Showing 24001 words to 27000 words out of 142169 words

Chapter 9 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

442

cewa bikin bai fi wata daya ba saura.

Ga yara nan kanana su biyu yan mata suna wasanninsu, kai daga gani babu tambaya tsatson Auwalu ne don kuwa kamar tasu har ta baci.
Kasa karasawa cikin gidan ma tayi, don kuwa tasan idan ta shiga to lallai aika-aikar da za ayi ba karama bace.
Suka juya suka koma gida. Suna ta zugata da mata hudubar kada ta bari ya raina mata wayau wannan karon tunda dai taga komi da idanunta, amma ita gabadaya hankalinta ma ba a kansu yake ba, sam bata fahimtar ma abinda suke cewa.

Tayi dauriyar da zata yi, da kyar ta iya jira aka yi sallah. Ta dauki waya ta kirashi kamar gaske tace yaje tana son ganinshi. Sai ga gogan cikin dan kankanin lokaci ya fado gidan yana ta fara'a, har da guzirin tsirenshi a leda.
Yana shiga ta maida kofar daki ta rufe gam. Ya juya don ya tambayeta lafiya? Sai yayi karo da ita da galam din kalanzir da ashana a hannunta.

Hauka ta mishi irin wanda bai taba gani a cikin duk matayen daya taba sani ba ko aure, kai ko a labari bai taba jin kwatankwacin wannan abu ba.
Ta rantse ta maya, sai dai ta kashesu su duka akan dai ta zauna da kishiyoyi har biyu ba ma daya ba. Ita tafi karfin a yaudarata a ci mata mutunci, tafi karfin ta hada miji da wata.
Ya bata baki, yayi lallashin, har ya rasa da irin kalmar da zai bata hakuri ma akan ta tsaya ta saurareshi.

Kai da taga fadan ma baya mata kawai sai ta hau kwararawa kanta kalanzir din wannan, shima ta fara watsa mishi. Nan yayi wuf ya cafko hannunta ya kwace ashanar ta karfi tare da amsar galam din ya rufe. Ya bita da kyawawan maruka har guda biyu, amma ta ki saduda, bakinta kuma ya ki rufuwa. Ta tashi daga faduwar da tayi dalilin marin daya mata, ta sake ciwo kwalarshi tana kokarin shakeshi.

Kici-kaca suka hau dambe dashi, shi abin har mamaki yake bashi wannan karfin hali. Da kyar ya samu ya yakiceta ya jefar, ya bude dakin ya fita tare da rufeta ta baya.
Yana ji tana ihun ya dawo ya gani, daga nan kuma ta hau fashe-fashen kayan daki tana auna mishi zagi da tsinuwa ta kowace fuska, yayi biris da ita. Ba shi ya koma dakin ba sai da dare ya tsala lokacin barcin wahala yayi awon gaba da ita.

Kwanakin da suka biyo baya kuwa cikin matsanancin fada da tashin hankali suka yi shi. Kwata-kwata ta ki bari su huta daga ita har shi. Ita tace matukar ba zai fasa zancen auren nan nashi ba sai dai ya sallameta ta tafi, shi kuwa yace bata isa ba. Ai shi yake aurenta ba ita ba. Kuma bata isa ta haramta abinda Allah bai haramta ba.
Sati biyu da yin haka ta sake tada wani bala'in jin ya kai kayan lefe, wannan karon wuka ta so caka mishi, wanda ba don Allah Ya matukar sanyawa da sauran shan ruwanshi a gaba ba, to da sai dai wani bashi ba.
Babu shiri ya samo mota ya sanyata ya dorata kan hanyar Maiduguri, ita kuwa tace tafi nono fari, tana jiran takardarta. Shi kuwa yace wannan shine ba zai yiwu ba.

Kuma ta tafin yayi aurenshi matar ta tare a gidan da Zahra din ta zauna.
Shikenan tunda ya auri Salamatu yadda kasan ya auri diyar gwal. Gabadaya hankalinshi ya juye ya koma kanta. Baya iya zuwa ko nan da can sai da izininta. Kai a takaice ma dai mantawa yayi da babin Zahra gabadaya. Ko nemanta baya yi, itama kuma da yake ta shaka bata nemeshi din ba.

Lokacin data haihu ma sai Iyani ce ta kirashi ta sanar dashi haihuwar. Bakin gwargwado kuma yayi abinda ya dace, ya aika musu duk kudaden abubuwan da suke bukata, sanar suna ta zagayo yarinya ta ci suna Nadiya.
Zahra tayi wankanta mai kyau. Kwatsam tana gama wanka sai ga shi ya dira, wai shi yaje daukarsu su koma gida.

Ta tambayeshi ya zancen aurenshi? Shi kuwa yace mata matar tana nan, karewa ma tare zai hadasu da ita taje su zauna. Tace to salin-alin kawai ya dauki takardarta ya bata, kada ma su ja maganar da tsayi. Don kuwa ita dai ta gama aure dashi har abada.

Wannan zance kuwa sai daya kaisu har gaban manyanta. Su kuma suka nuna goyon bayan hakan. Tunda a cewarsu ai yaudararsu yayi. Su 'ya'yansu basa zama da kishiya. Maimakon ma ya godewa Allah daya samu suka bashi auren 'yarsu, kuma sai ya kara musu da sakayyar kishiya? Ba zai yiwu ba.
In dai har ya dage lallai sai yayi zaman aure da ita, to kuwa babu shi babu hadata da kishiya. Shi kuwa yace ko yar gwal ce bata isa ta hanashi sunnah ba. Kai tsaye suka nemi ya saketa, shi kuwa sai yayi ban tsoro, ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro. Ya rubuta mata saki daya. A tunaninshi zata tsorata tace ta hakura, sai yaga ko a jikinta ma. Sai ma cewa da tayi kafin a tafi a zauna dashi ya kayyade abinda zai dinga bata na shayarwarta, kuma idan ta yaye diya zata maida mishi kayanshi tunda ba da ita taje ba. Ta dauki jaririyarta ta bar wajen.

Shima kuwa sai ya shaka. Bai sake bi ta kanta ba ya kada kanshi ya tafi. A ganinshi ai zata nemeshi tunda yasan tana sonshi, ba zata iya rayuwa babu shi ba.
Kwananshi biyu da komawa suka je daukar kaya har da Zahra din aka je. Suka samu amarya suka zazzaga mata rashin da'a, suka kuma kwashe kayan gidan tas ko allura basu bari ba. Har TV da firjin da sauran kayan amfani daya dauka ya ba Salamatu wanda shi ya siyawa Zahran sai da suka bi suka dauka, suka kara gaba.

Kwanci tashi asarar mai rai, Zahra har ta fita idda abinta. Auwalu daya zauna yana jiran ta nemeshi dasu mayar da aurensu yaji shiru, kafin ya ankare har an kwashi shekara da rabuwarsu. Gashi yana sonta don so, amma kuma yasan ta riga ta mishi nisa yanzu.

Zahra kuwa tana yaye Nadiya ta hade mata kayanta ta aunata Kaduna. Duk yadda Iyani da su Hauwau suka so ta bar diyar a hannunsu ki tayi, a ganinta hakan da zata yi shi zai kara konawa Auwalu rai.
Ta kai mishi diyar da kanta ta dungurar mishi da ita. Babu ko gaisuwa balle tambayar bayan rabuwa, sai bakar magana data yaba mishi ta kara gaba. Yarinya na kuka ta rarrafa ta kamata tana ihu, amma haka ta wancakar da ita ta bar gidan babu ko dar. Zuciya ta rufe mata ido.
Daga nan kai tsaye Kano ta nufa inda Karimah ta hadata da wani darakta, cikin kankanin lokaci kuwa ta fada harkar film.

Auwalu ya rasa yadda zai yi da diya. Ya ba Salame ita don ta rike, tayi tsalle tace ta rantse da Allah ba a isa ba. Ita da ko nata dan bata gani ba sai a hadata da rikon dan kishiya? Ba zata karba ba. Ala dole sai daukarta yayi ya kaiwa Juwairah don Inna Deluwa ba dadin jikinta take ji ba balle ya kai mata.
Ita kuwa Juwairah da lokaci daya Allah Ya sanya mata kaunar yarinyar, ta karbeta da hannu biyu ta rika tamkar ita ta haifeta.

Ba a jima ba ya gyarawa Salame daki a gidan ta baro waccan ta dawo nan. Rigima babu irin wadda bata tayar ba, duka yayi biris da ita ya kyaleta. Suka zauna ita da Juwairah wani zama na doya da manja, don kuwa babu zaman lafiya a cikinshi ko kadan.

Zahra kuwa ta shiga industry da kafar dama. Nan da nan sai gashi tayi wani irin suna na ban mamaki. Duk wani mai kallo kai har ma wanda baya yi yasan da sunan Zahra Madam. Wanda sunan ya dauko asali ne daga film dinta na farko inda ta fita a wata Madam mai sayar da abinci a tasha. Da yake kuma film din ya karbu sosai, sai sunan ya bi ta.

11.

Nadiya ta tashi a hannun Juwairah wadda daukacin gidan suke kira da Mama. Tasan cewa Mamar ba ita ta haifeta ba, amma kuma ita a wajenta Mama din Uwa ce. Domin kuwa bata taba bambantata da 'ya'yanta na cikinta ba. Duk abinda zata yiwa 'ya'yanta, to kuwa Nadiya tana ciki. Lokacin data tasa ta fara yin wayo, Mama ita ta daukesu ita da Haulatu diyarta da kuma Nazifi kaninta wanda kusan sa'an Nadiya dinne, watanni shida ta bashi, ta kaisu makarantar boko da Islamiya ta dinka musu uniform. Lokacin kuwa Saminu da AbdulHadi sun mallaki hankulan kansu, suna ta sana'o'in hannu iri-iri suna tallafawa Mama don kuwa Abbansu ta kanshi yake yi. Sannu a hankali yan siyasa sun fara watsi dashi. Idan ba lokacin da siyasa ta kankama ba, ba a cika nemanshi ba. Don haka wannan abu ba shi kadai ya shafa ba, ya shafi har mutanen gidan baki daya.

Zahra bata taba waiwayar Nadiya ba tun bayan tafiyarta sai da ta kusa yin shekara goma. Lokacin Allah Ya karbi ran Inna Deluwa bayan doguwar jinyar cutar hawan jini da ciwon sugar data sha, a lokacin Nadiya shekara biyar bata cika ba, don haka ba wani saninta tayi ba.
A wadannan yan lokutan ne kuma ya auro Lantana. Data shiga gidan kuma sai suka hade kai da Salame, ita har lokacin bata taba haihuwa ba. Wannan hade kai da suka yi sai suka mayar da gidan kamar wani gida na yan dirama da wasan kwaikwayo. Kullum cikin tsokanar Mama suke da jan ta da fada, Nadiya tana mamakin dalilin da yasa ta tsokale musu idanu, tunda shi wanda suke yi dan shi din Mamar dai ba a gabanshi take ba.

Tun bayan auro Lantana da yayi da kamar shekara daya da Mama ta haifi Maryam, bata kara taka kafa taje dakin Auwalu da sunan kwana ba. Shima kuma bai taba nemanta ba. A lokacin ya zama dai kamar kawai tana zaman 'ya'yanta ne a gidan.

Babu irin zagi da gori da Nadiya bata gani ba a wajensu Lantana. Tun tasowarta sun sha kiranta 'shegiya, diyar karuwa' ko su ce, 'shegiya wadda uwarta take yawon ta zubar!' da kalamai dai munana irin haka. Tun abun yana damunta yana sanyata kuka har ta hakura ta gaji ta zuba musu ido. To ita uwar ma bata santa ba, bata taba sakata ko wani danginta a ido ba, balle tasan wace kalar waina take toyawa ba. Tana ganinta a cikin fina-finai dai. To suma fina-finan ta daina yi, ta samu wani hamshakin mai kudi ta aura.

Lokacin data cika shekara goma kuwa kwatsam sai ga Zahra da yan'uwanta sun je ganin Nadiya. Zo kaga murna a wajen Nadiya kuwa ranar, yadda kasan tayi me.
Aka musu masauki a dakin Mama wadda ta karbesu hannu bibiyu. Suka je musu da tsaraba cike da bayan booth din wata rantsetsiyar mota da suka je a cikinta. Nan da nan kuma sai jikinsu Salame yayi sanyi. Domin kuwa a kallo daya idan ka yiwa Zahra, kaga macen da babu zancen raini ko wulakanci a tattare da ita. Ta fito a ainihin Madam dinta sak, kai daga gani hutu da naira sun zauna mata.
Irin shigar da tayi ma kadai ta isa ta isar maka da sakon bata daga cikin ajin su Salame da kurar data kawosu.
Da diyarta guda daya taje a hannunta yar kimanin shekara uku. Tayi aikin film na kusan shekara biyar, tauraruwarta ta haska kwarai da gaske, a sanadin haka Allah Ya hadata da Alhaji Shehu Balogun, dan garin Jos ne haifaffe, kuma suka yi aurensu ya tafi can da ita.

Shahararren dan kasuwa ne kuma attajiri, ya rike matakai daban-daban a gwamnati tun daga kan sanata ya dawo dan majalissa mai wakiltar jaha, daga karshe dai ya kama kasuwanci ya rike. Yana da mata har biyu a lokacin daya auri Madam Zarah, amma daga aurenta cikin dan kankanin lokaci sai da suka rabu dasu duka. Ya zamana ita kadai ce a gidan. Ya sakar mata kudi iya son ranta, ta fara fantamawa yadda take so.
To da yake itama bata son zaman banza, sai ta fara kasuwanci abinta. Ta kuma samu hanya ta Gwamnati da masu mulki a hannunta. A hankali-a hankali sai ta zama kamar wata broker a tsakanin manyan masu kudi. Tana da kudi tana da hanya tana da connections a sassa da fadin Najeriya har ma da kewaye. Idan wani babban yana son ganin wani babban, ita ake nema. Idan hanyar shigo da kaya kake nema daga kasashen ketare, ita ake nema. A halin yanzu Madam Zarah ta zama wata aba a cikin kasar Najeriya. Yan siyasa nemanta suke da idanunsu, domin kuwa magana daya tak idan tayi a kanka, zata iya canza maka kaddararka, maganarta zata iya sanyawa kaci zabe ko kuma ka fadi. Haka duk wani dan siyasa ko basarake ko wani dan kasuwa da zata goyi bayanshi, to shikenan fa shi kakarshi ta yanke saka.

A halin yanzu ta mallaki shaguna manya-manya da ake mata kasuwanci, kayan gado, kayan kicin, kayan ado da kawa na mata da maza. Hakazalika tana da gidauniya fiye da uku wadda kawai ta taimakon talakawa ce da marasa karfi. Duk inda taji wani labari na neman taimako, zata yi aike ko kuma ta taka da kafarta taje ta kai taimako. Da wannan sai ta saye mutane maza da mata, babu babba babu yaro kai babu talaka babu mai kudi. Mutane da dama fadi suke yi da zata daga baki tace tana neman takarar shugaban kasa ko ta Gwamna, to da a guje zata haye. To amma ita siyasar ba a ranta take ba, tafi son dai ta marawa masu yi baya, ta haka sai ta samu damar juyasu yadda take so.

Yini guda suka yi a gidan, har kusan yamma Auwalu yaje suka gaisa. Bakinshi yaki rufuwa da irin abubuwan arzikin da suka kai mishi, ga kuma aljihu da Zahra din ta cika mishi da kudi.
Da suka roki alfarmar ya basu Nadiya su tafi da ita taga danginta tunda anyi arashi lokacin an basu hutun makaranta, babu musu ya amince musu.
Suka tafi masauki suka kwana, washegari asubar fari suka yiwa Maiduguri tsinke.

Nadiya taje taga danginta suma suka ganta, dadi ranta har sai da tayi kukan murna.
Satinsu daya anan tana ganin gari, kafin kuma suka wuce Jos gidan Madam din.

Nadiya bude baki kawai tayi ganin irin gidan da Madam din take rayuwa. Fadar ya hadu ma bata baki ne, babu kuma zancen a kwatanta haduwa da tsaruwar gidan, don kuwa baki ba zai iya bayyanawa ba.
Gida ne gari guda, dauke yake da parts parts, wasu ma har ta gama satinta guda a gidan bata taba takawa taje bangaren ba.
Yaran maigidan su uku da yake duka mazajene, a gidan suke zaune amma har ta juya Kaduna bata taba sanyasu a cikin idanunta ba. Bangarensu ma bata sani ba, saboda basu cika shiga inda Madam din take ba, gashi inda suke din da yar tazara don haka ko fita zasu yi ba a sanin lokacin da suke fita da dawowa.

Komawarta Kaduna hankalinta ya kara nutsuwa, taji dadin bayyanar Mamanta sosai. Zagin da su Salame suke mata da gori ya ragu sosai, ko sun zaga dinma hakan sai ya daina damunta.
Karatunta take yi bilhakki, duk lokacin da suka samu hutu kuma Madam takan aika mota har gida a dauketa a kaita Maiduguri ko can Jos din. Ga dawainiya da take yi musu da iyalin Mama. Da yake Saminu da AbdulHadi sun jima da tafiya Lagos, Allah Ya taimaka musu duk suka samu abin yi a can don shi AbdulRazak ma har yayi mata a can, sana'a ta zauna mishi, to yana yiwa Mama aike duk lokacin daya samu to basu cikin matsala da matsi. Ba kamar da ba da idan Abbansu bai kai abinci gidan ba suke zama cikin garari, ko kuma idan matan gidan sun girka suka basu kadan suyi kwanan yunwa. Yanzu kuwa ko a jikinsu, abincin ma idan sun dafa suka basu suka ga bai musu ba, tuni Mama zata kunna sabon risho da Yaya Saminu ya sai mata, ta dafa musu wani abu su ci.
Shi Saminu Allah Ya taimakeshi ya samu aiki a wani kamfanin kera kayan robobi anan cikin Kaduna, da yake daga shi har AbdulHadi karatunsu a NCE ya tsaya wanda shima da fadi tashi suka gama, daga nan kuma suka tafi Lagos neman kudi. Dace ne aka yi yazo Kaduna yaga ana neman ma'aikata yayi applying, cikin ikon Allah kuma Ya samu. Don haka ya dawo nan yana aikinshi. Kuma iyaka bakin kokarinshi yana taimakawa su Mama din da duk abinda ya samu.

A haka da duk hutun da suka samu na makaranta take zuwa ta yi shi a Maiduguri ko Jos, sai suka fara fara sabawa da mutane. Hatta da samarin gidan Madam. Cikinsu sun fi sabawa da dan gidan Alhaji Shehun na biyu, Irfaan, shekarunshi a lokacin kusan ashirin kenan.
Idan taje ya kan taimaka mata da bitar karatuttukanta, musamman bangaren turanci, ya iya shi kamar wani bakin bature, don haka idan taje wajenshi take makalewa yana taimaka mata da spelling da pronunciations.

Matsala ta farko dake fuskantar gidan Madam, shine babu kwabar yara a cikin al'amuranta. Ita duk abinda yaro yayi kawai dai-dai ne matukar hakan zai mishi dadi. Wannan yasa bata taba sanyawa Nadiya da su Irfan ido ko wani shamaki game da kusancin da suka yi ba, kuma bata taba gargadinsu ba.
Sannan shigar mutunci da addini sam ba a gabanta suke ba. Ita a karan kanta ta sha fita da wandon leggings da yar bubu da hula kawai. Akwai lokuta da dama da idan zata fita din sai Nadiya ta mata magiyar ta samu gyale ta yafa. Balle a kai ga maganar sallah. Don kuwa a rana idan kaga tayi sallah akan lokacinta dubi gani.
Akwai lokacin da yini guda tana ta aikin tarbar mijinta da ya kwashe wata biyu a kasashen turai, haka aka kwashe yini guda bata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login