Showing 96001 words to 99000 words out of 142169 words

Chapter 33 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

475

sak, yadda kasan wasu identical twins. Abinda ya bambantasu da juna kawai shine ita Ummah zata nunawa Mami shekaru ne kawai da yanayin girman jiki.

Nadiya tana jin zancenta a bakin Babangida sosai, sai dai ko a hoto bata taba ganinta ba. Ya dai sha fada mata cewa a Jordan take da zama ita da mijinta da 'ya'yanta, yana kuma cewa zai hadasu koda ta waya ne su dinga magana amma kuma sai Allah bai taba bashi dama da ikon yin hakan ba.

Har suka karasa kusa da ita tana tsilla-tsilla da tunanin wace irin tarba zata yi mata ne? Tunda ga matakin da suke da Hajiya Ummah kadai ma wadda har zuwa lokacin bata gama sakar mata jiki ba, ita kuma ko da wacce ta zo?
Mami ta tsaya a gabanta tana dan murmushi tana duban inda Babangida din yake, tace mishi, "ko da ban tambaya ba dai wannan ce Nadiya ko?"
Ya ki bata amsa sai kafada daya daga mata, ganin haka ita sai ta rusuna, tace mata, "Mami sannu da zuwa, ya hanya?"
Kawai sai ji tayi ta rungumota kai tsaye tana yar dariya, "come on Daughter, kada kiyi mun gaisuwar kauyawa mana! Ni da kike ganina ba sarakuta ko jika da kaka zanyi da ke ba, 'ya ce a wajena kinji?"
Sai ta samu kanta da dan murmusawa cikin samun salamar zuci, don kuwa bata san ya zata yi ba idan ta mata karbar wasa-re-re irin na Ummah.

Ta kama hannun yarinyar dake tattare da ita ta bi bayansu ita da Babangida din inda suke tattaunawa game da rashin lafiyar Hajiya Ummah din da kuma sakamakon da likita ya fitar a ranar. Sai a lokacin take jin cewa ciwon sugar ne ta fara kamuwa da shi duk da dai ya fara shigarta ne kawai bai yi karfi ba, sai kuma jininta da ya hau sosai, ga kuma karin ulcer. A ranta take jinjina wannan abu, da kuma kara yarda da zancen Mama can wani lokaci da take ce mata ai yanzu Ulcer ba cu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tar yunwa bace, cutar zamani ce kawai.

Suka shiga falon a haka, suka samu Hajiya Ummah a kasan bene a tsaye, da alamu su take jira. Shukurah kuma tana zaune a tsakiyar falo akan kujera tana kallo.
Mami da saurinta ta karasa wajen Hajiya Ummah ta rungumota cike da doki da murna, sai Ummah din ce ta dinga kokarin janyeta daga jikinta tana mata fadan, "Ni kada ki kada ni don Allah! Wai ke ba zaki taba girma bane Sumayyah? Kullum ke baki taba yin abu na girmanki da shekarunki?"

Mami tayi yar dariya cike da farinciki, tace, "haba Ummanmu? Kina ganin tsawon lokacin dana dauka ba tare dana ganki ba, yanzu kuma sai ki hanani yin murna?"
Tace mata, "ke dai kika sani. Taho muje dakinki dai tukun kuyi wanka ku huta sai ku ci abinci."

Shukurah ta karasa wajen nasu itama tana yiwa Mami sannu da zuwa, "Mami sannu fa... Kun iso lafiya? Ya hanya?"
Mami din ta amsa, kafin suka runkuta zuwa sama inda aka gyarawa Mami din dakin da take sauka. Ita dai data samu ta rakata dakin taga ta shiga wanka, sai ta silale ta bi sawun Babangida daya sauka kasa din yana ce musu zai je ne ya dan kwanta zuwa la'asar. Itama Mami din tace mishi ai da ta fito wanka ko abinci ba zasu ci ba ita da Farida, diyarta, kwanciyar zata yi saboda sun kwaso gajiya sosai, kuma sun ci abinci a jirgi.

Ta wuce ta gaban Shukurah da tun bayan gaisawarsu da Mami ta koma inda take zaune ta zauna. Harara ta watsawa Nadiya din data bata baya, hakan duk bai isheta ba sai data kara da jan tsaki. Kiri-kiri yarinyar nema take yi ta dinga shigar mata hanci da kudundune. Ta fara bin mutanen gidan tana shige musu jiki sai kace wata mai aiki da asiri. Da can tana zaman-zamanta, hankalinta kwance. Duk abinda tayi a gidan dai-dai ne, babu mai daga kai ya kalleta balle a kai ga zancen ce mata ba haka ba. Amma yanzu daga zuwan wannan figaggar abar, wai ita ce har aka fara comparing dinta da ita. Ita kam me yayi ma hadinta da ita ne? Hanyar jirgi daban, ta mota daban. Ita dai ba zata iya cusa kanta jikin mutane ba, mutane ita suke cusawa kai suna kokari da son ta mu'amalancesu. Balle akai ga wani kula da dora dawainiyar da ba tata ba. Ita duka yaushe ma ta fara daukar dawainiyar kanta da kanta? Ita da tun tasowarta a gidansu bata san tayi abu da kanta ba sai dai ayi mata!

Ta sake jan wani tsakin tuno da yadda jiya wai Habib yake tuhumarta da tafiya yawon kamfen alhalin Ummah na kwance babu lafiya. Har da fada mata cewa da mahaifiyarta ce a wannan halin ita zata je ne? Ya kuma kara da fada mata wai ta duba dai yadda Nadiya ta dinga nan-nan da ita da kula da ita a jiyan. Wannan abu ya haddasa musu hawa sama shi da ita a gaban Ummah, don kuwa rufe ido tayi tace mishi kada ya sake hada sunanta dana Nadiya a cikin kalma daya, don kuwa ta fi karfinta. Wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Kuma kamfen din da yake ihun taje, tana cewa dai don shi taje da kuma Ummah din? Shi kuwa budar bakinshi sai yace mata ta dai kara nazari, don kuwa yasan don kanta take yi. Idan ma don shi dinne, shi ya taba daga baki ne yace yana bukatarta?
Sai da Ummah ta gaji da fadan nasu ne sannan tace musu duk su tashi su bar mata wajen ta sallamesu, sannan ne suka bari.

Ta sake jan wani tsakin a karo na barkatai. Tana so ta ji zafin maganganun daya dankara mata ma amma abubuwan dake gabanta suna janye hankalinta. Don haka ta watsar da komi, a ranta tana fadin idan ta jajirce da kyau, ta samu da taimakonta Habib ya ciwo kujerar Gwamnan Kaduna, ai wannan ma kadai ya isa ya sayo mata girma da mutunci a wajenshi da na Mami din tashi data kula tun ba yau ba dama ba sonta da Babangida din take yi ba. Bata ma raba dayan-biyu akan cewa da sanya hannunta aka auro mai wancan farin irin na yayan zabiya da idanu sai kace na yan maye! Ita kadai dai take ta wannan gulmar a cikin ranta.


?'?'''''?'?'


Can ta iskoshi a dakinshi tsaye a gaban mirror, har ya cire rigar jikinshi ya rage sai farar singileti kawai daya bari.
Kallo daya yayi mata tun shigarta dakin, ya dauke kai ya cigaba da maganar da yake yi a waya dake manne a kunnenshi.

Ta maida kofar dakin ta rufe tare da karasawa inda yake, kafarta tana nutsewa cikin tattausan carpet yadda kasan katifa. Dakin na Babangida madaidaicine dai-dai shi dai, lafiyayyun Turkish Royal set ne royal blue a jere a dakin. Kusan komi na dakin royal blue ne sai su labulaye da fentin dakin da suka kasance grey.

Ta amshi karamin comb a hannunshi da yake taje kanshi dashi, ta fara taje mishi sumar da kanta har zuwa sajenshi. A ranta take cewa 'wai mutumin da zai kwanta ne yake fama da gyaran suma' amma dai ta kame bakinta bata ce komi ba.

Har ta gama, ta dauki mai ta shafa mishi a sumar, wayarshi yake yi abinshi, yana ta yaryara yaren turanci tare da wanda yake yin wayar kai kace rainon kasar Amurka ne.

Ganin baya da niyyar barin wayar tashi, sai ta zagaya ta bayanshi ta rungumoshi da kyau. Ta kai hannuwanta saman faffadan kirjinshi tana shafawa a hankali cikin yanayi na son daukar hankalinshi.
Ta kuwa dauki hankalin, don kuwa tun yana iya fahimtar me ake fada mishi ta daya bangaren da kokarin jan zancen nasu, har yazo ya fara rasa zaren kamawa. Don kuwa Nadiya aikin damalmala mishi lissafi kawai take yi.

Babu shiri yayi sallama da wanda suke wayar, ya ajiye wayar tare da kama hannunta da ke ta yawo a ko'ina na sassan kirjinshi. Idan ya kyaleta tuni zata sanya ya manta da zancen fushin da yake yi da ita.
Ta zagaya tana kallonshi tana wani lankwashe murya da kai gefe daya, "haba Yallabai, Abban Ammar, ango a wajen Shukurah da Nadiya! Babangidan Ummah ikon Allah! Laifin nawa yayi girman da ba za a iya yafe min shi bane kuma?!"


39.



Kirarin nata ya so ya bashi dariya, amma sai ya fuske ya ki bari ko dan murmushine ya bayyana a fuskarshi. Don ya fuskanci dai idan ba ta haka ba, Nadiya ba a samo kanta ta sauki.

Ya janyeta daga jikinshi, ya wuce gefen gado ya zauna abinshi, tana biye da shi a baya itama.
Yace, "wane irin ango kike magana? Dama haka anguna suke ne? Suna bibiyar matansu suna yakicesu, wai har suna mantawa da zuwa kiran angunan nasu barci ya daukesu? Wannan ai ba ango bane, wanda ba a so ne!"

Tayi murmushi, ita rigimar tashi ma dariya ta koma bata kuma. Tace, "to ai nace kayi hakuri fa, kuma in Allah Ya yarda hakan ba zata sake faruwa ba."
Sai ya gyara zamanshi da kyau yana kallonta a nutse, yace, "ai dama tun ba yau ba tara ki nake yi in ga iyaka gudun ruwanki Nadiya. Shi kenan ni kullum bini-bini ina tafe kan hanyar dakinki wai na zo kwana, saboda nine makale mata ko me? Ko kuwa don na fi ki son yin abin? Shikenan ke dai in an zo inda kike kin iya ki dinga lankwashewa mutane murya da kanne idanu, amma in ba a zo inda kike ba kuma dai ko oho! Ai ba haka sauran mata suke yiwa mazajensu ba."

Tayi kasa da kanta cike da jin kunya, tace, "to shikenan ni kuma sai dai a dinga ganina ina tafe a sashenka kullum? Wannan abin kunyar har ina!"

Aikuwa ya jefa mata harara da duka idanunshi, "ok! Abin kunya ne kenan don ki faranta ran mijinki?"
Ganin yadda yake neman juya maganar sai tayi saurin ce mishi, "a'ah! Kayi hakuri na daina."

A lokacin dai zama yayi ya mata bayani daki-daki, duk wani abu da yasan tana mishi wanda baya so, kamar dai rashin zuwa kwana dakin nan nashi, da yadda yake fadin bata fifita al'amuran da suka shafeshi. Har gyaran dakinshi a ranar sai daya lankaya mata ya koma kanta. Tace taji ta amsa duka, zata gyara inda ta kuskure.
Sai ya ja ta jikinshi ya fara kokarin hade bakinsu waje daya, tunda dai ya gama neman fadan da ita yanzu.
Ta janye tana kallonshi, "abinci fa yana bangarena na ajiye, kada ya huce."
Yace, "bar zancen wannan abincin yanzu Nadiya!"
Ya mata rumfa da jikinshi yana fanshe bashin da yace sai ta biyashi. Ta kuwa biyashi da tsada sosai.

Ba ita ta samu sukunin komawa bangaren Ummah ba sai bayan Magriba. Ta shantake a can har dare ya tsala, suna ta hirarsu da Mami kamar irin ta 'yan'uwan da suka jima basu hadu ba.
Sai wajajen karfe goma ta yi mata sallama, ta tayata tashin Farida da Ammar da suka yi barci anan falon, suka rakasu zuwa sama. Sannan ta leka Hajiya Ummah tayi mata sai da safe da kuma fatan Allah Ya kara saukaka mata jikinta.

Ta wuce sashenta kai tsaye, ta cancada wanka tayi kwalliya da kayan barci masu daukar hankali, sai ta dora hijabi doguwa a saman kayan ta kulle bangarenta ta nufi turaka.
Tafe take har ta karasa, zuciyarta na cike da wasi-wasi da sake-sake. Wani abu ya tsaya mata a rai ya ki fita, ta rasa dalilin da yasa take kasa sakewa da Babangida kwata-kwata a shimfidarshi. Dazun nan duk irin burika data dinga dauka a kanshi da yadda zata sake dashi ta faranta mishi da kyau don ta wanke kanta a wajenshi, amma ta rasa dalilin da yasa kawai daya tabata sai taji ta kasa aiwatar da komi. Sai dai kawai ta sakar mishi ragamar komi.

Tana maida kofar dakin ta rufe, taji an janyota ta baya an rungume. Ya sanya fuskarshi a saitin kunnenta yana rada mata, "you are late."
Ba kuma tare daya bari ta amsa mishi ba, ya fara salube hijabin nata yana janta zuwa bedroom dinshi.


7'7'7'7'7'7'


Kwana biyu da yin hakan, Mami tayi sallama dakin Ummah bayan itama ta kammala nata shirin na kwanciya. Zaune ta sameta a gefen gado, ta tsiyaya shayin Chamomile a dan karamin mug tana kurba, da kuma takardu a gefenta tana dubawa.
Ta dauki wani mug din itama ta tsiyaya shayin ta zauna a gefenta, don kuwa yau hira ce zasu sha ba karama ba ta yaushe rabo, wadda tun zuwanta basu samu damar yi ba.

Kasa-kasa take kallonta tana ta dube-dubenta har ta kammala, ta bude drawer ta gefen gado ta sanya takardun. Ta daga kai tana kallon Mami da dan murmushi akan fuskarta, "wai wannan kallon na menene? Tun dazu kin sanyani a gaba kina ta kallo, kuma baki ce komi ba."

Mami ba mutum bace mai boye-boye. Halinta frank ne, kai tsaye take fadin magana gadan-gadan ba tare da tsoron abinda zai biyo baya ba, haka gaskiya komi dacinta ta kan zauna ta tsarge maka ita ne kai tsaye. In yaso daga baya ta yi dealing da abinda hakan zai haifar.
Tayi karatu a bangarori da dama na likitanci da ilimin halayyar dan Adam wato Psychology. A halin yanzu ita din Licensed Mental Health Therapist ce, wadda tafi kwarewa a Trauma and Family Therapy. Sai ta juye gabadayanta a lokacin, ta dauko rigar Therapist dinta ta sanya. Ta tunkari Hajiya Ummah din a matsayin therapist.

Tace, "ina mamakin irin kallon da naga kina watsawa surukarki ne Ummah. It's not like you sam. Ko kuwa dai tayi miki wani laifi ne?"
Ummah ta yamutse fuska a take, "don Allah kada ki janyo min zancen da zai bata min rai da wannan daren har in zo in gaza barci. Idan ba hirar yaushe gamo ko ta su Fu'ad zaki yi min ba, to don Allah hada naki-i-naki ki bani waje in kwanta."

Ta gyara zama da kyau tana kallonta, tace, "wannan hirar ma ai ta shafemu. Kuma ni dama koda kika ji ina dokin zuwa nan to saboda wannan ne kawai. Don nasan idan ma nace zamu yi ta a waya ne ba yarda zaki yi ba. Shi yasa nace zan jira sai mun zauna ni dake ido-da-ido."
Ta nisa tana kallon Hajiya Ummah din a nutse tana karantar yanayin da take ciki, kafin ta sauke numfashi, tace mata, "tun kafin ayi auren wannan, sai da na fada miki. Idan kin san ba zaki iya jurewa ba ki manta komi dake ranki, kada ayi auren nan. Maganin kada ayi, kada a fara. Amma kika nace. Yanzu kuma ki duba abinda ke faruwa, kwanaki biyu kacal nayi a gidan nan, amma tuni har na gama karantar yadda baki sakewa yarinyar wannan ko kadan. Kina ganin kuma yadda bata iya sakewa a cikin gidan aurenta saboda ke kawai. Wallahi ina jiye miki tsoron hakkinta da kike dauka, da tarin zunuban da kike karawa kanki saboda riko da mummunar gaba irin taki!"

A wannan gabar a fusace Ummah ta kalleta, tace, "yanzu Sumayyah har kina manta ko ita din tsatson wacece?"
Tace, "na sani sarai, tsatson makiyinki ce Alhaji Laminu! Sai dai abinda kike mantawa shine, duk ta inda aka shiga aka fita dai, tsatsonmu ce. Tsatson Alhaji Nalado ce. Don haka ko kin ki ko kin so, jininki ce. Tunda dai ba a canzawa tuwo suna. Wai ba Allahn da Ya haliccemu bane ya horemu da mu yi hakuri ba? Ba Shi bane ya mana alkawarin saka mana da rahama mai dumbin yawa ba a lokacin da muka yi hakuri a lokacin da aka zalunce mu? Me yasa ke ba zaki yi hakurin ba? Ke me yasa ba zaki manta da abinda ya riga ya faru ba? Lokaci ya ja, kwanaki sun tafi da yawa. Me rikon naki yake haifar miki a halin yanzu? Bayan cuta daya barki da ita da threat din kamuwa da cutar shanyewar barin jiki?!"

Hajiya Ummah tayi shiru tana sauraronta, hawaye suna cika mata idanu. "To ya kike so inyi? Ba zan taba iya barin wanda ya cuceni ba wallahi! Ba zan iya ba!"
Mami ta tari nunfashinta tun ma kafin ta dasa aya, tace, "shi din yana ina yanzu to? Da shi da Baban namu suna ina ne? Suna can sun koma ga Ubangijinsu, tuni sun manta da abinda ke kike fama dashi a ranki shekara da shekaru, kina sauke fushinki akan mutanen da basu ji ba basu gani ba. Saboda Allah menene laifin Nadiya a wannan abin? Lokacin da abin nan ya faru, ko uwarta ba a haifa ba. Balle ita kanta. To meye ruwanta anan? In fada miki gaskiya, ba fansa bace kike dauka anan, wallahi hakkine da tarawa kai dumbin zunubi kawai. Zan kuma so kiyi nadamar hakan tun kafin lokaci ya kure miki Ummah!"

Kawai sai ta saki wani kuka mai cin rai, Mami ta rungumota a jikinta tana kokarin tausarta da kalamai masu dadi.
"Yaya don Allah, ina rokonki ba don ni ba, ki manta da duk abinda ya faru haka nan. Don Allah ki samawa ranki salama, ko muma da muke damuwa da halin da kike ciki zamu samu salamar rai. Ita daukar fansar ma wai menene fa'idarta musamman akan wanda bai san kina yi ba? Zan so ki hakura haka nan, ki yarda duk abinda yake faruwa da bawa dama can rubutaccene tun kafin ma a samar dashi a allon kaddarar mu. Mu su wanene da zamu ja da hukuncin Allah? Bayan ita kaddara din ita take shaping dinmu zuwa wasu mutane na daban, masu iya hakuri da jurewa duk wani yanayi da zasu shiga a rayuwarsu?"

Ummah ta lumshe ido hawaye yana kwarara daga cikin idanunta, "ta yaya zan yafe mishi Sumayyah? Ta yaya zan iya yafe mishi?!"


/'/'/'/'/'/'


*HAJIYA UMMULKHAIRI KACHALLA!*

Sun taso cikin tsananin kulawa da kaunar iyayensu, musamman ita din da tazo a farko kafin haihuwar Sumayyah. Soyayya dai da gata, babu irin wanda bata gani ba a rayuwarta. Har kuwa bayan da aka haifi Sumayya, Ummulkhairi ita ce yar gaban goshin iyayenta musamman ma dai Alhaji Kachalla.
Tun kafin su girma, Alhaji ya gama shirya musu feature dinsu. Su dukansu karatun likitanci ya zabar musu, ya kuma dauki alkawarin zai kashe musu kudi komi yawansu don su cimma wannan buri nashi. Kasancewar bashi da d'a namiji, ya dauki Lamin tamkar wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login