Showing 33001 words to 36000 words out of 142169 words

Chapter 12 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

445

Umma din, tunda ba cika shiga cikin al'amuransu tayi ba. Ta dauki shekaru da dama bata ji ance taje Maiduguri ba, haka ma bata ji ance wani yaje inda take ba.

Maimakon Madam tayi amfani da hakan ta kusantota jikinsu, a'ah, sai dai ta kusanta kanta da ita saboda wani dalili nata na daban.
Ta girgiza kai a ranta tana addu'ar Allah Ya kawo karshen wannan takaddama tasu.

Sun yanke shawarar kawai su yada zango anan gidan Madam din har Aysha da kuma Safiya da zata zo, saboda gidan Dada ma baki za a kai sosai. Amma tunda Madam ba baki zata ajiye anan ba, nan din zai fi musu dadin zama.

14.

Karfe biyu na rana suna zaune a farfajiyar gidan akan kujeru da lemuka a gabansu da fruits suna ci suna hirarsu, suna kuma kallon masu gyara da suke ta kaiwa da kawowa suna hada wajen. Aka bude gate wata galleliyar lafiyayyar Benz munch ta gangaro ta shiga gidan.

Suka tsaya da hirar da suke yi duka suka juya suna kallon motar da kuma wadda take kokarin fitowa daga bayan motar.
Ta zuro kafarta daya waje dake saye cikin wani hadadden sneakers na kamfanin Ryka, da bakin wandon jeans.
Safiya ta fito daga cikin motar bayan wasu yan mintuna, hannu daya rataye da yar madaidaiciyar jakar hannu, dayan kuma rike da wayarta dake makale da earpiece a kunnenta tana waya.

Wandon jeans din jikinta irin crazy dinnan ne, an tsattsagashi daga tsakiya. Sai dai maimakon ya nuna fatar jikinta, sai aka done kofofin ta yadda dai akwai tsagar amma kuma bata nuna fata. Da yake skinny ne sai ya bi ya lafe mata a jiki gabadaya. Rigar bubu din data sanya data tsaya mata a tsakiyar cinya ma ba wani abu na azo a gani ta boye a jikin nata ba. Ta sha kitsonta kalba kuwa ta attach, ta zubo mata har baya. Sai ta dora siririn gyale a saman kanta.
A shekaru na goma sha tara kacal a duniya, tauraruwar Safiya tana matukar haskawa. Irin yan gatan yaran nan ne na masu kudi da suka tashi cikin gata da dadin rayuwa, iyayenta sun tsaye mata, bata san Fadi-tashin rayuwa ba kamar yadda sauran wasu mutanen suke fama. Wannan yasa ta tashi a matukar sangarce.
Kasancewar ta fi Nadiya garin jiki da kiba, ko a yanzu zata iya kamo Nadiyar a tsayi da fadin jiki. Don ba kowa bane zai yarda da cewa Nadiya ta bata shekarun data bata ba.

Ta taka cikin kasaita da nuna isa, cikin gidan take niyar shigewa ba tare data kalli inda su Nadiya suke ba, direban daya tukata kuma yana binta da akwatunanta a baya.
Nadiya kasa daga baki ma tayi ta mata magana tayi, ta manta rabon data sanyata a cikin idanunta.
Sai Anty Lima ce ta daga baki ta kwala mata kira, sannan ta waiga ta kalli inda suke.

Ta tafi da sassarfa cike da murnarta suka rungume juna ita da Anty Limar cikin murna. Nadiya tana zaune tana kallonsu fuska dauke da dan murmushi. A ranta tana jin babu dadi da kuma tunanin ta yadda aka yi suka rasa shakuwar yan'uwantaka a tsakaninta da Safiya din.

Ta tashi tsaye tana kokarin rungumar Safiya din lokacin da suka gama murnar ganin juna ita da Anty Lima. Jinta take yi banbarakwai, kamar wata sabuwar halitta.
Ita kuwa Sophie ko a jikinta, ta rungumeta tana tsallen murna, "Kanna! Kitawu nasaraye (Yaya! Na yi kewarki!)"
Tayi murmushi cike da jindadi tana maimaita mata itama hakan.

Bayan sun gama murnar ganin juna, suka tayata shiga da kayanta ciki. Dakinta daban wanda dama a ciki ta saba sauka, kusa da na Madam. Tayi wanka ta ci abinci, suka sake fita wajen masu shirye-shiryen suna kallonsu.

Sai wajen karfe takwas na dare ma sannan aka fara gudanar da taron bikin. Zuwa lokacin duk sun shirya cikin ankon bikin da za ayi a ranar, jar lafaya ce suka sha mai taushi. Sophie duk ita tayi musu kwalliya da yake ta iya sosai. Nadiya kam bata bari an fente mata fuska ba, ta dai ce a mata kwalliyar sama-sama. Su dukansu sun fito sharr abinsu kamar ka daukesu ka gudu.

Wajen event din ya tsaru iya tsaruwa. Su Madam ana can a teburin iyaye, sai feleke ake da iyayi. Idan kaga irin kwalliyar da taci da adon data dauka sai kayi zaton ko ita ce uwar amaryar ko ma amaryar gabadaya. Amarya kuma ita da angonta suna kan teburi a zaune, angon yayi shigar wata galleliyar shadda ruwan madara da babbar rigar ta sha surfani tun daga sama har kasa, da hularshi baka ta Dara. Amarya kuma tayi shigar lafaya itama ruwan madara, kitson da aka yi mata ya sauko a gefen fuskarta, hannu da kafa ta sha lallenta mai kyau. Kallo daya zaka mata kasan cewa ka ga yar asalin bare-bari. Sunyi kyau ita da angon nata kamar ka daukesu ka gudu.

Suna can a teburin da suka kebance kansu ita da Anty Lima da Safiya da kuma Aisha.
Nadiya bata yi wata kwalliya ba ta azo a gani. Ta nannade kitson da aka yi mata a cikin tafkeken ribbon ta kulle, duk da rashin fitar da gashin da tayi idan ka kalli gargasa da gashin daya kwanta a goshinta zaka san cewa tana da gashi.
Zaune tayi tana kallon Safiya data dame cikin kalar tata kwalliyar, kitson data yi duk ya barbazu, wani ya watsu a gefen fuskarta, wani kuma ya sauka a bayan wuyanta ya gangaro zuwa saman kirjinta. Selfie kawai take watsawa kanta a wayarta. Nadiya ta girgiza kai ta mayar da kanta ga su Anty Lima da suke hira.

Ko awa daya cikakkiya ba ayi ba da fara sha'anin taji har ta fara kosawa da zaman wajen. Dama can ita ba ma'abociyar halartar irin wadannan al'amuran bane.
Zuwa lokacin ita kadai ta rage a teburin nasu, tunda aka kira yan'uwan amarya filin rawa don su taka duk suka tashi suka barta da sauran daidaikun mutane da basu shiga filin rawar ba.

Ta dauke idanunta daga kan Madam da Safiya da suka dage tun karfinsu suna zabga rawa kai kace wasu shakikai ne. Don Safiya ma har kama kafadar Madam din take yi tana wani girgiza da kanainayewa kamar wata macijiya, ita kuwa Madam baki ya ki rufuwa, sai like take mata da kudi.

Tayi kwafa a sanyaye bayan da suka hada ido da Madam ta daga mata hannu kafin ta juya ta cigaba da kwasar rawarta, ta dauki kofin da suka tsiyaya lemu a ciki ta kai baki ta kurba. To me zata ce? Fadan da yafi karfinka ai dole ka maidashi wasa.

Zuwa can taji wayarta tana vibrating a cikin karamar pouch data rike a hannunta. Ta zaro wayar ta duba, ganin Rabi'ah ce mai kiran yasa ta tashi ta bar wajen, musamman data ga ta ajiye mata missed calls har uku tasan kiran gaggawa ne.

Can waje ta fita saboda har a farfajiyar gidan ana jiyo sautin kidan da yake tashi. Layin babu kowa sai motoci da suka yi jere suka kewaye wajen iri-iri.

Ta matsa gefen wata farar Sedan ta dannawa Rabi'ah kira. Tana fara shiga ta daga. Tun ma kafin su gaisa ta fara watsa mata tambayar idan za ayi velvet cake da kuma whipped cream icing ya za ayi? Kuma me da me ya kamata a sanya?
Tayi yar dariya tana tarar numfashinta, "haba Hajiya dan dakata mu gaisa mana tukuna! Saurin me kike yi?"

Tace, "wayyo Anty Nadiya Sorry, wallahi mantawa nayi. Kin ga second batch ne fa nake yi na cake din saboda na farkon bai yi ba yadda ake so, kuma nayi pre heating din oven dina already."
Nadiya tace, "to yanzu dai mu fara gaisawa tukun. Kin dai san bana son irin wannan wayar ko?"

Cike da saduda tace, "na sani Anty. To Assalamu alaikum, ina yini?"
Tayi dariya tare da amsawa. Tambayarta tayi abubuwan data sanya a cikin cake din, kafin ta mata karin bayani da gyara a inda ta kuskure. Hirar tasu bata yi tsayi ba suka yi sallama saboda Anty Lima data dinga danna mata kira.

Ta katse kiran Rabi'ah tare da amsa na Anty Lima dake kan kira a lokacin. Tambayarta tayi ko tana ina? Tace mata waje ta tafi amsa kiran waya amma ga ta nan dawowa.

Ta juya cikin takun sassarfa zata koma wajen bikin. Hankalinta yana kan kokarin mayar da wayarta cikin jaka lokacin data taka kafarta cikin gate din gidan.
Daidai lokacin shi kuma ya kawo kai zai fita, suka yi karo.
Kasancewar shi ya dan duka kansa kasa saboda kofar jikin gate din ba tsayi ne da ita ba, suka hada goshi ji kake garamm! Gabadaya sai da taji duniyar tana juya mata saboda buguwar da kanta yayi. Bata san lokacin da wayar hannunta ta fadi ba, ita kuma tayi taga-taga tana shirin faduwa saboda wanda suka yi karon dashi da karfinshi ya fito. Da ba don shi ba kuma da sai ta kai kasa din.

Yayi azamar sanya hannu ya rikota, bakinshi da nata na furta 'Hasbunallahu wa ni'imal wakil' a lokaci guda.
Ta samu ta tsaya akan kafafunta, hannu dafe da goshi, ta daga idanu tana kallon mutumin da niyar watsa mishi tambayar baya kallon gabanshi ne? Shi kuma bakinshi yana furta, 'sorry!' a lokaci guda.

Duk sai suka tsaya suna kallon juna cike da mamaki. Maganar da tayi niyar yi ta makale mata a makoshi.
Shi kuwa gira ya daga, cike da wannan izza da rainon wayau da bata manta ba. Yace, "such a small word huh? Ke idan kina tafiya baki duba gabanki ne ko me? Ko kina da matsalar idanu ne?"

Ta bata rai tana hadiyar wani yawu na takaici, wayarta ta duka ta dauka ba tare data dubata ba. Ta daga kai tana kallonshi fuska a cune, "ina ga dai naka idanun ne suke bukatar a tambayi ko suna aiki ko basa yi. Saboda in case baka gani, kai ka kawo min karo ba tare da ka duba inda kake zuwa ba. Kamar yadda kayi mun a wancan lokacin!"

Ta ratsa shi ta shige gidan rai a bace, bata cika son yin tsiwa ba saboda tasan bata da kyau idan ta fara. Taimakon da Allah Yayi mishi daya a wajen biki suke, inda bata son ja wa kanta attention. Amma da ba don haka ba da sai ta wankeshi tass ko ta huce takaicin daya kara kunsa mata a karo na biyu. Babu ma kamar data duba wayar hannunta taga tayi raga-raga, gashi bata sanya mata screen guard ba. Ji tayi kamar tayi me! Ta dai cije ta karasa wajen su Anty Lima inda suke zazzaune suna ta dambe da naman kaji da lemuka da aka shirya bayan fitarta.
Ta zauna tana harare-harare ita kadai. Saboda bacin rai ko kallon naman bata yi ba duk da yadda kamshin naman yake kai mata.

An cigaba da gudanar da shagalin biki har zuwa wajen karfe goma sha biyu na dare. Duk da haka basu samu sukunin tafiya makwanci ba sai wajen karfe daya na dare. Saboda sai da suka taimaka aka rage tarkacen dake wajen duk da wadanda suka shirya event din su suka yi aikin, amma Madam tace su sa musu hannu don a samu a gama da wuri. Don haka a matukar gajiye suka kwanta. Da kyar ta iya tashi tayi sallar asubahi.

Ta koma ta kwanta kenan, a ranta tana raya yadda zata kai har karfe goma ko sha daya ma bata tashi ba, sai ga Madam ta kwankwasa musu kofar dakin.
Ta tashi zaune tana kallon Madam din wadda har lokacin kayan barcine a jikinta, daga alamun fuskarta kuma ko sallar asubahin ma bata kai ga sallata ba. Ta amsa gaisuwar da suke mata a tsaitsaye, da alama sauri take yi.
Nadiya take kallo, "Nadiya ya za ayi ne? Jiya mantawa nayi fa in fada miki yau ma za a kaiwa Hajja Umma abin kari. Ina ga ai za a samu a hada ko?"

Jikinta a matukar gajiye yake, bata kuma tunanin zata iya aikin da Madam din ta bukata. Sai dai sanin halin Madam din, tasan ba tambayarta take yi ba, umarni ne kawai take bata, yasa ta daga baki tace, "to me za a dafa ne?"
Tace, "kawai ki dafa duk abinda ya dace da abinda dattijuwa zata ji dadinshi. Amma ki sake yin kunun gyada saboda taji dadin na jiya sosai."
Nadiya ta amsa da 'to!'
Ita kuma ta juya ta tafi.

Ta tashi da kyar ta nufi kicin din, Anty Lima ta bi bayanta zata tayata aikin. Duk da yadda taso ta koma ta kwanta, ki tayi. Don haka suka shiga tare.
Tuwon shinkafa ta malmala da miyar agushi ta yi kunun gyadar. Ta hada komi ta zuba a mazubai masu kyau ta ajiye. Sai ta kara yi musu couscous da sauce din kifi don tasan ba lallai Madam da Safiya su ci tuwo da safe ba.
Bata ma iya tsayawa karyawa ba saboda tsabar barci da take ji, ayaba kawai ta iya ci da tuffa, suka koma suka kwanta. Bata san lokacin da Madam ta bar gidan ba. Sai can wajen Azzuhur da suka tashi, suke jin tana can gidan Hajiya Umma, yau har da Safiya suka tafi.

Kasancewar shagalin ranar na yamma ne, da suka yi sallah suka ci abinci, sai ta dauki sauran tuwon da suka yi suka tafi gidan Dada. Acan suka shirya tare da su Aysha, suka tafi can wani wajen tarar baki na musamman inda a can ne za ayi Mothers Eve.

Suka fita daga motar Anty Lima ita da Aysha da Anty Lima din da wata cousin dinsu diyar kanwar mahaifiyar Anty Lima din, Zainab.
Wata tsanwar atamfa suka shiga, Nadiya an mata dinkin gown wadda ta bi jikinta sosai ta lafe. Duk da cewa ba wani matseta tayi na azo a gani ba, amma yanayin yadda ta fitar mata da surarta yasa data tashi sanya gyale, sai ta samu mai yalwar fadi kuma mai duhu ta yafa. Su Anty Lima ma sun fito gwanin kyau cikin nasu ankon. Ita skirt tayi straight, an tsaga mata shi daga baya. Nadiya har maganar yadda sharabarta take a waje ta mata, amma tace mata hakan ba wani abu bane, ai ta ma yi shigar mutunci. Ta sanya rigarta half gown wadda shape dinta ya fita da kyau, ta kuma yi mata matukar kyau. Ita da kanta ta kashewa Nadiya daurin kallabi mai kyau. Suka jera suka shiga wajen cikin taku na daukar hankali.

Gab da zasu shiga wajen da ake event din suka ci karo dashi cikin zugar matasan samarin danginsu, diyan yan uwansu Madam.

Ta duba iya dubawa, ita dai ta kasa gano ta ina suka hada iri da wannan dan wulakancin mutumi. Ta kasa daurewa dai sai data daga baki ta tambayi Anty Lima.
Ta saci kallon samarin da duk suka bisu da kallo sai kace sun ga wani danyen nama.

Anty Lima tace, "wai wancan? Nima gaskiya ban wayeshi ba. Amma cikin su AbdulHalim nake ganinshi. Watakila ko abokinsu ne tunda ba cikin zugar angwaye yake ba."

Zainab dake sauraronsu tunda suka fara maganar tayi caraf ta amshe zancen. Tace, "wai wancan haddaden gayen? Ance fa babban dan Hajiya Umma ne. Bata taba zuwa nan dashi ba sai wannan karon shi yasa duk ba a san shi ba!"

Suka kalleta da mamaki, Anty Lima tace, "kai jama'a! Dama Hajiya Umma tana da babban da kamar wannan? Ashe matar ba ta yau bace!"

Nadiya tayi dan murmushi. Zainab kuwa tace, "hummn! Aikuwa dai danta ne. Naji an ce ya kama naira har ya gaji. Yanmatanmu fa duk sun rikice wallahi, ance har da masu zarya gidan Hajiya Umma ko da wadda zata dace ya kyasa!"

Abin ma sai yaso ya bawa Nadiya dariya. Tayi murmushi tana girgiza kai, a ranta tana fadin lallai kuwa da aiki ya gansu. Don kuwa dai ita bata ga abin so a wajen wannan dan rainin wayau din ba da jiji da kai. Ai ko a kafa aka daura mata shi wallahi a sukwane zata cireshi ta yar!

15.


Kwanaki fiye da biyar ana ta shagalin biki kala-kala abin kamar ba zai kare ba. Har dai zuwa ranar litinin da aka daura aure. Washegari kuma aka tafi kai amarya gidan angonta. Su Anty Lima da Safiya su ne tan rakiya, ita dai ta lafe a gida tace sai sun dawo. Sun kuwa koma cike da zazzaudin gidan da aka kai amarya da santinshi. Ita dai tace Allah Ya bada zaman lafiya.

Har kuma zuwa wannan ranar kullum ita take dafawa Hajiya Umma abin kari.
Wani lokacin ma har da dare Madam ta kan sa tayi gashin kaza ko nama akai mata, ta kuma hada mata lemu na lemun zaki da kankana da take yi ko kuma na zobo akai.

Ranar Alhamis ta tashi da azumi a bakinta. Tunda asubahi da suka gaisa da Madam ta fada mata ranar Assabar take son komawa gida.
Tace to Allah kaimu. Ita kam sai ta kai litinin, saboda Alhamis ta sama Safiya zata wuce America.

Karfe goma na safe suka fito ita da Anty Lima, itama ranar zata koma can gidansu, zata sauke Nadiya a gidan Anty Hauwa wadda ta dawo jiya laraba.

Tun daga daki suke jin sautin kida yana tashi kasa-kasa. Sai da suka fito falo sannan suka ga ashe abin ba na wasa bane.
Safiya ce a tsakiyar falon saye da wani wando baggy, da karamar rigar top mai karamin hannu, kitson kanta ta barbaza shi ya zuba a bayanta da gefen fuskarta. Ta kure volume jikin speakers din falon, ga ring light nan ta tsayar tana ta tikar rawar 'Mi Gente' sai wani girgije-girgije take da juye-juye.
Abin ban takaicin shine yadda Madam tana can kan dinning a zaune da abincin karin da Nadiya ta hada musu tana ci hankalinta kwance, sai ma thumbs up da take jefawa Safiya din idan tayi wani juyin daya burgeta.

Suka ratsa ta gefenta suka wuce ko alamun ta gansu bata nuna ba. Nadiya tana so tayi magana, tsoron abinda zai kai ya kawo ya hanata. Dole ta kame bakinta ta bame.
Suka je suka yi sallama da Madam din. Ita kanta Nadiyar bata tunanin zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login