Showing 87001 words to 90000 words out of 142169 words

Chapter 30 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

465

a hankali, kafin ta mayar da kallonta ga shi Habibun don taji me zai ce. He was dumbfounded. Ya ma rasa abin cewa saboda tsabar mamakin wannan abu na Hajiya Ummah. Ta gaskiya kiri-kiri amma ki take saboda wani abu na daban? A iyaka saninshi da Ummanshi, macece ita mai tsayawa akan gaskiyarta. Duk inda karya da rashin adalci suke, to bata wajen. Amma yan kwanakinnan duk ta aro wani hali na daban, wanda bai santa dashi ba ta yafa. Wadanda ya rasa dalilin wannan sabuwar halayya tata.

Nadiya ta kulu matuka, rashin maganar da bai yi ba ya tunzurata, tasan tunda har Ummah ta furta hakan, shikenan ta zauna daram. Maganarta a gidan ai kamar tawwada CE da aka yi rubutu da ita ta bushe akan takarda, babu ja balle zancen ja-in-ja.
Ta juya ta fita daga falon da sassarfa, ranat cike da dana sanin shigowa wajen wannan dare. Da tasan irin bakin cikin da za a kunsa mata kenan, da bata tako kafa tazo ba.

Shi kuma sai bayan fitarta ne ya iya samu bakinshi daya rike ya bude, ya kalli Ummah din cike da mamaki, yace, "amma dai Ummah kin fi ni sanin cewa hakan ba dai-dai bane? Shiga hakki ne da rashin tsayar da adalci, wanda ke kike yi mun hani da hakan. Amma yanzu kuma sai kice inyi abinda baki dorani akan tarbiyarshi ba?!"

Wannan amsa daya bata sai ta tunzura Ummah. Wai yau Babangidanta ne take magana yake tsaga tsakiyar idanunta yana mayar mata da amsa. Saboda mace!
Ta kalleshi cike da bacin rai. Tace, "idan baka yi hakan ba ai ba zaka tabbatar min da cewa na auro mace na kawo maka ba ta mallakeka! Yaro ka dawo sai kace wani sha-ka-tafi! Ka duba irin rawar jikin da kake yi akan yarinya karama Babangida, sai kace a kanka aka fara yin aure!"

Maganar tayi mishi nauyi kwarai da gaske. Sai ya kasa bata amsa. Ya juya ya kalli Shukurah data coge tana sauraronsu, ranta fal da farinciki. Ya maida kallonshi ga Ummah, yace, "kiyi hakuri Ummah. Amma zai fi mun idan kina so in nesanta kaina da Nadiya ne ki fada min, zan iya yin hakan. Amma ba zan iya shiga hakkin wata ba a cikin iyalaina, bayan ba a kan wannan tarbiyar kika tada ni. Zan wuce sashena in kwanta, sai da safe!"

Ya juya ya fita, yana taku rai cike da bacin rai. Yadda ya fita din sai kace wata giwa. Ummah ta bishi da kallo na mamaki fal a cikin ranta. Har yaushe ne Babangida ya fara yi mata gardama har da hadawa da wa'azi? Lallai tayi sake kwabarta tayi ruwa.

Ya fita yayi tsaye a tsakiyar gida yana furzar da wani numfashi cike da bacin rai, ranshi idan yayi dubu to a bace yake. Shukurah ita ce ummul-a-ba-isin haddasa wannan fitinar ta yau, duk wani budget daya dauko ta wargaza mishi shi a kasa war-was! Yayi alkawarin idonshi-idonta a gidannan, sai ta yabawa aya zakinta. Don sai ya sauke mata kwandon rashin kirki iri-iri tunda abinda ta zaba kenan.

Bai yi niyar kwana dakin Nadiya ba, amma duk da haka sai ya wuce bangaren nata ganin yadda ta fita dazu cike da bacin rai.
Ya sameta ta shige daki ta kulle, ya sanya makulli ya bude kofar falo, amma bathroom dinta ta sanya sakata daga ciki. Yayi bugun duniya da magiyar ta bude, amma tayi biris dashi taki tashi.
Ta zauna a gefen gado tana ta sharbar kuka cike da takaici da bacin ran wannan rayuwa. Yau ga abinda tafi tsana da kyama a cikin rayuwar gidansu, wato daukar kwanan wata a kaiwa wata, ya faru da ita kiri-kiri tana gani, amma bata da halin tankawa. Shin dama haka mata suke ji ne?


35.



Yana dawowa sallar Asubahi kai tsaye dakinta ya wuce. Cikin sa'a ya samu ta bude dakin amma tana kwance tana barci. Da kamar ya tadata saboda yasan bata yi sallah ba, sai kuma yayi tunanin watakila ko tana fashi tunda yana kirge da kwanakinta dama. A yadda kuma ya san ta da rashin wasa da sallah, yasan mawuyacine ta makara da gan-gan. Don haka ya juya ya tafi nashi bangaren don shima ya kara dan runtsawa. Daren jiya kwana yayi yana saka da warwara ta inda yakamata ya bullowa wannan al'amari. Don ya kula maimakon abin ya fara yin kasa sai ma kara hawa da hau-hawa yake yi.

Sai wajajen karfe goma ya baro sashenshi ya fito. A farfajiyar gidan ya ci karo da motoci da escorts suna jiranshi saboda fita zasu yi da karfe goma din. Sai yace musu su dan dakata, ya shiga bangaren Hajiya Ummah ya gaisheta kamar yadda ya saba. Ta amsa mishi kamar kullum, kamar dai babu abinda ya faru daren jiya. Yayi mata sallama tana ta mishi fatan alkhairi.

Ya samu Nadiyar a zaune akan abin sallah tana lazumi. Kasancewar ta riga ta saba da gudanar da sallar walaha a dai-dai wannan lokaci a duk ranakun duniya, shi yasa koda bata sallah to sau tari ta kan nemi waje mai kyau tayi lazumi ko karatun Al Qur'ani mai Girma

Ta shafa addu'ar data gama yi, sai ta juya daga zaune din da take tana fuskantarshi. Murya a shake cike da rashin sukuni har zuwa lokacin a tattare da ita ta gaisheshi. Gabadaya sai ta kara bashi tausayi, ya taka da sassarfarshi ya karasa gareta, gabadayanta ya jata zuwa cikin jikinshi ya rungume a tsanake.
A haka din yake furta mata kalmomin, "tayi hakuri ta yafeshi, hakan ba zai sake faruwa ba yayi mata alkawari!"

Tayi kokari ta janye daga jikinshi a hankali tana ja da baya tare da girgiza mishi kai. Ya kyaleta din, amma duk da haka sai daya kama hannuwanta ya rike.
Tace, "kayi hakuri Abban Ammar. Amma ba zan iya yarda da kai ba a wannan gabar!"

Zuciyarshi ta karye, amma duk da haka sai ya dake. Yace mata, "kada ki ce haka Nadiya. Please have a little faith in me, ko yaya yake. Nasan cewa ban baki dalilai masu karfin da zasu sanya ki yarda da ni a take ba, amma don Allah wannan karon, ina rokon ki yarda da ni. Ki bani dama in gyara komi. Nasan ni nayi saken da har muka zo kan wannan gabar, amma zan gyara Nadiya. I promise!"

Hawaye suka shiga zarya akan fuskarta, tace, "ta yaya? Ta yaya zaka gyara iye? Tun ran gini tun ran Zane. Tun a farkon fari daya kamata ka yiwa tufkar hanci, baka yi ba. A yanzu da aka kawo kan wannan gabar kuma bana tunanin zaka iya yin wani katabus. Don Allah kaje kawai, wallahi a yanzu haka ganinka munana raina yake yi. Amma kaje na yafe maka hakkina da kuka shiga, ko babu komi ba zan so ka tashi a gaban Ubangiji ba a matsayin mutum marar tsayar da adalci a tsakanin iyalinshi!"

Ta juya da sauri ta shige cikin closet dinta tana kokarin rufewa, ya bi bayanta da sauri shima tare da rungumota ta baya.
Yace, "ina so ki san cewa duk duniya Nadiya, ba ni da wanda ya kai Ummah. Saboda a duk duniya, babu wani mutum mai karamci dana sani irin nata. Ta so ni, tana kuma so na fiye da yadda ni kaina nake son kan nawa Nadiya. Abinda zai sanya inyi musu da ita ba karami bane Nadiya, amma a kanki nayi, ina kuma kan yi. Saboda so da biyayyar da nake mata ba zasu sanya ni take miki hakki ba. Wanda nayi a baya ma ban ji dadinshi ba, kuma ina neman afuwarki akan hakan. Kuma abinda kike zargi bai faru ba, ban je ga wata ba a daren jiya, ban kuma dauki kwananki na kaiwa wata ba. Ba kuma zan taba yin hakan ba...!"

Ya juyo da ita suna fuskantar juna shi da ita, yayi kasa da muryarshi yana kallon yadda idanunta duk suka yi luhu-luhu.
Yace, "kiyi mun alfarma daya don Allah, kada ki kullaci Ummah a wannan abin. Don Allah ki tayani sonta da girmamata da yi mata biyayya. Na shaku da ita fiye da yadda na shaku da mahaifiyar data haifeni, zan kuma iya ce miki duk duniya babu wanda yasan halinta kamar ni din nan. Mugunta ba a jininta yake ba, all these abubuwan da take yi I promise you zata daina cikin dan kankanin lokaci. Idan kuma ta tashi son ki Nadiya, na tabbatar miki sai ta so ki fiye da ni dinnan a karan kaina!"

Anan sai ya sosa mata inda ya jima yana yi mata kaikayi, sai ta kalleshi a tsakiyar idanu tace mishi, "Abban Ammar duk kusancinku da ita da shakuwarku, ba zai taba kamo na wanda kake dashi da mahaifiyarka ba. Saboda wannan bond din Allah ne kadai yake sanyashi a tsakanin uwa da da kadai, shi kadai kuma yasan adadinshi. To ko ita din, ba huruminta bane ta sanyaka taka shari'ah da hakkin addini ba. Idan ma kuma tayi hakan, kana da damar taka kafa ka take umarninta, kuma ko a wajen Allah baka da laifi!"

Ya dan lumshe idanu yana dan girgiza kai, "I know, na sani Nadiya. Kiyi hakuri don Allah!"
Ta girgiza kai, "baka yi mun laifin komi ba ni, kawai ina tunasar da kai abinda na tabbata mantawa kayi. Iyayenmu wasu muhimman figures ne a cikin rayuwarmu da babu wani abu da zamu iya musanyasu dasu. A zance na gaskiya kuma kana shakulatin-bangaro da al'amarin Mahaifiyarka. Don Allah, don Allah Abban Ammar, ka daina hakan. Wallahi you've no idea yadda abinnan yake sanyani a cikin damuwa da tunanin me hakan zai zama makomarka? Ba lallai sai ka guji daya a cikinsu bane dayar zata san lallai kana sonta da girmamata ba, you can love and respect them both, a lokaci guda. Don Allah do this for us..."
Ta karashe maganar kwalla tana taruwa a cikin idanunta. Kallonta kawai yake tunda take magana ba tare daya iya cewa komi ba. Tsakaninta da Allah magana take saboda ta damu da shi, da halin da duniyarshi da lahirarshi take ciki. Yaji wani irin abu a tattare da ita irin wanda bai taba ji ba. Girmanta da so da kaunarta suka ninku a cikin ranshi ninkin-ba-ninkin, har ya rasa ina zai kai su.

Tunda yake a rayuwarshi, bayan Mami, baya tunanin akwai wani daya taba nuna damuwarshi akan halin da yake ciki da mahaifiyarshi. A kalaman Nadiya a yanzu kuma, sai ya dinga tsintar traces din maganganunsu shi da Mami din idan tana yi mishi nata zancen da nasiha cikin hikima irin tata da ribata.
Ya gyada kai a hankali, yace, "Allah Yayi miki albarka Nadiya, nagode da wannan tunatarwa taki. In Allah Ya yarda kuma, zan yi aiki da ita. Ina kuma fatan abinda ya faru a jiya shima ya wuce a wajenki?"

Tace, "ni ai na fada maka babu laifin da kayi mun."
Yace, yana matsawa jikinta sosai, "to idan hakane, dan bani lebbanki kadan mana inji ya suka kwana?"

Tayi baya da sauri tana kawar da kanta gefe daya, "kayi hakuri don Allah. Amma ba zan iya aikatawa wata abinda nasan idan ni ka min ba zan ji dadi ba!"
Sai ya saketa shima, ya ja da baya yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Barin nata shi zai fi a daidai wannan lokaci. Don kuwa shi kanshi yasan idan har ya sumbaceta din a yanzu, to fa ba zai iya barinta ba don wasa.

Yace, "shikenan Nadiya, na hakura. Bari inje. A sanyamu cikin addu'a please!"
A fili tace, "in shaa Allahu!"
A ranta kuma cewa take, 'addu'a ai kullum cikin yin ta nake, sai dai idan ban daga hannuna sama da sunan yin addu'ar ba!'
Ta bishi da kallo har ya fita daga dakin, kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali.

Ta sanya takalmi a kafarta kasancewar bata cire hijabin jikinta ba. Bangaren Hajiya Ummah taje ta gaisheta, cike da girmamawa da mutuntawa kamar yadda ta saba a kullum. Bata bari fuskarta ta nuna wani abu na daban ba, har ma ta hada da tambayarta ko tana bukatar ayi mata wani abu ne?
Ita gabadaya ma sai taji kunyar yarinyar ta rufeta. Tana so ta daga baki ta bata hakurin rashin kyautawar da ta yi mata jiya, tunda ita a karan kanta tasan ba dai-dai ta aikata ba, amma girman kai ya hanata cewa komi. Sai kawai ta ce mata bata bukatar komi, ta tashi ta haye sama.

Nadiya ta hau dinning ta zuba soyayyar doya da kwai da sauce din hanta, ta hada shayi ta sanya ciyawar shayin Victoria ta strawberry. Ta zauna ta ci abinda zata iya a nutse, ta kwashe kayan duka ta kai kicin inda masu aiki ke faman wanke-wanke da kokarin fara shirin dora abincin rana.

Don ta samu ta rage yawan tunane-tunane da take yi sai ta hau sama, ta shiga dakin Ammar ta shareshi ta gyara tare da fitar da kayan dattinshi ta ba masu wanki da guda. Ta sake dawowa falo nan ma ta kara gyarawa duka na sama da kasan, sannan ta wuce sashenta ta kwanta domin samun barcin da bai gama isarta ba.


***

Madam Zarah ta shiga gidanta a yammacin ranar Lahdi afujajan da ita. Hannu daya rike da jaka, dayan kuma ya sangalo gyalenta. Kitson attachment da aka mata ya sauka har gadon bayanta. Pencil skirt ne aka yi mata na kamfala da riga half bubu, amma duk da hakan bai hanata shiga falon ba a sukwane cikin sauri kamar wadda ake bibiya.

Sai kuma ta dan ja tayi turus ganin mijinta Alhaji Shehu da waya a hannunshi yana dannawa. Watanni fiye da uku kenan baya cikin Najeriyar gabadaya, ita dashi sai a waya kawai suke haduwa. Bai kuma sanar da ita zuwan nashi ba duk da cewa sunyi magana dashi a daren jiya.

Ta karasa wajenshi ta dan duka ta sumbaceshi a gefen kumatu kafin ta zauna kusa dashi.
"Yallabai, what a surprise! Ai ban san da dawowarka ba yau, da ban fita ba sam!"

Yayi dan murmushi, "afuwan my dear, tafiyar ce nima ta zo min kai tsaye shi yasa kika ganni yanzu din. Wannan sabon kamfanin da nake fada miki zan bude na energy drink aka samu wasu yan matsaloli, shi yasa na taho domin mu samu muyi tackling din matsalar da wuri."

Tace, "da gaskiyarka kam. Kana bukatar wani abu ne? Ban yini a gida ba don haka ko abinci ban samu damar yi ba. Amma zan iya sama maka wani abun da gaggawa."

Tun wani lokaci data kama mijin nata da yar aikinsu dumu-dumu akan gadon barcinshi, ta manna mishi hauka mai lasisi har da dauko wuka da cewa zata yanke mishi mazantakar tashi taga da abinda zai ke bin mata. Ya dai samu da kyar ta shawo kanta da bata hakuri kan cewa tsautsayine, bata kara daukar yar aiki ba.
Sai data sanya gardawa suka yiwa yar aikin data kasance wata Bakaniya lilis kafin ta sallameta. Ta gwammace gwara ta dinga yin girki da kanta, yan aiki kuma sai dai a kullum suje suyi mata ayyukan da za ayi mata su tafi, amma babu masu kwana.

Duk a dabararta na kada mijinta ya kyalla ido ya kara ganin wata a cikinsu ne. To in ma banda hayyata da jaraba irin ta namiji, mutum me mata kamar Madam Zarah me zai nema a wajen matan banza?
Yadda take kulawa da kanta da lafiyarta, duk watan duniya akwai ranaku na musamman da take warewa na zuwa spa kawai, ga gyara cikinta da wajenta da bata gajiya dashi. Shi yasa har kullum idan ka ganta sai kayi zaton bata kai adadin shekarun da take dasu ba. Musamman idan mijin nata yana gari, har soke harkokinta take yi gabadaya ta kasance a tare dashi. Duk dai don kada yaji kewar wani abu balle har ya kai ga kissima fita ya nema a wajen wata.

Bata san cewa namiji ba in dai mai halin bunsuru ne, mace ko uwar gyara da kayan mata za ta hadiya, su ko a jikinsu.
Don kuwa fitar nan da yake yi kasashen ketare babu abinda yake yi sai sheke ayarshi da matan banza yadda yake so.

Ya girgiza mata kai yace, "noo... Ban jima da sauka ba ai. Kuma na ci abinci a jirgi. Dinner kuma ki shirya sai mu fita mu ci a waje ko? Amma me ke faruwa ne? Naga alamun kamar kin shigo cikin damuwa."

Tayi ajiyar numfashi mai nauyi, "ka bari kawai Darling. Ina wannan arena da nake fada maka zan gina a Kaduna? Ina ta cin karo da matsaloli ne wallahi, ina tunanin kamar akwai wata a kasa, amma kuma ban san ta ina zan duba lamarin ba. A halin yanzu kuma ma ni Investors nake nema saboda budget din dana dauko babba ne. But I don't know who to trust."

Yayi shiru yana tunani, yace mata, "me zai hana ki barni inyi investing? Kinga hakan sai ya saukaka mana damar gabatar da sabon drink dinmu idan ya shiga kasuwa. Tunda akwai wajen events da kwallo a can, sai kiga mutane sun san shi nan da nan."

Ta saki murmushi cike da jindadi, "dadina da kai Yallabai, ba dai iya warware matsala ba cikin dan kankanin lokaci. Wannan shawarar taka na ji dadinta sosai da sosai fa! Bari inyi sauri in watsa ruwa, zan fito maka da duk tsarukanmu da muke yi, sai muyi maganar over dinner, yayi?"
Ya gyada kai, "of course!"
Ta duka ta kara sumbatarshi a kunci kafin ta wuce dakinta, wannan karon da kuzarinta.

Ya maida kallonshi ga wayarshi daya ajiye bayan shigarta falon, chat din da suke yi da yarinyar daya baro a kasar London ya bude yana kallon watsattsun hotunan data tura mishi yana sakin murmushi.


36.



Cikin yan kwanakin kewa duk ta bi ta dabaibayeta a cikin gidan nan kamar dai ita kadai take rayuwa. Habibun ya fita zagayen kamfen dinshi a Kauyukan dake kusa dasu fiye da kwanaki hudu kenan, Alhamdulillah kuma suna ganin nasara. Social media da su gidajen radio duk sun karade da zancenshi, duk inda ya sanya kafa kuma ya shiga jama'a ne ta kowane bangare ke dako da bibiyarshi suna nuna mishi kauna.
Ita da take a gida ba fita ba take yi, tana ta binshi da addu'o'in data saba yi a kowace rana.

Ranar Juma'ah bayan an fito Masallaci, ta shiga sashen Hajiya Ummah da kanta ta kamo hannun Ammar ta wuce bangarenta dashi. Gurasa tayi da rana, ta kuma fahimci daga Ammar din har Babanshi suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login