Showing 63001 words to 66000 words out of 142169 words

Chapter 22 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

458

karasa gida, ta bude mota ta fita Rashida tana binta a baya.
Tace mata, "to mu shiga ciki ku gaisa da yan gidan ko?"

Ta amsa mata da 'to.'
Sai kuma ta bude booth ta ciro wata leda mai dan fadi. Ta bi bayan Nadiya, Ammar kuma yana makale da ita yana ta zuba mata hira.

Matan gida duk aka zubawa Nadiya ido da Rashida kamar sun ga wasu sabin halittu. Mama na kofar kicin da amarya suna aiki, da Nadiya tace mata bakuwa ce kanwar Baban Ammar, sai ta ajiye aikin Amarya kuma ta amsa. Suka wuce dakin Mama, Rashida na gaida Salame dake aikin kulla lalle a leda wanda take sayarwa, tayi banza da ita ta kyaleta. Nadiya ta janye hannunta zuwa cikin daki ganin ta cigaba da auna mata gaisuwar ita kuma ta ki amsawa.

Rashida har kasa ta zube tana gaida Mama, ta amsa tana mata murmushi cike da jindadi.
Basu wani jima ba tace mata zasu tafi saboda Magriba ta matso.
Nadiya ta shiga uwar daka ta debo tarkacen kayan kwalliya da tayo guzirinsu tun bikin da taje Maiduguri. Ba wasu masu yawa bane ko tsada, amma haka Rashidar ta amsa tana godiya da nuna jindadinta kamar wata kyautar ban girma ce ta mata.

Sai kuma itama ta mika mata ledar hannunta, wai Yayansu yace a kai mata.
Ta amsa cike da mamaki, don kuwa ko da wasa bai fada mata hakan ba.

Ta rakasu har waje, suka shiga mota suka tafi. Ta daga jaka, ta ciro wata lafiyayyar shadda ruwan hanta ta sha wani irin surfani a hannu da wuya mai tsananin kyau. Nadiya bata san ya aikin surfani yake ba, amma dai wannan tasan daga gani ba karami bane. Ta kara ciro wani flat din takalmi da jaka na MK, ga agogo nan itama ruwan hanta da gyale mai yalwar fadi.

Ta zubawa kayan idanu da mamaki, Amarya data shigo ganin kaya, tayi guda tace, "Allah sarki, wani hanin ga Allah baiwa ne! Jiya har zancen wai ai wannan sallar haka nan zaki yi ta babu sabon dinki na tsinto ana yi a tsakar gida. Wai kina ta hura hanci da fankama na banza da wofi!"
Mama ta kama baki, tace, "kai! Ni da abin magana baya yiwa wadannan mutane kadan."
Nadiya kuwa tayi dan murmushi kawai. Ta maida kaya inda suke ta ajiyesu.

Da ya kirata suka yiwa juna barka da shan ruwa.
Tace mishi, "nagode da kayan da aka kawo. But you didn't have to!"
Yace, "duk abinki dai ba zaki hanani samun ladanki na zuwa idi ba Nadiya!"
Ta saki yar dariya, "ba abinda nake nufi ba kenan. Amma dai nagode!"
Yace, "anytime Nadiya!"

26.


Suna gama wayar da Nadiya sai ga kiran Hajiya Ummah ya shiga wayarshi kamar wadda take jira.
Ya tashi daga kishingide din da yake, ya dan runkufa yana gaidata bayan ya daga kiran.

Ta amsa a tausashe, "lafiya lau Babangida. Kun sha ruwa lafiya?"
Yace, "lafiya lau Ummah. Ya gida?"
Tace, "muna nan muna shan zafin Najeriya, kai dai ai ka gudo ka barmu!"
Yayi yar dariyar, yace, "Ummah ai ke kika ki zuwa, bayan har an kammala miki komi na tahowa."
Tace, "kai barni dai wannan karon kaji, nafi gane zamana cikin yan'uwa da dangi. Wannan na shiga wannan na fita."
Yace, "hakane kuma."

Ta gyara zama tana ambatar sunanshi a nutse, ta haka sai ya gane zancen nasu mai muhimmanci ne, sai shima ya gyara zama yana kara kashe kunne.

Tace, "me ya faru ne ga matarka nan tazo tace ka aikata mata rashin adalci."
Yace, "ni kuma Ummah? Me nayi mata ne bayan ba na ma garin?"
Tace, "cewa tayi ka dinkawa Amaryarka kayan sallah ka kai mata? Bayan kuma ita haka ka tafi ka barta zikal!"

Ya hade fuska kamar yana gabanta, "ita tace miki haka ne? To ki tambayeta kiji, da zan tafi nawa na bata na siyayyar kayan kamun azumi da kuma na sallah? Me take nufi da ni ne wai? Ko kuwa ba ita bace ta fada min iyaka adadin abinda take so ba, na kuma dauka na bata babu musu?"

Ummah tace, "duk da haka, gata nan tana korafin ita ai baka taba dinko kaya ka kai mata ba sai dai ka bata kace ta saya. Yanzu kuma ka dauki na wata daban, ka kai telan da yake mata dinki ya dinka mata. Anya ka so tsayar da zancen gaskiya anan Habibu?"

Ya shafa goshinshi da yaji yana shirin daukar zafi, yace, "Ummah, ni ban ma san ko wane tela ne yayi aikin ba. Sannan Shukurah ita da bakinta tace in daina yi mata dinki in dinga bata kudin. Saboda sau nawa ne zan kawo mata kayan tace kalarsu bata mata ba, watarana tace bata son design din, watarana ma haka zata ce kwata-kwata ba su take so ba. To ya zan yi mata ne? Ni Allan-musuru ne da zan san abinda ke cikin ranta? Ko kuwa a kanta zan kare ina bin kanta tana wulakantani? Wahayi aka min da ita ne?"

Ummah da taga ranshi yana neman baci sai ta jefawa Shukurah harara da tayi zaune tana sauraron hirar da suke yi. Tace mishi, "to naji, ta bangarenta dai bata kyauta ba kam. Amma duk da haka ka dinga kokarin daidaita adalci. Tunda dai kaga nauyi ne mai girma yake kokarin hawa kanka. Sannan daga yau na kashe zancen wai a ba mata kudi ta sayi tufafin sallah, ka sayo duk abinda kaga yayi maka ka bata. Idan bata amsa ba kuma zata gamu da ni ne."
Ta karasa fadin hakan tana kallon Shukurah don ta fahimci gargadinta. Sai ta dauke kai.

Shikuwa yace, "to shikenan Ummah."
Har zata kashe wayar sai kuma ta dakata, tace, "da ba munyi da kai ba za a yiwa Nadiya komai ba tunda nan zata zo ta tarar da lefenta?"
Yace, "ai Ummah nima Mami ce ta kirani dazu tace ta bada dinkin da za a kaiwa Nadiya din tayi kwalliyar sallah dashi. Nayi tunanin ma ko kunyi maganar ai."
Tace, "ita Sumayyah din?"
Yace, "ehh."

Ta jinjina kai, "ok. Ai shikenan. Goben kake tafe dai ko?"
Yace, "in shaa Allah Ummah."
Tace, "to Allah Ya kawo mana ku lafiya. Allah tsare mana ku."
Yayi murmushi cikin jindadin addu'arta, "ameen ameen Ummah na!"
Suka yi sallama.

Ummah ta juya tana kallon Shukurah dake tabe baki, tace, "to ke kin dai ji da kunnenki ko? To wallahi idan zaki shiga taitayinki ki shiga Shukurah. Ina kula dake ai, tunda zancen auren Babangida ya tashi kika tsangwami kanki, kina neman ki tadawa mijinki hankali kema kuma ki hana kanki sukuni. An fada miki dama haka ake yi ne? Ko kuwa kin taba jin an ce ana yiwa namiji haka a zauna lafiya? To wallahi ki kula, don kinga yana binki a hankali yana miki yadda kike so, ba wai tsoronki yake ji bane. Lallabine yake miki, duk kuma ranar da ya gaji ke zaki kwan a ruwa!"
Shukurah ta zumburo baki, "to kuma Ummah sai a yiwa mutum rashin adalci amma ya kasa furtawa haka ake yi?"

Ta jefa mata harara, "zo ki fada min rashin adalcin da aka miki a wannan zance inji don Allah! Yanzu tunda Babangida ya bar kasar nan, sau nawa kika kirashi a waya?"
Tayi shiru tana hararar waje daya. Ummah kuma ta tabe baki, tace, "ke dai kika sani ai. Kada ta kara kwabe miki wallahi don kin bar hakarki tayi ruwa da gangan kuma kizo ki ce zaki sanya min ciwon kai Shukurah." Ta tashi ta barta anan.
Itama tashi tayi ta fita daga sashen Ummah din ta koma nata tana sake-sake a ranta.


/'/'/'

Ranar sallah yan gida duk an zuba ido ana jiran a ga Nadiya ta fita da tsofin kaya zata je idi. Don Lantana tun da uwar safiya ta tashi ta ci kwalliya cikin sabin kayanta, ta je kofar dakin Salame ta nemi waje ta zauna. Fadi take tana karawa, "yau dai sai taga karyar masu karya!"

Sai ga Nadiya din ta fito ta ci kwalliyarta abinta tana ta bada kamshi. Salame da itama take ta saurin tayi tata kwalliyar ta fito sai ta koma tana lekenta ta taga. Musamman da su Maryam suma suka fito cikin shigarsu mai kyau wadda Mama ce tayi musu dinkin, suka tsaya a kofar dakinta suna kashe selfie abinsu. Da suka gama kuma suka dauki hanya suka tafi masallaci abinsu. Sai Lantana taja jiki ta koma daki kamar kazar da kwai ya fashewa a jiki.
Ranta fal bakinciki da takaici a cikinshi ya mata katutu.

Ana jimawa kuma sai ga Mama ta fito cikin rantsattsan leshinta da Yaya AbdulHadi ya dinka mata. Ta dinga kaiwa da kawowa a tsakar gida ita da amarya wadda ita ce da girki ranar, hankalinta kwance babu abinda ya dameta. Sai suka bar su Salame da makalewa a daki suna lekensu, reshe ya juye da mujiya.
Don kuwa da so suka yi ranar su gallazawa Nadiya su tura mata haushi da takaici. Sai suka ga kuma lamarin bai je musu yadda suka so ba.

Ita kuwa Nadiya har ga Allah ma tuni data manta da abinda ya faru game da dinkin sallah da ba ayi mata ba. Kwalliyarta tayi tsakaninta da Allah ba don ta turawa kowa haushi ba.

Da suka taso daga Masallacin, suka biya ta shago ta dauki abubuwan motsa baki, saboda tasan ranar ba zasu rasa baki masu zuwa yawon sallah ba. Tasan kuma dasu zasu bude baki a gidan ranar tunda abincin da za a dafa ma sai a ranar aka kai gida, tasan ba a kai ga saukewa ba yanzu. Suka sake tarar abin hawa suka wuce gida.

Ta mikawa mai Napep din daya daukosu kudinshi, ta biyo bayan su Maryam da suka rigata fita tana mai gyara zaman gyalen dake jikinta.

Kamar an ce daga kanki, tayi kyakkyawan gani da wanda ya zame mata tauraro a halin yanzu.
Yana tsaye ta can bayan gidansu a jikin motarshi, shi kuma da waya a hannunshi yana kokarin kiranta sai suka hada ido.

Duniya da abinda ke cikinta suka dauke mata a wannan lokacin. Tsakanin ita da shi bata san wa ya fara takawa zuwa ga dan uwanshi ba, sun dai tsinci kansu a kofar gidansu Nadiya dinne a tsaye, sunyi carko-carko kamar wasu tsofin zakaru.

Kamshin nan nashi ya lullubeta yayi mata kawanya, akwai wani abu a can karkashin ranta dake kokarin janta zuwa gareshi, wanda ta rasa ko menene.
Wata daya kacal daya wuce, idan wani yace mata wai zata kalli fuskar Habibu taji kewarshi ko dadin ganinshi, wallahi sai tace mishi bashi da lafiya. Amma sai gata din, bakinta ba ma zai iya furta irin yadda taji dadin ganinshi ba. Ta kasa dauke idanu a kanshi da yake kallonta yana sakin wani tausassan murmushi.

Yace, "ba kallona zaki tsaya kina yi ba haka kawai Nadiya, idan kinyi kewata ne just tell me. Kin dai san ba zan iya karanta abinda ke cikin ranki a halin yanzu ba!"

Sai ta kawar da kanta gefe daya, tana dan gyara fuskarta don kada ya fara karantar irin abubuwan da zuciyarta ke fitarwa. Abin ma nema yake ya daure mata kai. Yaushe ne tayi sake har Habibun ya yiwa ranta wannan kamun kazar kukun? Har yaushe suka yi sabon da zata ke jin shi kamar wani tsohon masoyi da tayi shekara da shekaru bata gani ba?
Tayi kwafa cikin kokarin boye abinda ke cikin ranta, "wani kewa kuma ana zaman lafiya?"

Ya sake yin dan murmushi a hankali yana takawa zuwa inda motarshi take, itama tana binshi a baya.
"Ko baki fada da bakinki ba ai idanunki sun gama tona miki asiri Nadiya! Shi yasa ma ban fada miki zan zo yanzu ba kenan. Saboda ina son ganin abinda kike kokarin boye min ne da idanuna."

Ta dakata da tafiyar da take yi, suka koma suna fuskantar juna, "ban dai san me kake son cewa ba, amma ni dai nasan babu wani sirri dana boye a cikin raina!"
Bai bata amsa ba sai dan murmushi kawai da yayi, ya dauko kallo ya kare mata tun daga tafin kafarta har tsakiyar kanta. A gefe guda kuma ita satar kallonshi take yi, sai lokacin ta fahimci ashe ma ankon shadda suka yi ita dashi.

Yace, "wai ni amaryar nan tawa kullum wani kara fresh kike yi abinki, wai don Allah menene sirrin?"
Dariya sosai ta saki tana kallonshi a kaikaice. Ta dai fahimci tsokanarta kawai yake ji da neman magana. Don haka ta biye mishi.
Suka jima dashi anan suna hira kafin yayi mata sallama ya tafi. Saboda daga Masallaci nan ya zarce kai tsaye bai koma gida ba.
Itama ta wuce gida, data tarar an sauke abinci ma zuwa lokacin ta zauna ta ci kayanta.

Washegari gidansu ya cika da iyalan gidan yan yawon sallah. Su Basira da Zainab da Habiba duk sun je da yaransu, haka Anty Aisha matar Yaya Saminu. Ita Haulatu sai zuwa biki sannan zata zo.
Suka yiwa Nadiya caa da zancen me yasa bata fitar musu da anko ba? Ita dai nata bada uzirin su yi hakuri an ce babu taron da za ayi ne shi yasa.

Washegari ta fara zuwa gidan mai gyaran jikin da Anty Hauwa ta samar mata. Can ake mata turaren jiki dana gashi, a kuma yi dilka da halawa. Kullum nan take zuwa yini guda ana wannan aiki. Ita kanta duk korafin da take yi nan da nan sai gashi ta fara yin wani irin 'fresh' kamar yadda Habibun nata yace. Ta fara kilewa tana kara yin bul da ita. Kamshi kuwa duk inda ta ratsa sai ka ji shi, har sai ta bace ta barka kana shakarshi.

Bikin saura kwana uku, su Anty Hauwa da Anty Lima da wasu kannen Dada da yan'uwansu suka dira a Kaduna. Gida guda Madam ta ware musu inda nan ne itama zata yi nata taron bikin.
Sai ga Anty Lima ta dira da akwatu guda shake da kaya wai na fitar biki.
Ta kama baki tana kallon kayan cikin mamaki, tace, "wannan fa daga ina?"
Tace, "daga ina kuwa idan ba daga Angonki ba? Tun cikin azumi ya kirani yace in mishi estimating din abinda zai isa ayi miki dinkin kayan fitar biki, har da kudin kwalliya da na gyaran jiki. Na mishi calculations ya turo min kudina cas. Anty Hauwa ce tace kada a fada miki, don shi dinma cewa yayi kada a fadawa kowa."

Ta dinga daga kayan tana dubawa baki a dage, "wannan kayan ai sunyi yawa wai a fitar biki kawai gaskiya! Duk ya zanyi da wadannan ne kam?"
Anty Lima tace, "sai ki mishi kwalliyar da sauran idan kinje gidanshi. Don na fahimci dai mijin nan naki dan kwalliya ne sosai da son kyale-kyale. Shi yasa nima na kawo miki gudummawata ta musamman..."
Ta janyo wata jaka ta bude ta fara zarowa Nadiya wasu shegun night wears da underwears. Kallo daya ta musu ta kauda kai, ita kunya ma kayan suka bata.
Tace, "ki rasa abinda zaki bani yanzu sai wadannan yan iskan abubuwan? Kin dai san ba zan taba sanyasu ba ko?"
Anty Lima ta maida kayan inda suke tare da sanyasu a cikin akwatun kayan data kai mata.
Tace, "ke kika sani ai, ko ki sanya ko kada ki sanya duk ya rage naki. Ni dai ai nayi mai wuyar. Amma dai in fada miki gaskiya, yadda jikin nan naki yake daukar gyara yana kyalli da shekinnan, wallahi gwara kiyi amfani da damar nan. Ki dinga shiga ta raina sa'a!"

Tayi dariya, "Allah Ya kyauta miki wallahi Anty Lima. Kuma sai aka ce dole sai nayi shigar rashin kirki sannan ne ba za a raina ni ba?"
Tace, "ahaf! Zauna anan dai kina mamaki. Zaki fahimci tsarin abin nan ba da jimawa ba. Tashi mu tafi gidan gyaran nan kinji? Don nima gaskiya yau dai sai an dan shafa min dilkar nan na dan yi haske!"
Ta kyalkyale da dariya, "wato abin ma har da sharri kenan?!"

Ta hade kan kayan ta rufe akwatu ta ajiye, ta zari hijabinta suka fita.

27.



Madam taje da tawagarta mota guda, daya kuma tana binsu a baya shake da tarkacen souvenirs na biki. An bugo jakunkuna da mugs na shan shayi da abin turaren wuta. Kowanne dauke da sunan Nadiya din da Habibu ana tayasu murnar aure da fatan kasancewa karkashin inuwa daya har karshen rayuwarsu.

Basu kuma jima da zuwan ba sai ga masu hada waje suma sun karasa. Aka hau gyaran waje babu kakkautawa, nan da nan sai ga wajen taro mai kyau an hada.
Mai kwalliya taje har gida ta yiwa Nadiya kwalliya, aka shiryata cikin lafaya mai kyau ruwan zaiba, suka fita cikin yan'uwa da abokan arziki ana gaisawa. Duk yadda bata so a sanya kida ba, sai da Madam ta sha casunta ita da abokanta aka yi ta liken kudi kamar ba gobe. Sai can wajen karfe tara na dare kafin suka koma gida.

Can ma gidan cike yake da yan biki. Su Anty Haulatu da su Anty Jamilah duk sun je da iyalansu. Da suka zauna zaman hira duk ba su suka nemi makwanci ba sai wajen karfe daya na dare.

Washegari Juma'ah ranar daurin aure. Tunda Asubahi Abba ya tura aka kira Nadiya din, taje yayi mata nasiha daidai gwargwado, ya kara mata da gargadin kada ta kuskura tace zata taba taka kafarta cikin gidanshi da sunan yaji ma balle ayi zancen kaso aure. Daga nan kuma ya mata addu'ar samun zaman lafiya, yace taje ya sallameta.

Ta lallaba ta tashi da kyar, ta fita daga dakin cikin mutuwa da sanyin jiki. Haka ta wayi gari ranar gabadayanta jinta take kamar wata wadda aka yiwa mutuwa. Duk ta bi ta rasa duk wani kuzari nata.
Koda ta koma daki, kasa biyewa hirar da suka sake jonawa tayi, ta shige can dakin Mama tayi lamo a kan gado. Ko abinci sai da Mama din taje ta kai mata shi da kanta, sannan ta samu ta iya tsakurar kadan.

Da gari ya washe kuma, Anty Lima ta matsa mata tayi wanka, aka yi mata kwalliya madaidaiciya. Ta samu leshi fari mai kyau cikin kayan fitar bikinta ta sanya, ta fita tsakar gida aka hau hotuna da ita haka nan ba don ranta ya so ba.
Duk wannan abin da ake yi su Salame suna lafe a cikin dakunansu sun ki fitowa ko nan da can, kiran duniya babu wanda ba a yi musu ba akan su je a dauki hoto dasu amma suka ki fita. Sai Lantana ce ma daga baya da taji mutane suna maida magana, ta lallaba ta fito tana dariyar yake.

Zuwa lokacin da ake gab da daura aure, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login