Showing 78001 words to 81000 words out of 142169 words

Chapter 27 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

467

sai ke. Amma dai a hakan kike burgeni."
Ya juyata ta fuskanci gado, kafin ta ankare sai ta tsinceta tsamo-tsamo akan gadon shi kuma ya bi ta yayi mata rumfa.

Abubuwan nashi neman wuce gona da iri suke, tuni sai ta hau magiya da neman hanyar tsira. Fadi take tana karawa, "don Allah don Annabi ka taimaka min kayi hakuri ka kyaleni. Wallahi Tallahi yunwa nake ji!"
Yace, "ai mai rabani da ke yau Nadiya, sai ikon Allah. Ko kin yi zaton jiya ban ga irin hararar da kika dinga auna min bane? Kuma nasan duk cikin jin haushin rashin kwana a dakinki ne, don haka yau dai sai na wanke kaina a wajenki tas!"

Sai hawaye shar! sharr!! Suka hau zarya a fuskarta, tace, "ka rufa min asiri, don Allah kayi hakuri. Wallahi ni ban harareka ba, in ma na harareka din cikin rashin sanine, don Allah kayi hakuri Abban Ammar!"

Tana ta magiyarta da neman hanyar guduwa shi tuni ya gama yin nisa a al'amuranshi. Yace, "kin ji ma Abban Ammar kike ce min kai tsaye, ba Angon Nadiya ba! Ai wallahi yau dai sai na amsa sunan nan!"

Daga wannan magana bai kara bata damar yin wata maganar ba, ya kara zafafa al'amuran nashi a gareta.
Da ta samu ya saki bakinta daya damka da nashi cikin yanayi na fitar hayyaci, sai ta bare baki ta hau kwala mishi ihu. Da taga abin ba kanta sai ta fara hadawa da bugu. Abin dai nashi yaki raguwa sai ma kara kaimi da yake. Idanunta suka gama raina fata, ta saki wani irin kuka mai cike da tashin hankali da wata azaba ta musamman da taji tana ratsata.

Sai ga ta ta hau kiran su Madam da Mama, a je a ceceta Habibu zai kasheta. Shi ai bai ma san kalar wainar da take toyawa ba.
Ta yi Ala-wadai da yar??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da da maganganun Anty Lima da tayi, da take ce mata wai ai idan budurwa ta jima bata yi aure ba fatar budircinta na budewa ne ta yadda ba zata ji zafi ba sosai a first night dinta. Ashe duk kanzon kuregene? Ita kuma ta hau kan magana ta zauna daram, a ganinta bulis zata ci. Ashe Habibu shi zai kwashi bagas! Gashi nan yanzu yana bambance mata tsakanin aya da tsakuwa.

Lokacin da yaji shi da kanshi yana neman wuce makadi da rawa, ya dakata, saboda tausayawa irin halin da yaga ta shiga ne na galabaita.
Ya lumshe idanu wani irin murmushi mai tattare da sanyi da salamar jiki data zuciya daya dade bai samu a tattare da shi ba kwance akan fuskarshi. A haka barci ya daukeshi mai nauyi. Ita kanta tana ta jan shessheka da auna mishi harara barcin yayi awon gaba da ita bata ankara ba.

Kiran sallar la'asar ya katse mishi barcin, ya tashi da sauri yana duba agogo. Allah Ya taimakeshi ranar baya da wani abu mai muhimmanci da yammacin, da lallai ya makara.
Ya juya yana kallon yadda ta kanannade a cikin bargo ta rufa gabadayanta, fuskarta ce kadai a waje. Barci take a nutse tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ga sawun hawaye nan a fuskarta da suka bushe.
Yayi murmushi a tausashe yana girgiza kai, tunano irin rigimar daya san za su kwasa idan ta tashi. Ya lallaba ya shiga bayi cikin taka-tsantsan din kada ya tasheta. A gurguje yayi abinda zai yi ya fita.

Lema-lema da sanyin ruwa da ta dinga ji a fuskarta ya sanya ta fara bude idanunta a hankali da suka yi mata nauyi.
Suka yi face-to-face da shi, ya duka a kasan gadon yana kallonta.

Wata irin kwalla ta ciko mata ido a take, ta mele baki da fuska tana shirin fara kuka, yayi saurin tashi tsaye yana kokarin boye dariyar data ciwo shi. Yace mata, "Masallaci zan je. Ga ruwa can a bayi na hada miki kiyi sauri ki yi wanka kafin ya huce."
Ya bar dakin cikin sauri kafin ta kai ga mayar mishi da amsa.

Sai data jima tana kara jinjina abinda ya faru a cikin ranta kafin ta tashi a hankali, ta lallaba da kyar ta shiga bandakin.

Ta fito tayi sallah ta gama. Yunwa take ji matuka har wani jiri-jiri take gani. Ta samu riga doguwa marar nauyi ta sanya. Ta fita falon tana jin jikinta babu karfi ko kadan. Tafiyar kanta sai take nema ta zame mata wani aiki na daban.

Sai ta sameshi already a falon, ya zuba dambun nan cike da faranti da farfesun kazar nan a gabanshi yana ta aikin durawa a ciki babu kakkautawa.
Haushinshi kifi da kifi ya lullubeta. Ji tayi kamar ta kwace kwanon hannunshi ta hanashi cin abincin. Ta dai daurewa ranta bata aikata hakan ba, ta wuce kicin itama. Yace mata, "zo nan mu ci wannan da na zuba mana? Idan mun cinye sai ki karo."
Tayi kunnen uwar shegu dashi.

Anan cikin kicin din ta zauna ta ci kayanta don tsakaninta da Allah ko ganinshi ma bata son yi.
Tana cikin cin abincin ya shiga da empty plates, ya ajiyesu a cikin sink. Ya daga firjin ya tsiyaya kunun aya ya kafa kai yana sha har da wani lumshe idanu. Harara kawai take jefa mishi, karaf suka hada ido da shi lokacin daya juya.

Yayi murmushi yana ajiye kofin hannunshi, "wato harara ta ma kike yi ko? Lallai ma ashe ban gama goge rainin da kika yi mun ba har yanzu. Da alama ina da sauran aiki kenan."

Ganin yana nufarta gadan-gadan sai ta mike tsaye sukwane tana shirin tserewa. Shi kuwa me zai yi in ba dariya ba?
Yace, "farar kura! Ga tsoro ga ban tsoro. Dawo ki ci abincinki babu abinda zan miki. Lokacin da zan damkeki a hannuna Allah na tuba ai you wouldn't even see it coming. Besides, ke din ai amaryace da bata laifi. Don kin harareni ai ba wani abu bane!"

Ta koma ta zauna din a darare, amma ta kasa sakin jiki ta ci abincin yadda ya kamata. Saboda ya sanyata a gaba yayi kikam, sai taji duk ta takura.
Ta kalleshi a kaikaice tace mishi, "ni fa gaskiya ban cika son ina cin abinci ba ana kallona. Ai sai ka sa in shake!"

Bai ce mata komi ba, taga yayi hanyar fita kamar tafiyar zai yi. Kafin ta sakankance ta ji ta a cikin jikinshi ya rungumota ta baya.
Ya lalubi kunnenta yana rada mata, "madallah da ke Nadiya. You've made my day! Allah Yayi miki albarka, Allah Yasa munyi dacen samun yan biyu..." da wasu zantukan da suka yiwa kunnuwan nata nauyin ji.
Ita dai tayi turus a zaune tana sauraronshi har ya gama fadin abinda zai fada, ya juya ya fita yana fada mata wajen tafsir da ake yi na yammaci a Masallacin dake makale da gidansu zai je.

Ita dai bata samu sakewa ba sai data ji da gaske din ya fita, sannan ta saki ajiyar zuciya. Ta zauna ta ci abincin sosai da sosai.
Data gama ta hade kwanukan ta wankesu duka. Sauran dambun da suka rage kuma ta barshi a cikin kular tunda dama ba wani na azo a gani ne tayi ba, wanda za ta ci da wanda zata kaiwa Ummah kawai ne. To kuma ga shi Habibun nata ya bi ta kanshi.

Sauran yammacin ranar a kwance tayi shi tana jinyar jikinta. Don kuwa sai a lokacin ma take gane kalar ta'asar da Habibun yayi mata ashe ba karama bace. Ko motsin kirki tayi sai taji a jikinta.
Sai can wajen Magriba sannan taji dawowar Ummah. Amma bata shiga bangaren nata ba sai da aka yi sallar isha'i.

Data shiga tayi mata barka da zuwa, sai ta ja Ammar gefe suka zauna tana tayashi yin assignment kamar yanda ta saba. Ta kula yaron yana da rauni sosai ta bangaren lissafi, haka kuma fannin addini ma yana da mas'aloli da dama. Ganin kuma babu wani tsayayye dake bibiyar lamuran makarantar tashi yasa ita ta azawa kanta wannan nauyin. Tana taimaka mishi da spelling, da kira'a, har ma da haddar abubuwan da ake yi musu a duka Islamiya da makarantar boko. Da suka gama suka cigaba da kallon Fina-finan yara da ake nunawa a tashar Mbc 3.

Kasancewar cikinta a cike yake tun bayan dambun da ta ci, bata ma tunkari teburin cin abincin ba.
Tana nan Shukurah itama ta shiga falon, ta zauna a dan nesa dasu kusa da Hajiya Ummah. Magana take mata kasa-kasa duk don kada Nadiya din taji me suke cewa, ta tabe baki a kaikaice ta kara dauke kanta daga garesu don kuwa itama ba son jin abinda suke cewa take yi ba.

Kamar ba zata gaisheta ba, daga karshe dai ta daga baki da kyar ta gaidata din, itama ta amsa a fuzge kamar wadda aka takurawa. Tasan ganin idon Ummah ne yasa ma ta amsa.

Wajajen karfe tara ta musu sai da safe ta koma bangarenta. Sauran farfesun data rage ta cinye da kunun aya. Ta shiga bayi ta watsa ruwa kafin tayi shirin barci cikin pyjamas masu dan nauyi pink masu digon fari a jiki. Hadari ne a garin sosai ta san ba dadewa ruwa zai sauka.

Sai da taje ta kulle sashenta kafin ta kwanta saboda kada Habibu ya mamayeta irin na dazu.
Ila kuwa tana kwanciya ba jimawa, aka tsage da ruwa kamar da bakin kwarya. Ta kara shigewa cikin bargo barci mai dadi yayi awon gaba da ita.

Kamar cikin mafarki kuma ta dinga jin wani abu na faruwa da jikinta. Ta fara bude idanu cike da magagin barci, tana kokarin fahimtar me ke faruwa.
Fahimtar da tayi mutum ne kwance kusa da ita yana mata wasu abubuwa yasa tayi baya tana kare jikinta da sai lokacin ta fahimci ashe babu kaya a jiki.

Ya kai hannu yana kokarin kamota, ta fashe da kuka tun karfinta. Ita ta ma rasa ta yadda aka yi har ya bude dakin nata ya shiga.
Tace, "kasan Allah ka tashi ka fita ka kyaleni. Haba wannan wane irin abu ne haka? Ba za a bar mutum ya huta bane?"

Kallonta yake yi kasa-kasa, "Nadiya dama akwai hutu a cikin rayuwar aure ne?"
Tace, "ban sani ba! Ni dai wallahi ko ka fitar min anan, ko ni in fita. Amma wallahi ba zan iya ba!"

Ganin yadda ta hakikance tana kuka bilhakki, yasa ya dauki kayanta ya mika mata, yace, "to naji, shikenan. Yi hakuri ki daina kukan."

Ta amsa cikin sauri ta sanya, ta tsaya tana kallonshi cikin alamun rashin yarda.
Ya kwanta tare da tapping din kusa da shi, yace, "taho ki kwanta kin ji? I promise babu abinda zan miki. For now."

Duk da haka dai kasa yarda dashi tayi din. Shi kuwa ganin haka sai ya juya mata baya yayi kwanciyarshi.
Ita kam sai da ta jima sosai a hakan, ta tabbatar da yayi barcin sannan ta silala kamar barauniya ta kwanta. Gunaguni take yi kasa-kasa, duk bata san lamo yayi mata ba sai da Asubahi tayi yaje yayi sallah ya dawo. Yayi ram da ita yana neman sake maimaita yar gidan jiya. Ta hau magiya da rokon ya daga mata kafa, yace, "a'ah, ba kin ce na dameki da kwarzaba da bita zaizai ba? Ai baki ga komi ba ma Nadiya, don kuwa ko farawa ma ban yi ba."

Tace, "to kayi hakuri ka bari in gama warkewa tukun. Wallahi bana jin dadi ko kadan."
Yace mata, "muna da magunguna ai a gidan."
Bai kuma kara barin ta furta wani abu ba sai daya karasa gudanar da abinda ya kudurta sannan.


32.


Cikin yan kwanakin amarcinsu suke ci ka-in da na-in, ko kuwa tace Habibu amarcinshi yake ci babu kakkautawa. Don kuwa tana ganin kwarzaba da bita-zai-zai din da yace mata zata gani, sai daya zamana har bata son girkinta ya juyo kanta ko kadan. Idan kuwa ta ganshi har wani faduwar gaba take ji tana ziyartarta.
Babu yadda baya yi da ita akan ta saki jiki, amma wannan din ya gagareta.

Wannan sabon kusancin da suka yi yasa ta kara fahimtar ainihin wanene Habibu Abdullahi Makama, Babangidan Hajiya Ummah.
Bawa ne ga duk abinda yake so da kauna, mai fahimta ga abinda baya ma kauna. Yana da kyautatawa da son kyauta ba kuma don a gani a yaba ba. Ga matanshi da Iyalanshi, mutum ne mai taka-tsantsan da gudun bacin ransu. Mutum ne mai saka alkhairi da alkhairi, sharri ma a wajen Habibu da alkhairin yake maidashi. Bakin kokarinshi yana yi don ganin ya kyautata musu, yana musu uziri a duk al'amuransu, haka yana da fahimta. Lokuta da dama idan suna tare da Nadiya ya kan maida kanshi kamar wani karamin yaro ne ko matashi, baya da girman kai kuma baya cikin mutane masu amfani da ikon dake kansu don su hanawa matansu motsin kirki. Abu daya da Nadiya ta fahimta a tare da shi shine wannan abu daya da bata so, zai iya hakuri akan komi ma, zai kuma yi uziri da fahimta, amma fa yau yace mata zo gyara shimfida tace a'a, anan ne kam take ganin rashin uziri da fahimta. Don kuwa baya mata wannan hakurin.

Shi yasa ma wani lokacin sauran kawaicin nashi baya burgeta.
Haka tsananin biyayyar da yake yiwa Ummah wani lokacin har tsoro take bawa Nadiya, saboda baya taba iya ce mata a'ah a duk wani umarni da zata bashi. Haka yana matukar kambama abubuwanta da yin taka tsantsan wajen gudun bacin ranta. Tana lura da yadda yake ta boye-boye da kokarin kada abinda ke tsakaninsu ya bayyana a wajen Ummah din. Saboda da aka kwana biyu ma sai ya zamana baya shiga bangarenta ranar girkinta sai can cikin dare ko kuma tunda Asubahi. Sai dai a ranta tasan da kyar idan Ummah bata gama ramfoshi ba a yadda dai idanunta suke a kansu a kodayaushe kamar wata mikiya.

Tun karon farko daya fita daga dakin Shukurah ya koma nata, ya sameta da rana a bangarenta da zancen ta bashi abincin rana. Ta kalli plate kwaya daya tal da ta yi roasted macaroni don ta ci, tace mishi bata dafa da shi ba.
Ya dauke plate din tana kallonshi ya tadashi a gabanta, ya gama ya kora da ruwa ya tashi tana kallonta, yace, "banda ma rashin kara irin naki, ranar girkin naki ma sai na dinga rokonki da barar kiyi mun abinci kenan? Idan kin ga dama ma gobe kada ki sa girkin da ni!" ya fita ya barta anan.
Tun daga nan ita kuma ta kan zauna ta tsara girki mai rai da lafiya ta ajiye mishi ranar girkinta da rana.

Daya dauko hanyar ranar girkin Shukurah ya je da rana yace wai ta bashi abinci, sai tayi saurin taka mishi burki tun kafin hakan ya kai ga kara janyo mata bakin jini a wajen Ummahn da Shukurah. Don kuwa ta kula hatta da abincin ranar da yake ci a bangarenta su dukansu ba son hakan suke yi ba.

Wani hali nashi dake kara burgeta shine yadda baya da halayyar korafin wata a wajen wata. Duk yadda Shukurah zata bata mishi rai, koda wasa bai taba yiwa Nadiya korafin hakan a wajenta ba. Hasalima kullum kokarin boye wata baraka ko matsala dake faruwa a tsakaninsu da Shukurah din yake yi. Hakan ita kuma sai yake kwantar mata da hankali, tunda tasan ba zai taba kai maganarta wajen abokiyar zamanta ba.

A haka kuma sai ta fahimci wani abu, zama a matsayin matar Habibu abu ne mai dadi da kuma wahala a lokaci daya.
Dadi saboda duk macen data samu miji kamar Habibu dai, to ta huta. Mutum ne mai saukin kai da tarin alkhairori, haka kuma yana matukar kokari wajen sauke nauyin iyalinshi daya rataya a kanshi.
Wuyarshi kuma shine ba kowace mace bace zata iya hakurin barin wadannan halaye nashi ya dinga rabasu a tsakaninshi da wata ba. A bangarensu kam, har Ummah ta shiga ciki. Tunda kuwa babu abinda yake zartarwa ba tare da hukuncinta ba. A gefen Nadiya kuma, ta kula Ummah din duk wani kokari nata, to shine na ganin bai kyautatawa Nadiya ba. Wadannan abubuwa dama wasu, suka sa dole sai data kara koyawa ranta hakuri da kawaici da kawar da kai akan wasu al'amuran. Saboda tasan idan tace akan komi sai tayi magana, ba lallai hakan ya haifar musu da da mai ido ba.

Ta cinye wata guda a hakan, tana so taje gida ta gaidasu amma fir hakan ya ki ya yiwu. Duk lokacin da tace tana so taje gida sai yace mata ta dan dakata, ba zai kara yi mata maganar ba kuma sai ta sake mishi. Daga baya ta gano umarnin Hajiya Ummah yake jira, don kuwa ta taba tsintar hirar tasu bisa kuskure inda taji Ummah din na mitar, 'ita Nadiya din me zata je yi ne a gidan nasu yanzu? Me ake yi? Ita fa bata son yawace-yawace marasa kan gado!'
Taga wani irin yawo ne a cikin zuwa ganin danginka? Tunda ga Shukurah nan ita ba zaman gidan take yi ba, babu ruwanta ma ita fita sai ta gama shirinta sannan take sanar da ita. Akwai lokuta da dama ma sai dai kawai ta fadawa Ummah din zata fita, Nadiya bata tunanin tana fadawa Habibun, amma da wasa bata taba jin Ummah tayi mata fadan yawo ba. Sai ita? Akan wane dalili? Me tayi mata? Don haka ta bar maganar fita ta hakura.

Iyaka tunani ita dai tayi akan ta gano menene wai ta yiwa Hajiya Ummah haka? Amma ta kasa gano dalili. Don haka sai ta kudirci wata aniya a ranta, ita zata kyautata, ba zata gaji ba kuma har sai ta ga abinda ya turewa buzu nadi. Hajiya Ummah za tayi ta shareta da kokarin hanata rabar jikinta, amma ba zata bata wannan damar ba.

Kullum idan tayi abincin rana to sai ta sanya da Hajiya Ummah ta kai mata nata, bata taba tsayawa ta ga ta ci ko bata ci ba, ita dai aikinta ta hada girki mai kyau mai cike da ganyayyaki na karin lafiya, hadin abinci kuma ya zamana irin wadannan tsofi zasu ji dadinshi ne sosai.
Haka kuma idan taje sashen nata ta kan yi mata gyare-gyare da goge-gogen falo da falon sama duk da cewa akwai masu yi, kuma itama Ummah din tana hanata amma bata bari ba.

Yau ba ita ke da girki ba. Zaman kadaici ya fara isarta da takurata, kwarai take bukatar fita ko yaya ne ko don ta samu ta ga gari. Bata saba zama a gida har haka ba, musamman wajen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login