Showing 69001 words to 72000 words out of 142169 words

Chapter 24 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

461

dare ya raba. Lokacin data samu barcin ya kwasheta da kyar, tuni duniyar ta gama kwanciya barci.
Shi yasa ta makara a washegari. Bata tashi farkawa ba sai can da gari ya fara yin haske. Ta tashi da sauri ta dauro alwala tayi sallah.

Da ta gama sai bata koma barci ba saboda tasan koda ta koma ma ba lallai ta iya yin ba, ta shiga bandaki ta bata lokaci mai tsayi cikin ruwan dumi dake tashin kamshin lemun tsami da citruss kafin ta fita, ta tsane jikinta da kyau kafin ta dauki lotion mai kyau na Dove ta shafe jikinta dashi.
Ta zaro wata doguwar rigar atamfa da aka yi dinkin rabi da net da bakin lace ta sanya. Data gyara gashinta ta nade, sai kawai ta dora karamin gyale a saman kanta bata dora dankwali ba. Data kai turare ta fesa, sai ta fito sak a amaryarta.

Ta zare wayarta a caji, ta kunnata kafin ta fita zuwa falo. Ta zauna kan luntsumemiyar kujera tana kara karewa wajen kallo cike da burgewa, lallai fa wanda ya samu ya huta. Waje sai kace fadar wata matar Gwamna ko First Lady? Sai kuma ta dan saki yar dariya kawai, data tuna ashe angon nata fa Gwamnan yake son zama.
Ta hau duba wayarta tana laluben missed call daga angon ko kuma text message, amma babu abinda ta tarar sai sakon Anty Lima dake bata labarin wai ta tabbata ta shiga ruwan zafi da kyau, kuma ta samu man zaitun mai kyau ta dinga amfani dashi. Taja wani dogon tsaki tana fita daga cikin message din.

Ba wai rashin kwanan da bai yi da ita bane yake bata mata rai, rashin sanin dalilin faruwar hakan ne ke bata mata rai. A da kam, watakila da babu abinda zai dameta. Da kila ma babu wanda zai kai ta farinciki idan Habibun ya gujeta. Amma yanzu fa? Abubuwa sun canza. Ta fara sabo da shi da alakanta kanta dashi cikin sani da kuma rashin saninta. Bayan hakan ma, wace mace ce zata so ayi mata fashin darenta? Amarya ma kuma a haka? Tasan cewa koda tayi ikirarin bata damu ba, karya kawai take yiwa kanta.

Tana nan zaune tana wadannan tunane-tunane taji an buga kofa, ta tashi taje ta bude saboda jiya sai data kulle kafin ta kwanta.

Kamshinshi kadai ya sanar da ita ko wanene a bayan kofar. Ta dakata, tana tunanin ko da wace irin fuska zata tare shi? Sai kuma ta bude kofar fuska kadaran-kadahan. Bata so ta nuna zakewarta a abinda bai kai ya kawo ba. Sai me ma wai don bai kwana a dakinta ba? Watakila yana da wani daliline ko uziri na daban.
Fuskarshi zane take baro-baro da alamun laifi da yasan yayi, idanunshi kuma sun nuna alamun rashin barci da shima bai samu ba.

Ta dan duka a nutse ta gaisheshi kafin ta bashi hanya alamun ya wuce ciki. Bai shiga ba, sai kafa daya daya zura cikin dakin. Ya kai hannu ya kamo nata cikin nashi yana shafawa da dayan hannun a tausashe, kallon da yake mata na tausayi da rashin abin cewa yasa taji hawaye na alamun cika mata idanu. Ta dai yi kokari ta danne su.

Yace, "I'm sorry Nadiya! Kiyi hakuri na bace miki jiya ba tare da wani uziri ba, wani abu na gaggawa ne ya taso min kai tsaye. Kiyi hakuri!"

Ta girgiza kai tana kokarin kakaro murmushin yake wanda yaki fita daga bakin nata, murya a shake take ce mishi, "babu komi. It's okay ai."
Ya girgiza kai da sauri, "no, it's not! Ba ni da wani abin cewa wanda ya wuce kiyi hakuri dinne kawai, amma nasan ban kyauta ba!"

Sai kawai ta gyada kai, saboda babu wani abu a bakinta a lokacin.
Kallonta yake da wasu abubuwa a cikin idanunshi, ji yake kamar ya hadiyeta danyar ta. Amma ba lokaci, sauri yake yi saboda zaman da yake dashi da karfe tara.
Yace, "fatan dai babu matsalar komi ko? Akwai wani abu da kike bukata ko wanda bai yi miki ba?"
Ta dan daga kafada tana girgiza kai alamun babu.

Yace, "ok, good. Fita zanyi yanzun ana jirana, ki wuce sashen Ummah ki gaisheta sai ki karya ko? Idan da wani abu da zaki bukata in taho miki dashi kuma sai ki kirani ko ki tura min sako. Yayi?"
Tace, "to. Allah Ya kiyaye, Allah Ya dawo da ku lafiya!"

Yayi murmushi a hankali, fuskarshi na nuna alamun jin dadin addu'arta. "ameen ameen Nadiya, nagode."
Ya jata cikin jikinshi ya rungume tare da nutsa kanshi a gefen wuyanta inda wani daddadan kamshin humra da oil perfume ke fita. Ya jima yana shakar kamshin kafin ya saketa yana sakin wani dogon numfashi, ya yi dan murmushi ganin yadda tayi wani sak! ta kafe a waje daya kamar wata sakago. Yace, "kamshinki gwanin dadi Nadiya. Kamar dai mu dawwama dake a hakan."
Ya karasa fadin hakan yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi, lokaci yana kokarin kure mishi. Don haka ya manna mata sumba a goshi, ya juya baya yana daga mata hannu. "Sai na dawo, Love!"
Ya barta anan tana binshi da kallo. A ranta take ayyana, 'ta haka kuma wai yake cewa tayi hakuri? Bayan shi ne yake tura mata wadannan alamu da signals, daga baya kuma ya janye babu wani kwakkwaran dalili ko hujja?'
Ta sauke numfashi a hankali. Ta rufe dakin ta wuce sashin Hajiya Ummah.

Tayi sallama cikin falon daya gama daukar sanyin ac yana ta tashin kamshin turaren wuta da freshener.
Ammar da Hajiya Ummah ta hanga akan teburi suna cin abinci, don haka ta taka ta karasa wajensu.

Ta duka har kasa a kusa da kujerar da Hajiya Ummah take zaune, tace, "Ummah Ina kwana?"
Ta kalleta a kaikaice, ta amsa da, "lafiya!" fuska babu yabo babu fallasa. Tun anan sai taji jikinta yayi sanyi. Ta samu kanta da mamakin ko ina fara'a da kulawar dake tattare da ita a jiya suka nufa? Ta dai tashi ta fara kokarin jan kujera kusa da Ammar itama ta zauna.

"Nadiya!"
Hajiya Ummah ta ambaci sunan nata a kausashe. Sai ta dakata da abinda take yi ta amsa tare da juyawa tana kallonta.
Tace mata, "daga yau zaki dinga kirana da Hajiya Ummah ne, ko Hajiya. Not Ummah. Wannan sunan na wasu ne ba naki ba, kina ji na?"
Ta gyada kai a sanyaye kirjinta yana bugawa cikin fargaba da wani taraddadi. Me take nufi ne?

Ammar daya tashi ya rungumeta cikin murna shi ya katseta daga tunanin da taso fadawa, ta rungumeshi itama tana murmushi tare da amsa gaisuwar da yake yi mata.
Ta zauna itama tana jan plate tare da fara bude warmers da aka zuba abinci a ciki. Chips din dankalin turawa ta zuba da farfesun kaza. Ta zauna tana cin abincin a nutse tana kokarin jan Ammar da hira.

Bata jima da zama ba Rashida itama ta fito, ta duka ta gaidata tare da Hajiya Ummah, kafin itama ta zauna ta fara karin.
Ta kalli Ammar tace mishi, "lokacin tafiyarka makaranta fa ya wuce."
Don haka ya musu sallama ya tafi tunda ya gama cin abincin nashi.

Hajiya Ummah tana gama cin abincin ta tashi ta haye sama. Ita da Rashida jifa-jifa suke hira. Ta kula yarinyar tana da sanyin hali, kuma bata da yawan magana da zantuka barkatai.

Suma suna gamawa, mai aikin gidan ta fita ta kwashe kwanukan da suka yi amfani dasu, ta koma kicin.
Rashida itama ta koma dakinta, sai aka bar Nadiyar ita kadai zaune a falo tana kallon TV ba don tana jin dadinshi ba.

Wajen karfe goma kuma sai ga Shukurah ta shiga, kai tsaye ta wuce kan dinning abinta ba tare da ta kalli inda Nadiya take ba wadda take kokarin gaisheta.
Taje ta zuba abinda zata zuba, ta dauki kwanon ta dawo kan kujera ta zauna. Kai tsaye ta dauki remote control ta sauya tashar da Nadiya take kallo zuwa Boom TV.
Hakan bai dameta ba, bata kuma yi kasa a gwiwa ba ta sake juyawa ta kalleta ta gaisheta.

Ta wani sha kamshi, ta dauki fiye da sakan goma idanunta akan TV din kafin ta amsa da kyar kamar wadda ake tursasawa. Da Nadiya taga haka sai ta tabe baki, a ranta tace, 'kinyi da yar halak!'

Da dai taga zaman jugum-jugum din da suke yi ba zai musu ba, sai ta tashi ta koma sashenta.
Ta kira yan gida suka gaisa, har su Abba da su Anty Jamilah ta musu ban gajiya da yake a ranar suka koma gida don har sun karasa Kanon take ce mata tunda fitar safe suka yi.
Da ta gama wayar kuma sai tayi komawarta ta kwanta, cikin ikon Allah wannan karon barci ya dauketa mai nauyi. Ba ita ta tashi ba sai bayan Azzuhur.

Ta cigaba da zama a bangarenta bata fita ba, saboda taraddadin fitar take yi. Hajiya Ummah ta nufi wani bangare da Nadiya din bata fahimci ko ina bane balle ta san ta yadda zata iya ji da shi. Shukurah kuma bata bata fuskar zuwa inda take ba balle ta ce zata je wajenta hira.

Tana nan sai ga Rashida da Ammar sun je bangaren nata. Ta nuna jin dadinta da zuwansu sosai, suka zauna suna kallo da hira. Ganin ta fara jin yunwa sai ta tambayesu ko sun ci abinci? Suka ce 'a'ah'
Don haka ta shiga kicin ta fara dube-duben abinda zata samar musu. Store din akwai danyun kayan abinci sosai, haka freezer cike take da kayan miya har da danyen nama da kifi.

Ta ji ance garar da Yayunta suka hada mata ce aka ajiye a store dinta, babu laifi kuma gaskiya sunyi kokari sosai da sosai.
Ta fara daga bokitai da aka zuba mata dubulan da alkaki da nakiya ta deba ta kaiwa su Rashida. Kafin ta koma kicin ta ciro kayan miya ta fara grating.
Rashida ta shiga wai zata tayata, tace mata ta koma wajen Ammar su yi kallonsu kawai tunda ba wani aiki ne na a zo a gani ba take yi.

Macaroni ta dafa musu da sauce din kwai. Ta hada musu a kwano daya suka zauna a tsakiyar falonta suka ci suka yi nak. Ta wanke komi da tayi amfani dashi ta mayar inda yake, ta koma ta zauna suka cigaba da hirarsu.
Haka ta biye musu yadda kasan wasu sa'anninta suka yi ta wasa da raha har aka kira la'asar. Rashida ta tafi ta taya Ammar ya shirya ta tafi makaranta, ita kuma ta tafi tayi sallah.

Wajajen karfe biyar lokacin ta sake yin wanka ta yi wani shirin cikin jan leshi. Anty Lima ta kirata a waya, ta daga da murnarta saboda dazu da safe bata nan lokacin data kira su Madam, bata kuma kirata ba don haka basu gaisa ba.
Tace mata, "Nadiya kin ganmu nan a bakin gate an hana mu shigowa wai ba a san da zuwanmu ba!"
Tace, "kamar yaya? Baku fada musu wajena kuka zo ba?"
Tace, "mun fada ya fi cikin carbi, amma sun ce sai Hajiya ta kirasu da kanta ta fada musu sannan ne zasu barmu!"
Tace mata "to bari in zo!"

Ta zura takalmi ta fita bakin gate din da kanta, amma wadannan masu gadi suka yi kememe suka hanasu shiga. Ta cije lebe ranta a bace, don kuwa abin ya bata mata rai. Kai da bakinka Amma sai an maka katanga da su? Ta juya ta wuce sashen Hajiya Ummah da kanta.

Ta sameta a falo tana latse-latsen waya da gilashi a idanunta. Ta duka kusa da ita ta gaisheta kafin tace, "Ummah baki nayi a waje amma an hanasu shigowa saboda wai baki fadawa masu gadi ba."
Tace mata, "kwarai kuwa. Haka dokar gudannan take. Ba a shigowa sai an san da zuwan mutum. Idan kin san wani zai zo miki tun farko, ki dinga fada da wuri ne saboda a dinga sanar da masu tsaron."

Ta hadiye wani yawu daya kafe mata a wuya, wannan abin nema yake ya fara isarta kuma. An yiwa mutum iyaka da mijinshi, an mishi iyaka da sunan da zai ambaci mutum dashi, yan uwanshi ma sai an sanya shamaki a tsakaninsu ne?
Ta daure tayi kasa da murya, "to kiyi hakuri Ummah, bamu san da hakan ba amma zamu kiyaye nan gaba in shaa Allah. Don Allah ayi mana wannan uzirin."

Tayi shiru tana cigaba da latsa wayar ta kamar bata ji abinda Nadiyar tace ba. Sai can an kwashe wasu kyawawan mintuna hudu, kafin ta kara wayarta a kunne, ta bada umarnin a bar baki su shigo.
Nadiya ta runkufa tana mata godiya.
Tana kokarin tashi ta dakatar da ita, "ba ke na cewa ki daina kirana da Ummah ba Nadiya?"
Tayi kasa da kanta, tace, "kiyi hakuri."
Hannu kawai ta daga mata alamun zata iya tafiya. Ta juya ta fita cikin salubewar gwiwa.

A waje suka ci karo da Anty Lima, da Maryam da Fatima da kuma Iya Lami wata kanwar Dada da taje bikin.
Ta musu maraba sosai ta kai su bangarenta, bata bari damuwar fuskarta ta bayyana ba. Sai hakuri data basu akan zaman jira da suka sha, ta nuna musu cewa matsala ce aka samu saboda umarni da aka basu na hana baki shiga gidan sai da izini.
Ta kai musu ruwa da lemu suka sha, suka zauna anan falonta suna ta hirarsu ana dariya.

Sai da suka kebe a dakinta ita da Anty Lima sannan take nuna mata bacin ranta game da abinda ya faru. Tana mata korafin Anty Lima ta dakatar da ita ta hanyar dafa kafadarta.
Tace mata, "Nadiya, kada ki bari hakan ya bata miki rai ko yasa kiyi kasa a gwiwa. Su dama mutane kowa da tsarinsu, kuma kowa da irin halinshi. Dole zaki yi hakuri, ki bi dokokin da aka kafa miki don a samu zaman lafiya. Ni ina ga ma hakan yayi ai, kin san akwai mutane da dama da zasu yi ta zuwa gulma da kinibibi, amma ta haka kinga sai a samu saukinsu. Kawai daga yanzu duk wanda zai zo gidanki ya fada miki da wuri, sai ki sanar dasu. It's not a big deal Nadiya, kada ki bari hakan ya bata miki rai..."
Ta samu da kalami masu dadi ta tausheta har ta dan sauko. Ta kula hankalin nata ma ba a waje daya yake ba, amma bata takura mata da son sanin ko me ke damunta ba.

Sallame suka je yi mata, saboda dukansu washegari zasu wuce. Itama Anty Lima zata je ta fara shirin nata bikin ne da za ayi bayan sallah Babba.
Ta jido musu kayan kwalliya ta rarraba musu. Iya Lami kuma cikin kayanta da ba a kai ga dinkawa ba ta dauko atamfa super Holland guda biyu aka bata tare da Tatuwa, dayar dattijuwar da suka je bikin da ita.

Sai da suka yi sallar Magriba anan kafin suka tafi. Wannan karon ta musu rakiya har gaban motarsu. Anty Lima take mata rada a kunne, "wai ya bata ga tana tafiyar amare ba?" Tasan abinda take nufi sarai. Ta jefa mata harara a kaikaice ba tare data bata amsa ba, a gefe daya kuma a ranta take cewa 'amaryar da bata kwan da ango ba?!'

Bayan tafiyarsu ta juya ta koma sashenta inda ta bude Al-Qur'ani ta fara karantawa.
Zaman ya isheta haka nan ita kadai muku, don haka tana gama sallar isha'i ta wuce sashen Hajiya Ummah don cin abincin dare.

Su dukansu ta samesu suna cin abinci. Don haka itama ta bi sahunsu ta zauna. Jollop din taliya ce aka yi spaghetti da hadin salad. Da yake ma ba wata yunwa take ji ba, kuma dai ba ma'abociyar cin taliya bace musamman jollop, sai ta zuba kadan. Ta zuba salad din da yawa tana ci.

Hayaniyar Rashida da Ammar kadai take tashi a falon, sai Shukurah da ke taba Ummah da hira jifa-jifa.

Zuwa can sai ga shi shima ya shiga falon. Saye yake da wandon pants baki da farar rigar shirt. Ya wuce kai tsaye inda suke shima ya zauna, ya gaida Ummah ta amsa cikin kulawa, Rashida da Ammar da ita Nadiya kuma suka gaidashi kusan a lokaci daya, ya amsa hankalinshi akan Ammar.

Yana zama yar aiki taje zata zuba mishi abinci, Nadiya ta fuskanci kamar hakan al'adar gidan ce. Don itama Hajiya Ummah sai dai ta cewa yar aiki ta zuba mata abinda zata ci. Ya dakatar da ita alamun ta barshi, ya tsakuri taliyar shima ya zauna yana ci.
Zaman ya isheta, tuni abincin ya fita kanta. Ta kasa fahimtar abinda ke faruwa a wannan gida da kuma ma'anar abubuwan dake faruwa.
Babu jimawa ta tashi ta musu sai da safe ta wuce sashenta.

29.



Ranar ma haka ta kwana ita kadai. Washegari kuwa da basu ko hadu a wajen kari ba sai itama bata bi ta kanshi ba. Sai zuwa can da yamma ya lekata, da alama ma dawowarshi gidan kenan don yayi wani wujiga-wujiga dashi.

Da daren kuma ya sameta ita kadai akan dinning tana cin faten dankalin turawa da yaji hanta da naman kaza a ciki, ga hadin zobo a gefenta tana sha.
Ya ja kujera a kusa da ita ya zauna, kamshin turaren nan nashi yana ta kai mata karo. Yace, "kaji manya manya inji kanana, Hajiya Nadiya ikon Allah! Abinci ake ci?"
Tayi dan murmushi kawai wanda bai kai zuci ba, don kuwa bata so hirar ta su tayi tsayi. Haushinshi take ji wasa-wasa, bata son yin wani yunkuri kuma na nuna mishi abinda yake mata yana sukan zuciyarta. Abinda take ji a lokacin kuma, tasan cewa zata iya bare baki ta tambayeshi dalilin da yasa yake mata haka. Idan tayi hakan kuma ai tasan ta barar da kanta a gabanshi.

Yace, "to! Yau kuma yan sarautar ne a kusa kenan? To madallah. Fara da zuba min abinci dai yanzu."
Ta tashi babu musu ta zuba mishi abincin. Farar shinkafa ce aka yi da miya, sai kuma faten dankalin da lemun zobo, ga kuma shayi ga mai son hadawa.
Ya fara ci ka'in da na'in, kamar wanda yayi yini guda bai ci abinci ba. Ita ma tayi gaggawar kammala cinye na cikin kwanonta, ta tashi tana kokarin wucewa. Yayi saurin kallonta,
"a'ah! Ina zuwa kuma haka? Har kin gama cin abincin ne?"

Tace, "ehh, dama a koshe nake. Dakina zan wuce saboda kwanciya zan yi saboda na gaji da yawa."
Ya dan watsa mata hararar wasa, "aikin me kika yi ne haka da har za ki gaji? Zauna ki tayani hira please!"
Ta girgiza kai a hankali, "sorry, maybe next time!"
Kokarin daga baki yake yi don ya mayar mata da amsa, sai ga Ummah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login