Showing 30001 words to 33000 words out of 142169 words

Chapter 11 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

438

da nata hasken. Daga ganinta kuma kasan zata dara Nadiya a shekaru a kalla da biyu ko uku.

Dada tace mata, "wannan Halimatu ce diyar kawunku Yasir, ba lallai ki santa ba saboda ba anan ta tashi ba. Gabadaya karatun sakandare dinta da na Jami'a a Amurka tayi, bata jima da dawowa nan ba."

Nadiya ta jinjina kai, kwarai tana jin labarin kam. Lokacin da shi Kawu Yasir din yaje can Washington DC yayi aiki da gidan Rediyon DW na tsahon shekaru bakwai. Taji ance dama akwai diyarshi da suka baro a can tana karatu.
Suka sake gaisawa kafin Dada ta dora da cewa, "Fatima ta turota kije ta miki awon kayan da za a dinka miki na biki, ita ce madinkiyar taku."

Tace, "to babu matsala, bari in karya da sauri sai mu tafi!"

Cikin yan mintuna kalilan kuwa ta gama. Ta tashi taje ta dauko takalmi da jaka, suka yiwa Dada sallama suka fita.
A motar Halima din suka tafi wadda taji su Aysha suna ce mata Anty Lima. Don haka itama ta bi bayansu.
Kafin su karasa shagon nata hira sosai ta barke a tsakaninsu. Nan da nan sai suka zama kamar wasu wadanda suka dade da sanin juna. Ta fahimci Anty Lima din bata cika son hayaniya ba da shisshigi, kuma Allah bai dora mata girman kai irin na sauran yan'uwansu da kannenta ba, don haka tasan tasu zata zo daya.

Bata tunanin duk cikin iyalin Kawu Yasir akwai wanda suke magana dashi. A duka iyalan nashi babu na zaba. Kowa kallon wani wanda ba su ba yake yi kamar wani mabaraci ko miskini, idan kaje inda suke sai su dinga maka wani kallo na raini da kaskanci, ita kuwa taga a wane dalili zata zauna ana rainata bayan ba nema ba take yi a wajensu? Don haka ta ja jikinta gefe. Ko Maidugurin taje idan ba wani abu na dole ba, baka ganinta a wajensu. Amma dai taga Anty Lima din kamar ba irinsu bace.

Shagon nata yana nan a Kuntau Road. Ta karanta fashion and Textile design ne a can Washington din, kuma yanzu haka tana aiki da wani kamfanin dake kera lesuka ne a Turkey, shi shagon kawai ta bude shi ne saboda tana son dinki. Amma ba ita take yin dinkin da kanta ba. Tana da madinka dake mata aikin, yawanci ita sai dai ta duba musu aikin ne ko kuma ta zana musu irin design din da take so su kuma su yi.

Wajen ya matukar burge Nadiya. Kai daga gani kasan cewa kaga wajen harkar manya ba ta yara ba.
Suka shige can inda Anty Lima din take gudanar da ayyukanta tana nuna mata kayayyakin Nadiyar da Madam ta bada a dinka musu ita da Safiya.

Wasu ma an riga an dinka, gown din da zasu sanya ranar dinner ce da kuma atamfar kamu tace mata tafi son ta dauki measurements dinta kafin a dinka.
Ta dauki measurements din nata ta ba wanda zai yi dinkin, ita kuma ta tsaya ta hade kan kayan Safiya da yake an gama dinka nata, idan sun je gidan Madam sai ta bada. Akwati guda haka ta cika shi ta shake kamar kayan amaryar ne ba na yan biki ba.

Suka fita suka shiga mota. Har sun dauki hanyar gidan Madam din sai Anty Lima ta kalleta, tace, "wajen kunshi zan je, ko zaki je kema sai a miki kunshin?"

Ta kalli hannunta da yayi fari tas, rabon da tayi kunshi har ta manta. Tace, "muje to. Bani da abin yi yau din dama. Gashi dama rabona da inyi kunshi har na manta."
Don haka ta juya akalar motar zuwa wani wajen.

13.

Ba su suka isa gidan Madam ba sai can bayan la'asar. Bayan kunshin da aka yi musu, har kitso sai da aka yiwa Nadiya din. Irin ainihin kitson bare-bari aka mata, wani ya yi gaba, wani kuma yayi baya. Da yake bata son fitar da gashi waje, sai ta hadeshi a tsakiyar kanta ta daure kawai.

Gidan Madam din madaidaicin gida ne, flat. Securities biyu ne a zaune suna gadi a lokacin. Sai da Anty Lima ta fada musu ko su waye su, suka kirata ta bada izinin a barsu su shiga sannan aka bude musu gate. Nadiya kai kawai ta dinga jinjinawa cike da mamakin wannan lamari na Madam.

Anty Lima ta ajiye motarta kusa da wata hadaddiyar jeep Rav4 baka tana ta sheki.
Suka fita daga motar, hannunta rike da akwatin kayan Safiya suka shiga falon Madam din.

Ita kadai suka samu a hadadden falon nata da ya sha saitin wasu Italian Royal kujeru.
Tana zaune akan daya daga cikin kujerun ta hakimce, hannu daya rike da wayar Samsung Galaxy tana dannawa, a ajiye akan karamin teburi kuma data dora kafafunta akai, sabuwar fitowar wayar iPhone ce.

Ta ajiye wayar da sauri ta tashi tsaye tana yiwa Nadiya din oyoyo, "oyoyo my baby! kitawu nasaraye (nayi kewarki sosai)" da yaren bare-bari.
Itama ta rungumeta fuska dauke da murmushi, ta manta rabon data sanya mahaifiyar tata a idanu, kullum sai dai ta waya. Sai dai tafi fahimtar su zauna a hakan, saboda zamanta ita da Madam a waje daya ba zai taba haifar musu da da mai ido ba. Ita dai Madam bata son a shiga harkarta, tana da son mulki ta yadda duk abinda tace kayi kawai ita a sonta kace mata to ne babu tambaya balle shakku. Ita kuma Nadiya bata iya gani ta kyale, sannan ba zata taba amincewa abinda ya taka shari'a ba ko kuma take ganin ya kaucewa tunaninta. Ta hakane sai ita da Madam din basu cika samun daidaito ba a lokuta da dama.

Ta saki Nadiyar tare da rungumo Anty Halima itama tana mata oyoyo kafin suka nemi waje suka zauna.
Hira ta barke sosai a tsakanin su ukun wadda tafi karkata tsakanin Madam da Anty Lima. Nadiya dai binsu take yi da ido, idan anyi abin dariya ta dara ko kuma ta bisu da murmushin yake. Tun kafin aje ko'ina zaman har ya fara isarta. Saboda hirar tasu duka ta ta'allaka ne a wajen yadda Anty Lima tayi sa'ar rayuwa take. Ta kammala makaranta cikin nasara, ga aiki tana yi, ga shago tana da shi, ga kuma hadadden saurayi dan masu kudi da take dashi a hannu, me yafi wannan dadi da alfahari? Nadiya tasan idan tace zata zakalkale to lallai sai Madam ta fada mata maganar da zata bakanta mata. Kila tace 'ba kamar Nadiya ba!' Ko kuma tace, 'dama ace Nadiya ce!'
Ire-iren wadannan maganganu ba karamin bakanta ranta suke yi ba idan tayi su. Sai taga kamar Madam din ta raina abinda take yi kuma take samu.

Anty Lima take tambayar Madam din, "ni ina Sophie ne ban ganta ba?"
Madam tayi dan murmushi, tace, "Sophie tana gida, sai gobe zata taho. Kin san fa tana ta shirye-shiryen tafiya Egypt. Medicine take son karanta. Yanzu haka ana zancen bude mata asibiti ne idan ta dawo!"

Anty Lima da Nadiya duk suka nuna jindadinsu game da hakan.
Madam ta kalli Nadiya kasa-kasa, "ke kam ai kin barar da garinki ya zube a kasa! Da ace kema kin nufi wani bangare na kiwon lafiya da ba shikenan ba kakarki ta yanke saka? Kinga da babu ruwanki da neman aiki tunda ga asibiti nan a gida!"

Tayi dan murmushin yake kawai, ta dauki kofi da aka tsiyaya musu lemu a ciki ta kai bakinta tana kurba. Tana so ta tambayeta, 'sai kuma tayi ta zama kenan tana jiran har a budewa Safiya asibiti kuma taje ta mata aiki? Ko kuma tace, saboda shi shagon da take managing bashi da muhimmanci a wajenta kenan ko kuma don Madam din ta raina sana'ar?'
Amma duk sai ta kame bakinta bata ce komi ba. Don tasan tana bude baki to hirar arzikin da suke yi zata watse ne.

Sai Anty Lima ce tayi yar dariya, tace, "Mommy ai kuwa suma caterers suna samun yan canji fa babu laifi. A yanda take fada min yadda shagonsu yake daukar manyan mutane nasan fa ba karamin kudade take damka ba!"
Maimakon Madam din ta bata amsa sai ta tabe baki ta dauki wayarta daya ta hau latsawa. Itama sai bata damu da hakan ba, don bata so hirar tasu tayi tsayi. Suka cigaba da hirarsu da Anty Lima.

Sunyi sallar magriba ta fara neman yanda za ayi ta koma gida tunda Anty Lima din anan wajen Madam zata zauna har zuwa bayan biki. Basu cika zaman lafiya da sauran yan gidan nasu ba. Ita ce diyar fari, mahaifiyarta kuma ita kadai ta haifa ta rasu. Sauran matan da Babanta ya aura ba wai son tsakani da Allah suke mata ba. Ta sha wahala kwarai da gaske a hannunsu. Shi yasa da zasu dawo Nigeria daga Washington ta makale a can ta ki dawowa. To da Allah Ya taimaketa mahaifinta yana sonta sai abubuwan suke mata sauki.

Amma a yadda take fadawa Nadiya, rayuwar gidansu kusan kwatankwacin ta gidansu ce, bambancinsu kadan ne. Ga yaran gidan duk sun rainata saboda iyayensu basu muhimmantata ba a wajensu. Ga matsalar rashin aure da ta sha fama da ita, shekarunta talatin da biyu a yanzu amma bata taba aure ba. Ta sha gori da suka da wulakanci har da na Allah tsine. Amma da yanzu kuma ta samu miji na nunawa sa'a, dan gidan wani tsohon Janar ne, kuma matukin jirgin sama, duk kuma sai suka koma suna neman wajen zama a wajenta. Ita kuwa tace ai ba haka ake yi ba.
Nadiya ma kam tace kwarai tayi gaskiya, don kuwa ba taren Allah da Annabi bace ba kenan, ta son abin duniya ce.

Madam ce ta hanata tafiya lokacin data leka dakinta da niyar yi mata sallama, "ki zauna wajen Halima kawai, saboda goben da safe ina so a hada abin kari mai kyau, za a kai gidan Hajja Umma!"

Ita bata ma ji labarin Hajja Umma din zata je wajen bikin ba. Duk da bata santa ba, amma tasan labarinta a bakin mutane sosai.
Tace, "to shikenan. Me kike tunanin za a dafa mata ne?"

Ta yi jim tana tunani kafin ta daga kafada, "just cook something fancy! (Kawai ki dafa wani abu mai dadi da kuma tsada), a hada da wuri dai kafin karfe tara. Mu kuma ki dafa mana wani abin mara nauyi saboda ban taho da cook dina ba, already har na fara gajiya da abincin restaurants din garin nan! Sam basu iya abinci to my liking ba!"

Nadiya dai tayi dan murmushi ta amsa mata da 'to' ta juya ta koma dakin Anty Lima.
Ita kadai ta shiga kicin din, ta bar Anty Lima a daki tana waya da wanda zata aura bayan sun gama sallar isha'i kenan. Kasancewar dare ne kuma sun yi yan ciye-ciye, sai ta musu jollop din macaroni, ta kuma hada musu shayin chamomile.

Suna gama ci Madam ta musu sai da safe ta wuce daki, itama Nadiyar kayan da suka yi amfani dasu ta wanke kawai ta koma daki tayi shirin barci. Anty Lima ta bata aron kayan barci ta sanya. Ta zauna akan stool din madubi da earpiece jone a kunnenta suna waya da Aramide.
Labari take bata irin fadan da iyayen Mijin nata suka mishi akan irin abinda yake mata, sun kuma yi yarjejeniya dashi akan cewa duk ranar daya kara daga hannu ya tabata da sunan duka to a bakacin aurensu, kuma babu su babu shi, yace ya amince.

Nadiya ta tayata murna da kuma addu'ar Allah Yasa karshen abin kenan. Daga nan suka jima suna kara tattaunawa game da yadda zasu kara fadada wajen kasuwancinsu da kuma abubuwan da suke ganin zasu kara jawo musu kwastomomi. Lokacin da suka gama wayar tuni Anty Lima ta jima da yin barci. Ta kwanta a gefen katifar tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta. Babu jimawa barci ya kwasheta.

***

Tun sallar Asubahi da tayi bata koma barci ba. Ta dora karamar hijabi a saman kayan barcin jikinta ta fada kicin. Duk wani abu da za a bukata akwai a ciki, komi a shirye tsaf kamar dama can da mutane a cikinshi ba wai zuwa suke yi su tafi ba.
Babu bata lokaci ta hau aiki. Alkubus tayi niyar yi, don haka ta yi kwabin ta ajiye.

Kafin ya tashi ta ciro tantakwashi da naman kasa a cikin firiza ta hau tafasawa. A gefe guda kuma ta hau kwabin special Banana bread dinta. Kwararren kwas tayi akan shi ta online a kasar Indiya wanda ya dauketa kusan watanni biyu, bata taba yi ba amma yana daya daga cikin menu din da suka tattauna jiya da Aramide akan zasu kara shi a shagonsu.

Zuwa karfe takwas na safe ta gama cin karfin aikin sai abinda ba a rasa ba. Da yake abincin da dan yawa tayi, sai ta samu warmers masu kyau ta zubawa Hajja Umma nata, sauran kuma ta shirya musu akan dinning table.

Madam Zarah ta fito daga dakinta misalin karfe takwas da mintuna arba'in. Bathrobe ce kawai a jikinta sai tawul data nada a kanta, daga ganinta daga wanka ta fita.
Ta samu Nadiya a kicin tana kokarin dura kunun gyada a cikin flask. Taga tuni har ta kammala komi sai wanke-wanke dake jiranta.

Tace, "thank God Nadiya, barci ya daukeni na manta in tasheki ashe har kin kammala komi."

Nadiya tayi murmushi, ta juya tana fuskantarta, "Nda watu ya (Barka da safiya Mama)"
Tayi murmushi, "Kin tashi lafiya Nadiya, ya aiki?"

Tace, "Klewa slai (lafiya lau).
Sau tari ko waya suke yi da Madam din basu cika hausa ba sai Kanuri ko Turanci. Shi yasa itama idan ta je can din take kokarin juya harshenta.

Ta nuna mata inda ta ware abincin Hajja Umma din a cikin wani kwandon zuba abinci mai kyau, tace, "ga shi an hada komi. Wannan kunun kawai zan zuba shikenan!"

Ta matsa tana daga kwanukan tana gyada kai cike da gamsuwa, "good, good! Yayi sosai. Bari in kimtsa yanzu-yanzu sai in kai mata!"

Nadiya ta bita da kallo cike da mamaki lokacin data fita daga kicin din.
Iyaka saninta ita dai Hajja Umma da Madam din basa ga maciji a tsakaninsu. Amma yanzu shine Madam din da kanta ce zata je kai mata abinci da kanta ba aike ba? Ta jinjina kai a ranta tana fadin 'lallai in da ranka ka sha kallo!'

Cikin yan mintuna Madam din har ta fito cikin wata doguwar rigar Bubu ta shadda data sha dinkin surfani na yan Senegal. Bata daura dankwali ba sai gyale data dora a saman kanta daya fitar da sassalkan bakin gashinta da yayi kwance luf. Idan ka ganta a lokacin sai ka rantse Yayar Nadiya ce ba mahaifiyarta ba, saboda iya daukar gayu da kuma yanda yarintarta take fita kullum.

Nadiya ta tayata daukar kayan zuwa wajen motarta. Ta shiga gidan gaba ta tashi motar tana fadawa Nadiya kada su jirata saboda ba anan zata yi karin ba. Amma ta zubawa security dinta abincin, kuma su zauna a gidan har ta dawo saboda masu planning da decorations zasu je, tunda anan gidanta za ayi kamu da misalin karfe biyar na yamma. Nadiya ta amsa da 'to'

Ta koma tayi duk yadda tace, kafin ta wuce daki. Anty Lima tana bandaki da alama wanka take yi. Ta dauki waya ta kira Aysha ta fada mata idan da yadda za ayi ta kai mata akwatinta ko kuma kayan da zata sanya saboda kayan Anty Lima sun yi mata yawa. Aysha tace tunda ga direban gidansu nan yaje kai wasu bakin Mamansu gidan Dada din, bari ta bishi sai ta kai mata kayan, ta mata godiya ta katse wayar.

Suna waya ita da su Maryam Anty Lima ta fito daga wanka. Ta zauna tana ta shafe-shafen mayuka da turaruka sai kace wadda zata canza fata, Nadiya dai tana ta binta da kallon mamaki. Ita sam wadannan shafe-shafen bata ganin amfaninsu.

Anty Lima ta kalleta lokacin data ajiye wayar akan katifa, tace, "Kanna (sister) sannunki da aiki, na jiyoki a kicin kina ta aiki wallahi barci da gajiya ne suka hanani tashi in tayaki."

Nadiya ta girgiza kai, "kai haba, babu komi wallahi. Wannan aikin a wajena kam ai ba komi bane, kada ki damu!"
Tayi dariya, tace, "kaji fa professionals. Bari inyi sauri dai inje in ci delicacy dinnan da zafinshi kafin ya huce, kin san yafi dadi!"
Tayi yar dariya kawai ta shige bandaki don ta watsa ruwa.

Allah Ya taimaketa kafin ta fito daga wankan har Aysha ta kai mata kayanta. Ta bude akwatin ta ciro riga da siket na wani material mai taushi. Da yake bashi da dankwali sai ta dora hular turban akanta.

Ta fita falo ta samu Anty Lima da Aysha suna hira. Ta zuba abincin da zata iya ci a plate, ta zuba kunun gyadar da yawa a cikin kofi ta kara madara da zuma a ciki, ta koma wajen su Aysha suka cigaba da hirar da ita.

Anan ne take jin cewa a ranar Safiya zata zo, don sunyi waya ma da Aysha tace mata suna hanya don a Kaduna ma suka kwana.
Anan kuma take jin ashe Madam hanyar bude wani babban Arena ne take yi a Kaduna mai dauke da manyan shaguna, kuma Hajja Umma tana da manyan Realtors a hannu da zasu iya taimaka mata. Ga kuma bugu da kari kanin mijinta Marigayi shine Controller Janar na Najeriya. Da yake tana samun matsala wani lokaci wajen shigo da kayanta daga kasashen ketare, shima tana bukatarshi a gefenta yayinda kuma yaki bata hadin kai. Shine take so ta biyo ta bangaren Hajja Umma din.

Ta tabe baki a ranta tana jin babu dadi, dama a ranta sai da tace wannan mutuncin da Madam take yiwa Hajja Umma ba na Allah da Annabi bane, wani abu take bukata.
Ita kam sai take ganin bata san inda Madam zata kai son kudi da duniya ba, daidai gwargwado tana da kudinta da rufin asiri, haka ma mijinta, amma ita sam bata gani, kullum cikin neman kari take.

Maimakon tayi kokari ta gyara zumuncinsu da Hajja Umma daya tabarbare, su koma tsintsiya madaurinki daya kamar dai yadda yakamata su kasance, amma ita ta kudi da duniya take.
Ta san hakan dama ce sosai da zata iya kusantasu da Hajja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login