Showing 93001 words to 96000 words out of 142169 words

Chapter 32 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

473

akai.

Babu jimawa barci ya kwasheta. Bata san lokacin daya fito daga dakin Ummah din ba, ya maida mata kofar ya rufe kafin ya karasa gareta a hankali. Yayi durkuso a gabanta yana karewa yadda take barcin nata a nutse kamar wata baby.
Ya shagala a kallon nata har ya fara manta a inda suke. Komai na Nadiya na daban ne. Halayenta daban suke da na sauran mutane, haka dabi'unta na daban ne da ba kasafai aka cika samunsu a cikin zamanin wannan ba.

Kasa ya sauka yana tambayar Lailah ina Ammar? Ta sanar mishi sai karfe hudu suke dawowa yanzu saboda an jima da yi musu canjin aji. Shi a karan kanshi sai yaji yar kunya ta kamashi, saboda tunda harkar siyasar nan ta tashi, ya rage ba yaron da al'amuranshi lokacinshi da hankalinshi. Kai ba yaron kadai ba, har iyalinshi da shi a karan kanshi ma. Sai kawai ya juya ya koma saman, yana fada mata kada a bari kowa ya hau saman nan har sai an sanar dashi, saboda Ummah bata jin dadi. Ta amsa mishi da 'to, Yallabai!'

Hannu ya sanya yana shafa fuskarta dake smooth sosai, Nadiya ba dai kula da iya kyalkyale jiki ba. Koda bata yi kwalliya ta sanya su foundation da tarkacen concealer ba, a kullum zaka samu jikinta laushi tubus, yana santsi da wani asirtaccen kamshi da yake hargitsa kwanyar mutum.

Ta fara bude idanunta a hankali, ganin shine a durkushe a gabanta, sai tayi tunanin ko Ummah ce ta farka. Ta tashi da sauri tana lalubar gyalenta daya salube ya fadi kasa, "Ummah din har ta tashi ne?"
Hannu ya sanya da sauri ya zaunar da ita daga mikewar da take shirin yi, yace, "wannan farkawarta ba yanzu ba. Don akwai magungunan sanya barci a magungunanta."

Ta dan ajiye zuciya a hankali, "oh!! Ta kuma koma ta zauna tana kallonshi kasa-kasa.
Wani irin murmushi ya saki, Nadiya da gulmarta! Kallon ma ba za ayi mishi yasan ana kallonshi ba sai dai a dinga satar kallonshi.

Yace, "idan kin yaba kwalliyar tawa ne, baki zaki daga da kyau ki yabani din ai in san na burgeki, ba wai ki dinga satar kallona ba kina wani basarwa!"
Ta ji kunyar kamata din da yayi tana kallonshi, sai ta dauke kanta da sauri. Shi kuwa ya kara sa hannu ya juyo da fuskarta suna kallon juna, "to wai shi kallon nawa haramun ne Nadiya? Ko kuma shi shakulatin-bangaro da kike yi da ni da al'amurana ladarsu kike samu?!"

A ranta tace, 'to! Yau kuma?!'
Amma a fili sai ta dan kalleshi a kaikaice, wani kallo daya tsirga mishi tun daga tsakiyar kanshi har tafin kafarshi, leaving goosebumps a duka sassan jikinshi.
Ta buda baki da kyar tace, "ni kuma me nayi maka?"
Bata san tuni ta gama kassara mishi gabbai da wannan kallon nata ba. Ya hau kan kujerar da kyau ya jata cikin jikinshi. Wannan kamshi nata da babu abinda yake so da marmari kamarshi yana mishi oyoyo, sai kawai fara nuna ma'anar kalaman nashi a aikace ba tare daya furta ba.

Ko daga urgency na yadda yake gudanar da al'amuranshi yau, tasan cewa ba karamin kewarta yayi ba. A kuma matukar bukace yake.
Ta fara kici-kici da kokarin janye jikinta gabanta yana faduwa a tsorace ganin cewa a saman bangaren Ummah suke. Ga azuminta dake makale a bakinta.

Ya kalleta da wasu idanu da suka fara canzawa, tsabar mutuwar da jikinshi yayi ma ya kasa iya daga baki ya tambayeta dalili. Musamman da yaga kwalla tana taruwa a cikin idanunta.
Sai itace tace cikin rawar murya, "don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri Abban Ammar. Ka manta a inda muke ne?"

Kawai ya kara janyota, ya cigaba da bin fatar ilahirin wuyanta da kafadarta da butterfly kisses a yunwace, wani abu da Nadiya ta gama fahimtar weakness dinshi ne. Shi yasa ta himmantu da gyaran wuyanta sosai da bayan kunnenta. Tana amfani da sabulai masu kyau wajen wanke fatar jikinta wadanda yawanci ma ita take hadasu da kanta da sinadarai masu gyaran fata. Haka kullum ba ka raba wajen da kamshin nau'in turaruka masu kyau, irin nasu na asalin Bare-bare da tuni har ya gama kama fatar jikinta. Ta hakane a kodayaushe, a kowane hali ya sameta, kamshin nan dai nata yana nan.

Bai fasa abinda yake yi ba, yace mata, "in dai don Ummah ne, ba yanzu zata tashi ba!"
Sai tayi kundunbala tace, "azumin tadauwu'i fa nake yi!"
Ya dan dakata yana kallonta, "it has nothing to do with me Nadiya, ai na fada miki matsayata akan hakan ko?"
Tayi rau-rau da idanu, "to kayi hakuri don Allah, kaga ai baka nan ne shi yasa."
Ya jinjina kai, humming softly kamar ya yarda da abinda take fada, sai kuma ya cigaba da gudanar da abubuwanshi alamun dai ba zai yarda din ba dai.

Sai kawai ta saki wani irin kuka a tausashe, tana shessheka a hankali hawaye na diga a kan fuskarta zuwa jikinshi, dis-dis. Da dai tasan abinda kukan nan nata ke haddasa mishi, to da ko da kudi ba zata yi shi ba. A dai halin da yake ciki.
Tace mishi, "to kuma a bangaren na Ummah? Kana kallon tsakaninmu da ita bai wuce wani taki na azo a gani ba, anan din?"

Wannan sai ya dan dakatar dashi, ya zuba mata shanyayyun idanunshi, "hakane kuma gaskiya. To taso mu koma can wajenki kafin ta tashi. Kinga dai ai bata jima da kwanciya ba."
Ta wawuri gyalenta ta dake mayarwa ta rufe kanta, ta gyara zip din rigarta da aka zuge shima. Ta fara goge hawayenta kafin cikin tausasa murya, tace, "to ka fara yin gaba dai sai in biyoka a baya!'
Ya tashi yana daukar rigarshi da itama yayi wancakali da ita, ya sanyata a jikinshi duk tayi squeezing kamar an cirota a bakin kura. Yace mata, "to kiyi sauri fa!"
Ya juya ya fita da sassarfa, tana binshi da kallo har ya sauka. Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba bayan ya sauka din. Lallai yau da drama a gidan nan idan ya gano aika-aikar da take shirin aikata mishi.

Ta shige dakin Ummah da har lokacin barcinta kawai take shaka, oblivious to all abubuwan dake faruwa. Ta shige toilet dinta ta kulle har da karawa da sakata duk da dai tasan cewa ai ba zai zo har nan yace sai ta je ta karfi ba.

Shi kam zuwa lokacin daya fahimci Nadiya dai kafa ta bashi ya wuce falau, tuni wasu masallatan har an fara kiran sallah.
Ya daure yayi sallah din, kai tsaye daga masallaci sashen Ummah din yayi niyar wucewa, ko a kafada ne sai sabota. Abinda ya kudurta a ranshi kenan. Sai suka yi clashing da motar da taje dauko Ammar daga makaranta, don haka ya dakata har yaron ya fito hannunshi rike da jakarshi da food flask dinshi. Ya daukeshi a hannunshi suka wuce tare, a ranshi yana fadin idan ya damketa a hannunshi, sai ta ba yan garin Maiduguri labari.

Suka zaune a gefen gadon Ummah bayan itama ta kammala sallah. Da taga shigarsu dakin sai ta tashi tsaye, ta mayar da hankalinta ga Ammar daya ruga wajenta ta tareshi da murna itama. Duk yadda yaso su hada idanu ta ki bashi damar hakan.
Daga karshe ma sai ta kama hannunshi suka fita don ta shiryashi da gaggawa ya wuce Islamiya.

Ya bisu da kallo, duk yadda yaso yaji bacin ran abinda ta aikata mishi, ya kasa ji. Yayi murmushi jin tambayar da Ammar yake jefa mata, 'wai gobe ma ita zata hada mishi lunch flask dinshi? saboda yau har saura yayi, kuma tare da abokanshi suka co suna ta cewa Mamanshi ta iya girki!'
Ita kuma tana dariya tana ce mishi zata hada mishi din.

Sai wajajen karfe biyar ta farka, shi da kanshi ya taimaka mata tayi sallah. Nadiya ta kai mata fura da ta sha nono ta sha da kyau. Cikin ikon Allah tuni har ta fara girgijewa. Amma ko bayan fitar Babangidan don gabatar da wasu kiraye-kirayen waya, kasa tafiya tayi ta barta ita kadai. Duk inda zata motsa to idanun Nadiya suna biye da ita, tana tsoron kada jiri ya dauketa ta sake faduwa. Ita a karan kanta Ummah din sai data fahimci tsoron Nadiya din. Tace mata, "wai ba azumi kike yi bane ba Nadiya? Ba zaki je kiyi shirin shan ruwa bane?"
Sai tace mata, kanta a kasa, "Ummah ai ba wasu abubuwa ne nake hadawa ba dama na shan ruwan. Idan na tashi zan dama kunu kawai!"
Don haka ta kyaleta.

Tana falo akan dinning tana shan ruwa, kunun tsamiya ne ta dama kadai take sha, sai fruits da aka yanka mata sun dau sanyi.
Shukurah ta shigo falon a lokacin, da alama ta dan jima da dawowa. Don ta canza shiga daga ta dazu da safe zuwa wata doguwar rigar cotton din material ruwan makuba.
Ta ja kujera ta zauna tana kokarin zuba abincin dare da har an gama shiryawa, yanzu an samu cigaba tunda tana zama akan dinning idan Nadiya tana nan ta ci abinci, ba kamar da ba.
Yadda bata yi mata magana ba, haka itama Nadiya bata yi mata magana ba. Tunda ai ko a ka'ida ma ai ita da ta tarar ya kamata ta fara yiwa sallama.

Ta zuba white rice and beans, da sauce din kayan miya da coleslaw. Ta ci abincinta tayi nak, ta kara da lemu mai sanyi. Sannan ta ja kujera, sauran abincin data bari ko rufewa bata yi ba ta barshi anan. Har flask din data debi abincin a ciki haka ta barshi bata rufe ba, sai Nadiya dince ta rufe don kada ya huce.
Ta haye sama da alama Ummah zata gaisar.

Ita dai ta zauna anan falo din har aka yi Isha'i tayi, sannan ne ta haura saman domin ta yiwa Ummah sai da safe, jikinta hutu yake bukata sosai da sosai.

A falo ma ta samu Ummah din zaune akan kujera, sauran furar data dama mata dazu a gabanta a cikin bowl mai fadi tana sha.
Ta duka a gefenta, yayinda Shukurah take zaune a kujerar kusa da ita tana aikin latse-latsen waya abinta, ga cingam nan a bakinta tana ta aikin tauna kas-kas! kamar yakin duniya.

Tace mata, "Ummah kina bukatar wani abu ne? Zan je in kwanta yanzu."
Tace mata, "babu abinda nake bukata Nadiya, jikin nawa ai ya warware Alhamdulillah, zan iya yiwa kaina komi yanzu. Kije ji huta da kyau tunda yau baki samu yin barcin ba. Allah Yayi miki albarka!"

Kawai sai taji wasu irin hawaye sun cika mata idanu. Bata taba zaton jin wannan kalmar daga bakinta ba. Mahaifinsu dai shi dama ba ma'abocin sanya albarka bane, haka Madam. Ita kam zata ma iya cewa tunda take da Madam din bata taba jin ta sanya mata albarka ba. Wannan sai Mama da kuma Dada. Sai kuwa Babangida. Shi wannan kullum cikin sanyawar albarkarshi take, duk kankanin abu idan ta mishi ya burgeshi, sai ya kalleta yace 'Allah Yayi miki albarka Nadiya!' Shi yasa take ta dagewa da zage dantsen kyautata mishi koda bata son yin abu kuwa, idan har ta kula yana so to kuwa itama zata so shi.

Muryarta tayi nauyi, ta kasa amsawa da 'ameen' sai kai kawai data iya gyada mata. Ta tashi cikin wata irin mutuwar jiki tace mata, "sai da Ummah, Allah Ya kara lafiya!"
Tace mata, "sai da safe Nadiya!"

Data sauka kasa sai da taji kamar ta kwala ihu don murna. Ta dai daure ta fuske ta tunkari kofar fita.
Tana kokarin bude kofa ta fita, shi kuma yana turo kofar. Tayi kokarin ja da baya da sauri, sai kafarta ta dan gurde ta yi baya zata fadi. Ya sanya hannu da sauri ya tarota cikin jikinshi, yace mata, "what's with you da kai min karo duk sanda zamu hadu ne Nadiya?"
Ta janye daga jikin nashi tana turo baki, "dadinta dai kullum kaine kake ture ni, ka zubar min da abu a jiki, ko ka fasa min waya, ko kuma kayi kokarin kayar da ni!"

Yayi murmushinshi mai kayatarwa, "ni me yasa baki taba tambayata illar da kike min idan kin kai min karon ba?"
Ta dan bude idanu tar akanshi, tace, "ni illar me zan maka ne?"
Ya dan sumbaci bakinta, "yanzu dai barka da shan ruwa. Kije ki shirya Nadiya, yau har dakina zaki zo ki sameni. Bashin da kika ci yau sai kin biyani da tsada!"
Tayi yar dariya ta bi ta gefenshi ta karasa fita. Sannan shima ya karasa shiga falon domin ya duba Ummah.


38.



Ba tayi tunanin da gaske yake da zancen taje dakinshi ta sameshi ba, tayi zamanta a daki bayan ta gama shirin kwanciya. Shiru-shiru lokaci ya ja bai je ba, kuma bai tuntubeta ba ko a waya. Tana tunanin kila ko wani aikine ya rikeshi ko wani abu, barci yayi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba sai da Asubahi, ta sauka daga kan gadon da kyar, gabadaya jikinta yayi wani irin nauyi ji take kamar wata tirela ta bi ta kanta.

Ta duba wayarta da taga tana blinking alamun an bar mata sako ko missed call. Tana dagawa ta ga sakon daga shi ne, 'kin kyauta!' kadai ya tura mata. Amma sai da taji jikinta yayi kamar an watsa mata ruwan sanyi saboda yadda sakon ya daketa.
A ranta taji babu dadi, kuma tasan bata kyauta ba ko kadan. Ya daga baki da kanshi yace mata ga abinda za ayi amma ta mayar da abun wasa! Anya ta kyauta? Ta tura mishi, 'I'm so sorry dear, barcine ya daukeni'
Gwanda ta tsaya a barci dinne ya saceta akan gaskiyar abinda ya faru. Ta kudira a ranta idan sun hadu zata bashi hakuri da kyau ta fatar baki, kafin sauran su biyo baya.

Tayi sallah ta sake komawa ta kwanta. Sai wajen karfe takwas ta farka. Ta watsa ruwan dumi a jikinta ta dan ji karfi sosai, ta zura riga da siket na atamfa a jikinta, tayi daurin kallabi simple ta fita. Kai tsaye sashenshi ta wuce da niyar bashi hakurin da tayi niyya. Sai ta samu bangaren nashi a rufe, tasan babu mamaki yana can wajen Ummah. Sai ta wuce can.

A can din kuwa ta sameshi, a zaune a gabanta a falon kasa suna hirarsu a nutse, da alama jikin nata ya samu sauki sosai. Itama ta duka a gefenshi ta gaishe da Ummah din kafin shima ta gaida shi, ya kalleta sau daya, ya amsa a tsaitsaye, ya kuma mayar da hankalinshi ga Ummah din ba tare daya kara tankata ba. Duk da cewa dama a gaban Ummah din bai cika yi mata zakalkalewar daya saba yi mata ba, amma ko yaya ya kan amsa mata gaisuwa da salama da kuma taushi a tattare dashi. Sai jikinta yayi sanyi ganin yadda ya amsa ta din yanzu cikin daure fuska da harhadewa.
Sai ta mayar da kanta ga Ummah tana tambayarta, "ya karin karfin jiki?"
Ummah ta amsata, "jiki da sauki Alhamdulillah Nadiya."

Tace, "kin sha magani ne kam?"
Tace, "ehh, yanzu na sha."
Itama Ummah yadda take amsa mata tambayar tana wani ciccijewa da dan yatsine fuska, sai abin duk yayi mata wani iri. Taji zama a wajen dai kamar she's not welcomed. Don haka ta koma kasa ta zuba abinci tana tsakura ba don tana jin dadin abincin ba.

Tana nan a zaune ya sauko kasa cikin takun nan nashi na nutsuwa da kamala.
Ganin yana shirin fita ne yasa ta tashi da sauri ta tareshi, tace, "Abban Ammar kayi hakuri don Allah!"
Ya tsaya yana kallonta, "hakurin me kike bani ne Nadiya? Kinyi min wani laifi ne?"

Yayi tambayar cikin wani kwantaccen bacin rai. Sai tayi kasa da kai, ta fara motsa baki cikin rashin sanin abin cewa. Da kyar ta iya cewa, "uhmm... Dama jiyan... Barci ne ya daukeni shi yasa."
Ya dan tabe baki, "eh, ai ban ce wani abu ba dama, or did I complain? Shi mutum dama ai sai ka damu dashi da al'amuranshi sannan ne baka mantawa da shi ko kuma sanyashi as a priority. Excuse me please ina da wajen zuwa!"
Ya zagayeta ya fita daga falon. Ta bishi da kallo rai a jagule, lallai yau ta tsokano ran manya.

Ganin har a wajen Ummah dinma dai babu wajen zama, sai ta lallaba ta koma dakinta.
Ta zauna a gefen gadonta tare da bude wayarta, ta rubuta message dogo mai cike da alamu na ban hakuri da neman afuwa ta tura mishi. Tana fatan Allah Ya sassauto da wannan fushi nashi.

Bata yi tunanin fushin na shi zai dugunzuma mata hankali har haka ba, sai taji gabadaya gidan ma yana wani sire mata daga rai.
Amma har aka kwashe awanni masu dama bata ga amsa daga gareshi ba. Sai kawai ta shiga kicin dinta, ta fara hada mishi lafiyayyen abinci mai kyau, watakila ta samu ta janyoshi da wannan.

Tana nan sashen nata har wajen karfe biyu cikin taraddadi da tunanin ya zata yi? Don kuwa ko keyar Babangida bata kara gani ba.
Yadda ya saba kuwa a duk ranar girkinta in dai yana gari to yana fita sallar Azzuhur wajenta zai nufa ya ci abinci da kyau, watarana ma anan zai shantake har bayan la'asar don sau tari shi yake jansu sallar la'asar din. Idan kuma yasan ma ba zai samu damar cin abincin ba to sai yayi mata waya ya fada mata don kada ta sanya girkin da shi.

Ta sake komawa bangaren Ummah domin taga ko yana can, ta kuma duba ko Ummah din itama ta sha maganinta na rana.
Kafin ta karasa taga an bude gate, aka turo hancin bakar Hummer Jeep da Babangida din ke fita a cikinta, tasan babu mamaki shine. Don haka taja tunga, tana jiran ya fito ya sameta, suyi duk wadda zasu yi ita dashi kawai su wuce wajen.

Security dake tare dashi ya fita daga gaban mota ya bude gidan baya, kamar yadda tayi kintace din, shi dinne ya zuro kafa ya fito. Sai kuma ta tsaya da mamaki ganin an bude dayan gefen da yake, wata mata ta fito hannunta jaye da hannun wata yarinya karama, amma zata girmi Ammar. Suka jero suna tafiya ita da shi din suna hirarsu, direba yana binsu a baya jaye da tarin trolleys kusan guda uku.

Sai dai tun kafin su karasa inda take, ranta ya gama bata wannan Mami ce, Sumayya kanwar Hajiya Ummah. Wadda duk a cikin danginsu bata tunanin wani ya sake ganinta tun bayan barinsu gida bayan rasuwar mahaifiyarsu. Kamanninsu ita da Ummah din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login