Showing 60001 words to 63000 words out of 142169 words

Chapter 21 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

456

abinda yake fada, sai ta kara hade fuska, "wai waye ne zai kira mutane cikin daren wannan a dinga musu wani zance maras kan gado?"

Yace, "oh, waye kike tunanin zai kiraki a daidai wannan lokacin ne kam? Ko kuwa dai dama kina da masu kiranki ne bila adadin?"
Tace, "don Allah idan baka da muhimmin dalilin da yasa ka kirani ka katse kiran nan. Kamar yadda nace, barci nake yi ka katse min!"

Ya ajiye numfashi, "Nadiya!" Ya ambaci sunan da wata irin murya data sanya taji wani abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har tafin kafarta.
Bata san me ya kaita daga baki zata amsa ba, amma koda ta daga bakin sai taji bata ma iya hada kalma waje daya. Don haka ta maida bakin nata ta rufe.

Ya sake ambatar sunanta, yace, "Nadiya! Me yasa kike kokarin nesanta kanki da ni ne? Me yasa kike gujewa duk wani kusantoki da zan yi?!"
Tayi shiru kamar wadda ruwa ya cinye.
Bai tsaya sauraren amsarta ba shi kuwa ya cigaba da maganarshi. Yace, "kwanaki dai-daya har goma sha biyar Nadiya, baki ji muryata ba ban ji taki ba. Na nemeki a karo na farko amma kin bude baki wai kina ce min idan bani da magana mai muhimmanci in kashe waya. Anya kin dauko hanyar tsayar da adalci kuwa?"

Ta yatsine fuska kamar yana gabanta, a gefe daya kuma tana yin kasa da muryarta saboda kada ta damu su Mama dake barci.
Tace, "to ni don na shekara ma ban ganka ba ko naji muryarka meye nawa? Idan da kai kaso jin muryar tawa ai da kaji tun ba yau ba kuma ko?"

Ya saki wata yar dariya mai taushi, "okay, na g???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anoki! Wato ita kewar tawa da kika yi ma ba zaki iya fada kai tsaye ba sai kin dinga kewaye-kewaye? Nadiya, halin nan naki yana bani dariya!"

Ganin nemanta yake yi da tsokana yasa tayi shiru kawai ta kyaleshi.
Yace, "da ai nayi wayon wai in kyaleki ne zaki nemeni da kanki. Sai naga ke baki ma da wannan shirin sam. Shine nace to ni na ci girman, bari in kiraki. Ya kike ne? Naji ance garin yau an sha ruwa sosai har dare ko?"

Ta koma ta kwanta tana cewa "uhm!"
Yace, "muma yau yini guda ruwan aka yini yi tun safe, har yanzu ma kinga yayyafin ake yi. Garin kuwa ya dauki sanyi gwanin dadi, sai dai ni dazu da ruwan ya dakeni sosai kin ga ya sanya min zazzabi kuma. Yanzu haka kin ganni cikin bargo na rufa."

Haka kawai ta samu kanta da jin babu dadi, tace, "Subhanallahi, garin yaya ka bari ruwan ya tabaka ne haka?"
Yayi dan murmushi, "sallah na fita. Da zan dawo kuma sai ban sanya bazara ba ganin cewa ruwan ba mai karfi bane. Amma duk da haka sai daya tabani din."
Tace, "to Allah Ya sawwake. Ka sha magani?"
Yace, "sai dana sha sannan na kwanta. Da sauki ai, zazzabin ya fara sauka."
Tace, "to ka kwanta ka samu barci mana? Sai kaga ka wartsake idan ka tashi."

Yayi saurin ce mata, "a'ah! Ai nace miki da sauki. Besides... sauraron muryarki kadai ma yasa naji zazzabin ya sauka!"

Bata san lokacin data saki wata dariya ba marar amo, ta dinga kyalkyalawa kamar wata sabuwar kamu. Yayi zaune da waya a kunnenshi yana murmushi kamar wani zautacce.

Tace, "kaji wata magana sai kace a shirin film? Irin wannan zantukan dai yawanci a 'teen fiction' kake ji ana furtasu!"
Yayi dariya, yace, "ko babu komi dai ai na sanyaki dariya ko? That was a first!"
Sai kuma tayi shiru tana raba ido.

Yace, "in dai ni ne Nadiya, don dariya dai da farinciki da nishadi, zan sanyaki a cikinsu bila adadin. Na miki wannan alkawarin. Yanzu dai me da me kike shirya mana na aurenmu ne?"
Ta tabe baki, "wani shirin aure kuma? Shirin me kake nufi bayan kun ce amarya kawai kuke so a kawo muku sai kace wadda za a sayar?"
Yayi yar dariya, yace, "idan ma sayan za ayi ai nasan baki da matsala da hakan. Ke da kanki zaki dauko kanki ki zo inda nake! Zan kuma sayeki da madaukakiyar daraja!"
Tace, "tabdijam! Lallai kuwa kana yaudarar kanka!"

Suka raba wannan dare yana ta janta da hira da tsokana, har sai data saki jikinta dashi.
Bata san lokacin da barci ya dauketa wayar manne a kunnenta ba. Sai shi da yaji alamun tayi barci, sannan ya katse kiran yana murmushi.
Ranar shi ya tasheta sahur.

25.



Shikenan, tun daga wannan lokacin sai ya zamana shi yake tashinta sahur. Idan an sha ruwa zai kirata ya mata sannu da shan ruwa. Idan aka jima kuma zuwa wajen goma zai sake kiranta su sha hirarsu sosai. Haka a yini ma zai dinga kiranta akai-akai.

A hankali a hankali, sai gashi ita da kanta wani lokacin zata dauki waya ta kirashi ta mishi barka da shan ruwa.
Hirarrakinsu suka fara tsayi. Ta fara tunanin wai ma me yasa tun farko take kin shi ne? Me ya mata?

A karo na farko a rayuwarta take shaida menene kewar Mutum? Menene jin shaukin wani mutum?
Don kuwa a hankali Habibun yayi kokari ya shiga can cikin kasan ranta, inda ita a karan kanta bata san da wanzuwarshi ba.
Yayi wani kabe-kabe ya kanannade mata zuciya. Duk yadda take kokarin yakiceshi da banzatar dashi abin ya ci tura.

Ta fahimceshi sarai a mutum wanda yake matukar girmama duk wani abu daya shafi mahaifiyarshi, baya wasa da al'amarinta ko kadan. Duk wani abu da zai yi, duk wata shawara da zai yanke, sai Ummanshi taji. Magana daya, biyu, yace Ummah.
Nadiya tana girmama hakan, a gefe daya kuma tana mamakin wannan abu. Ta yaya babban mutum kamar Habib zai zamana bashi da wani sha'ani na kanshi kawai sai na Mahaifiyarshi? Ba aibun abun take gani ba, kawai tana mamakin hakan ne.
Daga baya ta fahimci hatta da siyasar da yake shirin sanya kafa a ciki, burin Hajiya Ummah dinne ba nashi ba. Bata manta tambayar data taba mishi wani dare, ranar sun kai azumi na ashirin kuwa.

Sun gama wayarsu zasu yi sallama, yake jaddada mata da cewa ta dage da yi mishi addu'a a wannan darare masu albarka. Allah Ya basu sa'a da nasarar siyasar da suke tunkara.

Tace mishi, "wai me yasa kake son siyasa ne sosai haka?"
Bai kuma tsaya dogon tunani ba yace, "saboda Ummah bata da burin daya wuce danta ya hau kujerar Gwamnan Kaduna!"

Har ga Allah tayi tunanin jin abu mai kama da, 'saboda taimakawa jama'a ko kawo cigaba a kasata' ko wani abu mai kama da haka. Sai taji akasin hakan kuma.
Ta gyada kai kamar yana gabanta ba don ta fahimceshi ba, tace, "to in shaa Allah kullum zan sanyaka a cikin addu'ata. Da aurenmu da siyasarka idan alkhairi ne, Allah Ya baka dukansu. Idan kuma duka ba alkhairi bane, to Allah Yayi maka canji da mafi alkhairi!"
Yayi dariya sosai, yace, "alkhairin ne ma in shaa Allahu, Love."
Ta samu kanta da murmusawa jin kalmar daya kirata da ita.

Ta tashi ta dukufa da addu'a babu kakkautawa, da auren da siyasar tashi, duka Allah Ya tabbatar da alkhairi a ciki.

*

Anyi azumi na ashirin da biyu aka kaiwa mutanen gidan kayan sallah. Yawanci idan sallah tazo Abbansu ya kan siyawa yaran gidan kayan sallah ne gwargwadon yanda hali ya bashi. Su kuma matan sai ya basu kudi yace su sayi duk abinda suka ga yayi musu.

Wannan karon kuma har matan duka ya hada ya sayawa Atamfofi masu matsakaicin kudi.
Lantana ta fito tsakar gida daga dakinshi, da atamfar a hannu shekeke tana kara dubawa, tsaki take ja tun karfinta ganin anko aka musu da Amarya.
Nadiya kuma tana raba ido taga ta ina nata kason zai fito.
Salame ita ma ta fito daga dakin nashi tana yatsine baki, suka koma gefe daya ita da Lantanar suna magana kasa-kasa.

"...Dama ai nace wannan karon dai mai farar kafa aka dauko mana. Yanzu banda tsabar ci baya, mutumin dake bada kudin leshi guda shine zai buge da sayen karamar atamfa? Ina cigaba anan?" Cewar Salame.
Lantana kuma ta tabe baki, tace, "ke ta kayan sallah ma kike yi, kina jin ko dan abin yankar sallah ma da ake mana fa cewa yayi ba zai yi ba saboda bashi da kudi. Ga wannan kaddararren aure da aka hadashi da shi!"

Salame tace, "ke! Ki kama bakinki to tun kafin ya ji ki. Kin kuwa san yadda yake ji da wannan auren? To wallahi a kanshi sai ya tafka miki rashin kirki kin dai san halin Malam sarai. Yadda yake fadin alkhairin da auren nan ya kawo mishi idan yaji kina wannan maganar ai wallahi sai ya bata miki rai!"
Tace, "yo wai ina albarka anan? Kina kallo ana zancen za ayi aure amma gida yana kara lalacewa da ja baya, ina alkhairin? Ai ya gode Allah ma sun ce kar ayi kayan daki, da yaji kunya sosai da sosai."
Salame tace, "yo jin kunya na nawa kuma? Ai sai dai kar a kuma. An zo neman aure ka dauka ka bada babu wani dogon bincike, an ce za a kaika Makkah ka bude baki kana godiya babu dan jan aji ko nuna wadatar zuciya. An zo an ce ba a bukatar kayan daki, nan ma ka hau godiya da murna, wannan ai salon kaja a rainaka ne. Ga wannan aure na wannan zamani da ake yi, an yiwa mace kaya ma bata yi daraja ba ina ga ba ayi ba?"

Lantana ta kwashe da dariya, "ina kika ga amarya tayi sati daya ta yo kwana don ba a kaita da kayan daki ba?!"
Suka sake fashewa da dariya har suna shewa.

Abba daya gama jinsu suna ta bayani, yace, "to ta Allah ba taku ba munafukan banza da wofi! Wato saboda kun ga yarinya tayi goshi ta samu gidan hutu, shine kuke mata bakin ciki da hassada. To dai hassada ga mai rabo taki ce, kuje kuyi ta maganganunku da iface-iface, bori dai baya hana mutuwa!"
Salame ta fitittike zata fara nade tabarmar kunya da bori, ya kakkabe rigarshi ya rufe dakinshi ya barsu anan.

Da taga haka ita kuma Nadiya sai ta rufa hijabi da dare ta sameshi da tambayar ina batun kayan sallarta? Saboda tayi tunanin ko ya manta da ita ne.
Yayi fici-fici da ido yana kallonta, yace, "kayan sallar me zan miki ke kuma bayan da anyi sallah zaki bar min gida? Ke ni fa ko ciyar dake da nake yi ma a yanzu, yi nake kawai don tsoron Allah ne ba don wani abu ba. Amma ni ai tuni na fiddaki daga jerin wadanda ke karkashina!"

Tace, "to amma dai Abba ai ko auren ma za ayi, ana dinkawa Amarya abinda zata yi fitar biki dashi ko?"
Amarya dake gefenta tayi caraf tace, "kwarai kuwa. Ai ko ni nan da kika ganni, sai da aka yi min kala hudu na fitar biki. Wannan jan leshin ma dana sa ranar da zan tare ai Babanmu ne ya dinka min shi!"

Ya kankance ido yana kallonta, "ita kuma nata lefen da zata je ta tarar fa? Mutane sun ce ba sai anyi taro ba, aure kawai za a daura akai musu mata. To kuma me kuke so inyi? Idan dai har ba bakincikin kayan da aka dinkawa yan'uwanki kike yi ba, to ki daina min maganar dinki anan wajen. Ki je ki samu mahaifiyarki ta miki mana, tunda ita tafi cin gajiyar auren ba ni ba! Sai kizo ni ki sanyani a gaba da wani zance na banza da wofi?!"

Ta daga kai a sanyaye ta kalleshi da idanunta da suka tara kwalla, tace, "babu zancen wani bakinciki anan Abba, kayi hakuri da zancen dinki da nace kayi mun kuma."
Ta tashi ta wuce dakin Mama abinta.

Ta rasa ma dalilin da yasa tayi mishi maganar ya mata dinkin fitar biki. Abinda da daga farko bata da niyar yi. Duk da cewa har yanzu ba wani taro za tayi ba, amma kuma ko yaya ai ya cancanci a zo a ga amarya cikin shiga mai kyau ko? Sai kuma ta girgiza kai, tana dan murmushi a tausashe cike da mamakin zuciya wadda take iya canzawa a cikin dan kankanin lokaci.

Ta kai zancen dinki can bayan ranta ta ajiye. Don kudi tana da su wadanda zata iya yiwa kanta dinki, amma tana tsentsenin taba kudin ne saboda kada wani abu mai girma ya fado mata wanda zata dawo daga baya kuma tana dana sani.

*

Anty Hauwa ta kirata take tambayarta wai me take yi na shirye-shiryen biki? Tace ita kuwa wani shiri zata yi ne? Tunda dai ba wani taro za ayi ba?
Tace mata, "duk da ba taro za ayi ba, ina maganar gyaran jiki da sauran al'amura ne. Kunyi su dilka ne da halawa? Kin san fa mu normally wata guda ake dauka ana yin wadannan abubuwan, saboda gyaran yayi sosai, kuma kamshi ya kama jikinki da kyau! Mun fara magana da Zahra'u kwanaki, to abin na dan yi tafiya ne kwana biyu shi yasa bamu karasa zancen ba."

Tace, "ai gaskiya ni dai Anty babu wani gyaran jiki da zanyi. A barni a yanda nake, tunda dai su suka ce sun gani suna so a hakan!"

Tace, "gidanku Nadiya! Ashe dama baki da wani wayon azo a gani nake kallonki a haka? To ki kiyayeni wallahi. Zahra'u bata taba yi miki zancen gyara ba tunda maganar auren nan ta taso?"
Ta girgiza kai, "gaskiya bamu taba yi ba. Amma fa Mama itama tana nata aikin." Ta fada mata abubuwan da Mama din take kan bata tana ci da sha da wankawa.

Tace, "amma gaskiya Mama ta kyauta, zan kira inyi mata godiya sosai. Sai dai nata gyaran daban, muma namu daban. Don haka dole ma zamu yi maganar da Zahra'u. In banda ma shirme irin nata, haka za a kaiki gidan kishiya ba tare da mun gama kimtsaki ba? Wannan ai ganganci ne!"

Ta kashe wayar tana korafi, Nadiya kuwa ta tabe baki. Don kuwa tuni ta gama gano Madam din, ba wadannan abubuwan ne a gabanta ba. Ita dai tunda zancen aure ya tabbata, to ta gama da Nadiya, Nadiya ta gama mata amfanin da zata mata. Inda za a kaita kuma, da irin rayuwar da zata yi, wannan ba damuwarta bace.

A daren ranar Anty Hauwa ta sake kiranta. Ta fada mata yanda suka yi da Madam din, cewa da anyi sallah za a zo a hau aikin gyaran jiki tunda suna da sauran lokaci.
Tace mata, "ni dai wallahi Anty da kun bar wannan maganar..."
Tun ma kafin ta karasa ta katseta, tace, "kin san Allah Nadiya sai in bata miki rai akan wannan zancen. An ce miki ne wai mu sakarkaru ne kamar ki? Ki bar ganin wai shi Habibun yana miki rawar kai da kafa da dadin baki. Wallahi kina shiga daga ciki ya fahimci ba daidai kike ba, ajiyeki zai yi a sukwane kamar wata tsumma wallahi. Kila sai lokacin zaki fahimci abinda rayuwa take ciki!"

Maganar tata ma sai taso ta ba Nadiya dariya, tace, "ni dai babu wani rawar kai da dadin baki da ake yi min!"
Tace, "ke dai kika sani ai. Kafin masu gyaran su zo zamu yi waya dake muji yadda abin zai kasance dai." Suka yi sallama da ita.

Washegari ta shiga shago suka sha aiki kamar ba gobe. Saboda sallah duka bata fi saura kwana biyu ba zuwa uku. Zasu fara aikin snacks na masu odar sallah, da wanda za ayi delivering har gida, da kuma wanda zasu sayar anan. Aiki ne ba karami ba saboda wannan sallar sun samu order sosai har sai da suka kai ga rufewa.

Kafin karfe biyar ta rufa, ta gama gajiya tikis kamar wadda aka yiwa dukan tsiya.
Tayi sallama da ma'aikatan da zata bari anan, ta fito daga shagon tana tafe kafafunta har suna hardewa.

Tana shirin fita, taga wata farar Elantra tana kokarin shigowa. Ta matsa gefe don ta bata hanya ta shiga. Sai kuma taji zuciyarta tana wani tsalle da daka a sukwane lokacin data fahimci lambar motar irinta gidansu Habib ce wadda ta fahimci duka motocin gidan suna da shigenta.
Ta fara tunanin ko dai Habibun ne ya dawo babu sanarwa?
Lokacin da taga an bude murfin motar za a fito, sai da taji har wani kadawa da rawa jikinta ya dauki yi kamar mai fama da masassara.

Madadin Habibu, sai taga Ammar ya fito. Gefenshi kuma wata matashiya ce da zata iya yin sa'ar Maryam. Kai daga gani babu tambaya kanwar Habibun ce saboda idan ka ganta yadda kasan yayi kaki ya tofar, basu da bambanci.
Tana yawan mamakin yadda aka yi Habib bai dauko kamannin Hajiya Ummah ba, amma sai tafi ba kanta uzirin watakila ko Babansu ya biyo.
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali wadda bata san ta rike ba, ta nufi Ammar wanda ya ruga da gudu ya rungumeta.

Itama ta rungumeshi tana dariya, don kuwa duk da bata san yaron ba, dan zaman da suka yi dashi kwanaki taji kaunar yaron ta kamata sosai.

Budurwar da suke tare dashi ta dan duka tana gaisheta, ta amsa da murmushi akan fuskarta tana kallonta.
Ammar ne yake ce mata, "Anty Rashida ce tace in zo in rakota wajenki!"

Tayi dan murmushi, "aikuwa Allah Ya taimaka, da munyi sabani daku. Don kuwa fitowata kenan zan wuce gida."
Rashida itama tayi murmushin, "lallai fa. Tun dazu ma muka fito wallahi, sako muka tsaya amsa shi yasa muka dan jima. To ko zaki zo ne sai mu saukeki a gida?"

Ta girgiza kai da saurin "a'ah wallahi, nagode. Kada inje in tsayar daku."
Rashida tace, "laaa, babu fa inda zamu je. Musamman Yaya yace yau dai mu zo mu gaisheki!"

Tace, "to shikenan muje, kin ga ai sai ku tsaya ma a can gida ku sha ruwa."
Tace, "tab, ai gaskiya ba lallai ba. Saboda Ummah fada zata yi mana sosai."

Ta shiga mota direban daya daukosu ya ja suka wuce bayan ta fada mishi inda zai kaita.

Suna cikin motar ta kalli Rashida, tace, "amma dai ke kanwarshi ce ko?"
Tayi dariya, dogayen hakora jerarru suna bayyana, tace, "eh. Nasan ai da kyar idan ya taba fada miki hakan!"

Tace, "ko kadan. Kai ni ko wajen mutane ma ban taba sanin cewa Hajiya Ummah tana da wata diya ba. Duk munyi zaton ma ko shi kadai ne dan nata."

Rashida tace, "ai ba Hajiya Ummah ce Mahaifiyata ba fa, ni Ummana tana Makarfi."
Ta jinjina kai cikin mamaki da daurewar kai. Ganin kada ta dameta da tambaya yasa bata kara tambayarta ba.

Da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login