Showing 99001 words to 102000 words out of 142169 words

Chapter 34 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

469

babban dan shi, ya kuma yi burin tunda su matane babu ruwansu da kasuwanci, to zai damka harkokin kasuwancinshi ne a hannun Lamin din domin ya ci gaba da kula mishi da komi.

A wancan lokacin mutane sun fi gane su yi ta tattala kudinsu a hannunsu da dai su je banki ko wani waje su zuba hannun jari. Sai ya fi karkata hankalinshi wajen sayen filaye da gidaje kawai, da kudirin zasu amfani su Ummulkhairi a gaba.
Daga shi har su din babu wanda ya taba kawo Lamin zai yaudaresu haka. Su dukansu kuma babu wanda ya taba tunanin zai tafi ya barsu a cikin wannan duniya mai cike da rikici da mutane maha'inta, masu saka alkhairi da sharri.

Mahaifinsu ya kwanta jinya a gaban idonsu, Ummulkhairi da wayonta a lokacin, tunda har ta shiga aji hudu na gaba da firamare. Don haka duk wani abu dake faruwa ta sani. Mahaifinsu yazo ya rasu, kudinsu dake mallakinsu, suka nutse a hannun Lamin.
Lokacin da Mamansu suka shigar da kara kotu, ya bi dare ya dauki wasu yan tasha, suka je gidansu cikin dare da wukake da adduna. A gaban idonsu, aka dorawa Ummansu wuka a wuya. Yace mata idan bata janye wannan karar ba, wallahi sai ya sa sun daddatsata. Su kuma su Ummulkhairi zai sanya wannan gardawan su rabasu da martabarsu. Wannan abu shi ya tsoratata, ta janye karar ba tare da ko yan'uwanta sun san musabbabin hakan ba. Ta kuma hanesu da suma su fadawa kowa saboda tsoron abinda Lamin din zai iya aikatawa. Don kuwa yace matukar suka kuskura yaji zancen nan a waje to zasu dawo.

Sai gashi cikin dan kankanin lokaci suka koma yin wata irin wahalalliyar rayuwa. Basu taba sanin ana yini a kwana da yunwa ba, sai a wannan dan takin. Gidansu da a kullum abinci sai dai a ba almajirai, don ma Mamansu bata kasance mai almubazzaranci ba, sai gashi su ne suke kwashe fiye da sati ma ba tare da an dora sanwar abinci mai suna abinci a gidan ba. Kullum sai gamje-gamje kawai suke yi. Suna kuma ji suna gani dangi suka watsar da su. Kalilan ne kadai suke dan zagayasu ko su dan aika musu da wani abu na masarufi. Sai da ta kai ta sayar da kayan dakinta tsaf, ta fara sana'ar sayar da abinci anan cikin gidanta.

A haka cuta ta kama Mamansu, ta dauki lokaci mai tsayi tana yin ta a tsaitsaye. A hankali sai kudaden sana'ar suka fara lumewa wajen sayen magani da zaryar asibiti. Daga baya sai gashi ta kwanta jinya warwas itama, zuwa lokacin da suka ankara suka je asibiti, ta kamu da matsanancin ciwon koda har ya kai stage 4.
Kafin ma a kai ga tunani da shawarar ta ina za a bullowa al'amarin? Allah Ya karbi abinshi.
Fadin irin kukan da su Ummulkhairi suka yi ba kadan bane, a kullum idan ta tuna yadda Mamansu ta mutu akan gadon asibiti, yadda ta kade ta rame kafin rasuwar tata, gabadaya kamanninta suka sauya saboda tsabar cuta. Sai data yi kwanaki uku a gadon asibiti ko ruwa bata iya hadiyawa, sai karin ruwa da jini da ake mata ne kadai suke tallafa mata.
Duk kuma wannan zaman jinya da suka yi, a cikin danginsu aka rasa wanda zai iya tsayawa tsayin daka a kan maganar har dai ta Allah ta kasance. Idan Ummulkhairi ta tuna hakan sai tayi ta kuka.

Haka aka basu gawa suka tafi gida da ita, kafin su je gida zancen rasuwar ya zagaya dangi. Wai sai lokacin ne duk kuma suka hadu, suka je suka yi ta matse-matsen hawayen da ta kira na munafurci.
Lamin yaje da kayan abinci ya jibge musu bayan an dawo daga janazarta. A lokacin ne ta tashi ta musu wani dan karamin bori, ta musu tatas daga shi har dangin nashi akan banzatar da su da suka yi. Ta kuma ce a fitar musu da wannan kayan abincin na haram, ko ta konasu. Bata san ya aka yi da kayan ba, don shi Lamin din da tayi hakan dominshi ma tuni ya dade da barin gidan. Bai san tayi ba.

Yayan mahaifiyarsu wanda ya kasance shi kadai ne shakikinta, ya yanke shawara da mahaifiyarsu cewa zai sayar da gidan da suke ciki kawai tunda dai yanzu ya zama na magada, ya daukesu a mayar dasu gabansu kawai. Don basu san irin halin da zasu shiga ba idan suka barsu anan.
Ita kuma tayi na'am da hakan, sai ta bashi shawarar kada su sanar da kowa amma. Gudun kada su sake hanasu tafiya da su kamar yadda suka yi a bayan rasuwar Alhaji Kabiru. Kafin zagayowar bakwai kuwa aka sayar da gida, suka hade kan kayansu tas, ba tare da sunyi sallama da kowa ba suka koma Kaduna.

Ummulkhairi ta tafi zuciyarta cike da matsananciyar tsanar Lamin wadda bata iya misaltuwa. Ta kuma yi alkawari ta maya, komi daren dadewa, sai ta rabashi da duk wani farinciki na shi. Kamar yadda ya kwace musu nasu farincikin!


40.



Komawarsu Kaduna da zama yaje musu da wani irin sauyi wanda basu saba da shi ba. Dangin Mahaifiyarta mutanene su masu matsakaicin karfi, amma kuma suna da wadatar zuciya.
Dama can Hajiya Uwale ce take kula da su musamman mahaifiyarta Nenne wadda karfinta ya fara ja, har ma da Yayanta Tasi'u wanda shi har yau baya da wata tsayayyar sana'a sai tsilla-tsilla da kame-kame kawai. Bayan iftila'in daya sameta kuma sai suka koma yar gidan jiya.
Ga kuma karin su Ummah din da Sumayya da suka tare a wajen Nenne saboda dama ita kadai ce a gidan. Shi gidan Kawu Tasi'un kusa da na Nenne yake, don da duka gidan a hade yake kasancewarshi na gado, daga baya ne ya rabashi da nata din saboda iyalinshi. Yana da 'ya'ya shida maza da mata, don haka dawainiyar kanshi data yaranshi ta isheshi.

Amma duk da haka sai da yayi iyaka bakin kokarinshi wajen jansu a jikinshi. Wadannan kudi da aka sayar da gida da su yayi amfani su dukansu ya maidasu makaranta, Ummah ta shiga aji shida kai tsaye, yayinda Sumayya ta shiga aji uku don haka duk jarabawar fita zasu zana. Ya biya kudin, ya kuma yi musu yan saye-sayen kayan masarufi wadanda zasu amfana. Sauran kuma ya damkawa Ummah a hannunta yace ta kama sana'ar da zata rikesu da su.

Ta shiga tunani da taraddadin ya zata yi? Don kuwa zama bai kamata ba. A haka suka yi jarabawar NECO da WAEC duk bata gama yanke shawara ba. Ga kayan abincinsu sun ja baya sosai, kudaden hannunsu sun tasamma karewa. Don haka ta yanke shawarar fara sayar da abinci kawai.
Ta kuwa fara da hannun dama, shinkafa take yi da wake da kuma doya da miya. Ta yanka salad da albasa da kabeji da tumatir. Sai ta fita can bakin titi kusa da wani gareji inda ake gyaran mota. Kawu Tasi'u ya rokar mata alfarma a wajen mai garejin har aka fitar mata da yar rumfa take sana'arta hankali a kwance.

Abinka da farar mace da masu iya magana suka ce alkyabbar mata, ga ta budurwa danya shataf, kyawun jikinta da sura duk sun gama bayyana a lokacin. Duk da cewa ba kwalliya take yi ba idan zata fita, amma tana gyara jikinta da kyau. Don kuwa macece ita mai tsananin tsafta. Komi take yi cikin nutsuwa ne da tsentseni, wasu a wajen duk suna cewa girman kai ne da jan aji, amma ita haka tsarin halittarta yake. Da dama wasu mutanen basu san da zamanta ba sai data fara tallar wannan. Aikuwa nan manema suka yi mata caaa kamar kudaje, ita kuma ta ki kula kowa a cikinsu. A ganinta idan tayi aure yanzu, ya zata yi da Sumayyah?

Tafi-tafi likkafa tayi gaba, kullum kara yawan abinci take yi don kuwa yanzu har daga wasu wajajen zuwa saye ake yi don Allah Yayi ta da zakin hannu. Ga tsaftarta da tafi burge mutane. Ta kuma fara hadawa da zobo da kunun kanwa.
Da Sumayya ta gama tata jarabawar, itama sai ta fara binta tana taimaka mata da wasu abubuwan. Ita take wanke mata kwanuka idan masu saya sun gama ci, ita kuma take kaiwa wadanda suke tsallake dasu. Amma suka wannan cikin kulawar yar uwar tata, bata bari ta nufi bangaren da idanunta ba zasu hango ba saboda gudun abinda zai iya zuwa ya zo a wannan zamani da amana tayi karanci.

*

Doguwar tafiya suka yo tun daga Nasarawa a mota. Yana daga cikin wadanda suka yiwa Gwamnan Kaduna rakiya zuwa tattaunawa da gaisuwar ban Girma ga Maigirma Gwamnan Nasarawa din. Suna shiga garin Kaduna aka sanar dasu Gwamna kai tsaye zai wuce gidan sarautar Zazzau ne tare da securities dinshi, su kuma anyi releasing dinsu a nasu aikin, za su tafi da wasu sojojin. Su dukansu dama hutun suke bukata. Aikin tsaro musamman na manyan figures irinsu Gwamnoni, ba abu bane mai sauki. Kowa ya matsu ya dangana da gidanshi don ya samu ya huta kafin kuma su ga inda za a sake jefasu zuwa gobe.
Sun kusa karasawa Shagari Low cost inda nan ne main house dinsu yake za a saukeshi, motar tasu ta fara hayaki da rawa akan hanya, ala dole suka gangara gefen titi suka kasheta. Signboard da suka gani na wani gareji anan kusa da su yasa suka tura motar zuwa garejin shi da sauran abokan tafiyarshi su uku. Daya motar da suke tare da ita kuma ta wuce can Jaji.

First Lieutenant I. A Makama (Abdullahi Ibrahim) ya fito daga cikin garejin da suka kai gyaran motarsu bayan yayi sallama da abokanshi, niyarshi ya samu acaba ya karasa dashi gidansu ko kuma ya lallaba da kafa tunda babu nisa sosai. Saye yake da kakinshi na sojoji, ya cire rigarshi ta sama mai dauke da insignia dinshi a kafada wato l aligned silver stars guda biyu. Ya rage daga shi sai dogon wandon na kakinshi da bakar riga.

Lokacin shigarsu bai kula da mai sayar da abincin ba sam, sai bayan daya fito ya tsaya a bakin titi sannan ya ankare da ita zaune a cikin rumfa tana ta aikin zubawa kwastomominta abinci.
Kallo daya tak! Yaji ya samu matar aure yanzu-yanzu.

Yana da matarshi daya da aka yi musu auren lalle, zabin iyayenshi ce a gareshi daya karba da hannu biyu da biyayyar daya saba yi musu a kodayaushe. Amma ya fada mata, su ma iyayen ya fada musu, zai kara aure a gaba idan har ya samu wadda ta kwanta mishi a rai. Suka kuma yi na'am da hakan.
Ba mai kyalle-kyallen kallon mata bane shi, shi yasa ma yake tantamar anya zai ma iya daga ido ya kalli mace har ya samo mata? Sai gashi a yau kwatsam ya sameta.

Ya koma gefe daya yana kare mata kallo a nutse, yadda take gudanar da komi nata cikin nutsuwa da rashin rawar kai. Wani mai azababben surutu ne a kusa da ita kadan, an zuba mishi abinci yana ci yana ta zuba mata surutu kamar an bude kan famfo. Amma bata ce mishi komi ba, sai dan murmushi kawai da take yi.

Allah kadai Yasan iya adadin lokacin daya dauka anan kawai yana aikin kallonta, har aka gama gyaran motarsu abokan nashi suka fito. Itama nata abincin ya kare ta fara tattara kayanta waje daya.
Sai ganinsu yayi sun tsaya a gabanshi, Al-Ameen Tukur ya kalleshi da mamaki, "Abokina, naji kamar kace gida zaka wuce tun dazu? Ko jiranmu kake yi?"
Sai yaji yar kunya ta rufeshi, ya hau kame-kame cikin rashin sanin abin cewa. Bai iya karya ba, Allah Ya gani kuma ba zai iya yinta a yanzu ba.
Shi kuwa daya duba wajen da idanunshi suke, ya kula da yar kyakkyawar yarinyar daya tsurawa idanu, sai ya kyalkyale da dariya.
Yace, "Allahu Akbar! Lallai yau Allah Ya kama wani!Duk fadin ran naka da ihun baka ga macen da ta isa ka yiwa kallo biyu ba, ka tsaya kana kallon wata for hours? Lallai da labari ashe!" Suka ja mota abinsu suka tafi suna kyalkyala mishi dariyar shakiyanci.

Shi kuma ya ci gaba da tsayuwa nan har ta gama kwashe kayanta, almajirai biyu suka daukar mata wasu, itama da karamar yarinyar dake tare da ita suka dauki wasu.
Ya daga kafa as if in a trance, yana binsu a baya har suka gangara suka tsallaka titi, suka shiga gida. Ya kira daya daga cikin almajiran da suka kai mata kaya yana tambayarshi ko nan ne gidansu budurwar nan? Kuma ya sunanta? Yace mishi, 'gidansu ne. Kuma sunanta Ummulkhairi.'
Ya dauki kudi ya ba yaron kafin ya juya ya wuce gidansu.

Ummah na zaune da dare bayan an gama sallar isha'i tana gyaran kayan miya da za a kai mata markade na miyar gobe, yaro yayi sallama ya shiga, yace, "an ce Ummah ta zo ana kiranta."
Ta jefi yaron da harara, "kaje kace ba zata zo ba!"
Saboda duk a tunaninta Nasiru ne. Wani nataccen saurayine tayi anan cikin garejin yake aiki, ta fada mishi bata son shi, amma ko a jikinshi wai an mintsini kakkausa. Kullum cikin zarya yake gidansu, a wajen sana'ar tata ma baya barinta. Bini-bini yana nan yana ta zuba aikin surutu yadda kasan wani aku kuturu.

Nenne ta lallaba ta fito daga dakinta tana dafa bango, "kai kaje kace tana zuwa."
Ta kuma juya tana hararar Ummah, "ki tashi ki fita tun kafin kiga bacin raina wallahi. Ni na taba ganin haka? Yarinya ana binki amma kina wulakanta mutane? Idan baki tsaya kin saurari samari ba ta yaya za ayi auren kenan?"
Ta turo baki, "ni Nenne nace ina son yin aurene dama?"
Ta mata dakuwa, "aikuwa karyarki ta sha karya wallahi! Ba ido zan zuba miki ba kina abinda kika ga dama ba sai kace wata marar aikin yi. Bari kawunki ya shigo gidannan wallahi, cikin maneman naki ya cewa daya ya fito kawai mu aurar dake mu huta!"
Ta tabe baki, "tab! Allah Ya tsareni wallahi!"

Da haka dai ba da son ranta ba ta zari hijabinta ta fita, da niyar ta wankeshi tatas wankin babban bargo. Yadda ko a hanya ba zai yi fatan Allah Ya sake hadashi da ita ba.

Sai ta tarar da abinda bata yi tsammani ba. Don kuwa ba Nasiru bane. Wani kyakkyawan matashi ne da bata taba ganin mutum mai zati da kamala irin tashi ba. Duk yawan samarin dake zuwa wajenta, bata taba ganin wanda ya kama kafarshi a komi ba. Ga iya gayu. Ya sha kaftan dinshi fara tas, ya dora hula a kanshi yana ta bulbula kamshi.
Sai ta karasa wajenshi a nutse tayi mishi sallama.

Abdullahi ya sanya mata idanu yana kallonta cike da wata kauna da sanyayyar soyayya. Wannan yammaci da yayi, da kyar ya iya bari gari yayi duhu ya zo gareta. Wani abu ne da bai taba dandana ba a cikin tarihin kuriciyarshi har zuwa girmanshi da yin aurenshi, wai shi soyayya. Ya daga baki da kyar ya iya amsa mata sallamar yadda ta kashe mishi jiki.

Ya gabatar mata da kanshi a matsayin masoyi, wanda yaje da kokon barar aurenta. Bai boye mata ba, ya fada mata cewa yana da mata har da dansu wanda bai wuce shekaru shida ba. Kuma shi aurenta yake son yi da gasken-gaske idan ta amince.
Mutum ne smart, wanda yake da kwazo da naci, duk abinda ya sanyawa rai to fa sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi. Yaje mata da zance wanda ba zata iya kwabar da zancen aure daya mata ba, na cewa zai hada daga ita har Sumayya ya rika tamkar kanwarshi. Saboda a dan tsayuwar da yayi a dazu ya karanceta tsaf, koda bata sonshi, ba zata taba kin zancen kulawa da Sumayyah ba. Don kuwa ya karanci kaunarta da kulawarta zuwa ga yarinyar.

Ta mishi sallama akan cewa zata yi tunani, ta kuma kwana tana tunanin. Daga karshe taga me zata rasa ne a wannan auren idan anyi?
Don haka washegari daya dawo ta furta mishi ta amince. Yayi murna ya kuma ji dadi sosai da sosai.

Cikin dan kankanin lokaci sai ga iyayenshi sun je wajen su Nenne da zancen aure. Bangaren su Nenne sun yi bincike, suka samu gamsasshen bayani game da iyalan gidan Ibrahim Makama. Mutum mai tawali'u da wadatar zuciya kenan. Abdullahi shine babban dan shi, bayan nan yana da kani Hashim wanda shima aikin damara yake yi, Custom ne. Bayan su iyayensu basu kara haihuwa ba. An shaidi zuriyarsu da girmama mutane da bin na gaba, iyayensu mutanene masu tausayi da taimakawa na kasa dasu. Mahaifinsu ba mai arziki can-can bane, amma yana da rufin asirinshi dai-dai gwargwado. Tsohon malamin makaranta ne wanda yayi ritaya. Da suka gamsu da duk bayanan da suka samo, sai kawai suka sanya ranar aure kamar yadda suka bukata, yan kwanaki kalilan.

Aka sha hidimar aure sosai, dangin Uwale sunyi musu kara kwarai da gaske. Mutanen Maiduguri kuwa ko keyar wani basu gani ba, dama dai tuni ta ciresu daga cikin ranta. Don haka bata damu da rashin zuwansu ba.
Amarya ta tareta a gidanta dake Shagari Low cost, tazarar dake tsakaninsu da surukanta ba mai yawa bace, tare da kishiyarta Hadiza.

Hadiza da tabi ta tashi hankalinta ganin irin kudaden da Abdullahi yake kashewa amarya, duk da cewa dai itama yana yi mata bakin gwargwado, amma ba haka take so ba. Ta hau kan zugar yan'uwanta da abokai, kodayake dama can da halinta, ta shiga harkar malaman tsubbu da bokaye hankali tashe, bata so auren ya yiwu. Amma duk abinta sai da aka daura auren, aka kuma kai mata amaryar gidanta. Hakan bai sanyaya gwiwarta ba, tayi rantsuwa ta maya, in zata yi yawo tsirara, to sai ta raba wannan aure. Don kuwa gidan Abdullahi gidanta ne ita kadai, ba gidan da za a raba da wasu ba.

Don haka zancen zaman lafiya ma da Ummulkhairi bai tashi ba. Gaba ta dauka da ita sosai da sosai.

Ita dai tunda aka kaita take zaune da kowa lafiya, daga mijin har iyayenshi da yan'uwansu da ita kanta kishiyar, da zuciya daya take zaune dasu. Don haka duk abinda Hadiza take yi, bata taba tankata ba.
Mutanen unguwa data tsince wadanda suke son zaman mutunci da ita, sai ta kamasu. Ta zubar da masu kai mata zuga da gulma da kuma wadanda dama can a bayan Hadiza suke a gefe.

Abdullahi aka yi posting dinshi anan gidan Gwamnati a Kaduna din, don haka yana gida a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login