Showing 102001 words to 105000 words out of 142169 words

Chapter 35 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

450

zaune. Ya kuma cika alkawari inda tana cika wata daya a gidan, yaje ya dauko Sumayyah da kanshi da kayanta duka, ya maida ita hannunsu da zama tare da sama mata transfer din makaranta zuwa wadda tafi kusa da gidansu.
Wannan abu shi ya kara rura wutar tsanarta a wajen Hadiza. Duk kuma yadda Ummah ta so da su zauna lafiya, abu ya gagara. Danta daya tilo dake gidan, bata bari ya rabeta. Haka bata bari Sumayyah ta rabesu. Don haka Ummah ta kama kanta, ta daina shiga harkarta amma tana bata girmanta a matsayinta na babba.

Anyi auren nasu babu jimawa Allah Ya dauke Nenne. Sunyi kuka kwarai da gaske, don kuwa sai a lokacin ne suka tabbata marayu na gaske. Don ma dai Abdullahi a tsaye yake a kansu tsayin-daka, daga ita har Sumayyah din.

Hadiza dai tana gefe daya, shiga da fita gidajen malaman tsubbu kawai take yi. Sai gashi ta fara nasara da cimma burinta. A sanyawa Abdullahin tsanar Ummah, ko ita taji ta tsaneshi, a sanya ya dinga wulakantasu, a sanya ya hanasu abinci, abubuwa dai iri-iri babu wanda basu gani ba. Amma da yake Ummah din mai kara ce da hakuri, ko iyayenshi basu taba sani ba. Ta dukufa da addu'a babu dare babu rana tana neman tsari.

Akwai ranar da Abdullahi ya shiga dakinta cikin dare yayi mata dukan tsiya, ya kuma ce ta hada kayanta ta bar mishi gidanshi a wannan dare. Ta ci kuka har ta gode Allah a wannan rana, tunanin ina zata nufa cikin tsakiyar daren wannan ita da Sumayya ya rufeta, amma dole zata tafi din. Don ba zata iya irin wannan zama ba.
Haka ta tashi jiki duk yayi tsami, daga ita har Sumayyan kuka suke yi, ta dauki hijabi kadai ta sanya da yan kudaden da yake bata tana taraw?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a. Ta gama kudirawa a ranta idan ta fita daga wannan gidan, to ita da Kaduna sai labari. Don kuwa garin ma zata bari kwata-kwata ta huta. Yadda kasan wadda ake tunzurawa ko ake ja, haka suka nufi kofa su duka zasu fita.

Tana kokarin bude kyauren gidan ta fita kuma sai taji ya biyosu a sukwane. Da fari tsorata tayi, tayi tunanin ko bugun nata zai sake yi ya karasata. Sai taji ya kamota ya rungume, ya hau bata hakuri da magiyar don Allah kada ta tafi tayi hakuri, bai san me ya hau kanshi ba har yayi mata wannan danyen aikin.
Da kyar da jibin goshi ya jata ya maidata dakinta don itama kakarewa tayi tace kawai ya kyaleta ta bi duniya, abinda bata taba yi mishi ba kenan a tarihin aurensu wato musu.

Shi da kanshi ya hau kikiniyar dora tukunya a risho, ya dafa ruwan zafi yana gasa mata jiki. Ranar ita kuka, shi kuka haka suka kwana.
Tun kuma daga wannan rana ta dage da addu'o'i na kariya, da wanka maganin tsari irinsu ganyen magarya da kaikayi.


41.



Cikin ikon Allah kuma daga ranar ne suka sake daidaitawa ita da angon nata, suka koma tamkar tif da taya saboda tsananin kauna da kyakkyawar zamantakewa.
Suna cikin hakan kuma sai ga ciki ya bayyana a jikin Ummah. Wayyo, ina wuta in saka ki! Hadiza taji kamar ta shaketa ta mutu. Shi kuwa Abdullahi da Iyayenshi suna ta murnarsu, suka fara shirin karbar yaro ko yarinya.
Kulawa ta musamman suke bata kamar su dauketa su goyata. Babu abinda zata ce da iyayen Abdullahi a wannan lokaci sai godiya ga Allah kawai, domin kuwa sun rike amanarsu da suka dauka. Abdullahi ya zame mata mijin marainiya ita da Sumayyah.

Tunda cikin nan ya samu ita kuma Hadiza babu irin kokarin da bata yi ba don ta zubar dashi, amma fa abu ya gagara. Akwai ranar da ta dafa faten masara da wake yadda ta saba ci kusan kullum, ta barshi akan wuta ta shiga daki ta fito, ta juye fate a kwano ta sha. Shikenan jiki ya hautsine, ciki ya hau murdawa yadda kasan mai nakuda. Lokacin Abdullahin baya nan, Sumayyan kuma tana makaranta. Ta fito tsakar gida tana kuka rike da ciki, amma kiran duniya Hadiza tana jin ta a daki ta ki fitowa. Haka ta lallaba da kyar ta shiga makota, su ka tarairayeta aka nufi asibiti da ita. Likitoci suka hau kanta da kyar aka samu aka ceto abinda ke cikin. Suka ce akwai abinda ta ci wanda yayi yunkurin zubar mata da ciki, bata son doguwar magana da yin tashin-tashina, shi yasa bata ma fadi musu tana zargin wani abu ba. Shima Abdullahin da yaje sai kawai tace mishi ciwon ciki ne ba wani abu ba. Aka basu sallama da dokoki da aka kafa mata, suka koma gida.

Sai dai fa tun daga nan, ta kiyaye kanta da yin girki ta bari akan wuta ta fita. Musamman bayan hakan da kamar sati biyu data kama Hadiza din kiri-kiri tana zuba mata abu a cikin tukunyar miya data bari tana simmering ta dan zagaya bayi. Sai ta hau mata kame-kame da kokarin nade tabarmar kunya da bori. Bata ce mata komi ba, amma dai haka wannan miya ta zama haramiyarta. Wannan dalilin ne yasa ta dinga taka-tsantsan da duk abinda zata ci ko sha a wannan gida.

A haka cikinta ya dinga girma cikin kulawa da tattali. Kusan kullum Hadiza sai ta takaleta da fada, ta dinga yada mata kananun maganganu da habaici iri-iri, duk tayi kunnen uwar shegu da ita bata taba tankata ba. Don ta kula so take yi ta tanka din ta kai mata duka, motsi kadan sai tayi kamar zata kaiwa cikinta hari.

Cikinta ya fita wata na takwas, watarana da yammaci ta fito daga bayi tana tafiya da kyar. Duk ta kumbura, ga cikin nata ya fito sosai yayi mata kyau. Duk abinda yake tsone idon Hadiza kenan tana kara tsanarta da cikin jikinta.

Ta wuce Hadiza din zata shiga dakinta sai taji ta saki tsaki, tace, "matsiyaciyar kawai, mayya! Wadanda idan suka kama kurwar mazan mutane ba su saki. Ai wallahi sai nayi maganin dan iska anan gidan! An gama karuwanci wajen sai da abinci an yayimo cikin shege an likawa mijina don maita!"
Maganganun nata suka bata ran Ummah sosai, amma ta dakewa ranta bata tanka ba. Ta wuceta kamar kullum.

Kawai sai ji tayi an shakota ta baya, kafin ta ankare me ke faruwa taji an fara naushin cikinta ta ko'ina. Garin neman ta warci kanta tayi wani irin juyi, Hadiza kuma ta tunkudata. Sai gata ta fadi kasa yummm! akan ruwan cikinta.
Wata irin azaba ta ratsata da tunda take bata taba jin makamanciyarta ba, gabadaya kasa ko mosti tayi balle tayi ihu saboda yadda azabar ta fitar da ita daga hayyacinta. Jini ya tsinke mata a take, kamar an yanka rago.

Amma Hadiza bata sadara ba, sai ma gyara tsayuwa da tayi tana jiran ta ga ta tashi, ta kara mata da wani dukan.
Allah ne Ya jefoshi a dai-dai wannan lokaci, don kuwa yawanci sai dare yake komawa gida.

Ganin abinda yake faruwa yasa ya nufi kan Ummah cikin wani irin kidima da tashin hankali, musamman jinin da yaga yana malala daga jikinta.
Ya daga ido ya kalli Hadiza da bacin rai wanda bai fasaltuwa akan fuskarshi, "wallahi, Tallahi Hadiza. Idan wani abu ya samu da na ko matata, ki kuka da kanki. Ni kaina ban san irin hukuncin da zan dauka a kanki ba!"
Ya sungumeta yayi waje a sukwane.

Sabuwar mota da yayi awo tun daga Kwatano aka kawo mishi yau yaje ya amsa. Wannan ne musabbabin dawowarshi gida, ya dauki Iyalanshi a ciki ya zaga dasu su sanya mishi albarka. Sai kuma ya tarar da wannan tashin hankali. Haka ya sanyata a bayan mota, ya fuzgi mota a sukwane yayi asibiti.

Kakin jikinshi ya ceceshi a ranar, don kuwa da ba za su amsheta bama sai da yan sanda. Haka aka garata zuwa dakin tiyata cikin gaggawa yana ji yana gani, ya dawo yana ta safa da marwa a kofar dakin, addu'a iri-iri a bakinshi. A cikin haka ne ya tuna da Iyayenshi, sannan ne ya dauki waya ya kira ya sanar dasu halin da ake ciki, sai gasu nan da nan sun je sun sameshi a asibitin. Suna nan har zuwa lokacin da aka fito da ita bayan an kwashe kwararan awanni biyu.

"Kuyi hakuri, mun samu mun ceto uwar da kyar, amma bamu iya ceton dan ba. Kafin ku kai ga zuwa ma ya riga ya rasu saboda rashin isasshen oxygen a cikin cikin. Amma ita yanzu uwar tana lafiya, zamu yi mata sauran gwaje-gwaje idan ta tashi zuwa gobe!"

Abinda likita yace dashi kenan, aka mika mishi dan shi lullube a cikin zani. Ya amsheshi fuskarshi na bayyana rauni kwarai da gaske, duk karfin halin da yaso ya nuna sai da hakan ya gagara, ya zauna akan kujera dabar! Hawaye na cika mishi idanu. Ga d'a nan Tubarkallah kamar ka mishi magana ya amsa.

Innarshi ta amshi dan ganin yadda jikinshi yake rawa sosai, yayinda mahaifinshi ya dafa shi yana tausarshi. A haka jiki a sanyaye duk suka kwashi jiki suka koma gida, aka yiwa yaro sutura aka je aka binneshi kafin suka koma asibitin.
Mutane suka fara zaryar zuwa dubiya kamar su ci kansu, don kuwa Ummah macece mai mutane kwarai da gaske, yadda ta kama danginshi ta rike da hannu bibiyu kamar nata yasa suke matukar girmamata. Ga ta dama abin hannunta bai rufe mata ido ba sam.

Sai da ta kwana ta yini sannan ta farfado. Sumayyah ce a kanta da Abdullahin, su duka sunyi wani zuru-zuru da su kamar wadanda suka kwana suna jinya.
Suka shiga nan-nan da ita, amma cikinsu aka rasa mai kwarin gwiwar sanar da ita halin da ake ciki.

Likita yaje ya duba jikinta da kyau, nan ya zaunar da ita yana yi mata bayanin halin da take ciki...
Saboda mummunar faduwar da tayi kuma akan cikinta, da karin naushin da aka dinga yiwa cikin nata, uwa wadda take rike da d'a a ciki, ta rabu da mahaifarta (ana kiran hakan a turance Placental Abruption) wanda dalilin haka ne yaron cikinta ya rasa numfashi da nutrients da ake samu daga jikin mahaifa, saboda haka ne kafin su kai asibiti ya rasu. A yanzu dai komai nata normal bayan jininta da ya hau, don haka sun rubuta mata magunguna da allurai, za su cigaba da monitoring dinta kuma su ga abinda zai biyo baya.

Ta kwantar da kanta akan filo ta lumshe idanunta hawaye na tsiyaya akan fuskarta. Kuka take so ta fashe dashi, ta zagi duk duniya da mutanen cikinta ko zata ji dadin bakin cikin dake tukuki a ranta. Da zata iya tashi a lokacin, da zata je har inda Hadiza din take ta kamota, itama ta mata abinda tayi mata. Amma ba damar haka.
Wata zuciyar dake tausarta da likitan daya dage yana yi mata wa'azi da kara tausarta, yasa ta fara jan 'Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha!'
Kafin wani irin kuka mai karfi da daci ya kwace mata. Ta kokawa kanta a wannan rana, na maraicinta, da rashin iyayenta, da rashin Nenenta, da rashin da daya tilo da bata ko samu ganin kamanninshi ba balle ta dauka da hannunta. Wa ya sani ko zata sake ganin wani dan na kanta bayan shi? Likita ya fita ya barta tana wannan kuka na tausayawa kai.

Da Abdullahi suka shiga suka sameta, ta gama kukan ta share hawayenta. Idanunta sun yi ras kamar an soya gyada, amma daga ganinta babu tambaya an san ta sha kuka.

Ta yanke shawara daga wannan kuka, ta gama! Ta gama bari a takata, ta gama bari a dauki hakkinta, ta gama bari wani ya kwace mata abinda yake nata ne. Daga wannan rana, ta kulla bakar aniya da duk wani wanda zai nufeta da sharri. Ba kuma zata daina ba har sai taga karshen mutum!

Har tayi zaman jinyarta na kwanaki goma a asibiti, Hadiza ko a leke. Tana gida abinta ta mike kafa tana jiransu. Duk da ta dan sha jinin jikinta game da alwashin da Abdullahi ya dauka a kanta, amma gwiwarta bata yi sanyi ba. Saboda tasan a irin aikin da wani sabon bokanta yake mata akan Abdullahi, duk abinda zata mishi ba zai taba rabuwa da ita ba.

Shi kuwa da ba don ban hakuri daya sha ba a wajen iyayenshi, to da tun a washegarin ranar da abin ya faru ma zai sallameta. Amma suka tausheshi da kalamai masu kyau, suka ce yayi hakuri. Don haka yayi, amma shi kadai yasan kudirin daya dauka a cikin ranshi.

Aka sallameta ta warke dakau abinta, sai rama da tayi da rashin karfin jiki.
Ya daukesu su duka har iyayenshi dake tsaye a kanta da hidimarta kamar nata iyayen ne, da kuma Haule matar Kawu Tasi'u. Suka dauki kayansu yayi gidanshi dasu su duka.

A tsakar gida duk aka baza babbar tabarma aka zauna. Aka kira Hadiza taje, suka yi mata fada da nasiha kwarai da gaske, suka nuna mata rashin jindadin abinda ta aikata. Amma yadda fadan ke shiga ta kunnen dama, haka yake fita ta hagu. Da suka ce ta ba Ummah hakuri, ganin idonsu ne kadai yasa ta kalleta a kaikaice ta furta kalmar, 'yi hakuri!' da kyar.
Ta taune harshenta tana danne bacin ranta, amma ta kasa iya daga baki ta amsa ta.

A haka dai suka kara hadasu har shi Abdullahi din suka kara yi musu nasiha da kara nusar dasu akan zamantakewa da kuma yin hakuri da juna.
Yana jinsu har suka gama, kawai sai ganinshi suka yi ya tashi ya shiga dakin Hadiza. Ya fito sungume da dansu dake barci, a lokacin shekarunshi ba zasu haura shida ba, yana primary 1 a makarantar firamare, hannunshi daya kuma jaka ce shake da kayan yaron.

Kai tsaye ya kwantar da yaron a kusa da Ummah, ya dora kanshi akan cinyarta.
Ya juya ya kalli wadanda ke wajen, yace musu, "ina so ku zama shaida, daga yau, na mallakawa Ummah da na Habibu halak malak, na damka duk wata fada-aji nashi a hannunta. Daga yau kuma, ita kadai zata yanke hukunci irin na Uwa a kanshi! Ko Hadiza ban bata wannan damar ba. Ina kuma so in fada muku cewa, daga ranar da Hadiza tace zata tsallake wannan sharadi nawa, to wallahi a bakin aurenta! Kuma ko bayan nan gaba Umma ta sake haihuwa, ban yarda tayi zancen a bata dan ta ba. Allah Ya bata wani, Ya kuma sanya musu albarka."

Mutanen wajen suka yi shiru suna kallonshi jiki a sanyaye, Hadiza kuwa cikin kaduwar jiki ta mike tsaye tana ihu hannu a ka. Ta rantse ta maya wallahi bai isa ba, ai ba wani shege ya mata jinyar cikin ba har ta haihu, don haka wallahi ba zata sabu ba!
Ya tashi cikin tsananin bacin rai, dama tarata yake yi, yace, "ita da kika yi mata sanadin nata cikin, bata ce komi ba sai ke? Ba doguwar magana zan yi da ke ba Hadiza, wallahi ba don darajar iyayena ba, wallahi Allah da tuni na datse duk wata alaka dake tsakanina dake. Zabi daya ne zaki yi a cikin biyu, ko dai ki zauna a gidannan da hukuncin dana yanke miki, ko kuma in sallameki ki bar min gidana, shine kawai."

Da taga hatta iyayen nashi yau goyon bayanshi suke yi, sai kawai ta warci gyale ta bar gidan tana kuka. Ya tabe baki yace ta fi nono fari.
Cikinsu babu wanda yayi musun hukuncin daya yanke, sai sabuwar nasiha da suka yiwa Ummah na ta kara yin hakuri da yarda da kaddara, da kuma kulawa da amanar da aka damka mata. Daga nan kuma suka yi mata sallama suka tafi.

Ta dauki yaro da kayanshi, ta kama hannun Sumayyah suka shige dakinta Abdullahi yana binsu a baya.

Ba tare da an je biko ba ko wani abu, sai ga Hadiza ta koma gidan ita kadai da dare, ta shige daki ta kulle.

Shi kuwa Habibu koda ya farka ya ganshi dakin Ummah sai bai tanka ba, yayi zamanshi anan saboda dama can Hadiza din ke hanashi zuwa wajenta. Amma idan bata gidan a wajenta yake yini da Sumayyah. Ga zaman wajen Ummah da yafi na wajen Hadiza din dadi da sakewa, komi yake so shi za a bashi. Da yana wajen Babarshi ko kayan makaranta bata wanke mishi balle ayi zancen guga, kayan nan da zai je dasu ranar litinin haka zai yi ta sanyasu har zuwa juma'a, haka na Islamiya dinshi. Ga babu zancen duba mishi yadda karatunshi ke tafiya, babu kudin makaranta saboda duk sati Uban ita yake damkawa na satin, ta dinga bashi kullum. Amma bata bashi sai dai ta ce mishi ya tafi haka nan.

Amma da komawarshi wajen Ummah sai komi ya canza, kullum kaga yaro kal-kal dashi ya dau wanka. Kulawa take yi da shi kamar wani kwai.
Da yake ita kanta Hadizar bata zauna ba a gidan cikin satin, sai duk bai wani sanya kulaficinta a cikin ranshi ba. Kullum idan ta dau gyale tayi asubanci ta fita, to sai dare take dawowa. Gidajen malamai kala-kala take zuwa, ita ala dole sai an raba tsakanin Ummah da Habibu.

Ranar farko data zauna a gidan, ta tafi dakin Ummah kai tsaye lokacin su biyu ne kawai a gidan, shi ya fita, yara kuma suna makaranta.

Za ta shiga dakin, Ummah ta tareta fuska a murtuke, tace, "Malama lafiya?!"
Itama ta sha kunu, "dalla can munafuka ba ni waje! Ki fito min da kayan da na daga wannan matsiyacin dakin naki tun kafin in sake lakada miki na jaki wallahi!"

Ummah ta saki wani irin murmushi, tace mata, "an ki a fiddo kayan, na kwata ne!"

Wai sai ta kamata da dambe, kici-kici kafin ta ankare Ummah ta dagata sama ta maidata kasa ta kifar. Ta haye ruwan cikinta ta sameta ta dinga naushi da mari, sai data mata lilis.
Tace mata, "karyar iskanci ai kike yi dama, kinyi zaton haka zan zauna ki dinga buguna saboda ga ni jakar gidanku? Wallahi wannan kadan ne na miki, duk ranar da kika kara takalata a gidan nan wallahi sai an zo kwatarki a hannuna!"

Ta tashi ta barta anan, da kyar ta iya rarrafawa ta koma dakinta tana ta kukan zuci, a cikin ranta tana ta kara daukar alwashi akanta iri-iri.


42.


Daga ranar dai ta daina takalarta da fada. Habibullahi kuwa tunda ta fahimci yadda ya kwarewa Ummah kun san d'a da mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login