Showing 15001 words to 18000 words out of 142169 words

Chapter 6 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

443

farar safiya kawai ku dinga neman mutane da fada? Ina dalili.

Da suka kai kwanukansu Mama ta zuba musu nasu, sai da suka kara kokarin tada rigima. Wai su ala dole ta zuba musu kadan, me zasu yi dashi?
Mama ta nuna musu nata itama wanda bai ma kai nasu ba, tace, "ni kunga ma wanda na tashi dashi. Idan kuma kuna ganin ba zaku amsa ba sai ku dawo dashi ai, dama nema muke yi."

Lantana taja wani dogon tsaki ta juya ta shige dakin Abba tana maganganu kasa-kasa, Salame ta bi bayanta itama.
Nadiya ta bisu da kallo kawai, kafin ta jinjina kai tana mai furta 'Allah kyauta!' a cikin ranta.

Bayan Aminatu ta tafi makaranta, ita da Maryam suka zauna suka yi wanke-wanke suka gyara madafin, sannan suka je suma suka karya.


***
Sai ana saura kwanaki biyu ta tafi sannan ta sanar da Abbansu game da tafiyar. Ya tabe baki yace mata, "Allah kiyaye hanya!" shikenan karshen zancen.
Dama bata sanyawa ranta zai bata kudin mota ba ko wani abu, tace, "ameen!" ta kakkabe zaninta ta tashi.
Cikin satin taji an ce amarya zata tare, ta san ba lallai ba tana gidan, sai dai ta dawo ta tarar da ita.

Akwati daya karami ta shirya kawai, saboda Madam tace an dinka mata ashoben biki don haka ba sai taje da komi ba. Abubuwan da zata bukata kawai ta dauka.
Ranar Assabar kuwa tayi asubanci ta dauki hanyar Maiduguri bayan tayi sallama da mutan gida.

Tafiya ce mai tsayi da yawa, don ba ita ta shiga garin Maiduguri ba sai da ana kiran sallar isha'i.
Ta tari abin hawa ya kaita har Unguwar Lamido inda nan ne Kakarta, Dada Iyani take zaune. Mijinta ya jima da rasuwa, 'ya'yanta su suka gina mata gidan da take zaune a yanzu bayan an sayar da wancan wanda suke zaune a ciki da.

Ta sauka daga kan abin hawan ta biyashi, kafin ta karasa jikin gate din gidan ta kwankwasa. Maigadi ya bude mata yana mai yi mata sannu da zuwa, ta amsa da kyar saboda gajiya, ta wuce zuwa cikin gidan.

A falo ta samesu su uku a zaune suna kallo, Dada Iyani din na zaune a kasan carpet suna kallo, sai Aisha diyar Anty Hauwau da Al-Ameen kaninta suna tayata hira.
Tayi sallama ta shiga, su duka suka daga kai suna kallonta. Dada Iyani ta fara tafa hannu tana mata oyoyo, sai taji murna ta lullubeta da kewar wadanda ta jima bata sanya a cikin idanunta ba.

Ta ajiye akwatin ta tafi da sauri ta fada jikinta cike da murna. Itama rungumeta tayi tana "oyoyo ga mutan Kaduna. Ku ne da wannan daren?!"
Sai da suka gama murnar sannan ta koma ta zauna sosai akan carpet. Aisha da Al-Ameen suka gaidata ta amsa tana tambayarsu Mamansu.
Aisha zata iya yin sa'ar Maryam dinsu, don ba zata wuce shekaru sha takwas zuwa sha tara ba, shi kuma Al-Ameen ba zai wuce shekaru bakwai ba. A tsakaninsu akwai Tameem Yayan Al-Ameen da kuma Muhajjatu kanwar Al-Ameen, shekarunta biyu. Kasancewar Anty Hauwa din bata samu haihuwa da wuri ba.

Nadiya sun saba da Anty Hauwa sosai, don zata iya cewa sun ma fi sabawa da ita akan Madam Zarah. Lokaci zuwa lokaci su kan tuntubi juna su gaisa da tambayar juna ya suke, ba kamar Madam Zarah ba da idan ta kiraka to lallai akwai abinda take bukata a wajenka. Haka kuma da yake Anty Hauwa din tana aiki da WHO ne, su kan ziyarci garuruwa daban-daban, kuma tana yawan zuwa Kaduna. Duk lokacin da zata shiga Kaduna to sai ta lalubi Nadiya sun gaisa. Madam Zarah kuwa idan ba kai kaje inda take ba, to ba zata nemeka ba.

Dakin da zata sauka Aisha ta rakata, nan kusa da na Dada Iyani yake. Dakin yana da fadi, ga katifa babba da aka yada an shimfida mata sabon zanin gado. Ta ajiye akwatunta a gefen Katifar kafin ta fada bandaki ta watsa ruwa. Jikinta a matukar gajiye yake, ko'ina na sassan jikinta ciwo yake yi mata.
Bayan ta fito sallar da aka biyota tayi, kafin ta tashi ta nade abin sallar.

Zanine a jikinta wanda ta dora akan doguwar rigar barcin jikinta. Ta koma falo inda ta samu har Dada ta tafi ta kwanta sai Aisha da take kallo, Al-Ameen kuma yana barci.

Aisha ta daga kai tana kallonta, "yauwa, Adda, jiran fitowarki nake yi dama. Me za a kawo miki ki ci ne?"
Ta zauna yaraf a kan kujera tana mike kafafuwanta, tace, "gaskiya babu abinda zan iya ci yanzu saboda barci nake ji kwarai da gaske. Amma bari in shiga in hada shayi haka sai in sha kafin in kwanta."
Tace, "to bari in hada miki. Zauna huta naga alamun kin gaji sosai."

Cikin mintuna biyar kuwa ta hada mata shayin mai kauri, ta kai mata da burger wadda da alama daga oven ta fitar da ita saboda taji da dumi.
Ta ajiye kayan a gabanta tana dan murmushi, tace, "Madam ce ta kawo mana ita dazu. Kin san Dada ba cin irin wadannan abubuwan take yi ba shine aka ce bari a ajiye miki."

Ta dauka tana ci tana karewa hanyoyin da dakunan gidan suke kallo, tace, "ban ma ganta ba tunda nazo. Ko har ta kwanta ne?"
Aisha tace "wai Madam? Ai tunda yamma ta tafi gidan da take sauka."
Sai ta kame bakinta tayi shiru. Sam ta manta fa tunda dadewa take jin an ce Madam din gida ta gina na musamman wanda take sauka a cikinshi idan taje Maidugurin, saboda a cewarta wai can yafi tsaro.

Suna hira sama-sama har ta cinye burger din. Ta kai kayan kicin, ta dauki gorar ruwa ta yiwa Aisha din sai da safe wadda take ta kokarin tashin Al-Ameen ya wuce dakin da samarin gidan ke taruwa ya kwanta, ita kuma ta wuce wajen Dada tunda a can take kwana.
Tana shiga dakin baki kawai ta wanke ta yiwa kan katifa tsinke. Sama-sama suka gaisa da su Mama kafin ta kashe wayar gabadaya saboda mayen barcin dake janta kamar magnet.

Ranar sallar Asubahi ma sai da aka buga mata kofar daki. Ta tashi tana mika, har lokacin gajiyar bata barta ba. Sai lokacin taga alamun ta makara ashe don kuwa tuni gari ya fara haske.
Ta tashi da sauri ta dauro alwala ta yi sallah.

Bata koma barci ba, ta fita taje suka gaisa da Dada kafin suka shiga kicin ita da Aisha suna hada abin kari.
Suna aiki suna hira tana bata labarin bikin da za a fara a washegari. Wanda yarinyar zata aura dan gidan Sarkin Potiskum ne, shi yasa ake ta zuzuta bikin ba ji ba gani, ga kuma iyayen amaryar da suka kasance suma ba kananun masu kudi bane.

Iyalan Alhaji Idris Nalado, iyalai ne da suka yi kaurin suna a cikin garin Maiduguri. Ko ba daga bangaren arzikin da Allah Ya wadatasu dashi ba, kasancewarsu zuriya masu kyau kadai ya isa ya sanyasu a cikin jerin lissafi. Yawancinsu Kanuri ne gaba da baya, sai kuwa kalilan da suka kasance hadi da shuwa da kuma bafulatanai.

Shi Alhaji Nalado daya kasance shine Kakan Madam Zarah, mutum ne mai rufin asirinshi dai-dai gwargwado. Kaninshi kuma Alhaji Kachalla wanda suka hada uba daya dashi, shine mai arzikin. Sai dai sun taso kansu a hadene duk da kasancewarsu iyayensu mata daban. Kuma kasancewarsu manya a gidan, sun yi iyaka bakin kokarinsu wajen ganin cewa sun hada kawunan sauran kannansu da kuma 'ya'yansu waje guda.

Sai dai duk hakan ya zamana a kawai ne bayan da suka rasu. 'Ya'ya kowa ya kama harkar gabanshi. Hakan yasa suka tashi kai a ware, wani ma sai ya girma ya tashi da wani amma bai san dan uwanshi bane.

Mahaifin Madam Zarah Alhaji Lamin, shine babban da ga Alhaji Nalado, yana da kanne mata biyu da namiji daya. Mahaifiyarshi asalin shuwa ce, kuma da mafi akasari 'ya'yansu ita suka biyo, sai suke tashi tamkar wasu diyan larabawa saboda haske da kuma kyau. Duk cikin 'ya'yanta kuma babu wanda ya dauko kyawunta kamar Lamin din, wasu su kan ce idan ka ganinshi sai kayi zaton ko dan aljanine saboda tsabar kyau.

Bayan rasuwar Alhaji Nalado, rayuwar iyalanshi ta so shiga rikici saboda halin babu da rashi da suka shiga. Da ba don Alhaji Kachalla ba kam da basu san irin halin da zasu shiga ba.
Shi yayi ruwa yayi tsaki wajen kulawa da 'ya'yan marigayin, ya dauki Lamin ya mayar dashi cikin gidanshi da zama inda matarshi, Uwale, wadda ta kasance haifaffiyar garin Kaduna ta rike shi hannu bibiyu. Basu taba samun haihuwa da Alhaji Kachalla ba, kusan sau hudu tana samun cikin tana b'ari, ta haifi wani sau daya shima ko satin haihuwa bai cika ba ya koma.

Lamin ya cigaba da zama a hannun Alhaji Kachalla inda ya sanyashi a makaranta, a gefe guda kuma yana cigaba da daukar dawainiyar mahaifiyarshi da sauran kannenshi.

Cikin ikon Allah kwatsam sai Uwale ta samu ciki, tun suna taraddadin zubewarshi har dai suka saduda, da lokacin haihuwa yazo ta haifi diyarta mace sankaceciya aka sa mata suna Ummulkhairi. Lokacin kuwa Lamin ya haura shekaru sha biyar a duniya.

Tafi-tafiya rayuwa na ta juyawa, Lamin ya girma ya zama magidanci. Idan ba sani kayi ba, baka taba cewa ba Alhaji Kachalla bane ya haifeshi. Bayan Ummulkhairi Uwale ta sake haihuwar wata diyar taci sunan Sumayya.
Duk wasu harkokin Alhaji Kachalla suna hannun Lamin, shi yake kulawa dasu, kai sai da ta kai ta kawo ma gabadaya duk wasu shaguna nashi da kadarori Lamin dinne yake kulawa dasu, shi ya zamana kawai dai yana zuwa ya dan kewayasu ne ya dawo.

A haka cuta ta farat daya ta kamashi. Aka shiga zarya asibitoci da wajen Malaman gargajiya. Bayan doguwar jinya dai daya sha, daga karshe dai yace ga garinku nan.
Fadar irin tashin hankalin da iyalinshi suka shiga a wannan lokaci ma bata baki ne, sun yi kuka ba na wasa ba.

Aka yi zaman makoki aka gama, dangi da 'yan'uwa suka watse. Aka zauna aka zubawa Lamin idon ya tattara dukiyar mamaci ya ba magada amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Da aka ji shiru sai Uwale ta tunkareshi da kanta ita da yayanta da yaje daga Kaduna lokacin.

Ya rufe ido rikif ya hau fadan shi wata dukiya ke a hannunshi bayan wadda aka cinye a zaman jinyar Alhajin? Idan lissafi suke so ayi to su jira yayi lissafin, amma su kuka da kansu duk abinda zai biyo baya su suka ja saboda yana da tabbacin idan har yayi wannan lissafin to ko gidan da suke zaune a ciki ba zasu tsira dashi ba.

Aka kada aka raya, amma mutumin nan yace shi fa babu ko asin kwabo a hannunshi. Mahaifiyarshi kuma ta mara mishi baya.
Wannan dalili dai shi ya kawo lalacewar zumuncin wannan ahali. Dama tsakanin Uwale da Salma ba wani zumuncine na azo a gani ba, suna yi ne don ganin idon mazajensu ba wani dalili ba.

Daga baya dai zance har sai daya kaisu ga shiga kotu. Sai a kotun ne da yaji matsi ya dauki takardun filaye biyu ya bada a cewarshi abinda ya rage kenan. Shaguna kuwa duk babu kaya a ciki kuma ya sayar dasu, wai ai lokacin da Alhajin yana jiyya da su aka dinga amfani.
Da haka dai zance ya kare saboda babu wasu takamaimun shaidu da zasu karyata zancenshi. Saboda ko da Alhaji Kachalla din yana raye shi dai bai cika fadin iyaka adadin dukiyarshi ba da abubuwan daya mallaka. Shi Lamin din shi ya san komi. Ya kuma zambacesu da hakan.

Babu jimawa da yin hakan ya kyankyatsa ginin gidanshi mai kyau kamar a gidan sarauta, ya je cikin dangin mahaifiyarshi ya samu budurwa lafiyayya aka daura musu aure ta tare.

Shekara kwana ga mai yawan rai, abubuwa da dama kuma sun faru cikin dan kankanin lokaci. Mahaifiyarshi ta rasu jim kadan bayan da Iyani ta haifi Yasir. Tsakaninshi da Hauwau shekaru biyu ne. Bayan wasu yan shekarun kuma ta sake haihuwar Fatima Zahra.
Arziki kullum yana ta tumbatsar mishi, dukiya da duniya sun zauna mishi sosai yan ta facaka yadda yake so. Sam ya manta da marayun Allah da ya ci amanarsu ya tauye musu hakkinsu. Bai ma san a wani hali suke ciki ba tunda ba bibiyarsu yake yi ba. Danginsu ma kuwa kowa ta kanshi kawai yake yi, daga yan karkashinshi yan abi yarima a sha kida wadanda dukiyarshi suke wa, sai masu jin tsoron su tankareshi da maganar saboda kada ya daina hidimta musu, sai kuwa yan babu ruwana wadanda suma suna da nasu arzikin.
Rana guda kawai suka tashi da mutuwar Uwale, ashe rashin lafiya tayi da jinya sosai bai ma sani ba.

Yaji ana cewa dai taso ta koma can Kaduna da yaran, amma wasu daga cikin dattawan yan'uwansu suka hanata saboda sun san cewa idan ta tafi to bata da dalilin dawowa, zumunci da yaranta kuma zai yanke.
Amma su da suka hanata tafiyar kuma sun kasa tsaye mata. Dan sauran abinda ya rage na kadararta duk an siyar wajen jinyarta.

Ya kai kayan abinci ya zube musu, aka yi zaman makoki aka gama. Danginta da suka je suka hade kayanta waje guda tsaf, ba tare da sunyi shawara da kowa ba, ana yin addu'ar bakwai suka hade kan ya'yanta suka tafi. Sai zuwa aka yi aka samu gida kwalam. Daga baya ma ake jin cewa ashe an sayar da gidan shima.

Daga wannan tafiya da Ummulkhairi tayi da kanwarta bata kara bibiyar danginta ba.
Alhaji Lamin tuni shima ya shafe babinsu a rayuwarshi. Ya cigaba da fantamawa da facakarshi yadda yake so.
Daga baya ma sai ya yanke shawarar zai tsunduma harkar siyasa ne tsundum. Ya kuma fita din da karfinshi, nan da nan sai gashi yayi suna a ciki da wajen Maiduguri.

A kuma daidai wannan lokaci ne da yake ganin cewa tauraruwarshi ta gama yin hasken da babu abinda zai iya dusasar da ita, ta dauke wuta gabadaya.
Shagunanshi suka fara kamawa da wuta, kafin a samu a kashe wutar sai komi a cinye sai dai a tadda toka. Sai kwantainoni da suka dauko mishi kaya suka fara nutsewa a ruwa, masu kuma a kama.
Ya fara daga kadarori yana sayarwa, yana bin kan yan siyasa da manyan yan sanda da customs kan a sakar mishi kayan da aka kama, gefe guda kuma yana cigaba da kamfen dinshi.

Kafin shekara ta zagayo ya tashi a huhun-ma'ahu. Shi ba ga kudi da kadara ba, shi ba ga siyasa ba.
Tuni magoya bayanshi suka juya mishi baya da suka ga shima nema yake yi a wajensu, wadanda suka tsaya kalilan ne, suma don su karasa cinye yan canji daya rage mishi ne. Sune masu zuga shi da kara dorashi kan turbar bin malamai, suna kara gaya mishi lallai fa idan zabe ya zo to lallai zai cinye. Shi dai kawai ya saki kudi ya bada ana mishi sadaka da sauka, anan sauran yan kudaden nashi suka lume.
Kafin ya ankare zabe ya zo, kungiyar adawarsu ta ci. Ai hauka ne kawai bai yi ba a lokacin.

Sai gashi shine ya koma yana bin yan siyasa yana musu kanzagi da roko. Rayuwa dai ta juya mishi baya shi da iyalanshi, kamar ba a taba yi ba.

Su Fatima da suka taso cikin gata da jindadi da facaka, lokaci daya rayuwa tayi musu juyin bazata. Ta dilmiya su cikin garari da fadi-tashi.
Tana kan ganiyar yanmatancinta. Rayuwar dadi ta tashi a ciki, kuma ita ta sani, jinta cikin babu da rashi bakon abu ne a wajenta, wanda kuma ba zata iya dauka ba. Ta kasa hakurarwa kanta kamar yadda sauran 'yan'uwanta da iyayenta suka yi.

Ta daukarwa ranta alwashin, komai tsanani da wuya, sai ta sake taka matakin daula, sai ma gabanta ta fi bayanta kyau.

A gefe guda, a can Kaduna kuma. Mace daya ta sha alwashi kamar na Fatima, sai dai ita tayi ne domin ta rama wulakancin da aka yi mata. Ta ci alwashin tara kudi da mulki da duniya domin ta saka sharri da sharri. Ta ci alwashin jefa rayuwar Alhaji Lamin cikin garari irin wanda bai taba shiga ba, shi da iyalanshi, har ma da tattaba-kunnenshi, babu wanda zata bari! Wannan kenan.

8

*WACECE NADIYA?*

Alhaji Auwal Iko wanda aka fi sani da 'Dan Iko', irin yan kanzagin yan siyasar nan ne da sarakuna wanda hakan ya samu asaline tun yana dan kankaninshi daya taba aikatau a gidan wani Sanata.

Iyayenshi talakawa ne tilis, haifaffun ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????cikin garin Kaduna ne. Mahaifinshi ya rasu tun yana dan kankani, mahaifiyarshi ita ta raineshi har zuwa lokacin daya girma.
Bai yi karatun boko ba, na almajiranci ma da aka kaishi ki yayi ya gudo. Yarone mai matukar rashin ji da ra'ayin rikau, don dole mahaifiyarshi ta gaji da kaishi almajircin ta kai idanu ta zuba mishi. Da dan jarin da take ja na koko da kosai ta kaishi makarantar Arabi da boko, su dinma yaje yau ne gobe yaki zuwa.

Lokacin daya fara zama matashi ya samu aikin wanki da guga a gidan wani Sanata, yana kuma yi musu yan share-share da gyaran gida. Tafi-tafiya ya zamana ya fara yin suna a gidan saboda shi mutum ne mai shiga jama'a sosai kuma baya da shayin shiga ko'ina. A haka mai gidan ya fara sanyashi kananun ayyukan gida, a hankali sai gashi har ya zama direbanshi. Daga nan kuma ya zama na hannun damarshi wanda yake sanyawa yayi mishi yan ayyukansu na yan siyasa. Yau shine wajen wannan Malamin karbar taimako, gobe shine wajen wancan, jibi shine wajen wannan basaraken neman gindin zama da fadanci. Nan da nan sai yayi wani irin kaurin suna, kafin kuma kace me sai gashi ya fara tara yan canji.
A cikin wannan yanayi ya taso. Har zuwa lokacin da likkafa ta ci gaba lokacin da yayi sabon Ubangida wanda ya zama Gwamna.

Shi ya damka mishi filin gidan da yake ciki saboda yabawa da tsayawa da yayi ka'in da na'in ya goya mishi baya. Ya kuma bi shi da kudade masu kauri yace yayi gini dasu. Da yake kuma aure yake so, sai bai yi sanya ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login