Showing 108001 words to 111000 words out of 142169 words

Chapter 37 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

466

zaune, ki shiga ki fito min da kudi nace!"

Ita da Ummah din sai suka hau fadi-in-fada. Duk yana jinsu, jikinshi yana rawa da kakkarwa saboda tsananin takaici da bacin rai.
Abinda ita Hadiza din bata sani ba shine, ita kanta Ummah bata ma san iyaka adadin kudaden da Habib din ya mallaka ba na gadonshi, tasan dai har da wannan gida da suke zaune, da manyan filaye da gonaki. Kudade da takardu kuma duka ta damkasu a hannun Uncle Hashim, tace ya rike mishi har zuwa lokacin da zai kammala karatunshi, idan ya tashi aurenshi sai ya bashi kudin. Hatta da wannan makarantar da yake yi, a cikin aljihun Hajiya Ummah ne ba tare data taba mishi ko sisin kwabo a kudinshi na gado ba.

Ya duba yaga wai wannan ma wadda basu hada alaka bace ko ta jini take mishi haka. Me yasa to mahaifiyarshi ba zata mishi hakan ba? Me yasa ita kullum sai dai tace ya bata? Me yasa kuma duk lokacin da zasu hadu sai dai tace ya bata kudi. Kudi dai kullum!

Bai san lokacin daya danna kai ya shiga dakin ba. Sai ganinshi suka yi tsulum kamar wanda aka jefa daga sama.
Idanu cike da hawaye yake kallon Ummah, ya ma kasa duban inda Hadiza din take saboda tsoro da gudun abinda zuciya zata iya sanyawa ya furta mata.

Ya cewa Ummah, "Ummah, ki bata duk abinda take ganin zai isheta daga yanzu har rayuwarta ta kare. Amma don Allah kada ta sake waiwayar inda nake daga yau. Ke din k????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? e kadai kin isheni a rayuwata!"
Ya juya ya fita daga falon da sauri. Hadiza ta tashi zata bi bayanshi tana ihu da hargagin, "au!! A gabana kake nuna an gama wankewa an baka kenan! Ai ni dama nasan ba haka kawai aka barka ba, nasan dama da kyar idan ba farraku aka mana ba! Wane d'a ne zai fita sha'anin Uwar da ta haifeshi saboda wata bare? Ai wallahi daga gani dama ba kanka daya ba!"

Tayi zage-zagenta ta gama, ta koma ta zauna tana hura hanci kamar wata tsohuwar macijiya. Ummah tana zaune tana kallonta har ta gama, ta kalleta tana zare ido, "sai ki shiga ki dauko min hakkina ko?"
Ummah ta kalleta a nutse tace mata, "ki fadi abinda kike so, amma fa da sharadin ki fita rayuwar Habibu kamar yadda yace."
Ta ambaci kudaden da yawa kwarai, Ummah kuma bata yi musu ba, ta dauki waya ta kira Uncle Hashim a take aka tura mata ta lambar account din data bada.

Ta tashi cikin tsananin murna jikinta har yana rawa, ta yiwa Ummah sallama babu ko godiya. Sai data juya zata tafi Ummah ta tsayar da ita, tace, "ki dauka wannan shine karo na farko kuma na karshe da zaki zo nan gidan da sunan neman kudi. Ke baki ji kunyar kanki ba? Tunda yaron nan ya tashi, koda wasa baki taba neman inda yake ba ko kin duba halin da yake ciki ba, sai yanzu kuma wai kice ke kin zo a baki kudi sai kace kin ba wani ajiya?"
Hadiza tace mata, "aikuwa idan kina tunanin wai zan kyaleku haka to kina mafarki ma kenan!"
Ta sa kafa ta tafi.

Saboda takaicin wannan abu daya tarar yasa bai ma yi sati biyun da yayi niyar yi ba, kwananshi biyar ya juya. Tun kuma daga ranar bai kara waiwayar lamarin Hadiza ba. Zuciyarshi na shan gaya mishi ai tunda har ta kaisu ga haka, to zancen mu'amala irin ta uwa da d'a ta kare a tsakaninsu. Idan basu yi mu'amalar kirki a yanzu ba, yaushe zasu yi ta?

A haka har ya kammala karatunshi, aka musu aure da Hidaya. Har gida kuma aka je aka sanar da su Hadiza din, amma sai danginta ne suka yi dafifin zuwa amma ita ko a leke.
Lokacin tana can a kwance ita jinya ma take yi, mijinta ya lallaba ya ranci kudin data amso a wajen Ummah, ya dankaro mata kishiya. Shekara da shekaru kudi sun ki fita daga hannunshi, karshe data tambayeshi ma sai ya sameta da diyarta Rashida wadda ta haifa a wancan gidan data fita, ya musu lilis, ya dankara mata saki. Karshe sai kishiyar ce ta ja jikinta kofar gida ta yasar. Sai yan unguwa ne suka taimaka mata suka dorata akan abin hawa ya kaisu gida.
Wannan takaici da abin kunya shi ya hanata fita. Gashi a lokacin ta fara shiga taitayinta, don kuwa duniya tuni tayi mata atishawar tsaki. Shi kuma Habibu sai yayi tunanin duk cikin rashin son da take yi mishi ne ya hanata halartar bikin nashi.

Dukiyarshi duka ta koma hannunshi bayan aurenshi, sai ya bi bayan Ummah da take da manyan shaguna na kayan kwalliyar maza da mata inda ake kai mata su daga Turkey, Japan, Indiya da sauran kashashe na duniya. Shi kuma sai ya hada har da su electronics. Amma sai ya sanya ragamar kula da wajen a hannun Ummah din, shi dai kawai sunan mai wajen ne amma bai ma san ya yake ba, sai dai duk shekara a ware mishi ribar da aka samu a sanya mishi a akawun.

Ya dora degree dinshi na biyu akan politics saboda ya dade yana tunani da shawarar shiga harkar siyasa, koda kuma ya nemi shawarar Ummah sai ta mara mishi baya. A ganinta hakan zai kara mata wani karfi na musamman.
Bayan rasuwar Hidaya, ya kammala karatunshi. Bai shiga harkar siyasar ba kai tsaye, sai daya fara aiki da hukumar In-Land revenue ta nan Kaduna, ya kuma kara samun Ph.D akan Politics, har sai daya kai matakin Deputy Director, sannan ya fito harkar siyasar tashi gadan-gadan.

Ya samu goyon bayan Hajiya Ummah da Uncle Hashim sosai da sosai, don kuwa da taimakonsu ne sunanshi yayi shura ya zagaye fadin Kaduna da kewayenta. Ga kuma surukinshi mahaifin Shukurah wanda ya kasance shima tsohon dan siyasa ne wanda aka dama dashi a siyasar garin Kaduna.

Hadinshi da Nadiya zai iya cewa hadine na Allah. Tun bayan daya shiga harkar zabe officially, Ummah ta matsa lallau yana da bukatar karin wata matar saboda su kara samun karfi sosai da sosai.
Ya duba duka tarin hotunan da ta nuna mishi na yan matan dake cikin danginta da kuma 'ya'yan manyan mutane da sarakuna da take ganin zasu dace da tsarinshi, hotuna biyun data ware tana kara nuna mishi ne ya dan dauki hankalinshi. Yanmata ne kyawawa, zancen kyau ma ba a maganarshi don kuwa duk ta ko'ina Allah bai yi musu makusa ba. Sai dai daga ganinsu daya ta girmi daya. Take fada mishi cewa su dukansu yaya da kanwa ne, mahaifiyarsu tana da fada-aji sosai da sosai, za kuma ya iya takalawa duk inda yake son zuwa da taimakonta.
Kallon fi-sha yayi musu a lokacin su duka, a yadda yake shan takaddama da Shukurah ma kadai gani yake matsalarta ta isheshi ba sai ta kara da wata ba. Ya cewa Ummah din ta bashi lokaci zai yi tunani dai, ya kuma fadi hakan ne ba don har cikin zuciyarshi ya yarda zai yi tunanin ba.

Hadiza dai tun bayan kashin da ta ci, ta yiwa kanta karatun ta-nutsu. Ta koma gidan Hajiya Ummah da gwiwa a sage taje bata hakuri, Ummah da a lokacin yan zuga da shaidan sun gama zugeta ganin irin matsayin da Habibu yake shirin takawa. Tayi biris da ita ta kuma ki sanar da Habibu zuwanta, haka ta dinga mata zarya tana rokonta ta hadata dashi ta bashi hakuri ma, amma Ummah ta ki.
Sai can wani lokaci Allah Ya taimaketa taje fitowa daga gidan, taci karo da motarshi zata shiga. Shine ta tsaida shi, ta sanyashi a gaba da kuka da neman gafara. Ya dai furta mata shi dama bai riketa ba a ranshi, amma a ranshi ya kasa ya sake da ita balle har ya sakar mata jiki.

Haka take ta kokarin jan shi a jikinta amma abu ya gagara. A haka ta sake fitar da wani manemi dake zaune a Makarfi ta aura. Shi yayi musu hidimar komi ta biki, tun daga kan kayan gado da komi ma, ya kuma nemawa Rashida makaranta mai kyau a can tana zuwa, ya dauki nauyin karatun nata. Ya kuma ajiyewa Hadiza din mota da ake jigila da ita duk inda zata je. Abinda ke hadasu da Hadiza din kenan.
Duk zuwan da zata yi Kaduna sai taje ta gaishe da Hajiya Ummah, haka lokaci zuwa lokaci Rashida ta kan je gidan ta dan yi musu kwana biyu. Amma har lokacin daga Habibun har Hajiya Ummah din basu saki jiki da ita ba.

Rashida ce ta dameshi da waya tana kuka da ranta, tana rokon yaje ya ga Ummansu. Bata da lafiya kwarai, a kwance rake ranga-ranga amma sunanshi kadai take kira tana cewa tana son ganinshi.
Ummah da kanta tace mishi ya kamata yaje, a matsayinshi na magidanci kuma ma wanda ya fita siyasa, bai kamata a sameshi da wata baraka ba shi da iyayenshi.
Don haka ya shirya tafiya a wata safiyar ranar Lahdi, ya dauki Ammar suka tafi don kuwa daga shi har Ammar din wannan ne karo na farko da zasu je inda take.

Ya sameta din kuwa gata nan rai a hannun Allah, typhoid da malaria sun kaita kas. Takaicin halin daya samesu a gidanta ne ya bata mishi rai kwarai da gaske. Miji ya tafi ya barsu a gidan haya, a wata unguwa mai tarin kwatami da bola, ga babu abinci. Sai ya dauki fiye da sati biyu bai je inda suke ba, kuma wai da sunan anan cikin garin yake da zama. Yana da wata matar a can yake tarewa a wajenta.
Ranshi ya baci ya jagule kwarai da gaske. Yayi waya a take ya bada umarnin a sama musu gida madaidaici a unguwa mai kyau su koma can. Don ya nuna mata ta koma gida mana abinta? Ta nuna mishi ta dai fi ganewa zama a gidan aurenta haka nan. Gwanda kawai ta girbi abinda ta shuka, don kuwa hakkinshi ne da na Ummah yake bibiyarta. Sai ta hau kuka kuma.
Ya kalleta kawai, ranshi yana cike da tausayinta, amma kuma ya kasa yi mata wata magana ko ya bata hakuri.

Ya tashi ya fita sakamakon kiran da aka mishi cewa an samu wani gidan mai kyau anan bayansu ba nisa yaje ya gani, akan hanyar zuwan ne suka tsaya da niyar sayen wani abin ya sha shi da Ammar don kuwa ko karyawa bai yi ba, suka ci wannan karo shi da Nadiya wanda ya kira hadi na Allah.

Har suka je suka ga gidan da aka samu, aka gama komi da komi, amma ba zai iya cewa ga rabin abinda aka ce ba. Hankalinshi ya linka yayi wani waje na daban, tunani yake a ina ya taba ganin wannan fuska? Menene kuma a tattare da ita dake fuzgarshi kamar wani maganadisu?
Bai ganeta ba sai da suka hadu a hold up dinnan. Kai tsaye kawai ya tuna ashe fa hotonta ya gani cikin jerin yanmatan da Ummah ta nuna mishi, duka-duka ko sati daya cikakke ba ayi ba.

A wannan rana ya kwana ya wuni cikin wani irin tunani da tu'ajjibi mai tsanani, banda zuciya da rigima, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki?
Asubahin fari ya kira Mami, ya fayyace mata abinda ke faruwa. Wannan yarinya dai ta mishi, a kwatancen da yayi mata kai tsaye tace mishi Nadiya ce! Ya kama sunan nan yana nanatawa a fili da boye sai kace wani zararre. Tace mishi ya barta da Ummah, don taga hankalinta ya fi karkata a wajen wata diyar Sarkin Gumel, amma zata san ta yadda zata bi mata.

Don haka koda Ummah tace mishi ya shirya zasu je Maiduguri, ya ga ko da wadda zai zaba cikin yanmatan danginsu, babu musu ya bi bayanta musamman da Mami tace mishi ai Nadiyar ma zata je.

Abinda daga Nadiya har Madam din basu sani ba shine, tun ma kafin su Hajiya Ummah su karasa Maiduguri, Mami sun gama magana da Uncle Hashim kan cewa Habibu ya samu mata a can. Mami ita ta kira Ummah ta fada mata cewa ita da kanta ta zabarwa Habibu Nadiya, saboda ta binciki nagartarta ta kuma aminta da ita. Kuma ko anan, sai data gargadi Ummah da cewa idan ba zata iya kawar da kai ta manta baya ba, kada aja maganar auren da nisa. Da a auro yarinya daga baya Ummah ta dinga daukar alhakinta, babu yarinyar da namiji zai aura kuma uwarshi bata sonta, taji dadin wannan aure.


7'7'

Hajiya Ummah tayi kukanta ya isheta, Mami tana zaune kusa da ita tana shafa bayanta cikin alamun lallashi.

Ta cigaba da mata magana cikin sanyin murya, tace, "ki fa auna ki gani Yaya, sanadin abinda Yaya Lamin ya miki ne kika kasa hakuri har kika yi wannan kullaci da rikon, kike aikata wadannan abubuwa da ko wasu yaran ba zasu iya aikatawa ba. To a tunaninki, idan kika yi kwatankwacin hakan su su Madam suma ba zasu kullaceki bane? Ba fa zasu taba fahimtarki ba, su ma kuma zasu iya retaliating, su ce zasu dauki tasu fansar. Ashe kenan haka zamu cigaba da tafiya babu wata maslaha ko sulhu a tsakaninmu, har 'ya'ya da jikokinmu su zo su tarar da hakan?
Ke ce babba, ke ya kamata kuma ki tsayar da wannan abun haka nan don Allah! Ki fa duba Nadiya yadda take girmamaki da kallonki a matsayin Uwa. A ganinki me zai faru idan kika kaita bango, ta daina girmamaki, ta fara mayar miki da raddi? Wallahi Girma ne zai fadi Fadi!"

Hajiya Ummah ta bude kunne tana sauraronta da kunne na basira. A yau baya take dubawa, ire-iren abubuwan da take aikatawa musamman ga Nadiya, a yau duk sai taji kunyar yarinyar ta lullubeta. Lallai ko a haka aka tsaya ita tasan cewa faduwar Girma ai sai dai wani in akwai, amma da kyar idan wannan bai zube ba. Haka kawai duniya da son daukar fansa marar amfani ta rufe mata ido, ta mayar da yarinya sai kace wata kishiyarta? Duk da hakuri da ita da take yi da kokarin da take yi a kanta?

Ta juya ga Mami tace mata, "to ya zanyi yanzu Sumayyah? Ina so in so ta nima, in bata hakkinta na diya kuma suruka. Amma wallahi da na ganta na tuna ita din jikar Lamin ce, sai inji na kasa! Mutumin nan ya cucemu a rayuwarmu!!"

Mami ta kara sanyaya murya, tace, "Yaya wannan aikin ke kadai zaki iya yin shi. Daga lokacin da kika cire tsanar Lamin a ranki, wallahi komi na rayuwarki ma sai yafi miki dadi. Ki daga ido ki dubi yarinyar nan ki tunawa kanki, bayan jikar Lamin, ita din diya ce a wajenki, kuma suruka. Sai kiga hakan ya wanke miki duk wani kullaci na ranki. Ke zaki fuskanci Ubangiji, ki rokeshi yafiyar kin sanyawa ranki salama da hakuri da afuwa da yace ayi idan an zalunci mutum, ki kuma rokeshi ta yaye miki wannan kuncin na ranki. Rayuwa dai tafiya take yi, wallahi bamu da sauran lokacin tsayawa tuhumar wani kan laifukan da suka yi mana bayan muma masu aikata laifin ne. Watakila ma idan aka waiwaya namu yafi nasu yawa a wajen Ubangiji. Ni dai ina baki shawarar, ki yi hakuri ki taushi ranki, ko kin samu salama a cikin ranki. Maiduguri kuma in Allah Ya yarda zan je, nima ina so in gano yan'uwana haka nan!"

Ta gyara gefen gado tayi kwanciyarta ta juyawa Ummah baya ta barta tana saka da warwara. Barci ya dauketa ba tare da tasan lokacin da Ummah din ta kwanta ba. Amma can cikin dare ta farka ta ganta ta fuskanci gabas a cikin sujjada, sai tayi murmushi mai dadi a cikin ranta, ta juya ta cigaba da barcinta.

44.



Cikin kwanakin gabadaya ta kasa ganewa kanta abinda ke faruwa da ita. Wani irin bacin rai na babu gaira babu dalili take fama dashi. Da abinda ya kai, da ma wanda bai kai ba sai kawai taji ranta ya hau ya baci. Shi yasa ta ke baya-baya da kowa ma a gidan don tasan ba lallai ta dinga iya kawar da kai idan an yi mata wani abun ba.
Ta koma yini a dakinta ta kure volume din karatun Qur'ani tana ji, ko ta dauka ta dinga karantawa ko Allah Yasa ta samu sassaucin ranta. Ta kuma rike hailala da tasbihi tana ta yi babu kakkautawa.

Suna zaune akan dinning su dukansu ana karin safe, ranar Alhamis ce. Bata tashi da azumi ba ranar saboda ranar girkinta ne, ga Babangidan yana gari.

Duk kayan ciye-ciye da aka cika musu kan dinning din dasu, ta kasa cin komi. Ga masa nan anyi tayi sharr gwanin kyau da miyar gyada wadda ta sha alayyahu da ganda da tantakwashi. Daga fari dai yawunta har gudawa ya dinga yi lokacin data ga masar, amma kuma tana kai ta baki da kyar ta iya hadiyewa, zuciyarta ta fara tashi.
Sai tayi tsam ta tashi, ta lalubo lemon tea a kicin ta hada shayi da ita ta zauna tana sipping a hankali.

Kan teburin ya kaure da hira ana ta raha, in ka dauke ita da take binsu da kallo kawai tana dan murmushi, sai kuwa Shukurah da take fama da tablet a hannunta, bata ma fahimtar me suke cewa.

Mami ta kalli Hajiya Ummah tana ce mata, "Ummah ni dai jibi in Allah Ya kaimu zan tafi wajen bikin Halimatu. Ina so in ga dangi sosai kafin a fara hidimar bikin nan."
Ummah tace mata, "to ni menene nawa? Allah tsare kawai zan ce muku, na gama hada gudummawata tunda ba zan samu damar zuwa ba. Idan zaki tafi sai ki wuce musu da ita."

Jin haka sai Nadiya tayi saurin cewa, "aikuwa dai nima zan biki sai mu tafi tare. Tunda dama nima kafin bikin zan tafi, kuma kinga nan da kwana hudu ne ake fara bikin."
Mami ta kalleta kafin ta maida dubanta ga Babangida daya tamke fuska, tace, "to! wannan kuma ga ki ga mijinki nan ai!"

Ta daga baki da niyar cewa ai dama sun riga sun gama yin maganar da shi, kawai sai taga mutum ya ci magani yana kallon Mami din, yace, "Mami kiyi gaba ke, ita sai gobe daurin aure zata je!"
Ta juya tana kallonshi cikin tsananin mamaki, "kamar ya? Tun ranar nan fa muka magana da kai, ka kuma ce babu matsala. Idan na tafi ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login