Showing 48001 words to 51000 words out of 142169 words

Chapter 17 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

459

Mun sanya ranar aurenki bayan sallah da kwanaki goma!"

Tsabar kidima gabadaya sai ta tafi tayi wani irin zama a gaban Abban nasu daga durkushen da tayi. Tace, "me?!" Cikin tsananin fargaba da tashin hankali.

Ya kalleta yana hade fuska, "ihun meye wannan kike mana a wannan wajen ana maganar arziki? Ki kiyayeni fa Nadiya, ki fita nesa da ni wallahi! Ni ai dama nasan shegen bakin ciki irin naki ba lallai ya barki ki barni in dangwali arziki yadda yakamata ba. Zance dai ya riga ya gama mutuwa, an zo neman aure, ni kuma na bada. Babu kuma zancen fasawa. Don haka ki zama cikin shiri, da an gama sallah zan sallameki kema ki kara gaba."

Ya maida hankalinshi ga Mama, "ki fada mata sai ta gayawa sh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i wancan da take bada sakon zai turo, iyayenta sun mata miji. Ki kuma sanya mata ido da kyau, idan ta kuskura ta sake waya da wani kato wanda ba mijinta ba, wallahi sai na sassaba mata!"

Nadiya ta rasa duk wata kalma daya kamata tayi magana da ita a wannan lokacin.
Maganar ma da Abbansu yake yi sama-sama take jinta.
Tana jin shi yake ba Mama umarnin kudin saman dubu dari, ta daukesu ta mika mishi. Su kuma su alewar da biskit, ta zauna ta daukarwa matan, a warewa Madam nata da na yan uwanta, itama Nadiya a daukar mata wanda zata ba abokanta. Sauran kuma ta ajiye mishi su.

Sai ta ji ta fashe da wani irin kuka mai cike da gunji, ta hade hannuwa biyu tana rokonshi, tace, "ka yiwa Allah da ManzonSa Abba, kada ka yi min haka. Don Allah don Annabi ka barni in auri zabina!"

Ya kuwa zaburo mata, yace, "wani zabi kike nufi? Duk zabi da damarmakin da na baki a baya sau dubun-dubata baki taba kawo min zabin naki ba sai yanzu da kika ga arziki ya tako ya zo inda nake da kafafunshi sannan? Nadiya idan baki kiyayeni ba fa wallahi zan mugun sabar miki! Aure kuma kamar anyi an gama ne, tashi ki fita ki bani waje, mutuniyar banza kawai!"
Ta tashi ta fita da sauri, fuska ta gama jikewa da hawaye.

Ta shige can kuryar dakin Mama ta haye kan gado ta lafe, ta saki wani irin kuka mai cin rai. Tayi-tayi, har sai data ji kanta yana sarawa. Tana jin wayarta tana ta kara amma ta kasa samun kuzarin daga kiran. Haka Mama ta shigo ta sameta, ta zauna tana lallashinta da ban baki da kalamai masu sanyaya rai, amma ran nan na Nadiya ya gama dugunzuma. Ta kasa daina kukan.
Mama sai ido ta kai ta zuba mata, ta kyaleta tayi kukan ma'ishi, ta zauna tana shessheka da jan hanci.

Mama ta kalleta cike da tausayi, tace, "yanzu su wannan koke-koken da kike yi na menene Nadiya, Iye? Ashe ke ba zaki yarda da kaddara ba? Ba zaki iya rufe ido ki bi maganar iyayenki ba? Anya Nadiya rayuwa zata yiwu a haka?"

Sai ta kara dargwajewa da wani kukan, tana kukan take cewa, "haba Mama! Abun ai sam babu adalci a ciki ko kadan! Ta ya za ayi ace a fitar min da miji ba tare da sanina ko amincewata ba har a karbi kudin aure da aka kawo? Kuma a ce min dole sai na aureshi ba tare da ni an duba abinda nake so ba? Waye zai zauna da shi idan ba ni ba? Ko babu komi ai sai a sanar dani ko? Kuma a tambayeni ba a bani umarni ba!"

Mama ta dan hade fuska, tace, "ki fa dinga tauna maganganun dake fita daga cikin bakinki Nadiya! Ke in banda zamani ma da yazo mana da wani sakaran canji, ina har 'ya mace take da zabi akan wanda zata aura? Mutane nawa aka daurawa auren ba ma su san junansu ba, amma gasu har yanzu suna zaune da mazajensu lami-lafiya? Me kike tunanin ya kawo hakan idan ba bin maganar iyaye da yi musu biyayya ba? Idan kika hakura, kika mikawa Allah lamarinki kuma kika yiwa iyayenki biyayya, sai kiga sakayyar hakan ta zame miki abinda zaki duba a gaba kiyi farinciki da alfahari da shi!"

Ta daga baki zata kara mayar mata da wata amsar mai cike da gardama, sai taji wayarta tana kara yin kara. Ganin Anty Lima ce mai jera mata kiran yasa ta daga ta karata a kunne.

Ita kuwa tana jin ta daga tace mata, "amarya manya!"
Tayi dum, "kamar ya amarya?"
Tace, "amarya mana! Naji ance yau an kai kudin aure har an sanya ranar auren ma!"

Tace, "ashe ku har labarin ya riskeku? Ni sai yanzu nake jin labarin ma!"

Sai Anty Lima tayi dum, tace, "wai kin ma san waye zaki aura?"
Tayi dan tsaki, "ina fa! Ai bani ma da wannan mutuncin da za a fada min. Sai gargadin dolene in aureshi ko ba na so!"

Anty Lima kuwa ta kyalkyale da dariya, tace, "to fa! Wannan wane irin aurene haka?"
Ta tabe baki, "oho! Ni dai nasan rabon da ayi irin wannan auren tun zamanin su Inna Deluwa!"
Ita kanta Mama dake jinta a lokacin sai data saki dan murmushi, ta mata dakuwa da hannu tana cewa, "ki fa kiyayeni Nadiya!"

Anty Lima kuma tace, "ai ki ma kwantar da hankalinki. Don kuwa kin san ko ma wanene, kuma nasan ma In shaa Allah ba zaki ki shi ba don kuwa ba shi da makusa. Dan gidan Hajiya Ummah ne, Habibullahi!"

Kawai sai ta kashe wayar. Ta dora hannu aka ta dargwaje da kuka. Mama sai ta tsaya kawai tana kallonta cike da mamakin wannan abu na Nadiya.

Cikin kuka tace, "tabdijam! Wallahi Allah in dai wanda za a aura min ke nan na rantse da Allah sai dai a kai mishi..."

Mama tayi maza ta tareta, tace, "kul! Nadiya, kul! Ki kiyayeni da wannan zancen naki na banza da wofi!"
Sai ta kara sautin kukan nata, tace, "haba Mama! Wannan rashin adalcin da me yayi kama? Shi Abban yasan halin mutumin ne? Ko kuwa yasan da irin niyyar da suka zo neman auren nawa? Kawai don dukiya ta rufe mishi ido sai ya kama ya aurar da ni haka kawai?"

Mama tace, "ban fahimci abinda kike cewa ba? Wace niyya kike magana a kai?"
Ita kuwa ta zauna ta fada mata duk abinda Anty Lima ta fada mata, da dalilin auren da manufarshi.

Mama tayi shiru tana saurarenta har ta gama, tayi ajiyar zuciya. Tace, "hakika wannan ba dalili bane na neman aure. Amma kuma hakan ba zai zama sanadin wargajewar aure ba. Don haka shawarar da zan baki ita ce, ki dage da addu'a kawai. Idan alkhairinki ne, Allah Ya tabbatar da auren. Idan kuma ba alkhairinki bane, Allah Ya musanya miki da wanda ya fi shi. Don kuwa Nadiya, idan kinga an fasa wannan auren to ikon Allah ne kawai. Ya fi miki ki sanyawa ranki salama!"
Ta tashi ta bata waje tana kara fashewa da wani kukan.

Nan Amarya ta sameta itama da nata kalar ban hakurin da shawara, amma Nadiya bata yi alamun ta saduda ba. Sai gajiya tayi ta tashi, Mama da take jinsu ta girgiza kai kawai a ranta tana addu'ar Allah Ya sanyaya ran Nadiya din. Don kuwa rigima ce kawai za a sha da bacin rai a banza, don ta bangaren Abbansu fa aure babu fashi.

Ranar barci sai barawo. Nan ya saceta akan gadon Mama tana ta bakin rai, ko kayan jikinta bata iya cirewa ba.

Tunda asubahin fari kuma sai ga kiran Madam. Wai kiranta tayi ta tayata murnar auren da zata yi, sannan kuma tana so su fara tattauna shirye-shiryen da zasu yi. Duk da cewa dai ta bangaren ango sun ce aure kawai za a daura, babu events babu komi, sannan kuma basu bukatar a yiwa amarya komi, haka nan suke so a kaita zikal dinta. Amma ita Madam din saboda jama'arta dake nan Kaduna din da wadanda zasu biyota, dolene zata shirya liyafa.

Nadiya tace mata, "Mommy ki daina wannan shirye-shiryen don kuwa aure dai ba da ni za a daura shi ba. Nace bana so, kuma ba shi nake so ba. Don haka tun wuri ma a fada musu cewa su je su nemo matarsu a inda take!"

Madam kuwa tace, "an ki a fada musu din Nadiya! Amma ke za ki iya zuwa ki tari Abbanki ki fada mishi tunda shi ya amshi kudin ya kuma furta musu ya basu, ki ga idan bai karya miki kafafu ba! Wai ke me yasa baki da tunanine ko kadan? Arziki yana kiranki amma kina guduwa?"

Ta cune baki kamar tana gabanta, "to ni ai ban ce yazo inda nake ba ko? Kuma ma auren ai ba don manufar Allah da Annabi bane za a yi shi. Dukanku son ranku kuke bi shi yasa ni kuke shirin sanyani a tsakiya!"

Madam tace, "lallai Nadiya wuyanki ya isa yanka! Ni kike fadawa wannan maganganun?"
Tayi shiru tana ta harare-harare ita kadai.
Ita kuwa ta cigaba da cewa, "wallahi ki gode Allah ba a kusa dake nake ba da sai na zubda miki hakora wallahi, sai dai a kaiki gidan mijin da wawulon baki! Aure kuma ko? To sai dai kiyi duk abinda zaki yi, amma kamar an daura ne an gama! Ban da ma shashanci irin naki da rashin sa'a da rabo, kamar irin Hajiya Umma su nemi hada zuriya dake amma ki ce baki so? Kin kuwa san irin matan da ke kara-kaina a kanshi kuwa?Suna so ya daga ido koda sau daya ne ya kallesu amma ke kin samu hakan a banza ki ce baki so? Kina ganin kin kai ajin Habibullahi kuwa? Ko baki san ya wuce da ajinki bane? Shashashar yarinya kawai wadda bata san Annabi ya faku ba!"
Ta kashe wayar.

Nadiya tayi zaune da waya a hannunta tana kallo, hawaye suna gangarowa akan fuskarta.
Can kuma sai ta share hawayen, ta shiga cikin jerin contacts dinta ta lalubo sunan Anty Jamila ta danna mata kira. Tana dagawa, kafin ta kai ga yi mata sallama ma, sai ta fasa mata kuka.
Nan da nan ta rikice ta fara tambayarta lafiya? Tana kuka da shessheka take fada mata ai Abbane zai mata auren dole. Bayan ita bata ma san mutumin ba kuma bata san halinshi ba.

Anty Jamila ta kama baki da mamaki, tace, "shi Abban?"
Ta amsa mata da saurinta, "eh! Wai har ya sanya rana bayan azumi da kwana goma...!"
Ta karashe tana kara sakin wani kukan.

Anty Jamila tace, "kada ki damu Nadiya, daina kuka kinji? Bari in kira shi muyi magana da shi ta fahimta. An mishi zancen Abdullahi ne?"
Tace, "ehh mana! Amma yace wai ya riga ya bada ni!"
Tace, "to daina kukan! Bari in kirashi yanzu!"
Tace, "nagode Anty. Don Allah ki fada mishi ni ba shi nake so ba, kuma mun riga munyi alkawarin aure da wani!"

Anty Jamila dai ta samu ta lallabata ta kashe wayar.
Ta koma ta kwanta tayi wani lamo sai kace abin tausayi. Bata yi niyar zuwa shago ba ranar sai da taga mutan gidansu suna neman wuce makadi da rawa sannan.

Shiga goma idan Amarya zata yi dakin Mama to sai ta rangadawa Nadiya guda ta bita da kirarin amare.

A gefe guda kuma ga su Salame can a tsakar gida suna ta sakin maganganu marassa kan gado suna shewa. Salame cewa take 'auren banza! Karyar tsiya ce kawai suke ba wani abu ba! Amma in banda haka, me zai hadin biri da gada? Farin ne fa kawai na fata ba wata tsiya ba!'
Maganganun nasu suka isheta, shima zaman ya isheta. Saboda bayan tunane-tunane da saka-da-warwara babu abinda take yi. Ta kuma kasa samun mafitar da take so.

Wajen karfe goma da rabi dai ta lallaba ta fito, rataye da yar karamar jaka a kafadarta. Har zuwa lokacin bata ko karya ba, har tayi wani zuru-zuru ta yi yar fuska.
Suka ci karo da Lantana a tsakar gida ita da wata yarinyar makotansu wadda yar dakin Salame ce. Hadiza ta kalli Nadiya tana ce mata, "kaji amare manyan mata! Sai muka sha kayan sanya rana yau. To Allah Ya sanya alkhairi!"
Nadiya ta kakaro murmushin yake tace, "uhm!" kawai tayi gaba.

Lantana kuwa ta tabe baki, ta harari Hadiza, "kin ji matsalarki ai ke kam! Kin iya zubar da aji a wajen da bai dace ba. Shi taya murnar auren na menene? Ni ai gwanda ma dai mutum yayi auren, ya shiga daga ciki dai yaji me ake ji, da irin masifar da ke cikinshi. An gama rabar da abinda ake auren dominshi a waje dai nasan mutum ai wallahi bai isa yayi daraja da mutunci a wajen namiji ba! Irinsu ne da sun shiga zaki ga an yo waje dasu! Yo ba a ganinsu da kima!"

Nadiyar tana jiyota, Amma ba ta tata take yi ba. Sai lokacin take fahimtar masu iya magana da suke cewa wai, 'ana ta kai wa ke ta kaya?!'
Hadiza kuwa sai ta kalli Lantana ta kyalkyale mata da dariya kawai ta shige dakin Salame.

Yadda kasan wadda kwai ya fashewa a jiki haka ta dinga takawa tana tafiya har ta fita bakin titi.
Kanta a kulle yake gam, ta rasa ta ina yakamata ta dafowa wannan al'amari daya kullo mata.
Tasan tunda Madam ta gama yin na'am da zancen, shima Abba ya amsar musu kudi, to zance ya kare. Don kuwa idan da akwai abinda Abbansu baya yi shine ya karbi kudin aure kuma daga baya yace zai maida haka kawai siddan, bai taba yi ba. Tasan kuma a kanta ba zai fara ba.
To amma kuma me yasa zai fara auren dole a kanta? Ya sha yin ikirarin cewa shi dai ba zai taba tursasa d'anshi ya auri wanda bai so ba tunda ba shi zai mishi zaman auren ba. To amma me yasa ita zai yi mata auren dolen? Saboda rashin galihu? Ko kuwa kudin daya gani ne suka rufe mishi idanu?

Ranar babu aikin data iya tsinanawa, yini tayi tana kiran Yayunta da abokan Abban da sauran Dattawan cikin danginsu da take ganin zasu iya sanyashi ya canza ra'ayi, amma bata samu taji zancen daya kwantar mata da hankali a wajen ko mutum daya ba.

21.


Ruwan da aka yini ana yi duk shi ya kara sanyaya mata jiki. Ranar ko da suka rufe shago bata tafi ba, ta zauna ita kadai anan tana ta lissafe-lissafen iska. Don kuwa duk zaren data kama sai taga karshenshi a cukurkude yake. Kawai sai ta tashi ta hau kaude-kauden kayan wajen. Washegari dai za a tashi da azumi da yardar Allah. Don haka sai can bayan Azzuhur zasu shiga shagon. Hatta da abubuwan da zasu bukata a washegari duk sai data fitar da komi, wai duk don ta cinye lokacinta anan don kuwa bata ma son komawa gidan da wuri.

Tana gudanar da yan goge-gogenta, yayinda take sauraren suratul Ma'idah daga speaker dake jone a shagon tana bi a hankali, ta ji alamun kamar ana kallonta.
Ta juya da shirin fadawa wanda ya shiga din cewa sun rufe shago, sai ta tsaya tayi kim tana kallon Habibullahi Babangidan Hajiya Ummah da shima yayi tsaye a bakin kofa yana kallonta.

Ya jima a wajen yana sauraren yadda take bin kira'ar karatun cikin taushin murya da kwarewa yadda kasan ita ce ma Alaramma Gwani Abdullahi Zariya gabadaya.
Ya dade yana kallon yadda take gudanar da ayyukanta cikin natsuwa da taka-tsantsan da kulawa. Yadda jikinta yake juyawa cikin wani salo mai daukar hankali da ita kanta bata san ta mallakeshi ba. Ya dan lumshe ido a hankali bakinshi dauke da murmushi marar sauti ganin yadda tayi wani kicin-kicin da rai, dan leben nan mai tudu da cika yana tabewa da melewa cikin alamu na tsiwa. A ranshi yake cewa, 'manta da matan da babu abinda suka iya sai kwalliya kawai da iya yi. Who like boring things? Ta kowace siga kuma, Nadiya is not boring. Macece mai cike da kalubale a tattare da ita iri-iri. Wannan challenge din, he wants to taste it!'

Ya taka a nutse zuwa kan kujeru da kwastomomi ke zama ya zauna yana kallonta, murya kasa-kasa mai cike da tura haushi yace mata, "two chocolate cupcakes please."

Aikuwa ta shaka din kamar yadda ya so, ta fara danna mishi harara kafin tace, "mun rufe shago na yau, za ka iya karawa gaba please."

Maimakon kuma ya tashi din, sai ya sake sakin murmushi, ya gyara zamanshi yana fuskantarta sosai. Yace, "Nadiya ko babu komi in ci darajar Angonki na gobe da zan zama. Bakonka Annabinka, ko kun rufe shago a matsayina na bakonki na cancanci ko da ruwa ne ai da lemu ko?"

Ta wani yatsine baki, "wani ango? Kuma wani aure? Ka je ka tambayi wanda ya baka auren kaji idan na yi na'am da hakan. Bako ko? To ba na maraba da kai, don haka zaka iya karawa gaba zuwa inda ake so ka je."

Ya dan yi ajiyar numfashi, "Nadiya, ki fa dinga duba irin maganganun dake fita a bakinki, ki bar ganin kina yaba min duk zancen daya zo bakinki fa ina yin shiru. I have my limits."
Ta kara tabe bakin dai, "sai ka daina zuwa inda nake kuma ka daina ja na da zance kaga idan hakan zata faru. Aure kuma ina kara fada maka, kaje ka kwashi kayan da kuka kai kasan ma inda zaka kaisu tun kafin lokaci ya kure maka. Ba zan aureka ba, ba kuma zan yi zaman aure da kai ba!"

Ya koma ya jingina da kujera tare da linke hannuwanshi a kirji yana jefa mata wani irin kallo, kallo mai cike da gargadin ta kama bakinta kamar yadda yace. Jikinta ya so yayi sanyin, amma ta ki ta saduda balle ta sadda kai. Gani take kamar idan ta mishi rashin kirki, zai iya janye maganar auren.

Sai kuma ya sake sakin wani murmushin, ya mata nuni da kujera tare da cewa, "ki zo ki zauna magana nake so mu yi dake ta fahimta."

Ta harareshi, ta harari kujerar daya nuna mata, ta kara gyara tsayuwarta alamun dai babu inda zata matsa.
Tunanin ta tafi ta barshi anan ma kawai take yi, ya ci kanshi shi kadai idan zai iya.
Shi kuma da yaga haka sai ya daga kafada, ya tashi shi ya bita har inda take. Ya tsaya a gabanta yana kallonta, hannu saye cikin aljihun wandon nikakken yadin Nules mai taushi ruwan zuma. An yiwa rigar dinkin senator daya tsaya mishi a gwiwa, hannun rigar kuma gajere ne.

Kusancin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login