Showing 54001 words to 57000 words out of 142169 words

Chapter 19 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

449

gama shirin barci.

Ta haye gadon kai tsaye ba tare data tankashi ba, ta fara kokarin jan bargo ta rufa. Ya bita da kallo ranshi yana kara baci, yana kokarin dannewa.
Kawai ya kai hannu ya warci bargon yayi jifa dashi. Ya bita da kallo fuskar nan a hade, yace, "bar ganin wai ina binki kiyi zaton wannan guntun fushin da kike yi yana damuna ne Shukurah. Kawai ina kokarin sauke hakkinki ne dake kaina, tunda naga ke baki san sauke nawa hakkin dake kanki ba. Don zan kara aure shikenan sai in zama makiyi a wajenki, dama ana hakane Iye? To idan zaki sanyayawa ranki ki hakura, kiyi hakan. Idan kuma ba zaki iya ba, sai kije kiyi tayi. Aure dai ba zan fasa yi ba, ina ga ita kanta Ummah ai ta fada miki hakan ko? Ni dai kam ta bangarena, ba zan zauna ina bin kanki ba kamar yadda take yi. Jibi zan tafi Umarah kamar yadda kika ji ana fadi, kuma ba zan dawo ba har sai bayan sallah. Don haka ki zana min duk abubuwan da kike bukata inji, id??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an kuma har yanzu kina ganin bani da wannan matsayin a wajenki, sai ki fadawa Ummah."

Ya tashi tsaye yana kallonta, tayi zaune tana hararar waje daya idanunta sunyi rau-rau kamar zata yi kuka. Ganin ita yake kallo yasa ta daga baki da kyar tace mishi, "ni ba na bukatar komi!"
Ya tabe baki yace, "ba laifi!" ya juya abinshi.

Har ya kai bakin kofa yana kokarin budewa, ya ji an rungumoshi ta baya. Kawai sai ta fashe mishi da wani irin kuka mai sanyaya jiki. Tayi-tayi har ya isheta, bayan rigarshi ya jike da lema.

Yana da tausasawa, kuma in ta shi ne, mace ba zata yi kuka a gaban idonshi ba. Ko me yake ganin zai yi, zai yi kokarin yi wajen ganin hawaye bai kusanci idon kowace ya mace ba, balle matar da yake aure. Ya kuma san sanin hakan da tayi ne yasa take mishi kukan, bata san ko hawayenta karewa zasu yi ba akan maganar wannan sai dai su kare, amma ba zai fasa auren wannan ba. Ko ba don Ummah da burikanta ba, ko ba don sanin manufar wannan aure ba, to don kanshi kawai, ba zai iya fasa wannan auren ba.

Ya sanya hannu ya zagaya da ita gabanshi suna fuskantar juna. Abinka ga farar mace, fuskarta har tayi ja na kukan da tayi. Ya fara share mata hawayen idanunta yana kokarin tausarta, ta kama hannunshi ta rike kam, hawaye na kara cika idanunta.
"Honey, ba zan iya hadaka da wata ba, ba zan iya rabaka da wata ba, ba zan iya zuba ido in ga kana kulawa da wata kamar yadda kake kulawa da ni ba. Me nene bana maka? Menene baka so a tattare da ni? Zan iya canzawa, zan iya gyarawa. Don Allah Honey...!"
Sai ta sake rushewa da wani kukan tana kara rirrike mishi gaban riga.

Ya kama hannunta ya ja har zuwa bakin gado, suka zauna su duka.
Yace, "wai har sau nawa ne kike so in fada miki cewa babu ko daya daga cikin wadannan abubuwan? Ko baki ji me Ummah tace miki bane ranar nan wai? Ba tace miki kiyi hakuri ba? Me yasa wai ba zaki iya hakuri ki yarda da kaddara bane? Ina ce matan ma bayan ke an halatta min har guda uku matukar zan iya yin adalci? Kuma ina da yakinin zan iya daidaita adalcin. Me yasa ba zaki yarda da maganar Umma ba at least, idan baki yarda da maganata ba?"
Sai tayi shiru tana shessheka. Tace, "to naji, amma kayi min alkawarin koda ta zo, ba zaka taba daukar soyayyarka ka bata ba!"

Ya saki wani dan murmushi yana kare mata kallo, "kin taba jin irin wannan auren ne dama Shukurah?"

Taga dai kwata-kwata abinda take son samu ba zata sameshi ba, sai ta juya mishi ta wani bangaren. Tasan ta wannan bangaren, ba zai taba iya ce mata a'ah ba. Tunda sau nawa take cimma bukatunta ta wannan hanyar?
Ta fada jikinshi tana sanya hannunta cikin rigarshi inda boturan basu gama rufewa ba, ta fara yawo da hannun cikin salo na daukar hankali da kissa. Nan da nan kuma sai ta samo kanshi, abinka da mai neman kuka aka jefeshi da kashin awaki.
Sai data bari yayi nisa a can duniyar data kaishi, jikinshi ya gama dauka gabadaya har wani bari yake yi, sai kawai ta janye jikinta, ta ja bargo tana rufe jikinta.

Ya zuba mata idanu da suka shige ciki, suka fara rinewa cikin wani irin yanayi, bacin rai yasa ya ma kasa yi mata magana. Ta kalleshi tana yin wani takwa-takwa da fuska, "ni dai gaskiya ba zan iya hada jikina da naka ba bayan nasan cewa nan gaba kadan zaka taba jikin wata. Kayi min alkawarin jikinka ya zama nawa ni kadai, kayi min alkawarin ba zaka mallaka mata jikinka ba, ni kuma na maka alkawarin mallaka maka nawa jikin."

Ya lumshe idanu zuciyarshi na wani zafi, jikinshi ma kokarin daukar zafin yake yi. Lokaci mai tsayi ya dauka a haka, kafin ya tashi zaune ya dauki kayanshi da suka yi fatali da su ya sanya, kafin ya kalleta da idanunshi da suka yi mici-mici.
Yace, "mantawa kike yi, cewa daga lokacin dana bada sadakinki kuma shaidu suka shaida aurenmu, jikinki ya gama zama nawa. Zan kuma iya yin duk abinda nake so da shi a duk lokacin da naga dama, ke kanki baki isa ki hana ni ba. Don haka ki daina mistaking cewa kina da ikon hanani, bana son tursasa mutum, ba kuma zan kusanceki alhalin baki so ba shi yasa kika ga nake binki a hankali. A hakan kike so in miki alkawarin ba zan kusanci wata matar bayan ke ba? A hakan Shukurah? Kina hanani hakkin nawa a lokacin da nake so? Kina wancakali da duk wani lamari nawa kamar ba mijinki ba? Kina amfani da abinda yake hakkina ne kina blackmailing dina da sanyani yin abinda ban yi niyya ba bayan Allah ne Ya halasta min? A hakan Shukurah?!"

Kawai ya juya ya bar mata dakin. Saboda yasan idan ya cigaba da magana ma ranshi ne zai kara baci. Bai san ma ya aka yi har ya biye mata ba, bayan dama zuciyarshi sai data dinga mishi saka da wasi-wasin kada ya biye mata ya afka cikin dana sani.

Ya tura kofar dakinshi a zafafe ya shiga, kai tsaye bandaki ya fada ya sakarwa kanshi ruwan sanyi. Yayi shiru yana sauke wata irin ajiyar zuciya mai matukar nauyi. Ranshi ya kara dagulewa. Shekaru uku kenan tun bayan aurenshi da Shukurah. Har yau yana iya tuna lokacin da Ummah take fada mishi cewa ta samar mishi wata matar bayan da suka gama gano cewa wadda yake gab da aure ba son Allah da Annabi take mishi ba. Shi kuma ya amshi auren a take, ba tare da musu ba. Aka kuma daura auren cikin abinda bai gaza wata daya ba. Ita kanta Matar sau biyu kadai ya ganta kafin bikin nasu. A kuma duk ganin da zai mata, bai ga bambancinta da wadda suka rabu ba. Su duka arzikinshi da rayuwar dadi da zai samar musu suke so, ba shi a karan kanshi ba.

Lokuta da dama kuma yana zama ya tuhumi kanshi, me yasa bai ce a'ah ba? Me yasa bai ce a'ah ba?

Ya jima sosai a cikin bayin kafin ya fita, ya sake kimtsawa kafin ya kashe wuta ya lalubi gado. Har zuwa lokacin ranshi a jagule yake. Jikinshi kuma ya mutu murus. Yayinda a can kasan zuciyarshi wani sashe yake tambayarshi, 'me yasa wannan karon bai ce a'ah ba? Me yasa ba zai ce a'ah ba?'

23.


Washegari da yamma, ya shiga sashen Ummah sanye cikin dakakkiyar shadda fara, yana ta baza kamshin nan nashi.
Falon nata tuni ya gama rikicewa da kamshin kala-kalan abincin buda baki da ake hadawa.

Ummah ta kalleshi cike da mamaki, "ina zuwa ne haka Babangida da wannan yammaci?"
Yayi dan murmushi yana gyara zaman hular dake kanshi, "wai wata yar unguwa ce zan leka amma yanzun nan zan dawo."

Ta kalleshi cike da mamaki, "unguwa kuwa da wannan yammaci Babangida, ana gab da shan ruwa?"
Yace, "ehh. Abin gobe zan tafi, Matar abokina Mus'ab ta haihu shi yasa nace zan je in gano baby saboda da dare ina da wata tattaunawa da su Kawu Haruna to ba lallai in samu zuwa ba!"
Sai ta gyada kai cikin alamun gamsuwa, ta san shi da son yara sarai, duk inda yaji anyi haihuwa, to shi kuwa a tafe yake yaje ya ga baby. Baya da wannan kasa a gwiwa din.
Tace "to a dawo lafiya. Kayi kokari dai ka dawo da wuri kafin lokacin shan ruwan ya kure."
Ya amsa mata da, "to Ummah"
Ya fita.

A bakin kofa suka ci karo da Shukurah ita kuma zata shiga. Tana ganinshi ta wani dauke kai kamar bata ganshi ba. Shi kuwa ya ratsa ta gefenta ya wuce shima bai nuna alamun ya ganta ba.

Mota daya ya dauka, kuma shi kadai. Koda direba ya taso da securities dinshi biyu, sai yace musu su yi zamansu kawai saboda ba jimawa zai yi ba.
Aka bude mishi gate ya fita, kai tsaye ya dauki hanyar 'Diamond Ara Cakes and Snacks'
m
Farfajiyar wajen babu komi idan ka dauke ababen hawan ma'aikatan wajen. Yayi parking din motarshi, ya dakata daga ciki bai fita ba ganinta da yayi tana kokarin fitowa daga shagon.
Abaya ce a jikinta ruwan zuma da aka yiwa adon furanni ruwan madara. Tayi nadin gyalen a fuskarta inda ya fitar mata da fuskarta tayi round, kumatunta da lebunanta da suke a cike suka mayar da ita kamar wata Balarabiyar kasar Oman.

Ya kara gyara zamanshi yana kallonta, yadda take tafiya a nutse, hannunta daya dafe da wayarta a kunne tana kyalkyala dariya. Komi na Nadiya ya mishi. Bai san ta yaya, ko a wane lokaci Nadiyar tayi mishi irin wannan kamu na kazar kuku ba.

Ya bude murfin motar ganin tana kokarin wuceshi. Kawai ganin mutum tayi a gabanta sai kace wanda ya dira daga sama.

Tayi baya da sauri hannu dafe da kirjinta saboda yanda ya tsoratata. Da ta fahimci ko waye yayi mata wannan aika-aikar, sai ta ja fuska kawai tayi kokarin bi t gefenshi ta wuce, shi kuma yayi saurin sake shan gabanta. Ta sake juyawa ta daya bangaren, nan ma ya sake binta.
Sai ta cewa Rabi'ah da suke waya da ita, "zan sake kiranki Rabi'ah!"

Ta kashe wayar, shi kuma ta bi shi da wani irin kallo cike da kufula, tace, "lafiya?"
Ya langabar da kai gefe daya, "don Miji ya zo gaishe da Matarshi dama hakan ya taba zama laifi ne da za a ke tambayarshi lafiya?"

Ta ga idan tace ma zata tsaya bashi amsa rai kawai zai bata mata a banza, sai ta kankance idanu tace mishi, "ba ni hanya in wuce to!"
Yayi wani irin murmushi, "ko kuma ki shige mota mu tafi ko?!"

Ta ma rasa me zata ce mishi. Wannan abu na Habibun Hajiya Ummah nema yake yi ya wuce misali. Ta rasa ta ina zata bullo mishi kuma. Mutum a dinga yakiceka amma kana bin mutane sai kace wani guntun cingam?

Tace, "Malam ka bani hanya in wuce wallahi ko in tara maka jama'a a wajen nan!"
Yace, "kafin mu kai ga hakan ma zaki shige mota mu tafi..."
Ta daga baki zata mishi musu, ya hade fuska, "I am not asking Nadiya. Ki wuce muje kawai kafin in miki abinda ke zai tara miki jama'a anan wajen!"

Akwai wani abu can cikin idanunshi data hanga dake nuna mata cewa da gasken gaske yake, ba kamar ita dake cika baki ba da ban tsoro, shi kam idan ta kai ga hakan, zai aikata abinda yace din ba tare da bata lokaci ba.

Ta daga kafa ta nufi wajen motar tashi as if in a trance, kamar wadda wani maganadisu yake ja. Yayi murmushi cike da samun nasara, ya wuce ya bude mata gaban motar da kanshi ta shiga, ya mayar ya rufe.
Ya zagaya ya shiga, ba tare da bata lokaci ba ya ja motar suka dauki hanya.

Tuki yake yi cike da kwarewa da natsuwa a tattare dashi. Ta kurawa waje daya idanu tana kallo tun bayan shigarta motar. Shima kuma da yake tunda ya fara tukin bai sake nemanta da wani zancen ba sai abin yafi yi mata sauki.
Ya kaita har kofar gidansu yayi fakin. Ta bude motar ta fita abinta babu ko godi bare na gode. Tana jin lokacin da shima ya bude bangaren da yake ya fita, ya kira sunanta da wata irin murya mai sanyi da taushi data sanya ta dakata da tafiyar da take yi ta juya tana kallonshi ba tare da zuciyarta da gangar jikinta sun gama aminta da hakan ba.

Yace mata, "Gobe zan wuce Umarah, ba zan samu ko addu'ar Allah kiyaye bane a wajenki Nadiya?"
Tace, "idan kaje don Allah ka roka min Allah Ya yaye min wannan kidagar auren da aka kakaba min, ya koma kan mai so!"
Maimakon abin ya bata mishi rai kamar yadda taso, sai ma hakan ya bashi dariya. Yayi dan murmushi yace, "zan dai yi addu'ar Allah Ya baki ikon fito da wannan son nawa dake makale a cikin zuciyarki kina kokarin boyewa. Ya kuma kakaba miki son nawa ya zamana idan zan yi tafiya irin haka ba zaki taba iya jurewa ba!"

Tayi wani irin murmushi na bacin rai, tace, "son ka kuma? You wish!" Ta wuce gida abinta.
Shi kuwa har da komawa ya jingina da motarshi yana kara kallonta har ta shige gidan. Yayi ajiyar zuciya a hankali yana furzo da wani numfashin daga bakinshi.
Yara biyu matasa ya samu ya bude musu booth din motarshi yace su kwashi kayan su shigarwa Nadiya da su. Ya sallamesu kafin ya ja motarshi yayi gaba kafin ma su gama shigewa gidan don yasan kadan daga aikin Nadiya ne ta sanya su yo kwana da kayan nan.

Tuki yake yi wannan karon cike da tunani da sake-sake har ya karasa gida. A ranshi tunani yake ko ya Hajiya Umma zata ce idan taji cewa saboda Nadiya kadai ya daga tafiyar daya kamata ace yayi ta a yau? Da yanzu ya gama shan ruwa a Makkah. Amma idan ya tuna Nadiya, da yadda suka rabu da ita, sai ya tsinci kanshi da yin murmushi. Shi yasan ba zai taba damuwa ba idan ya kara daga tafiyar tashi ta yan kwanaki, batawa Nadiya rai da ganin tsiwar nan tata ma kadai sun isheshi debe kewa.

Tana ganin yara suna ajiye katan-katan din Maltina da madara peak ta ruwa da tarkacen kayan shayi har da su crates din kwai, duk kuma wai inji Habib, ta zabura tace musu su wuce su mayar mishi da kayanshi. AbdulBaqi yace mata ai tuni daya riga ya tafi. Ta rufe ido ta fara zazzaga musu masifar me yasa to suka amso kayan tun a farko? Tace musu tana bukata ne? Suka yi tsuru-tsuru a tsaye suka kasa gaba ko baya. Mama data ga haka tace musu su ajiye kayan anan. Ta dauki dari biyar ta basu, su kuwa suka ce mata ai tuni daya sallamesu suka wuce.

Ta kalli Nadiya da take jefawa kayan harara kamar su ne suka aikata mata laifin. Tace mata "sai ki dauke kayan ki kai daki ko?"
Ta wani turo baki gaba. Da kamar ba zata dauka din ba, sai kuma ta kira Amina suka fara jidar kayan suna kaiwa dakin.
Mama ta kalli yanda take ta guna-guni da bata fuska, tace, "Allah Ya kyauta miki Nadiya wallahi. Zan so in ga wannan zaman aure naki!"

Amarya dake aikin dama kokon da za a sha ruwa da shi tayi dariya, tace, "Mama ki kyale diyar nan taki da zurfin ciki, tana son kayanta ne kuma tana kaiwa kasuwa. Muna nan dake tsit zaki ji ta idan aka yi auren, ko motsinta ba zaki dinga ji ba. Watakila ma sai kin dinga nemanta da kanki ma sannan!"
Nadiya dake jinsu tayi caraf tace, "tab! Allah Ya tsareni wallahi!"
Mama da Amarya kam me zasu mata idan ba dariya ba?

Da aka nunawa Abba kayan da aka kai mata kuwa cewa yayi a kaisu dakinshi, haka aka sake jidarsu aka kai mishi. Ya dauki Maltinar nan da madara da ruwan gora ya kai kuryar daki ya ajiye, kwai yace matan su raba kowa ta dinga soyawa ita da 'ya'yanta idan an sha ruwa. Kayan shayin kuma yace a ba Nadiya ta dinga hada shayi tunda dama ma'abociyar shan shayin ce.
Daga fari ma da cewa tayi su Mama su raba ita da Amarya, sai da Mama din ta rufe idanu ta manna mata shirme sannan ta amshi kayan.

Washegari tana shago, ta dan bude datar wayarta tana duba halin da duniya ke ciki kafin su fara aiki.
A WhatsApp dinta ta kula wata sabuwar lamba ta tura mata sako. Ta bude cike da mamakin ko wanene? Sai ta ci karo da hoton mutumin nata, yana sauka daga jirgi. Yayi shigar wata bakar jallabiya wadda ta haska shi, gashin kanshi da sajenshi sun kwanta luf-luf gwanin sha'awa, ya dora farar hula a kanshi. A kasan hoton ya rubuta 'mun sauka lafiya. Nasan dai kina nan kina ta tunanina!'
Ta saki wani irin dogon tsaki har sai da Aramide ta juya ta kalleta tana tambayar lafiya? Ta girgiza kai.

Ta rasa abinda mutumin nan ke ji da yake da wannan confidence din. Ta fita daga WhatsApp din ma gabadaya. Tayi tunanin tayi blocking din lambar tashi ma gabadaya, sai kuma ta fasa daga baya.

Sai ta koma ta cikin messages ta zauna da kyau tana karanta dogon sakon da Abdullahi ya tura mata dazu da safe.
Sai jiya da dare sannan ta samu kwarin gwiwar kiranshi a waya ta sanar dashi abinda ake ciki tare da bashi hakuri. Saboda bata so yaji maganar a wani waje na daban. Ko babu komi sun yi alaka ta mutunci da shi, za kuma taso su rabu akan hakan.
Ya kuma saurareta da kunnuwan rahama, ya kuma nuna mata ya fahimta, ya kuma yarda da hukuncin Allah don haka ba shi data cewa. Hakan da yayi duk sai ya kara sanyaya mata gwiwa, har suka yi sallama dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login