Showing 3001 words to 6000 words out of 142169 words

Chapter 2 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

433

kallo na rainin hankali, "kije ana nemanki!"
Ta furta hakan cike da gatsali wanda ya kara sanyayar da gwiwar Nadiya din. Amma tayi ta maza ta matse don ma kada ta gama gano abinda ke cikin ranta. Sai dai fa ayi duk abinda za ayi a gidan don kuwa she wouldn't go down without a fight! Nadiya ce fa!!

Ta tashi tsaye tana watsawa Salamen kwatankwacin irin kallon da take mata, ta gefenta ta ratsa ta wuce ba tare da ta tankata ba.
Tana ji ta biyo bayanta tana fadin maganganu marasa dadin ji da daukar alwashi iri-iri. Tayi kunnen uwar shegu da ita, can a kasan ranta tana furta addu'a iri-iri, tana kara maimaitawa, wai Allah Yasa ta yiwa Abban nasu kwarjini ya ki yi mata ta'asar da tasan an shirya mata.

Tayi sallama a dakin a nutse, ta durkusa a gabanshi tana mishi sannu da zuwa, yayinda yake zaune akan kujera mai cin mutum biyu, Lantana a gefenshi tun kayan data sanya da safe data tashi barci sune a jikinta bata canza ba, itama Salamen kuwa duk zani ce ta tarda muje mu. Warin hayaki kawai suke yi duk sun cika dakin da hamami.

Da kyar ya amsa gaisuwar yana jefa mata wani irin wulakantaccen kallo, "me matana suka miki da zaki far musu da rashin kunya da maganganun banza dana wofi? Wai ke ba nayi miki shamaki da su bane?"
Ta daga kai tana kallon mutumin da ke amsa sunan mahaifi a wajenta. Amma mahaifi ko kuwa dai _sperm donor?!_
Don kuwa dai ba haka mahaifa suke ba. Ba haka iyaye suke treating 'ya'yan da suka haifa ba. Da ba don tana da tabbaci ba daga Mama wadda tace mata lallai shi din mahaifinta ne, kuma tasan Mama bata karya ko da wasa, to wallahi da cewa zata yi ba shi bane ya haifeta. Kila ma har wasu daga cikin iyalan gidan.

Tace, "Baba ina fa dawowa daga wajen aiki kawai suka tareni da maganganu da zagi, har suna kiran mahaifiyata da karuwa"
Budar bakinshi sai yace, "to dama mecece idan ba karuwar ba?!"
Sai tayi duf kamar an dauke ruwan sama. Yayinda shi kuma ya rufe idanu ya fara zabga mata ruwan fada, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Zagi kuwa ta uwa ta uba, kai kace sa'arshi ce ita din ba wai diyar shi ba.

Duk yadda taso ta daurewa ranta ta danne kukan da yake cinta, gazawa tayi, dauriyarta ta kare, murya cike da rishin kuka take cewa, "ai dama ba so na kake yi ba, kafi girmama matanka akan 'ya'yanka. Shi yasa ba zaka taba iya tsayawa ka kwatanta adalci ba. Idan ka so adalci ai kamata yayi ka fara tambayata abinda ya faru ne, ba wai ka hau min fada ba haka kawai!"

Aikuwa nan ya kara harzuka, ya fara fadin wasu irin maganganu marassa jin dadi, har da cewa shi wallahi da haihuwar diya irinta gwara ma babu, "mutuniyar banza mutuniyar wofi! Ni zaki zauna ina fada kina fada saboda kin maidani sa'anki? Yar iska kawai, banza, bari ki gani...!"
Ya zabura ya taso da niyar bugunta, Salame tayi saurin rikoshi wai tana bashi hakuri, "haba Malam da girmanka ina kai ina biyewa yara marassa kunya kuna ja'in'ja? Don Allah kayi hakuri kada kayi fushi. Ni dai kawai na kawo maka maganar ne ba wai don bacin ranka ba sai don kawai kaja mata kunne, a matsayinmu na matanka, kuma iyayenta...!"

Tayi gaggawar katse maganganunta masu kama da digar dalma a cikin zuciyarta, "kinyi kadan wallahi, kinyi tsararo, baki ko kama kafar taka wannan matsayi a wajena ba! Mahaifiya daya na sani a gidan, kuma ba ke bace! Ba zaki taba zama ba kuma! Kije can dai ki nemo inda diyan naki suke amma ba ni ba!!"

Abbansu ya zabura yana kokarin tashi, "kun gani ko? Kun gani ko? Wannan yarinya... Wannan yarinya... Tashi ki bani waje kafin in sassaba miki kamanni a wajennan..."
Bata jira ya rufe baki ba ta tashi tayi gaba, ta wucesu tana watsa musu harara kasa-kasa. Tana ji ya bita da wasu kalamai da maganaganun zagi. Bata waiwaya ba har ta dangana da dakin Mama.

Maryam da Aminatu, sauran diyan Mama da suka rage a gabanta, suna falon sunyi tsuru-tsuru suna sauraron diramar da ke wakana a gidan. Ta wucesu ta shige can uwar dakan Maman inda ta sameta tana zaune akan abin sallah tana jan carbi.

Ta haye can karshen gadonta na karfe ta cusa kai a tsakankanin cinyoyinta ta saki wani irin kuka mai cin rai.
Tana jin Mama ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafadarta ta shiga bata hakuri da tausassan lafazi.
Tace, "ba tun yau ba ina fada miki, kiyi hakuri da duk wani halin mahaifinku, ki daina ja-in-ja dashi musamman idan yana yi miki fada Nadiya. Iyaye har kullum hakuri muke yi dasu ba wani abu ba!"

Tace, "haba Mama! Haba don Allah!! Shi kenan kuma sai ya kasance kullu-yaumin ba za a taba tsayawa a saurari uzurin mutum ba sai dai duk zugar da za a kai a kanshi a hau kai a zauna babu wani bincike? Wannan ai ba adalci bane. This is not fair wallahi!"

Mama ta dan yi murmushi mai nuna takaici, tace, "kin san halin Abbanku sarai Nadiya, kin kuma fi kowa sanin haka halinshi yake. Don haka ban ga abin tada jiniyoyin wuya da bacin rai ba a nan. Kiyi hakuri ki jure koma menene, saboda watarana sai labari!"

Bata iya cewa komi ba sai jan shessheka data cigaba da yi tana sharar kwalla ranta a matukar cune.
Maryam da Aminatu suka shiga dakin suka zauna a gefenta suna kara tausarta, har dai taji ranta yayi mata dan sauki.
Ta umarci Aminatu da taje dakinta ta dauko musu take away din data je da ita. Maryam kuma ta dauko musu ruwa mai sanyi da kunun aya da Mama take yi na sayarwa. Nan suka zauna a falo suna cin abincin suna hirarsu har suka gama cin abincin.
Da yan wuta suka kawo suka kunna kallo a yar karamar tv dake manne a jikin bango a dakin. Ta zauna tana tayasu Assignment dinsu da bitar karatu. Ba ita tayi musu sallama ba sai da karfe sha daya ta gota.

Ta shiga bandaki ta watsa ruwa tare da dauro alwala, ta koma dakinta ta sanya kayan barcinta riga da wando marasa nauyi. Wandon ya tsaya mata a iya gwiwa, rigar kuma kamar vest take mai siririn hannu.

Tana dora kai akan katifa da niyar barci, abinda take gudu ya fara aukuwa.
Yau kam abin har yayi yawa, wani lokacin ma sai taga kamar da gayya suke yi mata abinda suke mata. Saboda ta kula sun fi kwaratsi da daga murya a ranakun da suka samu sabani da ita. Musamman Lantana din daya kasance ita ce da maigidan ranar, har wani ahi take da wani abu kamar wadda take shirin tayar da aljanu.

Ta dauko earpiece dinta ta makala a kunnen ta jona da wayarta. Karatun Qur'ani ta kunna ta kuma kure volume, ta koma ta kwanta. Amma duk da hakan barci ya kauracewa idanunta. Ta kasa tsayar da hawayen da suke mata zarya akan fuska suna kwarara, haka kuma ta kasa hana kanta daina hasko mata munanan abubuwa da sake-saken da ranta yake mata. A haka wani irin wahalallen barci ya dauketa.

Ko da alarm dinta ya buga da asubah, ta kwashe fiye da minti goma a kwance kawai ta kasa tashi, jikinta kamar wadda trailer ta bi ta kanta haka take ji. Ji take kamar ma wadda bata yi barcin ba saboda yadda take jin kanta yana sarawa kamar zai rabe gida biyu.
Haka ta kokarta da kyar tayi alwala tazo tayi sallah.

Ta koma ta kwanta akan abin sallar, rabin jikinta kuma akan katifarta tana yin azkar dinta har dai gari yayi haske. Kafin ta tashi taje tayi duk abubuwan data saba.

Bakwai mai kyau ta gama shiryawa cikin riga da skirt na atamfa. A-shape ne wadanda suka bi jikinta kuma basu kamata ba. Bayan yar hoda da wet lips data sanya ta kuma zizarawa idanunta kwalli babu abinda ta kara. Ta dauki karamar hand bag ta leather ruwan kasa ta zuba abubuwan da zata bukata, ta fito ta kulle dakinta.

Ganin yan yaran duk a tsakar gida yasa ta shiga dakin Abbansu domin ta gaisheshi.
Sai data dan yi turus, ganin Lantana da Salame a kame a kan kujeru sun sanya shi a gaba kamar wani karamin yaro yana karyawa. Koda yake dama mai take tsammani? Ana gama Asubahi haka zasu shiga dakin su sanya shi a gaba. Da ace zai yini a gidan, to da ko nan da can ba zasu motsa ba. Duk kuma hakan gadin kada su kebance ne da Mama ko kuma ya dan yi tattaunawar sirri da iyalanshi. Magana ko wace iri ce sai dai ayi a gabansu. Shi yasa ai daga 'Ya'yan gidan zuwa abokai da danginshi, basu ganin kan kowa da gashi.

Ta riga ta san abinda zai biyo baya tun ma kafin ya furta lokacin data zube a gabanshi ta gaisheshi. Ya amsa a tsaitsaye, sai kuma ya tsayar da ita lokacin data fara yunkurin tashi, "su kuma iyayen naki ba zaki gaishesu ba saboda rashin ta ido ko? Wai ke Nadiya me yasa ba kya jin magana ne?"
Bata iya cewa komi ba sai dan juyawa da tayi tana kallonsu kamar ta hadiye zuciya ta mutu, tace, "ina kwananku?"
Suka kuwa yi caraf suka amsa kamar dama jira suke yi.

Ta mike gwiwa a sage, rai yana suya zata fita. Sai kuma suka ci karo da Mama ita kuma ta danno kai zata shigo dakin hannunta rike da kwanon da zata dauki abincin da zata dafa tunda ita take girki ranar, kuma store din a cikin dakinshi yake.

Sai ta dan yi baya ta bata waje ta shiga, ta kuma koma ta tsuguna tana gaisheta. Ta amsa tana kallonta fuska dauke da fara'a, tace, "Nadiya har an fito kenan?"
Tace, "ehh wallahi Mama. Yanzu nake cewa bari inje in sanar dake zan tafi."

Tace, "to sai kin dawo, Allah Ya tsare. Yau ma ba zaki karya din ba zaki tafi?"
Tayi dan murmushi, "Mama kin manta yau alhamis? Azumi nake yi."
Tace, "hakane fa. To sai kin dawo."
Daga haka ta sa kai ta bar gidan.

Aikin ranar kamar na kowace rana ne, akwai kwastomomi da tarin ayyuka shi yasa ta koma gida a matukar gajiye likis. Tun ma kafin karfe tara tayi ranar ta kwanta.
Barci mai dadi da nauyi ya sureta. Kawai gabannin asuba sai taji ana maimaita yar gidan jiya kamar a cikin mafarki. Tayi lamo a kan katifa tana kokarin tunano me yake faruwa ne? Musamman data jiyo Salame ce tare da mahaifin nata yau. Girkin Mama ne, kuma ta tabbata ba a nemi izininta ko shawararta ba. Ta hau girgiza kai gabadaya kanta a juye da lamarin wadannan mutane. Su basu san suna take ka'idar Allah bane?

Akwai wani lokaci data taba tunkarar mahaifin nata da zance makamancin wannan. Farkon komawarta dakin ne lokacin tana makarantarta ta jami'a. Gani tayi shiru-shiru da kawaicin da kawar da kai da take yi duk basa yi. Ta fara samun matan nashi da maganar, ta ga dai basu da niyar su fahimceta ko kuma su gyara. Sai ma muzguna mata da suke yi musamman da suka fahimci cewa abin yana damunta kuma bata jin dadinshi sam. Wai sai ya zamana ma suna mata habaici da tutiya dashi. Sai abin ma ya koma yana bata dariya. Ta ga akan wani dalili to ita da ba kishiyarsu ba?

Don haka ta badawa idanunta toka ta tunkari Abban nasu da maganar. Ta nuna mishi rashin dacewar hakan da kuma illolin da hakan zai iya kawowa musamman ga yaran gidan da suke tasowa. Tunda watan watarana dai zata bar dakin ai, kuma 'ya'yansu sune zasu maye gurbinta. Bai dace su taso suna shaida wannan abin ba.
Babu abinda ya fi ci mata tuwo a kwarya ma irin daukar kwanan wata ya kaiwa wata, musamman kwanan Mama. Tunda dai ita tace ta hakura dashi shekara da shekaru, kuma zaman 'ya'yanta take yi.

Ya zauna yana saurarenta tana ta zuba bayanai kamar wani abin arziki. Sai data dasa aya sannan ne kuma ya rufe ido ya fara zuba mata rashin mutuncin da sai data yi dana sanin yi mishi maganar. Har da mata kashedin idan ta sake yi mishi katsalandan a al'amuranshi to lallai kuwa zai koreta ta bar mishi gidan, in yaso sai taje can wani waje na daban ta musu rashin kunyar.

Don haka ta daurewa kanta, ta kai na mujiya ta zuba musu kawai. Ta koma gefe tana addu'ar Allah Ya shiryesu, ita kuma ya bata mijin aure tayi ta bar musu gidan ta huta.

Shekaru ashirin da shida tana shirin haurawa da bakwai, amma har yanzu babu wani tsayayyen miji na a zo a gani.

Ranar haka ta yini cikin yanayi na bacin rai da damuwa da tunani. Rashin yin aure da son barin wannan gidan yana daya daga cikin manyan abubuwa da suka jagoranci damuwoyin da suka dabaibayeta.

Kasancewar Juma'a ce, sun fi samun kwastomomi da rana idan an fito daga masallaci, don haka zuwa lokacin da karfe hudu ta yi, abubuwa sun fara lafawa.

Tana bayan kanta tana lissafin cinikinsu na ranar da shigar da bayanai, Aramide ta shiga shagon hannu rike da makullin mota, gyale a kafada yana neman faduwa kasa.

Aramide abokiyata ce tun makarantarsu ta Jami'a, kuma ita ce jigon shagon nasu. Don haka tare suke kula dashi duk da cewa dai ita tafi zuwa a ranakun mako saboda tana aiki da kamfanin Indomie da bangarensu yake anan Kaduna.

Ta mata sannu da shigowa. Ganin yadda ta amsa a tsaitsaye, tasan watakila ta kwaso gajiya ko kuma bata jin dadi. Don ita din mutum ce mai kazar-kazar da barkwanci, shi yasa ma tasu tazo daya da Nadiyar sosai.

Ta dauki cup cakes da doughnuts da lemu mai sanyi ta kai mata. Ta amsa tana mata godiya, ita kuma ta koma ta cigaba da abinda take yi.
Tana aikin ne wani tunani ya darsu a ranta. Tunanin komawa gida ranar yasa take jin kamar ta dora hannu a ka tayi ta ihu kawai. Ta gaji kwarai da gaske, hutu take bukata daga wannan gidan da wannan rayuwar.

Tayi sauri ta gama abinda take, taje ta samu Aramide tace mata zata wuce gida da wuri. Bata tsaya jan dogon zance ba tace mata ta gaida gida.
Ta fita ta tari abin hawa, kai tsaye ya kaita tashar Kawo ta shiga motar Kano.

Tana zuwa motar saura mutum biyu ta cika da yake golf ce. Don haka ta zauna jiran cikon mutum daya.
Sai lokacin ta ciro wayarta a jaka ta kira Mama wadda ta daga nan take.
Tace mata, "Mama a mana addu'a, gani nan a hanyar Kano!"
Mama tace, "Kano kuma da wannan yammacin Nadiya? Anya? Ga dare yayi kuma ga yanayin hanya da wannan rashin tsaro da muke fama?"
Tayi dan murmushi, "babu abinda zai faru in shaa Allah Mama. Ni dai kawai kiyi mun addu'a!"
Mama tace, "to Allah Ya kiyaye hanya Nadiya, Allah Ya saukeku lafiya. Kin fadawa Abbanku dai ko?"

Nan da nan sai fara'ar fuskarta ta dauke. Tace, "in kira shi in ce mishi me? Na tabbata dai babu wani fatan alkhairi da zai mun, kila ma sai dai ya min fatan inyi hatsari a hanya in mutu tunda dama ba yau ya saba hakan ba!"

Mama tace, "duk da haka, mahaifinki ne ai. Kuma idan kinyi hakan hakkinshi kika fitar. Ki daure ki kirashi din!"
Tayi dan jim, kafin ta gyada kai kamar Maman tana gabanta, tace, "to shikenan, zan kira shi din in shaa Allah."
Mama tace, "yauwa Nadiya haka ake so. Ki gaishe da Jamilar idan kin je."
Tace, "zata ji in shaa Allah."
Nan suka yi sallama.

Lambar Anty Jamila ta kira, sai dai har tayi ringing sau biyu ta gama ba a daga ba. Sai ta kira lambar diyarta Rabi'ah.
Tana shiga ta daga kamar wadda take jira. Ta fara magana cike da azarbabi, "Mommy Nadiya ina yini?"
Tayi yar dariya, "kai Rabi'ah, Allah Ya shiryeki wallahi. Ina sallamar to?"
Sai itama tayi yar dariya cike da alamun jin kunya, tace, "Assalamu alaikum wa rahmatullah"
Ta amsa, "wa alaikumussalam wa rahmatullah. Ina Mommynki ne, ina ta kiran wayar tata amma bata dagawa?"
Tace, "aikuwa yanzu babu jimawa suka fita ita da Daddy. I??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na tunanin ko wayar tana jaka ne ko kuma ta barta a gida."
Tace, "ok, to idan ta dawo da wuri ki fada mata ina kan hanya. Don kada ta tarar da missed call ta kira kuma yanayin network bata sameni ba."
Rabi'ah tayi tsallen murna ta dire, "da gaske? Allah kiyaye Mommy sai kin iso! Ki kawo min tsaraba fa!!"

Yadda taji tana murna da dokin zuwanta sai taji itama murnar ta kamata, tace, "to shikenan Rabi'ah, zan kawo miki in shaa Allahu!"

Suna gama wayar aka samu fasinja. Nan da nan aka rufe mota direba ya dauki hanyar fita daga Kaduna.
Sai da suka fita a tashar sannan ta lalubo lambar Abbansu ta tura mishi sakon ita dai ta tafi Kano gidan Anty Jamila. Sai dai har suka fita daga Kaduna suka dauki hanyar Zariya bata ga ya maida mata da amsar sakon ba. Don haka ta kada kanta gefe guda ta jinginar da gilashi tana kallon gari.

Karfe takwas da rabi suna cikin Kano, amma bata karasa gidan Anty Jamila dake can cikin Nasarawa GRA ba sai wajen karfe goma saboda yanayin abin hawa.
Mai napep ya tsaya a gaban tangamemen gate din gidan nasu. Bakin gate ne mai gida-gida sai wasu adon furanni da aka yi a jiki masu kalar zaiba. Kai daga gani ba sai ka tsaya tambaya ba kasan cewa ya ci kudi ba kadan ba.

Ta sallami mai abin hawar kafin ta karasa jikin gate ta kwankwasa, mai gadi ya leka yana tambayar waye? Daya ganta sai ya koma ya bude mata yana mai yi mata sannu da zuwa. Ta amsa mishi a matukar gajiye.

Motocin data gani a cikin gareji ya tabbatar mata da cewa su Antyn sun dawo. Ta raba ta gefen garejin ta bi ta gefen madaidaicin lambu da kuma wajen shan iska na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login