Showing 36001 words to 39000 words out of 142169 words

Chapter 13 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

453

dawo gidan idan ta tafi, watakila gidan Anty Hauwa zata yi zamanta har zuwa jibin, ko ta koma gidan Dada kawai. Kayanta ta dawo ta dauka ko ta tura Aysha ta dauko mata.

Rayuwar Madam da iyalanta ba abinda idanunta zasu rufe bane ta nuna kamar bata gani ba. Don kuwa rayuwace da zubinta da tsarinta yafi kama dana mutanen Turai ba wadanda karatun Allah da Annabi ya ratsa ba.

Haka za ka tsinci uwa da diya ana hira ana shan hannu kamar abokai, wannan duk sharar fa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ge ne akan ka duba ainihin menene ya sanyasu dariyar. Wadda yawancinta akan tik-tok da Safiya din take yi ne inda take da mabiya masu tsananin yawa. Kuma yawanci raye-raye ne take yi da bin wakoki, sai kuma bangaren fashion da take tabawa. Tana nuna trending abubuwa dake tafiya da zamani da sauransu. A cikin rawar, da kuma fashion din, Nadiya bata ga na zaba ba, tunda dukkaninsu babu wanda zaka gani da shiga ta mutunci ko wadda musulunci ya bada umarnin ayi.

Kuma babu wanda Madam din ta taba daga baki tace ba daidai bane, sai ma kara mata karfin gwiwa da take yi da kuma yaba mata.

Ga rashin iya magana da girmama na gaba a wajen Safiya din. Ita kanta Madam bata tsira ba a wajenta balle su Nadiya yan karere. Ana hira sai kaga ta kalli uwar wai tace mata, "Mom you are silly!" ko kuma Idan wata maganar tayi kaji tace, "this is so stupid!"
Kuma da rana daya hakan bai taba bata ran Madam ba. Ko a fuska bata taba nuna mata ba. Shi yasa Nadiya ta kame kanta waje daya, don bata bukatar raini ko kadan. Musamman tun watarana data taba yiwa Safiyar magana akan gashin attachment data sanya a kanta da kuma wani wando mai kama da 3 quarter data sanya wanda bai saukar mata idon sawu ba wai zata tafi unguwa a haka. Ta kalli Nadiya din kerere tace, "gaskiya ki daina shiga harkata kin gane? Iyayena ma da suka haifeni basu takura ni, duk abinda naga dama shi nake yi, don haka kada ki kara sanya min baki a cikin al'amurana! Ina ruwanki da ni ne? Kiyi rayuwarki inyi tawa!"
Taja tsaki ta kara gaba tana wasu maganganu cikin turanci. Tun daga ranar Nadiya ta kai na mujiya ta zuba mata.

Madam ta kalli Nadiya lokacin da suke kokarin wucewa bayan sun mata sallama.
Tace, "kinga na manta shaf! Ki shirya anjima da dare zamu je mu gaida Hajiya Umma."

Kafin ta maida mata da martanin wani abu, Anty Lima tayi tsalle cike da murna ta dafeta, cewa take yi, "Mommy don Allah nima zan je kinji?"
Madam tace, "to shikenan, amma fa ki shirya da wuri kinji?"
Ta gyada kai cike da murna, yayin da Madam ta juya ga Nadiya tana kallonta, tace, "ke kuma ki kimtsa cikin shiga mai kyau. Na sanki da rashin son daukar ado, amma yau dai gaskiya kiyi shiri da kyau, kina ji na?"
Bata iya ce mata komi ba sai kai data daga mata.
Suka wuce ita da Anty Lima.

A mota take bayyanawa Anty Limar mamakin wannan hali na Madam da yadda take shigewa Hajiya Umma.
Anty Lima ta dan kalleta rabin hankalinta a kan tuki. Tace, "ke na fa ji ana kishin-kishin din da gaske Hajiya Umma mata take nemawa danta. Ita kuma Madam shagone babba suke son budewa a nan Kaduna, to kuma dai basu da takamaiman mai shige musu gaba a wannan harkar. Ita kuma Hajiya Umma tana da mutane sosai a ofishin haraji da harkar filaye. Naji ma an ce kamar dan nata yayi aiki da Ministry of Tax."

Nadiya ta jinjina kai tana dan tabe baki. Anty Lima ta cigaba da cewa, "naji an ce ma kokarin neman kujerar Gwamna fa yake yi. To a yadda dai naji, ita Madam tana son yin amfani da connections din Hajiya Umma ne, ita ma Hajiya Ummar tana nemawa danta diyar da take da connection ne da kuma mutanen da zasu goyawa danta baya a harkar siyasarshi, kin gane?"

Nadiya ta gyada kai, ba wai don ta fahimta din ba.
Anty Lima ta kalleta dai-dai tana danna hancin motarta gidan Anty Hauwa, tayi parking. Nadiya na kokarin fita ta dakatar da ita ta hanyar tambayarta, "kin san dalilin abincin da kike dafawa ana kaiwa Hajiya Umma kullum kuwa?"
Nadiya ta kalleta cike da alamun tambaya, "ba na tara bane da bakunta?"

Anty Lima tayi wata irin dariya tana girgiza kai, tace, "gaskiya you are so naive! To bari in fada miki, wannan abincin na kamun kafa ne. Don kuwa a yadda nake jin labari a gari, shine Madam ta sanya 'ya'yanta cikin jerin matan da Hajiya Umma take nema. Ki kuma tsaya da kyau kiyi tunani, duk cikin danginmu wa yake da exact abun da Hajja Umma take dashi bayan Madam? Tana da manyan mutane a hannu, tana da talakawa masu yawa da idan tace su zabi wane zasu zabeshi a guje. Musamman a yankunan Kaduna da nan wajajen Jos saboda tana yawan tallafawa mutane."

Nadiya ta ja numfashi tana kallonta alamun tambaya zane baro-baro akan fuskarta, tace, "yanzu duka meye amfanin wadannan abubuwan da kike fada min? Don bana tunanin ni dai na fahimceki!"

Anty Lima ta dafa kafadarta, tace, "saboda bayan Safiya akwai ki! Kin kuma fi ni sanin cewa idan ta kama, a tsakanin ku biyun nan fa za a iya zabar daya. I'm just telling you ne saboda kada abin yazo miki as a shock idan muka je can, don naga Madam din bata da niyar sanar dake komai!"

Nadiya tayi zaune a wajen ta kasa ko daga kafarta saboda tsananin mamaki da tu'ajjibi. Jikinta yayi sanyi kamar wadda aka watsawa ruwan kankara. Kafin daga baya ta motsa da kyar cikin rashin kwarin jiki ta bi bayan Anty Lima da tuni tayi nisa.
Ta auna duk awon da zata yi taga kwata-kwata zancen ma ya girmami kwakwalwarta. Sai kawai ta watsar da komi ta barsu a inda Anty Lima ta furtasu.

Shigarsu gidan Anty Hauwa da irin tarar data musu yasa ma gabadaya sai ta karasa mancewa da komi.
Yinin nan guda haka suka yi shi a gidan. Anty Lima taje gida ta dawo can wajen Magriba.

Bayan ta sha ruwa, sun cika cikinsu sunyi nak, suka yi sallama da Anty Hauwa din suka juya.

Suka samu tuni har Madam ta kammala shirinta don haka suma a gurguje suka fada daki suka shirya.
Anty Lima ta saka wata doguwar riga ta atamfa gown mai kyau, ta yafa mayafi madaidaici ba tare data daura dankwali ba. Nadiya kam Abaya ta sanya maroon kirar kasar Turkiyya. Tayi nadin gyalen abayar a kanta. Sai ta fito das gwanin kyau duk da cewa ba wata kwalliya ta azo a gani ba ta yi. Musamman da yake rigar ta bi jikinta das. Yanayin jikinta mai kiba dai-dai wa dai-da yasa mawuyaci ne ta sanya kaya basu amsheta ba. Tunda tana da kira da zubi da tsarin jiki mai kyau.
Suna gama sallar isha'i suka fita.

Safiya yau riga da siket aka sanya na leshi. Ta ci kwalliya kamar zata gidan biki. Ta nada daurin dankwalinta aka ya zauna daras kamar inji ya daura mata. Suka fita su duka suna ta zuba kamshi wane kamfanin turare.
Anty Lima da Nadiya suna gaba Anty Limar na tuki a cikin motarta, Madam da Safiya na baya sun hade kai suna ta kus-kus baka jin me suke cewa. Suka dauki hanya suka tafi.

Gidan da aka yiwa Hajja Umma masauki a can main house din family dinsu yake. Unguwa ce guda da suka ware ya zamana kusan duk su suka mamayeta sai daidaikun mutane da ba a rasa ba.
Madaidaicin gidane, flat mai dauke da dakuna uku sai kicin da kuma sitting room saboda shan iska.

Aka yi musu iso zuwa cikin falon inda suka samu Hajiya Umma din a zaune akan kujera mai daukar mutum biyu.

Duk yadda Nadiya take tunanin ganin matar sai ta ga ashe ganinta ya fi jinta. Yadda taji ana 'Hajiya! Hajiya!!' Sai tayi tunanin wata babbar mace zata gani, sai ta ga ashe girman nata ba wani can bane. Sai taga magidanciyar mace mai cike da izza da takama da mulki da dukiya. Kwarjininta ya cika falon. Duk rawar kan Safiya dana Madam sai gasu sun shige taitayinsu. Suka zube a kasa kan gwiwoyinsu suna gaisheta.

Ta amsa musu fuska kadaran-kadahan, babu alamun wasa balle a ga fuskar raini a tattare da ita ko kadan.

Sai da tayi musu umarnin su zauna sannan ne suka nemi kujeru suka zauna.
Nadiya dai ta zauna a darare kamar ace mata 'arrr!' ta ruga. Falon take karewa kallo, a sace kuma tana karewa Hajiya Umma kallo wadda suke hira da Madam. Kodayake Madam din ce take kokarin janta da hira ita kuma tana amsawa da kyar kamar wadda ake tursasawa.

Wannan mulki da iko sai ya daurewa Nadiya kai. Mace sai kace wata jinin sarauta? Ta girgiza kai kawai cike da Al'ajabi. Lallai fa gaskiyar bahaushe da yake cewa wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Ita dai kam yau taga hakan da idanunta. Har Madam ce take zama tana yar murya a gaban wani? Lallai in da ranka zaka sha kallo.

Aka shigo musu da kayan motsa baki da ruwa da lemuka. Ta tsiyaya ruwan a cikin kofi kadan tana kurba saboda har zuwa lokacin cikinta a cike yake. Tun kafin su dade a wajen amma tuni har ta kosa a tashi.

Tun kafin ya karaso cikin falon, kamshin nan nashi ya sanar da zuwanshi. Yayi sallama da tausassar muryarshi, duk suka amsa.
Sai lokacin taga alamun murmushi akan fuskar Hajiya Umma. Ta daga kai tana kallonshi, tace, "yauwa Babangida! Yanzu nake kokarin aikawa a kiraka. Karaso ka zauna!"

Ya zagaya ta bayan kujerar da Nadiya take zaune, kamshin nan nashi more prominent, duk kinta, sai data lumshe idanunta tana kara shakar kamshin.
Ya zauna a kujerar kusa da Hajiya Umma hankalinshi kacokam a kanta. Yace, "gani Ummah!"

Ta mishi nuni da su Madam, "Ga Zahra'u da 'ya'yanta da nake fada maka, ku gaisa!"
Sai a lokacin ya daga kai ya kallesu daya bayan daya. Kallon nashi yaso yayi tsayi akan fuskar Nadiya, kafin ya janye ya mayar kan Madam. Ya dan zame daga kan kujera ya gaisheta ta amsa fuskar nan cike da fara'a.
Dan dakatawa yayi yana kallonsu, hakan yasa suka bude baki suna gaisheshi. Nadiya dai baki kawai ta dinga motsawa har aka gama gaisuwar. Daga nan ta bame bakinta ta daure, yar hirar da yaso yaja su da ita bata yi tsayi ba ta mace saboda babu abin cewa.

Falon ya dan yi shiru na yan mintuna. Sai Hajiya Umma ta sauke kallonta akan Safiya dake danne-dannen waya. Tace, "'yata Safiya! Yau ko a gidan nawa za a hada min kunun da ake kawo min? Kinga mai son kunun nan a zaune, tun jiya yake mita da tambayar kunun gyada!"

Falo sai yayi tsit! Aka hau kallon-kallo tsakanin Madam da su Nadiya. Safiya ta fara raba kallo tsakanin Hajiya Umma da Madam cikin alamun tambaya. Madam kam sai ta hau kame-kame, in ba don dare ba, Nadiya sai ta rantse da Allah ko zufa ce ta gani tana yanko mata.

Hajiya Umma ganin shiru babu mai shirin motsi yasa ta kalli Madam cikin alamun tambaya. Tace, "Zahra'u diyar taki ko kunyata ne take ji?"

Madam ta dan zaburo, "ah! eh... Dama!! Nadiya ko ke zaki shiga ki dama mata kunun?"
Ta juya tana kallon Hajiya Umma cikin dariyar yake, "dama... dama gani nayi Nadiya ta fi ta iya kunun shi yasa...! Nadiya tashi mana!!" Ta yi maganar cikin daga murya ganin Nadiya din bata da alamun motsawa balle ta tashi.

Da sauri ta tashi itama tana inda-inda, "ina ne... kicin din...?"
Hajiya Umma tana shirin daga baki tayi magana, Babangidan nata ya tashi da sauri, "bari in nuna mata. Dama ruwa na shigo zan dauka saboda na dakina ya kare!"
Ya wuce yana kallon Nadiya a kaikaice, "yauwa nan ne!"
Jiki a sanyaye ta bi bayanshi tana satar kallon Madam dake ta raba idanu. Gabadaya ta kasa gane me yake faruwa ne balle ta iya rarrabe tsakanin fari da baki.

Kicin din nasu kusa da kofar shiga yake. Ya tura kofar ya shiga tana bin shi a baya. Kai tsaye wajen firjin ya nufa ya daga ya dauki ruwa, ya fasa ya juya ya jingina da firjin din yana sha. Ya daga gira ganin har lokacin tana a tsaye, ya mata nuni da dirowa, yace, "ki daga nan, zaki samu duk abinda kike so anan. Amma ki dan dama kunun da yawa saboda wanda ake bani baya isa ta."

Ta kalleshi, a ranta tana mitar 'rashin ta idon wannan mutumin!' amma a fili sai kawai ta wuceshi ta kara gaba ta hau dage-dagen drawers din tana fito da kaya.

Tana jinshi ya gama shan ruwan ya jefa gorar cikin dustbin, amma maimakon ya fita sai ya tsaya. Ita kuwa tayi kamar bata jin shi ta cigaba da gudanar da ayyukanta.


16.


Tana jin shi yana ta yan kaiwa da kawowa a cikin kicin din ba tare da yace mata uffan ba, itama bata furta mishi din ba. Ya gaji da bin-binintun shi dai ya bar kicin din.
Ta kammala komi cikin kankanin lokaci tunda suna da komi a ajiye. Ta dauko flask mai kyau ta fara zubawa a ciki. Sai gashi tsulum! kamar wanda aka jefo daga sama. Yana ganin ta kammala shima ya sungumo wani flask din wanda ma ya fi wanda ta dauka girma, yace, "yauwa, dan zuba min anan. Ai dama ke nake ta jira tun dazu don kada ki juye duka!"

Bata ce mishi komi ba ta warci flask din ta fara zuba mishi. Data zuba kamar rabi zata maida ta rufe, yayi sauri yace, "a'ah, cikawa zaki yi. Wannan ai har da safe ma zan sha kayana."
Ta watsa mishi harara a kaikaice, ta cika mishi ta ajiye flask din a gefe. Ya dauki kayanshi shi kuwa yayi gaba babu ko na gode. Ta ja dan siririn tsaki kafin ta cigaba da abinda take yi.

Bata bar kicin din ba sai data wanke duk abinda tayi amfani dashi, ta gyara wajen kamar ba ayi komi ba. Ta dauki flask din da kofuna ta koma falo. Ta samesu duk sunyi jugum-jugum kamar a gidan makoki, banda karan TV dake aiki baka jin komi.
Ta karasa ta ajiye kayan a gaban Hajiya Ummah, ta tsiyaya kunun a kofi ta mika mata, ta koma ta zauna.

Sai data shanye kofi daya ta kara zuba wani ta sha rabi, sannan ta kalli Madam, ta kirata da murya mai nuna rashin wasa, "Zahra'u!"
Madam ta amsa cikin sagewar gwiwa.
Tace mata, "'ya'ya, 'ya'ya ne, sannan kowa da irin baiwar da Allah Yayi masa. Don haka babu zancen wai ace wance ce tayi kaza alhali kuma ba ita bace. Wannan tauye hakki ne da rashin gaskiya, kada ki sake yin haka kina jina?"
Madam ta gyada kai kanta a kada. Nadiya tasan kunya ce da takaici suka mata rubdugu. Ita kuwa Hajiya Umma ko a jikinta, sai kai data gyada.

Tace, "zaku iya tafiya. Duk abinda ake ciki zaki ji daga gareni."
Ta daga murya ta kira daya cikin yan aikinta, sai gata ta taho dauke da jaka ta mikawa Hajiya Umma. Ta amsa ta sanya hannu a ciki ta fito da envelope-envelope ta mikawa su Nadiya kowa dai-daya, suka amsa suka mata godiya. Daga nan suka mata bankwana suka tafi.

A mota ma haka suka tafi babu mai cewa uffan har suka karasa gida. Suna zuwa kuwa kowa makwancinshi ya nufa.
Sai da suka shiga daki suka daga abinda Hajiya Umma ta basu. Kudi ne yan dari biyar-biyar sabbi gal, kowa dubu hamsin. Nadiya ta nade su ta sanya a jaka, ta fara shirin kwanciya barci.

Har ta kwanta, suna cikin yin waya da su Maryam, Anty Lima data fita daukar ruwa kicin ta shigo dakin da saurinta tana tsallen murna.
Nadiya ta kashe wayar tana kallonta fuska dauke da dan murmushi, "ke kuma lafiyarki lau kuwa yau?"

Ta zauna a gefen katifa har lokacin bakinta dauke da murmushi, tace, "ke Madam naji tana waya da Hajiya Umma yanzu!"
Ai sai Nadiya ta gyara zama tana kallonta, "ya aka yi, me ya faru?"
Tace, "abin fa ya fado kanku ku biyu. Naji tana ce mata cikin ku biyun dai za a dauki daya!"

Sai ta dan yamutsa fuska, "wane abu? Kuma kamar ya cikin mu biyu za a dauki daya? Ban gane ba!"

Anty Lima ta dan ja tsaki, "ke fa matsalata dake kenan wallahi, baki cika tsayawa ki fahimci al'amura da kyau! Ina nufin a jerin matan da ake shirin zabarwa Habib, dan wajen Hajiya Umma, to ke da Safiya aka zaba. Yanzu a tsakanin ku biyun ne za a zabar mishi daya!"

Ta dafe kirji tana kara gyara zama, "Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un! Me kika ce?!"
Anty Lima sai ta tsaya tana kallonta kamar wata wadda wani sabon kai ya tsiro daga jikinta, ta danna mata harara, tace, "to menene a ciki? Sai in ga hakan ai ba wata matsala bace. Ina ganin Habib ai mijin aurene na nunawa sa'a. Yana da hankalinshi, yana da sana'arshi, ga iliminshi, don naji ance har phD yayi. To kuma me za a nema a wajen miji da yafi wannan? Ko kuwa matar da yake da ita ne zata tsorataki?"

Ta ja dan siririn tsaki, "ba zaki gane bane wallahi Anty Lima. Gayen ne kwata-kwata bai min ba, kuma fa ni har ga Allah ni fa har yanzu ban shirya yin wani aure ba. Idan ma auren ne a barni inyi shi da wanda nake so. Amma ni don wata matarshi meye hadina da ita? Tayi rayuwarta inyi tawa. Kawai auren da shi dinne bana tunanin zai haifarwa wani da mai ido."

Anty Lima ta tabe baki, "aikuwa sai kiyi ta fatan kada ta fada kanki!" Tayi kwanciyarta ta bar Nadiya tana canki-canka.

Itama kwanciyar tayi, amma gabadaya sai barci ya kauracewa idanunta sam. Tsoro kai tsaye ya bi ya mamaye mata zuciya. Tunaninta daya idan fa aka ce ta auri wannan mutumin me zata yi? Bata tunanin gaskiya zata iya zaman aure da mutumin da bata so kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login