Showing 72001 words to 75000 words out of 142169 words

Chapter 25 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

444

da Ammar suna saukowa kasa.

Ammar ya ruga wajen mahaifinshi ya rungumeshi yana murnar ganinshi, Hajiya Ummah kuma ta ja kujera ta zauna tana tambayarshi, 'har ya shigo?'
Ya amsa mata da 'ehh!' cike da girmamawa.
Nadiya tayi amfani da wannan dama ta silale ta koma dakinta abinta.

Ta fito daga wanka tana tsane jikinta, taji alamun an tura mata sako. Wai tambayarta yake yi, 'shine ta tafi ta kyaleshi bayan yace ta tsaya ko? Zai rama kuwa!'
Tayi kwafa tayi jifa da wayar ba tare data damu akan ta mayar mishi da amsa ba.
Ta gama shirinta tsaf na kwanciya ta kwanta abinta.

Washegari Rashida ta shirya zata koma gida saboda makaranta da suka koma. Nadiya bata ji dadin tafiyar tata ba, saboda yarinyar ita ce take dauke mata kewa ita da Ammar a gidan. Tana tunanin irin yanayin da zata shiga idan babu ita a yanzu. Saboda daga ganin take-taken Habibun, ba zata samu hakan a wajenshi ba.

Ta jata zuwa dakinta suka shiga wajen kayan kwalliyarta, tace mata ta zabi duk abinda take so a ciki. To da yake ma Nadiyar ta girmeta nesa ba kusa ba, kayan nata duk sun yiwa Rashidar yawa. Sai tarkacen janbaki da hoda data bata da danginsu turare da humrori. Ta kuma dauko atamfa babba ta bata tace ta kaiwa Mamansu. Ta amsa tayi ta mata godiya.

Tace, "to kuma Rabi'ah sai zuwa yaushe?"
Yarinyar tayi yar dariya, tace, "to Aunty, kawai dai sai dai in ce sai na zagayo. Saboda gaskiya ban cika zuwa Kaduna ba sai ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kama."
Tace, "to ai shikenan. Idan ma ke din baki zo ba, mu sai mu je ai."
Rashida ta yada kai gefe, tace, "to Allah Yasa Ummah ta bari!"

Anan sai wani abu ya darsu a cikin ranta. Ta kama hannun Rashida suka zauna a gefen gado. Tace mata, "Rashida don Allah dan fahimtar da ni wani abu mana. Shin wai, menene alakarki da Baban Ammar? Kin ce min Yayanki ne, amma kuma ba mahaifiyarku daya ba. Kuma Babanku daya, sannan kuna kama. Ki fada min don Allah."

Rashida tayi kasa da kanta tana kokarin tauna abinda zai fita daga bakinta. Kafin ta kalli Nadiyar tana dan taune lebe alamun nervousness, "to amma dai ba zaki fadawa kowa ba ko?"
Ta gyada kai da sauri, "in Allah Ya yarda babu wanda zai ji."
Tace, "uhmm... Dama dai gaskiya Hajiya Ummah ba ita ta haifi Yaya ba fa, Mahaifiyarmu daya dashi. Ita kuma tana Makarfi ne a halin yanzu."

Ta kama baki cikin tsananin tu'ajjibi da mamaki, "wai kina nufin dama ba Hajiya Ummah ce mahaifiyar Habibu ba?!"
Ta gyada kai.
Sai Nadiya taji tana fahimtar wasu abubuwa da suka jima suna daure mata kai.

Alakar ta Hajiya Ummah da Habibu tsurar alaka ce ta 'Da da Mahaifiya ziryan. Ba ta tunanin akwai wani dalili da suka taba bata na tayi zargin akasin haka. Amma a yan kwanakin ta fara zargi da tambayar kanta, anya dai babu wata a kasa kuwa?
A ganinta, wata Uwa ce ta gari zata yi hani da danta tarawa da Matarshi ta Sunnah kawai saboda wani ra'ayi nata na daban? Anan sai ta samo amsar tambayar data dade tana mata yawo a ka, me yasa ne Hajiya Ummah din ta dage sai ta hada iri da Madam duk da daddadar gaba da kiyayyar da take a tsakaninsu? Ta jima tana zargin ba wai saboda a tallafawa Habibu a fannin siyasarshi bane kadai ya assassa aurensu ba.
Kada dai ace akwai wata magana ta daban dake faruwa a wannan lamari?

Ta tashi gwiwa a salube ta yiwa Rashida din rakiya zuwa inda direba yake jiranta zai mayar da ita.
Ita kadai ce a yan rakiyar, babu kyallin Hajiya Ummah balle na Shukurah. Shi dama Habibun tunda safe da zai fita ya damka mata kudaden da zata yi guziri da su. Ta samu kanta da tambayar, 'shin ko Shukurah ta san ko wacece ainihin mahaifiyar Habibun? Kuma a wane matsayi take a cikin wannan gida a halin yanzu?'

Ta yini cikin wannan tunani da saka da warwara. Da kyar ta iya tashi tayi sallah lokacin da aka kira Azzuhur. Barci ya dauketa anan, sai can wajen karfe uku ta tashi. Shima yunwa ce ta dinga nanikarta shi yasa ta tashi babu shiri.
Tayi tunanin ko taje bangaren Hajiya Ummah ne ta ci abincin acan kawai? Sai kuma ta canza shawara saboda bata san abinda suka dafa ba a ranar.
Ita kuma kayan kwadayi kawai take bukata saboda a yan kwanakin kwadayin take ji. Ta kula idan tana kusa da fara period tana yawan yin wadannan kwadaye-kwadaye kamar wata mai laulayi. Sau tari kuma sai ta haddasa mata kasala da yawan gajiya.

Ta samu ta lallaba ta fara yin sallah kafin ta fada kicin kai tsaye, ta lalubi fulawa ta hau kwabin wainar fulawa. Ta yanka su kabeji, cucumber, karas, albasa a ciki. Data tashi soyawa Kuna sai ta soya da manja.

Tana cikin aikin shi kuma ya fado kicin din. Ya shaki numfashi yana leka abinda take yi, "lalalaaa... Menene haka kike yi Nadiya, kuma ba zaki laluboni kiyi mun tayi ba?"
Ta dan juya ta na kallonshi. Sweat pant ne a jikinshi ash color da farar riga, da alama tun dawowarshi bai fita ba. Tace, "ni kuwa ina zan ganka da har zan yi maka tayi?"
Magana ce ta danna mishi a kaikaice. Ko ya fahimta ko bai fahimta ba? Ya basar da zancen ta hanyar ce mata,
"to ai ga ni nazo yanzu. Sai a zuba min in ci."
Ta kama baki da mamaki, "wainar fulawa ce fa?!"

Yace, "eh, ita din. Kin kuwa san yadda nake son wannan abin?"
Shi da kanshi ya dauko faranti, ya lalubi waje ya coge, duk wadda ta dauke a wuta sai ta zuba mishi ya lamushe abinshi, ga yajinta mai dadi da amarya ta daka mata yana dangwalawa.

Sai ga shi ita mai aikin ta tashi da yar kadan. Ta zauna itama ta ci bayan ta kammala, tana sauraronshi yana zuba mata santin wainar.

Ta hada kwanukan ta wanke, duk yana coge a kicin din ya ki matsawa ko nan da can. Data gama ta koma falonta, nan ma sai ya bi bayanta.
Ta lalubi kujera ta zauna tana canza tashar da ake haskawa a jikin TV.
Ba zato kawai sai jin mutum tayi ya kwanta a kan kujerar da take, kanshi akan cinyarta.

Tayi sauri ta zabura zata tashi, sai ya sanya hannu ya sakalo kugunta, ya nutsa kanshi a ruwan jikinta yana shaka da fesar da numfashi.
Tace, "wai meye hakan kake yi don Allah? Ka tada ni!"
Yace, "ni da jikina ma sai anyi min iyaka ne Nadiya?"

Tace, "ni dai gaskiya ka kyaleni, idan kwanciya zaka yi sai in bar maka wannan kujerar in koma karama."
Yace, "babu ruwanki da inda zan kwanta, nan din dai nayi niyar kwanciya. Bani minti ashirin kawai in dan runtsa, barci nake ji wallahi sosai da sosai!"

Ganin dai tsayawa ja-in-ja da shi ba zai mata ba, sai ta kyaleshi din. Ya gyara kwanciyarshi da kyau ya lumshe idanunshi kamar mai barcin da gaske. Ta ci gaba da kallonta, sai dai ta kasa tsayar da hankalinta waje daya ta fahimci abinda ake yi. Kusancinta da shi ya fara sanya mata wata kadawar jiki data 'ya'yan hanji data kasa fahimta.

Wayarshi ta hau kara a dai-dai wannan lokaci, Ya tashi a kasalance, da alama har barcin ya fara daukarshi. In da ba don Ummah bace mai kiran bama da zai daga ba saboda yaji dadin kwanciyar.
Ya daga kiran yana mai yin sallama. Kasancewar a kusa da Nadiya yake zaune, tana tsintar abinda Ummah din take ce mishi.

Wai tambayarshi take yi ina ya shiga ne tana ta nemanshi tun dazu, har sashenshi an je baya nan?
Yace, "Ummah Ina cikin gidan ai. Akwai wani abu ne?"
Tace, "ehh, kayi maza-maza kazo ina son yin magana da kai ne."
Yace, "to gani nan."
Ya kashe wayar ya mike da kyar yana kallon Nadiya, "bari in je Ummah tana son ganina."
Ta gyada mishi kai.

Yace, "idan kina da Groundnut paste ki dama min kunun gyada mana, zuwa dare zan zo in amsa."
Tace, "to bari in duba in gani."
Ya fita ita kuma ta shiga kicin.

Babu kullin a kicin dinta, sai ta yanke shawarar ta duba ko akwai a bangaren Hajiya Ummah tunda itama ma'abociyar shan kunun ce.
Bata samu kowa a falon ba, don haka ta wuce kicin. Ta samu Lailah mai dafa abinci tana ta aikin dafe-dafe, suka gaisa da ita ta tambayeta ko suna da kullin gyada zata yi kunu? Ta dauko mata shi a bokiti ta debi iyaka wanda zai isheta, ta koma sashenta.

Suka ci karo da Ammar ya dawo daga makaranta. Sai ta ja shi suka wuce sashenta. Ta tayashi ma yayi bitar karatunshi da assignment da aka basu, sai da aka kira Magriba sannan ya tafi.

Zuwa karfe takwas ta gama hada mishi kunun yadda ta saba hadawa.
Itama data samu ta shanye kofi daya, sai taji cikinta a cike. Don haka bata ma fita wajen cin abincin ba. Koda Lailah taje kiranta sai tace mata yau a koshe take.

Ta kwanta akan kujera two-seater tana chatting a wayarta. Karfe tara taje ta shige goma na shirin kawo kai, amma babu alamun Habibu.
Data gaji kawai sai ta tashi ta wuce daki ta kwanta.
Wani irin suya da juyi ranta yake mata. Wannan wace irin rayuwace wai take yi ne haka? Abu sai kace a almara ko tatsuniya? Abinda yafi bata mata rai shine yadda duk kokarin da take wajen ganin kada ta bari hakan ya dameta, amma kuma dai abin yana damunta.

Da Asubahi koda ta tashi yin sallah ta ga ta samu rashin tsarki, sai kawai ta kimtsa jikinta ta koma tayi kwanciyarta tunda dama barcin ba isarta yayi ba.

Wajen karfe goma ta fita zuwa bangaren Ummah. Bakar Abaya ce a jikinta, tayi nadi da gyalen a kanta. Wayarta a hannunta tana laluben kiran su Maryam don su gaisa ta fita daga sashen nata.

A bangaren Hajiya Ummah ta samu Shukurah akan dinning itama tana kari. Ta ja kujera ta zauna tare da gaisheta.
A yan kwanakin ta gama fahimtar ba lallai su yi zaman mutunta juna ba ita da Shukurah din. Ta dauke kanta kamar bata ganta ba, bata kuma amsa sallamar tata ba.Don haka itama bata kara gaisheta ba. Tana cikin zuba abinci kuma ta ga ta dauke plate dinta ta koma tsakiyar falo ta zauna. Haka yake faruwa duk lokacin da Nadiya ta sameta tana cin abinci, sai tashi ta koma falo. Idan kuma ita ta samu Nadiya din, to sai dai ta debi abincin ta tafi wani wajen ta ci, amma bata zama waje daya da ita.

Shi cin abincin ma a falon ta kula Shukurah din ce kadai take ci, saboda babu wanda Ummah take bari yayi mata wannan aika-aikar. Hatta da Ammar bata bari.
Nadiya ta tabe baki, ta zauna ta ci abincinta tayi nak.

Da taga ta gama Ummah bata sauko kasa ba, sai ita ta haya saman da kanta. Wannan shine karo na farko tun zuwanta gidan data hau saman.
Wani madaidaicin falon ta ci karo dashi da kujeru masu fadi irin na shan iska dinnan, a kasa kuma akan kafet Ummah ce a zaune ta mike kafafunta akan filo.

Nadiya ta durkusa a gabanta tana gaisheta, "Ina kwana Ummah? An tashi lafiya?"
Kullum ta Allah, bata fasa kiranta da Ummah din da bata so ba. Haka itama kullum ne sai ta gyara mata, tayi mamaki yau da bata taga mata ba. Ta amsa ciki-ciki kamar yadda ta saba.

Yanayin zaman nata sai ya ba Nadiya mamaki, tace, "Ummah ko baki jin dadi ne?"
Da kamar ba zata amsa ba, amma kuma sai tace mata, "lafiyata lau. Kafafuna ne suka dan motsa kawai."
Tace, "assha, sannu. Ya jikin? Kin sha magani? Ko kuma akwai na shafawa ne sai in shafa miki?"

Tace, "bar shi kawai kije kiyi karinki kinji?"
Tayi caraf tace, "ai yanzu na gama shirin. Idan akwai na shafawar kawo in shafa miki mana."
Ta nuna mata kwalbar maganin neurogesic, tace "ga shi nan."

Ta tashi da saurinta ta dauko maganin. Kafin ta shafa mata din sai data dauko ruwa a tasa da dan karamin towel, ta je ta goge mata kafafun tas kamar yadda taga Dada tana yi itama saboda tana da ciwon kafafu. Sannan ta bi ta shafesu da man wannan tas, ta kuma bi ta dinga massaging dinsu tun daga gwiwoyi har zuwa tafin kafarta.
Ta dauke kwanon ruwan ta shanya towel din, ta zubar da ruwan.

Komawa tayi tana tambayarta ko da akwai abinda take bukata kuma?
Tace mata 'babu komi'
Tace, "abinci fa? Kin karya ne?"
Tace mata, "na karya Nadiya, ki je kawai."

Tace "to, Allah Ya sawwake."
Ta tashi ta tasamma komawa kasa, sai kuma ta ji Ummah din na kiranta. Ta juya tana kallonta, tace, "ki dama min kunu a zuba a flask. Idan na sauko anjima sai in sha."

Ta amsa da "to"
Ta sauka kasa din ta shiga kicin, ta mata damun mai kyau da kauri. Na Habibun ma da yasa ta dama mishi ya ki zuwa ya dauka yana cikin flask. Data gama hadawa ta dauka da wasu kofuna biyu, ta kai wa Ummah din. Sannan ta wuce sashenta itama.

30.



Kwanaki uku suka zo suka shude a haka. Sai ga shi tana kirgan washegari Habibun zai fita daga dakinta, duk da cewa ba kwanan yake yi ba har yanzu. Kai a takaice ma rabon data sanya shi a kwayar idanunta tun ranar da yace ta dama mishi kunu bai koma ba. Ko a bangaren Hajiya Ummah ba sa haduwa, bata san ko arashi bane hakan ko kuma shi ne yake gudunta.

A daren kuma kamar da kiranye, sai ga shi ya diro dakin nata. Lokacin har ta gama shirin kwanciya ta kwanta amma ba ta kai ga fara yin barci ba.

Ya karasa har gefen gadonta ya zauna yana kallonta ta cikin dim light data kunna lokacin daya shiga dakin.
Yace, "har kin kwanta ne Nadiya?"
Ta gyada mishi kai ba tare data bashi amsa ba.

Yayi shiru din shima yana kallonta cikin wani yanayi da ta kasa fassarawa. A hankali ya kai hannu cikin tattausan gashin kanta daya kwanta har baya yana shafawa. Suka dauki lokaci mai tsayi a haka, cikinsu babu mai cewa wani abu.

Zuwa can kuma sai ya tattagota kamar wata karamar yarinya, ya zaunar da ita a tsakiyar gadon. Maganganu da yawa a cikin zuciyarshi, amma ya rasa da wane harshe zai iya furtasu. Idan ya daga bakin sai ya gaza cewa komi. Tausayinta da ma kanshi ya lullubeshi. Dalilin da yasa a duka yan kwanakin ya ma kasa zuwa inda take kenan balle ya nemeta. Kunyarta yake yi kwarai da gaske, ya rasa da wane ido zai kalleta, balle bakin da zai mata bayanin abinda ke faruwa.
Bai san dalilin Ummah na aikata hakan ba, amma shi kanshi dai yasan hakan bai dace ba, kuma yasan babu ta yadda za ayi ace Nadiya itama tana jin dadin hakan. Haka kawai saboda wani dalili na daban da ba shi da ruwa da tsaki akai, an yiwa kwanakin amarcinsu dirar fataken dare. Robbed, just like that!

Wani abu kamshin turaren jikinta ke haddasa mishi. Ga purple din rigar data sanya yau, gabadaya saman rigar net ne da kuma siririn hannu. Dan hasken daya rage a cikin dakin bai yi wani abu ba wajen boye kafatanin kirjinta.
Wani irin kallo ya koma yana watsa mata ba tare da yasan yana yin hakan ba.

Akwai lokuta da dama da yake rasa kalmomi a cikin bakinshi na neman afuwa ko uziri, a wadannan lokuta sai ya fi aikatawa da nunawa a jiki, cewa lallai yasan yayi laifi. A wannan lokacin kam, yasan cewa sai dai ya nuna mata a aikace. Wani aiki kuma yafi wanda yake kokarin nuna mata a halin yanzu?
Ya duka ya fara shinshinar wuyanta kamar wani tsohon puppy, kafin ya fara lasa da bin ko'ina na wuyanta zuwa fuskarta da ruwan kisses. Abubuwan da yake mata nema suke su dilmiyata a wata nahiya ta daban. Ta fara kokarin kwatar kanta, amma Habibun ya hana hakan ta faru.

Zuwa lokacin da tayi nasarar zamewa daga jikinshi da kyar, yar rigar tata da ta tsokane mishi ido an rabata biyu, ta zube akan cinyoyinta.

Idanu a lumshe cike da wata rigima da ta girmami tunaninta. Murya a dusashe yake ce mata, "why?!"
Itama tata muryar a shaken take, sai data hadiye miyau ta dan jika makoshinta sannan ta iya ce mishi, "fashin sallah nake."
Jin haka sai ya dora kanshi akan kafadarta ya lumshe idanu yana sakin numfashi a wahalce. Hakika da ba don wannan ba, bai ga abinda zai hanashi tabbatar da yiwuwar aurensu ba. Ummah sai dai tayi hakuri.

Sun kwashe fiye da mintuna sha biyar a haka kafin taga ya zame ya kwanta da kyau akan gadon.
Tayi zaune tana kallonshi a matukar tsorace. Ganin yanda take ta zare ido yasa ya kalleta yace, "me kike jira ne? Taho mu kwanta mana!"

Tayi jim kamar ba zata kwanta din ba, sai kuma ta lallaba ta gyara rigarta da aka wulakanta, ta kwanta itama, amma ta matsa can nesa dashi ta kuma bashi baya.
Babu wanda ya sake cewa dayansu uffan. Ita kam har barci ya daukeshi bata iya runtsawa ba. Sai zuwa can kafin barci barawo ya silale ya dauketa.
Da Asubahi tana jin motsinshi lokacin daya tashi zai wuce masallaci, har da gyara mata zaman bargo a jikinta. Ta kara gyara kwanciyarta abinta.

Ita kanta tasan cewa farincikin data tashi dashi na musamman ne ranar. Ko banza tasan cewa abinda take ta sakawa a cikin ranta ba haka bane. Habibu ya damu da ita, ko babu komi dai abinda ya faru a daren jiya hakan yake nuna mata.

Tayi kwalliyarta kamar yadda ta saba, kafin ta fita bangaren Hajiya Ummah don tayi kari. Yau ma sai data je har sama ta gaishe da Hajiya Ummah din, ta kuma tambayeta ko yau ma zata bukaci kunu ta dama mata ne? Ciwon kafar tata yayi sauki cikin ikon Allah. A kwanakin da suka biyo baya kuma kullum Nadiya ta kan je bangaren nata ta dama mata kunu ta kai mata. Har sai da ita da kanta tace mata ta dakata, idan tana bukata za tayi mata magana. Ta amsa gaisuwar tata sama-sama, tace a'ah bata bukatar komi. Sai ta sauka ta koma kasa don tayi kari.

Suka yi karo da Shukurah ita kuma za ta hau sama din. Kokarin bangajeta taga tana yi, don haka tayi gaggawar matsawa gefe ta lafe a jikin bango gudun kada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login