Showing 66001 words to 69000 words out of 142169 words

Chapter 23 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

457

sake yin wata kwalliyar cikin atamfa holland abinta. Da bakin Madam yan Maiduguri suka je gidan nasu, aka hadu dasu aka cigaba da gudanar da hidimar biki.

A ranar ta Juma'ah bayan an fito daga sallar juma'ah a babban masallacin unguwarsu, aka daura auren na Nadiya Auwal Iko da Habibullahi Abdullahi Makama. Akan sadaki naira miliyan daya, lakadan ba ajalan ba.
Mata suka dauki guda da shewa, yara suka hau tafi da murna lokacin da sakon daura auren ya riskesu.

Tana can cikin zugar su Anty Lima da su Aramide da suke ta mata tsiya, ita kuwa gabadaya ta rasa sukunin biye musu ma kwata-kwata.
Aka shiga sanarwar ango zai shigo gida a gaisa da mutane. Nan ya shigo har cikin falon Mama cikin zugar abokanshi, ya sha shadda fara tas tana ta sheki. Suka kwashi gaisuwa tare da godiya suka juya suka tafi.

Tana jinsu har suka gama gaisawar, zuciyarta na aikin bugawa a gaggauce. Rabon data sanyashi a cikin idanunta tun ranar sallah da yaje. Da bikin ma ya kara matsowa sosai, sai wayar da suke yi ta ragu.
Tana dai jin su Anty Lima na gulmar irin kyawun da angon nata yayi, bata iya ce musu komai ba.

Aka cigaba da hada-hada da hidima a gidan. Anty Hauwa da Amarya su suke ta shige da ficen hada mata kayayyakin da masu kai amarya zasu wuce mata da su.
Ana yin sallar la'asar, taji ance wai a fara shirya amarya ga motocin daukar amarya nan sun taho. Sai idanunta duk suka raina fata, hawayen da tun safiyar ranar suke son zubo mata tana makalesu, suka hau kwarara. J??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in abin da take yi kamar a mafarki, sai a yanzu ta fara yarda da lallai gidansu zata bari.

Anty Hauwa ta ja ta bayi, ta hada mata wani irin ruwa tayi wanka dashi mai tsananin kamshi da sanya fata laushi. Data fito kuma ta tareta da turare kala-kala, tayi na tsuguni, aka yi na jiki, aka yi na gashi, aka yi na kaya. Abu fa sai gata ta zama kamar wata gidan kamshi. Duk inda ta motsa sai kamshi ya watsu.

Wani swiss lace aka sanya mata riga da skirt, rigar ta sha adon stones da net, idan ka gani sai kayi tunanin ko inji ne yayi dinkin ba mutum ba.
Gashin nan nata da ya sha gyara yana ta kamshi, aka sakar mata shi ya sauka har baya, saboda ta hana a fiddo wani ya zuba a gaban goshinta. Aka kai bakar Alkyabba aka dora mata.

Da aka kaita gaban Mama tayi mata nasiha, kawai sai ta dora kanta akan cinyar Mama din ta fashe da kuka sosai. Baiwar Allah itama Mama din sai ta kasa cewa komi, ta dora hannunta a gadon bayan Nadiya din tana shafawa a tausashe, daya hannun kuma tana share mata hawayen.
Da za a fita da ita har dakinsu Salame da Lantana aka shiga da ita son suyi bankwana, Salame dai cewa take, "ayi hakuri, zaman aure dan hakuri ne."
Lantana kuma na aikin amsawa da "kwarai kuwa. Hakane kam!"

A haka su Anty Jamilah suka ja ta aka fita da ita zuwa inda motoci suke jiransu.
Ba wasu mutane aka dauka da yawa ba, daga Anty Jamilah din, sai Anty Hauwa da Maryam da Anty Lima da Amarya. Da suka tsaya gidan Madam itama ta mata nasihar da zata musu, sai abokiyarta daya ta bi bayansu.

*

Gidansu Habibun gidane ba kamar sauran gidaje da suka sani ba, haka ba irin gidan da Nadiya tayi tunanin tararwa bane.

Kanta a kasa yake tunda aka fara tafiya, jifa-jifa hawaye kan diga daga cikin idanunta tasa hannu ta share.
Daga bakin mutanen cikin motar take jin irin hirar da suke game da haduwa da tsaruwar gidan.
Masu jan motar suka kaita har kofar sashen da Nadiya din zata zauna, acan suka samu Rashida a tsaye tana jiransu. Ita tayi musu jagoranci har zuwa ciki.

Suka shiga ta wani lafiyayyen falo, ya sha leather seats jajaye, suka ratsa ta wani karamin corridor suka karasa dakin Nadiya din.
Dakin madaidaicine, gado ne sambal dan kasar Italy ya sha lullubi da zanin gado mai taushi, aka kama hannunta aka zaunar da ita a gefen gadon.

Su Anty Lima sune masu karade gida don ganin me ya kunsa? Kuma kowannensu ya yaba, ya kuma gamsu da abinda ya gani. Don kuwa tsayawa fadar irin daula da aka narkar a wannan waje ma bata baki ne. Aka shigar musu da abinci a cikin kuloli da lemuka.

Da suka gama zagaye da yan gyare-gyaren da zasu yi, Rashida ta musu jagoranci har wajen Hajiya Ummah. Ta musu tara ta girmamawa, ta bisu daya bayan daya ta runguma, fara'a fal fuskarta da nuna jindadi. Da ta yiwa Nadiya nasiha game da hakuri da rayuwar aure, sai ta bisu da godiya da ban gajiya. Ta kuma bi yan kawo amarya da dubu ashirin-ashirin, kafin tace a kaita sashen Uwargida don tayi mata maraba. Haka suka tafi ransu fal farinciki da jindadin wannan mutunci da karamci na Hajiya Ummah.

Zuwanau sashen Shukurah kuma sai ya sage musu gwiwoyi. Sun samesu su uku ne kadai a falon. Suka yi sallama aka amsa, sauran gaisuwa kuma data biyo baya babu wanda ya taga musu. Su Anty Jamilah suka karaci maganganunsu suka gama, in bango yayi magana to sun tanka. Don Uwargida ma ana cikin bada amanar ta shuri takalminta tayi cikin daki abinta. Suma da suka ga haka sai suka lallaba suka juya.

A dakin Nadiya Anty Jamilah ce take kara yiwa Nadiya fada da wa'azantarwa, zaman aure dan hakuri ne musamman gida na kishiya, wanda kuma za a zauna tare da suruka. Tace tasan dai ba zata samu wata matsala daga Hajiya Ummah ba, itama kishiyar tata tayi kokari ta fahimceta, ta bata girma da hakkinta, don ta taimakawa mijinta kwatanta adalci a tsakaninsu.

Miji kuma tsakaninta dashi yi, na yi. Bari, na bari. Matukar hakan bai sabawa addini ba. Ta girmamashi, ta girmama mahaifiyarshi. Ta kaunacesu tsakaninta da Allah, ta kuma kiyaye hakkinshi dake kanta.
Da suka gama nasihar, lokacin har an fara kiran Magriba, suka mata sallama zasu tafi.

Anty Jamila tace mata, "na cewa Yaya AbdulHadi ya amshi sadakinki ya ajiye miki, bayan biki zan mishi magana sai ya turo miki su ko kuma a duba wani abu a saya da su."
Ta gyada kai tana sharar hawaye. Bata yi mamakin jin hakan ba. Don duk yanmatan gidan da za a aurar a gidansu to Abbansu idan ya amshi sadaki baya badawa, idan kuma an mishi magana yace hidimar biki yayi dasu. Don haka daga baya sai Yayunsu maza suke amsa da kansu, in yaso daga baya sai a ba amaryar tayi abinda zata yi da su.

Haka tana ji tana gani su Anty Lima suka tafi. Ta zauna tsuru ita kadai anan. Kadaici da tunane-tunane suka dameta. Daga karshe dai ta mike a hankali ta shiga bayi.
Bata tsaya duba abubuwan ciki ba da yabawa yadda aka tsara wajen, aka wadatashi da duk wasu abubuwan da za a bukata a bayi. Kawai tayi alwala ta fita.

Kofar da taji ana cewa nan wardrobe take ta bude, sai ta tarar da walk-in closet. Nan kam tsayawa tayi baki a bude kawai tana karewa komi kallo. Duk wata sutura, babu wadda babu. Sashen komi kuma daban. Sashen atamfofi da lesuka gasu nan, shaddodi gasu nan, ga jakunkuna da takalma suma ba su kirguwa. Ga mirror da itama aka shake samanta da kayan shafa da turaruka, a kusa da ita kuma wani dogon show glass ne da aka shakeshi da humrori da turarukan wuta da mayukan shafa hadin hannu, tasan wannan aikin su Anty Hauwa ne.

Ta samo hijabi mai tsayi ta sanya, ta fuskanci alkibla ta tayar da sallah. Koda ta gama bata tashi ba, ta cigaba da zama akan abin sallar tana lazumi har aka kira isha'i, ta yi. Ta daga hannunta sama tana addu'a, duk akan Allah Ya jibanci lamuranta game da wannan sabuwar rayuwa data shiga.

Bayan lokaci mai tsayi ta tashi tana nade abin sallar da hijabin jikinta, sai taji an yi knocking, kafin aka turo kofar dakin aka shigo. Ta juya a hankali tana kallon angon nata dake saye da doguwar farar jallabiya, shi kuma ya karasa shiga cikin dakin tare da maida kofar ya rufe.
Kallonta yake, in appreciation. Kayan sun matukar yi mata kyau fiye da tunani, haka sun fitar mata da kirarta kwarai da gaske. Musamman da yake babu kallabi a kanta sai gashinta da yayi baya ya kwanta, hakan sai ya kara kayatata a gareshi sosai.

Ya tsaya a gabanta yana cigaba da kallonta, ita kuma haka kawai ta tsinci kanta da rawar jiki da sagewar gwiwa. Yasa hannu ya karbe hijabin hannunta ya ajiye a gefe.
Yayi murmushi ganin yanda tayi wani tsuru-tsuru tana muzurai kamar wadda aka kama ta yiwa sarki karya.
Yace, "Tubarkallah Amarya. Ma shaa Allah. You look so breathtaking wallahi Nadiya! Anya zan iya jumurin bari wani ya kalle min ke kuwa, ba zan kulleki a dakina inyi ta kallonki ni kadai ba?!"
Ta rasa kalar amsar da zata bashi, kawai sai ta buge da gaidashi, tace, "ina yini?"

Yayi dariya sosai, ba zato kuma sai tsintar kanta tayi cikin jikinshi. Kanta saman kirjinshi tana iya jiyo bugun da zuciyarshi take yi, yace, "lafiya lau Love. Ya bakunta?"
Ita ai tuni bakinta ya gama macewa, abubuwan da kusancin da suka yi suke haddasa mata a jikinta suna da yawa. Bugun da zuciyarta yake yi shi kanshi sai daya jiyo shi. Yayi dan murmushi, "to, tun kafin a kai ga zuwa ko'ina har na kashe bakin tsanyar? Ko kuwa dai saduda ce kika yi tun yanzu?"

Ita dai ta kasa ce mishi komi, yadda kasan wadda aka cirewa duk wata laka ta jikinta.
Yace, "ki zo muje Ummah take nemanmu, idan mun dawo sai ki fada min dalilin wannan shan kamshi da ake min. Da kuma tukuicin yabawa kwalliyarki da nayi, tunda ni na cire tawa kafin ki kai ga yaba min din."

Yadda kasan wata mutum-mutumi, haka ta tsaya ya taimaka mata ta sanya hijabi. Sannan shi da kanshi ya lalubo mata takalmi flat mara nauyi ta sanya, kafin ya kama hannunta suka fita.
Har sai daya daga kofa zasu fita, sai kuma ya mayar da ita. Ya juya ga Nadiya dake jefa mishi kallo mai dauke da alamar tambaya, sai dai kafin ta kai ga tambayar, ya hade bakinsu waje daya.

Zuciyarta ta hau daka da lugude a kirjinta cikin wata dimuwa data ziyarceta. Wani al'amarine yake faruwa da ita wanda bata taba tsintar kanta a cikinshi ba tunda take.
Habibu kam bai ma san abinda ke wakana da ita ba, bidirinshi kawai yake yi. Don kuwa lebunanta sun jima suna tsole mishi idanu. Sai daya gama shanye duk wani janbaki da wet lips dake bakinta kafin ya saketa, ya hade goshinsu waje daya idanunshi a lumshe yana sauke wani irin numfashi. 'Da ba don Ummah bace me kiransu...' Sai kuma ya girgiza kai.
Ya bude idanunshi a hankali yana kallon yadda nata idanun suke a rufe itama, numfashi take ja tana fesarwa a sukwane kamar mai fama da cutar numfashi.

Ya kai hannu a tausashe yana goge gefen bakinta inda ya damalmale da janbaki, sai daya goge mata shi tsaf kafin ya kalleta da rinannun idanunshi. Data kasa daukar kallon nashi sai tayi kasa da nata idanun. Murmushi ya saki mai sauti, yace, "bari dai muje mu dawo, zan fayyace miki wasu sirrika na musamman Nadiya! Na ga alamun dai ke baki san kalar wainar da nake toyawa bane a cikin raina!"

Ya sake bude kofa suka fita, ya rufe kofar da makulli ya damka mata a hannu kafin suka wuce sashin Hajiya Ummah kai tsaye.

Sun sameta a zaune a falo ita da Shukurah akan kujera. Ya wuce kusa da ita kai tsaye, ya zauna a kasan kujerar da take kai kusa da kafafunta. Da Nadiya taga haka, itama sai ta bi sahunshi. Ta zauna a gefenta na dama tana mai dan bada nisa dasu kadan.

Hajiya Ummah ta hadesu waje daya. Nasiha tayi musu sosai wadda yawancinta maimaicin abinda ake ta fadawa Nadiya ne tun da garin ranar ya waye. Bayan nan kuma sai dokar gidan da take a kafe tun ba yau ba, ana haduwa anan sashenta duk safiya a karya, haka ma abincin dare a can ake ci. Don haka ko kina girki ko ba kya yi, dole sai kin halarta. Idan ma kaga zaka iya, har da rana zaka iya zuwa ka ci abinci. Idan kuma kaga dama, zaka iya hada naka a bangarenka, tare da maigidan idan kaine da girki ranar. Ta tambayesu sun fahimta? Duk suka ce mata ehh.

Sai kuma ta juya ga Habibu tana tambayarshi kwanaki nawa ya debar musu na girki? Ya amsa da bai kai ga yanke wannan hukunci ba. Don haka tace musu to bayan Nadiya tayi kwanakinta bakwai kamar yadda al'ada da addini suka zartar, zasu cigaba da yin kwanaki bi-biyu a tsakaninsu. Da suka yi na'am da hakan, sai tace to kowace ta wuce sashenta sai da safe.

Nadiya da Shukurah suka tashi suka fita. Suna fita Shukurah ta daga kafa ta wuce abinta kamar dama mintsininta ake yi. Nadiya kuwa ta tabe baki ta wuce sashenta itama.

Suna bada baya Hajiya Ummah ta kalleshi, tace, "Habibu ka bani hankalinka nan, akwai magana mai muhimmanci da zamu yi da kai!"

Sai ya mayar da hankalinshi gabadaya kanta.
Tace, "amarya dai gata nan an kawo maka. Na gode maka da biyayyarka a gareni, Allah Yayi maka albarka!"
Yayi murmushin jindadi, "Ameen ameen Ummah!"

Tana shiru tana kallonshi a hankali kafin ta nisa, tace, "abu daya nake so kayi min Habibu. Ni nasan ba zan hanaka zama da matarka ba, sai dai ka fahimci cewa, auren nan naku na wucin gadi ne!"

Ya daga idanu da sauri, a birkice yana kallonta. Yace, "wucin gadi kuma Ummah?!"
Ta gyada kai, "kwarai! Dogon labari ne, wanda ba zai yiwu a gama shi da wuri ba idan nace mu fara. Saboda haka nake so, ka takaita yawan haduwa da ita. Bana son abinda zai dawo daga baya ya bata maka rai shi yasa nake fada maka wannan yanzu. Da zarar lokaci yayi, zaka sallameta ne. Saboda bata dace da kai ba ko kadan. Akwai mata da yawa a ciki da wajen Kadunar nan. Zan kuma yi kokari in mayar maka da wadda ta fita a komi. Ta zauna dai da sunan tana a matsayin matarka, amma hada jini da ita shine abinda ban amince ba. Ba zama tazo yi ba, don haka ban ga amfanin hada zuri'a da ita ba. Ka na jina?"

Ya gyada kai a matukar sanyaye. Duk wani buri da kudiri na duniya, babu wanda bai dauka ya ta'allaka ya dora akan wannan dare ba. Me ya faru ne haka? Ya shirinshi yake kokarin shan ruwa ne?

Tace, "yauwa. Kayi kokari ka kiyaye hakan. Ka kuma dinga tunawa da cewa kana da wata Matar a gefe, wadda zata iya baka duk wani abu da zaka bukata a wajen mace. Mace ai macece, menene zata nunawa yar uwarta mace? Don haka ka tashi abinka, kaje ka kwanta. Gobe kuna da muhimmin meeting kai da Maigirma Gwamna da Mai Martaba Sarki. Karfe tara ne na safe bana so kayi kuskuren makara... Ka wuce sashenka kai tsaye, ban amince da wai ka kwanta a sashenta ba kana ji na?"
Maganar ta karshe ta dira a cikin kunnen Nadiya wadda ta manta makullin dakinta ta koma don ta dauka. Tayi sallama a nutse, kamar dai babu abinda taji. Tunda tun asali ma dai bata fahimci inda zancen nasu ya sa gaba ba.

Suka amsa mata, murya a shake tace, "makulli na manta."
Hajiya Ummah ta mata nuni da inda ta zauna, "aikuwa gashi nan, muma bamu kula dashi ba ai da an kai miki. Ko gajiya ce ta sa kika fara mance-mance ne?" Tayi mata tambayar cike da tsokana.
Nadiya dai dan murmushi kawai tayi ta dauki makullin ta juya, don bata son katse musu hirar da suke yi.

Sai da ta fita kafin ta kalleshi, "ka fahimci me nake fada maka ai ko?"
Murya a matukar shake yace, "ehh Ummah!"
Ta gyada kai, "to madallah. Tashi kaje. Allah Yayi maka albarka!"
Ya tashi babu musu ya wuce. Ranshi cike fal da tambayoyi da daurewar kai, sai dai ya kasa daga baki ya furtasu.
Hajiya Ummah ta bishi da kallo har ya fita. Tausayinshi ya darsu a cikin ranta. Saboda duk yadda ya so ya boye yadda abin yaje mishi, fuskarshi ta kasa boye hakan. Sai dai saboda wannan kadai, ba zata iya bari wannan dama ta subuce mata ba. Ba zata yi kuskuren hada zuriya da su ba. Wannan ma da suka hada da ita ta isa. Ta san ma idan ta gama sauke abubuwan data kudirta a kansu, zasu rabu ne rabuwa ta har abada. Don haka babu zancen ma sake kawo wani lamari da zai kara dagula mata shiri.
Da wannan tunani ta gyada kai cike da gamsuwa da wannan shawara, ta tashi ta wuce dakinta.

Shiru-shiru Amarya har ta kammala shirin kwanciya barci cikin fargaba da taraddadin alkawarin da Habibun ya daukar mata. Tsoron haduwarsu dashi take yi tsakaninta da Allah. Tsoron ya fayyace mata wadannan sirrika take yi. Bata tunanin ta shiryawa hakan.
Ta lalubi waje ta kwanta tana zaman jira, har dai daga karshe dai ta yanke wannan dai ba zuwan zai yi ba. Ga yunwa da take nanikarta kamar me, tana tunanin rabonta da abinci tun karin safe da tayi. Shi din ma ba wani abu na azo a gani bane ta ci.

Ta tashi ta shiga kicin da shima yake a shake da kayan kawa. Ga mamakinta sai ta tsinci kaza a cikin microwave wadda ta sha gashi tana ta tashin kamshi. Bata san lokacin data watsawa kazar harara ba, ta kara duba agogon wayarta taga har karfe goma saura. Babu kira daga angonta babu sako a rubuce. Sai tayi kwafa kawai.
Sauran abincin da su Anty Jamilah suka yi ta bude ta zuba dan kadan ta ci, ta hada shayi mai kauri ta sha. Ta koma dakinta tayi kwanciyarta.
Har barci ya fara daukarta, ta bude idanunta tarwai wani tunani yana darsuwa a cikin ranta; 'ko dai ita ce ake cewa ba a yarda a kwana a sashenta ba?!'

28.



Ranar dai barci ga su duka biyun sai barawo. Duk da gajiya da barcin dake tattare da Nadiya, amma haka tayi ta juye-juye da sake-sake har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login