sati biyu fa kenan kike fada min zaki yi!"
Tace, "to ai kaga ta hakan zan samu damar zuwa in ga dangi suma su ganni sosai ko? Itama da bikina ba haka ta yi mun ba?"

A ranshi yake raya, 'Allah tsareshi da ganin wannan rana shikuwa. Haka kawai sai ya bar matarshi ta dauki hanya wai ta tafi biki fiye da sati biyu? God forbid!'
Amma a fili kuma sai ya jata cikin jikinshi daya hango zai iya yin amfani da wannan damar ya tafi zagaye na biyu. Yace, "to bari dai lokacin yayi sai mu gani!"
Jin haka ita kuma sai ta bada kai bori ya hau, duk da tarin gajiya da barci dake tattare da ita.

Washegari tafiya ta kamashi ta gaggawa ya tafi wadda zai kwana a can. Yayi sallama da su cike da kewa ya tafi, wani taro ne aka kira na gaggawa a can Abuja. Tafiyar tasu ma sai tayi tsayi ta daukesu har kwanaki biyu.

Ranar da zai dawo Nadiya ta san zai karasa mata cikon kwana dayanta da bai yi ba ne, don haka ta shirya tarbarshi ta musamman ta hanyar da tafi gwanancewa, wato girki. Don tunda ya tafi, kullum korafinshi abinci ne. Don haka ta shiga kicin dinta ta gasa mishi kaza gashi mai kyau da ruwa-ruwa, ta barta a cikin microwave. Ta san shi gwanine wajen cin abincin tsakiyar dare, sau tari sai dai ta farka ta ga baya gado, da safe kuma ta shiga kicin ta samu ya cinye mata snacks da kayan motsa baki da bata rabuwa dasu. Wannan dalilin yasa ita kuma ta himmantu wajen ganin cewa ta bar mishi wani abu da zai ci koda ya tashi cikin dare a bangarenta.

Shigowar yamma yayi, tana can bangarenta tana wanka bayan girkin data gama, duk da kasancewar bata da tsarki hakan bai hanata dauro alwala ba, saboda a kodayaushe ba zaka rasata da ita ba a jiki.
Ta sanya doguwar rigar shadda ruwan goro da aka yiwa surfani a wuya da hannuwan rigar da green din zare mai kyau. A fatar Nadiya da take ta kara tumbatsa da yin fari da yin kyal-kyal a lokacin kamar ka taba jini ya fita, Nadiya ba karamin kyau tayi ba. Ga jikinta dake kara wani budewa yana direwa waje daya. Saboda tana matukar kula da jikinta da cimar da take ci mai kyau da karawa jiki kyau, shi yasa a kullum take ta kara rikita maigidan nata kamar wata sabuwar amarya.

Ta jira aka yi sallar isha'i, kafin ta dora dan siririn gyale green a saman gashinta da ya sha gyara. Ita da kanta ta zauna ta wankeshi tayi steaming din kayanta dazu, sai ya kara yin luwai yana tashin kamshi mai tsananin dadi. Yadda gashinta ke kamshi daban, haka jikinta yake fitar da wani kamshin na daban, haka ma kayan jikinta nasu kalar kamshin daban. Ta dauki wayarta ta fita daga falon tana taku dai-daya abinta.

Suka ci karo da shi a corridor wanda zai sadaka da bangaren Hajiya Ummah. Bakar Jallabiya ce a jikinshi, yana ta tashin kamshin turarenshi na gado.
Ya tsaya yana kallon yadda take tafiyarta a nutse, jikin nan yana rangaji sai kace bishiyar icen turare da iska yake kadawa a sanyaye. Ya shagala da kallon nata har sai data karasa inda yake, tayi diddige saboda yanayin tsayi daya fita, ta hura mishi iska a idanu.
Yayi firgigit yana dan ja da baya, sai ta saki wata tattausar dariya ganin yadda yayi.

Yace, "wato ma ni kike tsokana ko Nadiya?"
Tace, "to ai kai dinne naga kana ta kallona kamar ba zaka daina ba, kallon na nawa ne ma wai da?"

Ya kamo hannunta yana dan murmushi, taushin fatarta da santsin da take yi tana kai mishi har tsakiyar kanshi. Yace, "ki bari in muka hadu anjima zan fada miki ko na nawa ne!"
Ta fizgi hannunta ta wuceshi tana yar dariya, "lallai ma na ki wayon!"
Ya bita suka jera yana jifanta da kallo cikin burgewa, "ina gab da hanaki yin kwalliya a gidannan Nadiya! Saboda gaskiya na fara kyashin wadannan ma'aikatan dake kaiwa da kawowa a gidan suna gane min ke fa!"

Ganin sun shiga tsakiyar falon Hajiya Ummah kuma ga Hajiya Ummah din da Shukurah a zaune suna magana, sai bata mayar mishi da amsa ba.

Mazauna falon suka zuba musu ido suna kallonsu yadda suka jera dinnan. Ai ko hasidin iza hasada dai a wannan lokacin idan ya ga Nadiya da Habibullahi, sai ya kara juyawa ya kallesu, sai kuma ya yaba. Saboda tsabar haduwa da suka da dacewa. Wani abu ya daki kirjin Shukurah a lokacin har take jin numfashinta yana yin sama kamar wadda take fama da athma.
Hajiya Ummah ta samu kanta da yin tasbihi a cikin ranta saboda ba karamin kwasarta suka yi ba. A ran nata tace, 'wannan shine ma'anar match well made!'

Suka karasa wajensu a nutse. Ya zauna a kusa da Hajiya Ummah kamar yadda ya saba, Shukurah a gefenshi na hagu. Ita kuma sai ta zauna a tana mai fuskantarshi kusa da Hajiya Ummah kenan. Ta fara gaishe da Hajiya Ummah din, ta kuma fara zuba mishi abinci kafin ta nemi waje ta zauna. Don tun ranar daya ce ta zuba mishi abinci da kanta, bata kara fashin zuba mishi abincin ba matukar ranar girkinta ce.

Fried rice aka yi da taji kaji da hanta da nama a ciki. Ta zauna ta ci sosai, saboda da rana bata samu sukunin yin abinci ba saboda shirin tarar Maigidan data yini yi. Tana kula da yadda ya dinga tsakurar abincin shikuma kamar a koshe yake.
Falon ya kaure da hira a tsakaninsu wadda rabinta game da taron da yaje ne, da kuma irin nasarori da suke gani a yawace-yawacen kamfen dinsu. Ganin ba a sanyata a ciki ba, sai itama bata tsoma musu baki ba.

Ta tashi a nutse lokacin data gama cin abincin, tayi musu sai da safe da niyar wucewa bangarenta.
Shi kuma kamar wanda yake jira dama, sai yayi fatali da cokalin hannunshi shima ya fara musu sai da safe.

Hajiya Ummah ta bishi da kallo na bacin rai da takaicin wannan abu na Babangida. Tun yana kokarin boye mata dai har ta kai yanzu bata baya ma shayi ko jin kunyar idanunta ko kadan. Shukurah kuma ta mike tsaye yana kallonshi cikin kunar rai. Su dukansu kasa boye wannan doki da yayi a yau dai ya bakanta musu rai. Amma Shukurah sai tayi kokarin dannewa cikin kissa da kisisina.

Ta kamo hannunshi babu ko kunyar Hajiya Ummah dake kallonsu, tace, "Honey ina zaka je ne kake gaggagawa haka? Ko ka manta yau girkina ne?"
Jin haka Nadiya sai ta dakata da tafiyar da take yi ta waiwaya tana kallonsu, ita bata ma san Habibu ya tashi tana shirin bin bayanta ba.

Ya kalleta yace, "me kike fada ne haka Shukurah? Hala kin manta cewa kwana daya nayi a wajenta kafin tafiyar nan ta sameni ko?"

Tayi caraf tace, "to ai ka cinye kwananka shekaranjiya, jiya da yau kuma ni ce da miji. Ita ai sai gobe zata karbeka."

Yayi maza yace, "wannan wane irin zancene wai kike yi haka marar kan gado? Ai a doka da tsari da ka'ida na Islama, sai na karashe mata kwananta daya sannan zan dawo wajenki!"

Amma Shukurah ta rufe ido tace bata san wannan zancen ba, Nadiya da mamaki ya kamata ma ita sai ta kasa magana. Kawai tayi tsaye dososo! Tana kallonsu kamar wadda aka kafe a wajen, wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama!

Ummah da taga zancen nasu ya ki ci ya ki cinyewa sai ta tsoma musu baki, tace, "kaima Babangida dai so kake yi ka ja zancen da tsayi. Tunda dai wancan lissafin ya riga ya gama karewa ba sai kawai ku jona wani sabo ba? Ni ma dai naga kyawun tsarin da Shukurah ta fitar. Ka hakura kawai ka karasa kwanan yau a wajenta, in yaso gobe sai ku zuba sabon lissafi!"

Nadiya ta daga kai ta kalli Ummah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login