Showing 111001 words to 114000 words out of 142169 words

Chapter 38 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

463

gobe daurin aure, yaushe har na huce gajiyar tafiya kuma mu juyo Kano da kwana biyu?"

Yace mata, "idan hakan bai yi miki ba kinga sai ki hakura da zuwa bikin kawai. Idan an kawota Kano din sai ki cire rana guda kije ki mata yini ki dawo!"
Kasa ce mishi komi tayi har ya hada kan wayoyinshi ya fita daga falon. Mami ta bishi da kallo tana dan murmushi kafin tace mata, "kar ki biye mishi kinji Nadiya? Fade kawai yake yi amma ai shima yasan wasa ne hakan."
Sai ta gaza ce mata komi, don kuwa tasan shi da iyakar gaskiyarshi yake fada.

Da dare ta iskeshi a dakinshi, har zuwa lokacin ranta bai gama warwarewa da wannan abun da yayi mata ba. Ta yini tana tura mishi sakon ya taimaka ya canza shawara, ya bari itama ta ramawa kura aniyarta, tunda dai shima ai ya shaida irin kokarin da Anty Lima ta musu a nasu bikin. Amma ya ki maida mata da amsa ko daya.

Ta shiga dakin ran nan a cune, dama mai neman kukane aka jefeshi da dunkulen kashin awaki. Shi kanshi kuma sai daya kula da hakan.
Ya janyota jikinshi lokacin da take zaune a gefen gadonshi, ta shaki kamshin turaren nan nashi da a lokacin take jin kamar an kara mata dadinshi a cikin ranta.

Yace, "wai maganar tafiya bikin nan dai ba zata kare bane Nadiya? Kiyi hakuri ki zauna a gidanki don Allah Nadiya, wallahi a ko'ina nake kawai idan na tuna kina gidana a zaune kina jiran dawowana, sai inji dadin hakan a cikin raina da wata kwanciyar hankali ta musamman na shigata!"

Tace, "to kuma kai da kasan mun fa gama maganar nan tun ba yau ba Baban Ammar, kuma gidan nan naga ba ni kadai bace, ga Anty Shukurah. Hakan ai ba zai zame maka wata matsala ba."

Ya fara gudanar da abinda yafi so a tattare da ita, wato bin ilahirin wuyanta da sumba, har ya gangara zuwa kunnenta ya kama masangalin da harshenshi. Yace mata, "ba zaki gane bane Nadiya! Ke din ce bani son rabuwa da ke ko da na dakika ne, ina ga kwanaki dai-daya har goma?!"

Ganin yana kokarin canza hirar tasu yasa ta ja baya daga gareshi tana kare kirjinta da hannu. Ya dakata yana kallonta cikin wani yanayi data kasa fahimta, "meye hakan Nadiya?"
Ta dan ciji lebenta na kasa, "ni dai gaskiya sai ka bari zan bi Mami sannan!"

Sai ya mike tsaye cak, wannan karon bacin ranshi ya nuna sosai akan fuskarshi, irin wanda bai taba nuna mata ba. Har sai data fara dana sanin bin wannan approach din. Amma wata zuciyar na zugata, kada ta karaya, kada ta bashi kofar da zai fara yi mata kulle da hanata zuwa sabgar dangi.

Yace mata, "ashe kenan kema ban isa dake ba Nadiya? Yanzu ban isa in gindaya miki sharadi ki bi ba? Shine zaki biyo min ta wannan hanyar? Ina fada miki wannan ne don kawai nan gaba ki kiyaye, babu abinda na tsana a duniyata irin wannan abun, holding sex against me akan wani abu can na daban da neman biyan bukata. Ita wadda take min hakan ki tambayeta kiji abinda hakan ya haddasa mata a wajena, idan ma ita take zugaki kika hau kai kika zauna saboda baki da kan gado, to ta gama dake. Tafiya biki kuma na kasheta gabaki daya. Don Allah idan ke kike da ikon kanki ki tafi ga hanya nan!"

Ya juya ya fita fuu! cikin fushi. Ta bishi da kallo, ita ba abun tayi fushi ba ko tayi dariya. Ban da abinshi, yaushe ma ta samu damar yin maganar arziki da Shukurah balle har ta zugata wai akan ta dinga guje mishi?
Ita tunda take da shi ma bata taba sanin irin wannan rayuwar suke yi da Shukurah din ba sai yanzu. Don haka sai taji ranta duk babu dadi. A ranta ma dai tasan hakan ba dai-dai bane, ba kuma haka yakamata ta bullo mishi ba. Don haka ta tashi ta gyara jikinta ta fita ta sameshi a falo a zaune yana latse-latsen channels da remote, har lokacin cikin fushi yake kwarai.

Ta karasa a hankali kusa da shi, fuskarta na nuna nadamar hakan data aikata mishi. Ta duka ta dafa gwiwarshi tare da tausasa muryarta, tace, "kayi hakuri Abban Ammar, nayi nadamar abinda na aikata maka. Don Allah ka yafe min, idan kuma zancen tafiya ne in shaa Allah na cireta daga raina tunda baka so!"

Ya dan kalleta, da gaske fuskarta ta nuna nadamar hakan, ya kuma hangi alamun da gaske take yi, zata iya hakura da tafiya wajen bikin duk da yadda take matukar son zuwa. Sai yaji ta bashi tausayi, ya kamota ya zaunar da ita cikin jikinshi yana mata magana a hankali.
"Zan fi so ko abu kike so ko nayi miki wani laifi na daban Nadiya, ki zaunar da ni ki fada min. Ko ban amince ba ko na amshi laifina a take ba, I promise idan kika yi hakuri kika dan bani lokaci kankani, zan iya canza shawara. Amma bana so, Koda wasa ki sake yi mun hakan, bana so ko kadan kinji baby?"
Yadda ya kira babyn ne cike da kulawa da so, sai taji jikinta yayi sanyi. Ta kwantar da kanta a kirjinshi tana gyada kai a hankali. Ta dauki hannunsu daya sarke da nashi, ta mannawa bayan hannunshi sumba a tausashe, "kayi hakuri!" ta furta hakan a cikin karamar murya.

Ta samu dai ya yarda ta bi bayan Mami din, da sharadin da an kai amarya to washegari ta dawo gida, bai kara mata ko kwana daya ba. Tayi sauri tace taji ta yarda ta amince.
Daren ranar dai ita da barci suka yi hannun riga, don kuwa cewa yayi sai ta fanshe mishi kwanakin da zata tafi ta barshi shi kadai yana yawo a garin Kaduna sai kace wani gwauro.

Washegari su Ammar suka tasheta daga barcin wajen karfe goma sha daya. Ta bude musu kofa shi da Farida suka shiga, su suke fada mata cewa Mami ce tace su je su tayata hira, ita ta tafi unguwa.
Lokacin kari ya wuce, kuma ba yunwa take ji ba. Tasan ko ta fita ma ba lallai ta iya cin wani abu ba. Don haka ta barsu a falo suna wasansu, ita kuma ta shiga kicin ta fara tunanin abinda zata hada da sauri ta karya.
Ta hada wapple da yayi taushi tubus, ta yi topping da whipped cream da inabi ta zauna tana ci bayan ta hada shayi ta zabga mishi lemun tsami. Don gani take idan bata ci wani abu mai lemun tsami ba tashin zuciya zata cigaba da yi.

Su Farida suna gefe ita da Ammar suna cin wanda ta zuba musu.
Sai ga knocking anyi, ta bada iznin a shiga. Sai ga Bishola, ma'aikaciyar gidan. Tana ganinta ta sha jininta, ila kuwa tana gama gaisheta, sai ce mata tayi, "Ummah ce tace a kira Ammar!"

Yaron ya kalleta da sauri yace, "to ai Ummah ce da kanta tace mu taho nan. Kuma ranar nan ma da kika ce tace inje, tace ba ita bace!"

Nadiya bata fahimci inda zancen nashi ya nufa ba, kawai sai ta kallesu tace musu, "ku je tunda ita ta aiko!"
Suka tashi simi-simi suka bi bayan Bishola.

Ta bisu da kallo a ranta tana wani tunani. Wannan wai wace irin rayuwa ce suke yi a gidan nan ne?
Taji wani irin bacin rai ya dabaibayeta, taga yau idan ta shanye wannan maganar kila zuciyarta ta buga, ta fadi ta mutu a banza babu wanda za a yiwa asara a gidan.
Kawai sai ta sabi gyale a kafada, ta wuce sashen Hajiya Ummah buguzum-buguzum kamar wata kububuwa.

Yaran suna falo suna kallo, ta haye sama da sauri ganin Ummah din bata nan kasa.

Ta ci nasarar samunta a falon kasa tana kallon labaran safiya a tashar Farin Wata.
Ta duka a gabanta tana kwasar gaisuwa, kafin ta kai ga gama amsawa Nadiya ta rushe da kuka.
Sai ta bita da kallon mamaki, murya a dan daburce ta fara tambayarta, "subhanallahi, Nadiya! Me ya faru ne? Me aka yi?"

Ta bude baki tana magana, amma yadda shessheka da kuka suka ciyota, ba a ma fahimtar abinda take cewa.

Ganin haka sai Ummah ta kamo hannunta da kanta, ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita, tana shafa bayanta a hankali cikin lallashi da kulawa da suka ba Nadiya mamaki.
Ita har ga Allah bata ma san takamaiman kukan me take yi ba ko musabbabinshi ba. Amma bata yi tsammani samun wannan kulawar daga gareta ba. Tayi tunanin kyararta zata yi ko tace ta tashi ta bata waje bata da lokacin wannan shirmen.

Ummah sai data ga ta nutsu, ta daina kukan, sannan tace mata a tausashe, "yanzu kiyi min bayanin abinda kike cewa yanzu. Menene akan zancen Ammar da rashin son kusancinku da menene? Na kasa fahimtar abinda kike fada sam!"

Sai ta sadda kanta kasa a kunyace, a ranta tana fadin dama tayi hakuri ta taushi zuciyarta bata zo da zancen ba. Me zata ce mata yanzu? Ta dai tari aradu da ka, ta fara magana kanta a kasa.

"Ummah, nasan cewa I'm not your favorite person a gidannan, wanda ban san dalilin hakan ba amma idan ma nayi miki wani laifine da ban sani ba, ko wani nawa ne yayi miki hakan, don Allah a madadina da nasu su duka ina rokonki da kiyi hakuri. Amma sai in ga hanani kusanci da kike yi da Ammar kamar ba mafita bace mai kyau, tunda ko babu komi naga yana son zuwa wajena, kuma nima ina son yaron. Sannan bana tunanin ina kokarin canza mishi halinshi ne ko dabi'a."

Ummah tayi shiru tana saurarenta a nutse. A ranta cewa take ranar da Sumayyah take ji mata tsoro gata nan ta zo! Tunda har an fara zuwa ana confronting dinta, ai ana gab da fara fadi-in-fada ita da suruka.
Amma abinda bata gane ba kuma take son ganewa, shine;
"... me ke faruwa da Ammar ne da kike cewa ina son shiga tsakaninku? Ban fahimceki ba?"

Nadiya ta kasa kallonta, sai ta gyara zama ta fada mata yadda duk lokacin da Ammar yaje bangarenta take aika Bisola ta ce yaje tana nemanshi?
Ummah zaune tayi sandardar a zaune cikin mamaki, don kuwa ita dai bata ma taba jin wannan zancen ba sai a ranar.

Don haka ta kalli Nadiya tace mata, "dan bani minti daya!"
Ta tashi ta dauki waya ta kira chief security ta gidan, suka yi maganarsu kasa-kasa wadda Nadiya bata jin abinda suke cewa. Amma dai ta sha jinin jikinta da cewa akwai matsala. Gabanta ya hau faduwa, a ranta cewa take dama dai bata hau dokin zuciya ta biye mata ba ta zo wa Ummah da wannan zancen.

Shukurah tana zaune gaban madubi, shafe-shafe ta gama, tayi kwalliyarta sosai cikin wata jar abaya. Wani taro ne ta hada na manyan mata yan siyasa, don su taru su karawa juna sani akan hanyoyi da dabarun samun nasarar kamfen da iya tafiyar da mulki. Don har matar Gwamna mai ci sai data gayyata.

Aka buga kofar dakinta sau biyu, ta bada izini, aka shiga.
Yar aikin ta karasa gabanta, ta duka tana mata rada a kunne. Kai kawai ta gyada mata alamun ta gamsu, ta daga gaban drawer dinta ta ciro kudi a cikin envelope ta mika mata. Ta amsa da rawar jikinta tana mata godiya, ta bude kofar dakin ta fita cikin murna. Sai tayi turus ganin Mrs. Atiku, Chief Security dinsu. Ita ce mai kula da duka securities da yan aikin gidan. Wadda bata wasa da aikinta ko kadan, bata kuma taba bada kofar da za ayi wasa da aiki tana gani. Karya da zamba da munafunci suna cikin manyan abubuwan da bata aminta dasu.

Don haka tunda Bisola taci karo da ita, tasan cewa tata ta zo karshe! Tun ma kafin ta mata magana ta fara hawaye da neman gafara, ta duka kasa takardar kudin da aka bata itama tana faduwa. Ta duka, ta duba taga kudin dake ciki shake, ta dan gyada kai tana kallonta cikin nuna alamun ba sani ba sabo, tace, "kije wajen Shu'aibu, zai baki takardar sallamarki da kudin da kika ci na wannan watan. We no longer require your service!" Ta tsallaketa ta wuce ta barta anan tana kukan nadama.

Dakin Shukurah ta wuce da take jiyo abinda ke faruwa. Duk da cewa jikinta yayi sanyi da jin abinda ke faruwa, amma wani sashe na zuciyarta yana kara karfafarta da cewa kada ta karaya. Don haka koda Mrs. Atiku ta sanar da ita cewa Hajiya Ummah tana son ganinta, da confidence dinta ta tashi ta bi bayanta. Tana fada da karawa a cikin ranta, ita din ai ta gama cin dubu sai ceto, don haka babu abinda hakan zai zame mata. A wajen Ummah da Habibu, ita din ai ta zama duwawu, ko ana so ko ba a so dolene a zauna da ita.


45.



Suka nabba'a a gaban Ummah ita da Shukurah, kai a kasa suna sauraren irin fadan da Ummah din take zubawa sosai da sosai cike da bacin rai. Saboda abin bai mata dadi ba sam.

Ta cewa Shukurah, "akan me zaki aikata haka iye? Har ki dinga amfani da sunana a cikin gidannan kina aikata abinda bai dace ba? To daga yau, kada in sake jin abu makamancin hakan ya faru anan gidan. Ammar da ne a gareku ku duka, ban ga dalilin da zai sanya daya ta dinga hana daya mu'amala dashi ba, a kiyaye. Sannan daga yau, idan na kara jin wai an hada baki da yan aiki ana yin abinda bai kamata ba, to mutum zai gamu da bacin raina kwarai!"

Shukurah ta kyabe baki cike da wani sobaranci da sokanci, tace, "Ummah kina ganin yadda dai ta janye yaron wannan jikinta duk ta kanainayeshi, shi dama Ubanshi tuni ya gama zama mijin tace a kanta. Sai a zuba mata ido kenan tana juya mutane?"
Ummah tace mata, "shi da ya zama mijin tace din ai shi ya so hakan, kema kuma da kin zage dantse tun farko da kin zama matar mijin tace din. Da kuwa da kike ganinshi ai shi yana wajen duk mai sonshi ne da kyautata mishi and lets face this Shukurah, yaron nan ba jan shi kike yi a jiki ba, hasalima idan yazo wajen da kike baki bari ya rabeki. To zai zauna yayi ta biye miki ne?!"

Kawai Shukurah sai ta dargwaje da kuka, ta tashi tsaye tana sakin maganganu cike da rashin da'a da kirki. Ai dama ita tun ba yau ba tasan cewa Ummah din tafi son Nadiya a cikin gidan. Yanzu har ta kai a dinga mata gorin haihuwa da yi mata shune akan d'a? Kenan ita duk kokarin da take yi a gidan ba a ganinta da mutunci? To ta gama zaman gidan, zata tafi inda ake ganinta da mutunci ake girmamata.

Ummah ta kama baki cike da mamaki tana kallonta, tace, "Shukurah! Wane irin zance ne kike yi haka? Me kuma ya kawo wadannan maganganun? Ashe ban isa kiyi kuskure a gidannan in tsawatar miki ba?"
Tace, "wace tsawatarwar? Wannan ai son kai ne kawai! Idan ma fadan ne kiyi mun daga ni sai ke mana, sai ki hadamu da wasu banzaye can sanadin su dinga raina ni?!"
Ummah ta daga murya cikin bacin rai, tace, "Shukurah ni zamu zauna muna sa-in-sa dake a gidannan?"
Sai ta daga hannu sama kamar mai surrender, "kinga, gidan ma zan bar miki ni. Sai ki kama wannan akwajalar da kike neman kamawa, kiga idan zata iya yi miki rabin abinda nake miki!"
Ta juya ta fita fuuu! Tana sakin wasu maganganu marasa dadin ji.

Jikin Nadiya yayi wani irin sanyi a wajen, ta kasa motsa ko dan yatsanta ne. Da tasan abinda zai je yazo kenan, da bata dauko maganar wannan ba.
Tace, "Ummah don Allah kiyi hakuri. Wallahi da nasan haka zata faru, da na hakura na bar zancen."

Sai taga Ummah din tayi dan murmushi, tace mata a tausashe, "kada ki damu Nadiya. Ki kuma daina bani hakuri akan laifin da baki aikata min ba. Akan gaskiyarki kike, ina so daga yau kuma idan abu irin haka ya faru ki dinga sanar dani ko Maigidanki, saboda wannan zancen bai kamata ayi shiru ba kinji?"
Sai ta gyada kai a hankali, "to Ummah!"

Tana kokarin tashi din ne taji Ummah ta mata magana, tace, "ya ki zo nan Nadiya!"
Ta gurgusa, ta matsa kusa da Ummah din inda take nuna gefen kujerar da take zaune, amma ta kasa zama akan kujerar. Sai kawai ta zauna a kasan kafafunta. Ita kuma sai ta kama hannuwanta ta rike tana kallonta da idanu masu cike da kauna irinta Iyaye.

Tace, "zauna muyi magana dake sosai Nadiya, akwai misunderstandings da dama da nake so mu warware yau!"

A lokacin ta zaunar da Nadiya ta bata labarin ko wacece Hajiya Ummah. Duk wani fadi-tashin rayuwa da suka shiga bayan abinda ya faru da su, da kuma irin burika da ta sha akan duk wani iyalin Alhaji Laminu.
Tace mata, "amma a yanzu duk na ajiye wadannan abubuwan, na nemawa zuciyata maslaha. Ina kuma baki hakuri akan abubuwan da duk na aikata miki bayan shigowarki gidannan, har a yadda muka gudanar da neman aurenki ba tare da mun baki zabi ba. Ki yafe min kinji?"

Nadiya sai ta hau share hawaye, tana jin wata irin salama da sanyi na shigarta a duka sassan jikinta.
Tace, "ni dama can ban taba rikeki ba Ummah. Kuma a yau nima, a madadina da duka zuriyar Laminu, don Allah ina neman yafiyarki Ummah. Ki yafe mishi ko Allah Yasa ya samu sassaucin kwanciyar kabari!"
Tayi murmushi wanda ya fito tun daga can karkashin zuciyarta, "na dade da yafe mishi Nadiya. Allah Ya yafe mana baki daya. Allah Yayi muku albarka ku kuma tare da duk zuriyarku bakidaya!"
Nadiya ta amsa da ameen bakin nan nata har kunne saboda tsabar farinciki da jindadi.

Ta mike kafa anan kusa da Ummah, hira suka sha sosai irin wadda basu taba yi ba. Hira irin ta iyaye da yan'uwa, ba ta suruka da suruka ba.
Ba tasan lokacin da barci ya kwasheta ba anan tsakiyar falon. Sai da Ummah ta tasheta tace ta koma daki ta kwanta. Barcin ya gama cin karfinta, ko fahimtar abinda Ummah din ke cewa bata yi. Ta dai koma kan sofa ta mike kafa sadidan ta cigaba da barcinta.

Ranar ko zarafin tashi ta dafa abincin rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login