Showing 129001 words to 132000 words out of 142169 words

Chapter 44 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

460

har yanzu baki gama wayewa ba sai an kwana biyu kila!"
Ta tabe baki, tace, "aikuwa in dai wannan dabi'ar kike kira wayewa to wallahi kina da sauran samun sanayya akan wayewar mutane. Ke yanzu ina wayewa ga diya mace, musulma, ta tashi ta dinga tika rawa a gaban iyayenta da yan'uwa da mazan da ba muharramanta ba, ana kallonta. Ina kika baro addininmu da al'adarmu Safiya? Ni dai kullum ina fada miki wallahi ki dinga kiyayar kanki, don kin iya rawa ba a hanaki ba, kiyi kayanki ke daya mana..."

Anty Lima ta katseta ta hanyar cewa, "... ko ta jira idan tayi aure ta dinga yiwa mijinta ba! Kinsan fa mazajenmu like that chic-thing. Twerking da...."
Nadiya ta katseta, "...to kara turata don Allah ni ina kokarin yi mata nasiha da fada."

Anty Lima ta daga hannu sama tana yar dariyar tsokana, ta tashi ta bar wajen ta koma wajen Mami bayan ta karbi Khairiyya dake hannun Hajiya Hadiza.

Nadiya ta maida kallonta ga Safiya, "ni dai ina kara miki fada da jan kunne Safiya, ki rage wadannan abubuwan. Don kina zaune a kasar waje kina ganin babu mafadi a gabanki, hakan bai baki damar dagewa ki dinga cin karenki babu babbaka ba. Kiji tsoron Allah wallahi. Wannan raye-rayen naki ni bana ganin fa'idarsu wallahi. Maza da dama kuma basu cika ganin mace mai wannan raye-rayen da mutunci ba sam!"
Tayi kasa da kanta jiki a sanyaye, "in shaa Allah Adda zan daina. Ai na Tiktok da Insta din ma duk na daina fa, na goge duk accounts dina wallahi."
Tayi dan murmushi "hakan yayi. Allah Yasa to Safiya. Allah kawo miji nagari mu sha biki!"

Ta tabe baki, "tab! Ai ni da aure ba yanzu ba tukun. Sai na gama karatuna na zama cikakkiyar likita, an bude min asibitina sannan."
Nadiya tayi dan murmushi kawai.

Bata san lokacin da Fu'ad ya fito daga filin rawar ba, sai juyawa tayi ta ganshi ya ja kujera a kusa da Safiya din ya zauna yana janta da hira. Ta bisu da kallo tana dan murmushin ganin yadda ya dauki gabadaya hankalinshi ya maida gareta. Duk wani motsi da zata yi to akan idanunshi suke, baya ko kifta ido haka yake kallonta tana mishi magana cikin jan aji da kwainane.
Ta kara murmusawa, a ranta take cewa, to bari mu ga yadda zata kaya dai!

Zuwa bayan isha'i an gama taro, sunyi sallama da mutane, aka tafi aka barsu su kadai da tarin ma'aikatan dake shake a gidan.
Ummah ta samo mata wata yar dattijuwa, Baba Adama, daga cikin danginsu dake nan zaune a Kaduna, wadda zata dinga tayata kulawa da yaranta har zuwa lokacin da zasu gagije.

Kowacce daga cikinsu tana da dakinta babba, falo mai dauke da bedrooms biyu kuma dukansu manya ne kuma well furnished. Duk da cewa dakunan daya yana kallon daya ne, sai daya ba Shukurah zabi ta fara zaba.
Shi na shi yana gefe da su kadan, kusa da dakunan yara.
Kasancewar bangaren baki a can waje yake kuma akwai doguwar tafiya kafin a karasa, sai kawai ta nunawa Baba Adama daya dakin dake bangarenta tace ta zauna. Ammar yana wajen Ummah. Suna hutun makaranta ne a lokacin, kuma tace tana so su je Maiduguri da shi a cikin satin. Don haka sai idan ta dawo sannan za a mayar dashi wajensu. Duk da cewa dai Ummah na nuna take-taken ita zata rikeshi a hannunta.

Suna shiga daki wanka kawai suka yi, ta kwantar da su cikin crib dinsu bayan ta shiryasu. Itama ta fara nata shirin na kwanciya.

Washegari da safe wajen karfe goma ya bukaci ganinsu a falonshi. Ta riga tayi wankanta ta shirya, yaran ma ta shiryasu tsaf. Sai ta goya Abulkhairi, Khairiyya kuma ta rungumeta ta wuce falon nashi cikin shigar doguwar riga ta atamfar Holland mai ruwan ganye. Ta cake daurin dankwalin nan sassalkan gashinta ya fito wanda ta kame da band a keyarta. Daga ita har yaran kamshi kawai suke zubawa mai taushi.

Ta sameshi shi kadai a falon da takardu a gabanshi yana dubawa, ta duka ta gaidashi ya amsa mata a nutse yana binta da wani irin kallo kasa-kasa. Musamman data kwantar da Khairiyya a gefenshi ta kuma duka tana shirin sauke Abulkhairi. Sai ya saki ajiyar zuciya, ya ture takardun gefe yana shirin damkota, tayi sauri ta zille tayi gefe tana sakar mishi wata irin dariya a tausashe. Ya lumshe idanu yana jingina kanshi da kujera, "ni kike tsokana ko Baby? Zaki yi bayani ne duk ranar dana kamaki a hannuna!"
Tayi murmushi ta ajiye mishi Abul akan cinyarshi, kamshin turarenta na kara kai mishi karo.

Sallamar Shukurah ce ta sanya ta matsa daga gefenshi, ta koma kujerar kusa da shi ta zauna.
Ta kalleta tana dan murmushi, "Anty Shukurah Ina kwana?"
Ta zauna a kusa da ita, "lafiya lau Maman biyu, ya gajiya?"
Ta amsa mata da, "gajiya ta bi lafiya ai."
Ta matsa ta dauki Khairiyya kafin ta kalli Habibun itama tana gaidashi, "Honey barka da safiya!"
Ya amsa mata a hankali.

Hadasu yayi ya sake musu nasiha da wa'azi na sabuwar rayuwa da suka shiga, da kuma nuna musu girman irin nauyin da ya hau kansu, ya kuma hada da rokon yana fata zasu bashi hadin kai su tayashi ya sauke wannan nauyi. Duk suka amsa da 'in shaa Allahu'

Daga nan ya dawo kan yadda zamantakewarsu zata kasance. Zasu cigaba da yin kwanaki bi-biyu kamar da, ga masu aiki nan da masu girki a gidan, su samu lokaci su zauna da su saboda su sanar da su irin cimar da suke so a dinga yi. Bai hana yan aiki yin abinci ba, amma yana rokon alfarmar duk wadda yake a wajenta ta dinga yi mishi girkin dare da hannunta, zasu iya? Duk suka ce babu matsala in shaa Allah.
Ya gyada kai, "ok! Nadiya yaushe kike yin arba'in?"

Ta kalleshi bakinta na son yace ya taimaka ya bari tayi kwanaki sittin, amma tasan ba zai karbi maganar da hannu biyu ba musamman da yake ga Shukurah nan, sai ta langwabe kai gefe guda, tace, "nan da kwanaki uku masu zuwa."
Yace, "It's settled then, nan da kwanaki ukun idan kunyi canjin girki sai dokar ta fara. Akwai mai tambaya ko karin bayani?"
Suka yi shiru suna kallonshi.

Ganin haka sai ya gangara kan ainihin zancen daya sanya ya tattarasu, wato wa zata rike mukamin First Lady a cikinsu? Shi yana tunanin idan zasu iya, su yi running din ofishin su biyu. Tunda dai babu wata doka ta Constitution da tace dole sai mutum daya ko kuma ga wani na daban da zai iya rike kujerar. Amma me suke gani?

Nadiya ta gyara zama tace, "ni dai ina ganin kawai gwanda mutum daya yayi wannan din, saboda gudun samun matsala da abinda ya danganci haka. Bugu da kari kuma gaskiya ni bana ma ra'ayin hakan gaskiya. For the time being ina so in samu lokacin kula da yarana da kuma tunanin abinda zan yi da rayuwata."

So take yi in da hali, ta samu ta cigaba da Masters dinta ko da ta online ne. Bata gama yanke shawarar abinda zata yi ba har yanzu saboda so take yi sai ta fara mishi maganar taji yanda ya karbi zancen sannan.

Shukurah kuma cewa tayi, "ni dinma zan so ace mun rike din tare gaskiya. Amma duk abinda kuka yanke, bani da matsala ni."

Yayi shiru yana tunani kafin ya nisa, yace, "to shikenan. Shukurah zata kula da abinda ya shafi ofishin First Lady, amma title din First Lady ku dukanku zaku amsa regardless of ga wadda take rike da ofis da sauransu. Kema Nadiya akwai kungiyoyi da dama da suke yi min zancen suna so su gayyaceki tun bayan wannan shirin da kuka gabatar kwanaki. Don haka zamu zauna mu fitar da wani program kawai, ta yadda koda sau daya ne a wata za a gabatar da wani shiri na daban domin wayarwa da mata kai akan abubuwa mabanbanta, in yaso ke sai ki dinga jagorantar shirin. Ina tunanin hakan ma ai wani aikin ne na daban ko?"
Ta gyada kai cikin yin na'am da hakan. Da haka dai suka kare zaman bayan ya hadasu da Aides dinsu, suka gabatar musu da ma'aikatan gidan da duk abubuwan da suke yi.
Har tour dinsu aka yi a cikin gidan, haka kuma an hadasu da wasu matan guda biyu wadanda zasu dinga taimaka musu game da harkokin gidan Gwamnati da siyasa for the time being, kafin kansu ya gama wayewa.


*

Kwanaki uku kenan, ta gama shirinta cikin kayan barci marassa nauyi, saman rigar net ne yayinda kasanta kuma silk ne, sai dan wandonta na 3-quarter shima silk.
Tayi addu'a ta tofe jikinta da na yaran, ta gyara gado ta kwanta abinta.

Barci ya sureta mai dadi sosai, sai jinta tayi cikin jikin mutum. Ta juya a hankali tana fuskantarshi ta cikin hasken bedside lamp guda daya data bari a kunne mai taushin haske saboda yaran.
Ta kai hannunta ta kamo nashi dake yawo a jikinta, ta dan turo baki cikin yanayin alamun ban tausayi, "kai Abban Ammar, abin ma ai da tausayi!"

Bai dakata da abinda yake yi ba, sai ma kara zafafa sumbata iri-iri da yake manna mata a duk inda bakinshi ya kai a jikinta.
Yace, "ni ai dama na dade da sanin ba ki tausaya min Nadiya ko kadan. Shikenan daga kinyi 'ya'ya sai ki manta da ni, kika shareni kwata-kwata, kika wancakalar da lamurana. Yanzu kuma kina fada min wai da tausayi? Tausayin me zan ji, bayan ma nine abin tausayin?"

Ta dan janye jikinta daga nashi tana kallonshi, "ni dai don Allah kayi hakuri ka bari mu kara kwana biyu tukun. Ka ga fa su Abul basu gama yin kwari ba."

Ya kama baki yana kallonta cikin mamaki, "lallai ma, kin kuwa ma san abinda bakinki yake furtawa? Ina ganinki ko sati uku baki cika da haihuwa ba kika fara sallah. Nayi hakurin, na kara hakurin akan wanda nayi, yanzu kuma kike wai bani wani labari na daban?!"
Ya rarumota ya hade da jikinshi, "na rantse da Allah na gama hakurin, yau dai, da yardar Allah sai mun samo wasu yan biyun!"

Da yake itama maganar tata bata gama kaiwa zuci ba, don kuwa itama tayi kewar mijinta. Jan baki ne kawai da tsokana, sai ta biye mishi. Suka raya wannan dare cikin tsananin kauna da soyayya mai sanyaya rai. Yayi sa'a har ya gama cin angon nashi yaran basu motsa ba.


52.



His Excellency (Dr.) Alhaji Habib Abdullahi Makama. Magidanci dan kimanin shekaru arba'in da takwas. Yana daya daga cikin Gwamnoni wadanda suke da karancin shekaru akan karagar mulki a wannan lokacin.
Ya fara aikinshi da gasken-gaske ba da wasa ba, Yayi sa'a kuma ya dauki amintattun mutane a matsayin wadanda zasu tayashi rikon mulkin, don haka komi yana tafiya cikin dadin rai. Dan abinda ba a rasa ba bai wuce sukar makiya da yan adawarsu da suke binsu suna bata musu suna da kokarin nunawa Talakawa da mutane babu aikin da suke yi. To da yake dai idanu ko da ba mudu ba amma sun san kima, talakawan suna ji kuma suna gani a aikace irin aikin da Gwamnatin tashi take musu babu dare babu rana, sai sukar tasu take faduwa a banza.
Cikin watanni takwas kacal da yayi da karbar aiki, an ga canji irin wanda aka jima ba a gani ba a cikin garin Kaduna da Kauyuka.

Ya tsayawa makarantu na Gwamnati da asibitoci da kuma ma'aikatanshi, babu jinkirin yin albashi, asibitocin Gwamnati an cikasu da magunguna na kyauta. Kuma duk wanda aka kama da kokarin satar kayan Gwamnati babu bata lokaci ake cireshi daga kan mukaminshi. Wannan ya matukar sayo mishi mutunci da kima a wajen mutane kwarai da gaske.

Haka suma matan nashi suna matukar kokarinsu wajen ganin sun sauke nasu hakkin dake kansu.
Duk da cewa Nadiya bata fita ko'ina, tana gida tana kula da yaranta. Hakan bai hanata tashi tsaye wajen ganin cewa tayi nata kokarin ba. Ta dukufa wajen ganin cewa ta inganta rayuwar kauyuka.
Ita da Shukurah su kan zauna su zabi kananun kauyuka, a duba matsalar da tafi addabarsu, abin amfanin gona ne? Ko kuwa matsalar ruwa ce? Ko kuma matsalar rashin kyawun hanya ne? Sai ayi compiling din binciken, a turashi ofishin Mai Girma Gwamna daga ofishin First Lady. Inda shi kuma zai dora alhakin bincike da kwangilar yin aikin a hannun Kwamishinoninshi domin a gabatar da aikin. Haka kuma baya yin kasa a gwiwa, ya kan tashi wani kai tsaye domin yaje yaga aikin da aka yi. Idan kuma damar hakan ta samu sai ya taka yaje da kanshi.

An gina rijiyoyi bila adadin a kauyuka da dama ta dalilin haka. An gina masallatai da makarantu na Arabi da boko a Kauyukan da suke da karancin wadannan, haka kuma an samarwa manoma da dama taki da iri na noma sosai. Ciki da wajen Kaduna idan ka zagaya zaka ji kalamai na yabo da sanya albarka ta wannan Gwamnati daga mutane tana tashi kawai.

Yaranta suna ta girma da wayo tubarkallah. Idan ka gansu baka taba cewa wai watanninsu tara yanzu. Rarrafe suke yi zuwa ko'ina, don Abul da yake ya fi Khairiyya kazar-kazar da rashin gwabin jiki har ya fara tsayuwa yana kokarin takawa.
Baba Adama ta tafi gida tun bayan da suka cika watanni hudu. Ita da Maigidan nata suka yi mata sha-tara ta arziki lokacin da zata tafi.

Ummah kuwa da gaske dai ta kwace musu Ammar. Ta hanasu rikonshi kiri-kiri, tace tunda ga yan biyu nan a gabansu, kuma da wasu masu zuwa nan gaba ma da Allah kadai Yasan iyakarsu sai su bar mata shi a wajenta tunda ita babu kowa a gabanta, ta samu mai tayata debe kewa.

A halin yanzu Ammar din yana wajen su Nadiya din, Ummah din ta tafi Umarah tun watan daya wuce.
Gida ake gina mata mai suna gida a can Shagari Low cost. Tace dama can ai estate din Makama mallakin Habib ce, don haka ita zata koma nata mallakin itama.
Yace mata, "Ummah ko dai munyi miki wani laifi ne? Barin estate dinnan kai tsaye sai kace ana korarki? Naga dai zamanmu lafiya lau ko? Idan kuma ginin cikin estate dinne bai miki ba to ki fadi irin wanda kike so sai a rushe wancan a gina miki shi din. Amma don Allah kiyi hakuri kada kiyi nisa da mu. Gidan wallahi fadi zai min sosai idan baki nan!"

Tayi dan murmushi mai kayatarwa, a babban falonshi suke da yake shakatawa tare da Iyalinshi a cikin gidan Gwamnatin.
Ranar wata Asabar ce taje gidan da hantsi domin tayi musu sallama saboda washegari jirginta zai daga kasar Jordan. Taje ta gano Mami wadda ta samu minor accident a hanyarta ta zuwa aiki ta samu gocewar kashi a hannu, daga can ne kuma zata wuce Saudiya yin Umarah. Bata fadi ranar dawowa ba saboda tace sai sun ganta kawai.

Tace mishi, "laifin me kuma Babangida? Kada ma ka sanyawa ranta wannan abin, don kuwa ba haka bane. Kawai dai naga lokaci yayi daya kamata in barku hakanan, in koma cikin 'yan uwa nima. Ka Girma yanzu, ka zama abinda mu da kai muka jima muna fata. Bayan hakkin iyalanka dake kanka, ga na Jihar Kaduna gabadayanta, ba zan kara maka wani nauyin ba. Ka cigaba da jagorantar da rayuwarka data iyalanka da Jaharka yadda kake yi, in shaa Allah Allah zai dafa maka!"

Yadda kasan wani karamin yaro haka ya koma a lokacin, yana tuno yadda tun tashinshi bai taba rabuwa da Ummah ba sai ta sanadin lalura. Son samu daga shi har ita su zamana a waje guda kamar yadda ya tashi a gabanta, ace koda mutuwa ce tazo ta dauki dayansu a gaban dayan.
Yadda duk damuwa da rashin jindadi suka bayyana akan fuskarshi sai abin ya bata dariya, ta sake murmusawa tace, "in banda abinka Babangidana, dukanmu muna cikin garin Kaduna ai ba wahalar ganin juna zamu samu ba. Yanzu ma ai ba waje daya muke zaune ba, gashi kuma dukanmu muna zaune lafiya lau? Me ya canza?"

Yace, "wannan ai daban yake Ummah, nasan dai komi daren dadewa zamu dawo mu sameki a inda kike. Tashin naki ne bana jin zan iya dauka ko kadan Ummah, don Allah ki sake shawara!"
Tayi murmushi kawai, daga karshe dai yasan cewa ta gama yanke shawararta, babu zancen canzawa.

Haka Iyalan nashi suka shigo suka sameshi zaune jugum-jugum a gaban Ummah din, jikinshi duk yayi sanyi. Jin labarin tashin Ummah daga Estate din su ma kansu bai yi musu dadi ba. Haka suka dukufa a gabanta suna rokon tayi hakuri, ta daure su karasa zamansu kamar yadda suka faro. Amma ta riga ta gama yanke shawararta, don zancen da take yi musu ma tuni filin data saya an fara foundation din gini. Tana sa ran lokacin da zata dawo daga Saudiyyah an kammala ginin sai dai ta tare kawai.

Ganin ta dage dole suka yi hakuri, suka yi fatan Allah Yasa hakan ya zame musu alkhairi gabaki dayansu.
Ta karasa yinin ranar anan gidan cikin jikokinta suna ta wasansu da kaiwa da kawowa a gabanta, ranta fal da farinciki da jindadi. Sai da yammaci sannan direba yaje ya dauketa domin taje tayi sallama da sauran yan uwa da dangi.

Kwana biyu ayyukanshi kanshi sai da suka dan yi sanyi saboda har lokacin ya ki hakurarwa kanshi da zancen barinsu da Ummah zata yi. Sai da Nadiya ta dage da bashi baki da nuna mishi yayi hakuri ya marawa hukuncin Ummah baya, ya kuma cigaba da addu'ar Allah Yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu, sannan ya iya samu ya hakura din.

Ko sati biyu Ummah din bata yi da tafiya ba, Shukurah ta dawo gida daga ofis dinta da yammacin ranar Talata. Maigidan nasu yayi tafiya zuwa garin Kano domin amsa gayyata ta musamman da Maigirma Sarkin Kano, Alhaji Ibrahim Auwal yayi mishi domin bashi lambar yabo da girmamawa akan kwazo daya nuna na dawowa da ma'aikatan Makarantar Gwamnati fiye da dubu biyu da aka cinye musu albashi na tsayin wata bakwai, tare kuma da gurfanar da wadanda suke da wannan alhaki a gaban Alkali. Wannan jajircewa da yayi da nuna gwaninta da kwazo yasa Mai Girma Sarkin Kano din ya gayyaceshi fadarshi domin jinjina mishi da bashi lambar yabo da girmamawa.

Tana zaune a babban falonsu inda suke karbar baki. Tare take da wakiliya ta musamman da Matar Shugaban Kasa, wato Hajiya Badariyya Kamal ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login