Showing 90001 words to 93000 words out of 142169 words

Chapter 31 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

464

son ta sosai. Don haka ne in dai tayi, to ko bata ajiyewa Baban nashi ba shi sai ta ajiye mishi.
Suka zauna ita dashi suna ci a kwano daya, tana tambayarshi game da rayuwar karatunshi da mu'amalarshi da sauran yara cikin hikima da dabara. A ta haka ta tsinci zancen akwai wani yaro daya takura mishi a makarantar saboda ya fishi kokari, yana hanashi sukuni ta hanyar muzguna mishi tare da fara janye mishi abokanshi. Ranar nan har littafinshi ya yaga mishi.
A ranta ta yanke shawarar zata tuntubi mahaifin nashi game da zancen, in ta kama ma ita zata iya bin kanun zancen domin ta yiwa tufkar hanci tunda wuri kafin lokaci ya kure. Cases irin haka a hankali suke juyawa su koma bullying, sai kaga yaro mai kokari ya dawo dakiki saboda rashin samun sukuni a makaranta da kuma takurarwar abokai. Wanda hakan kan iya affecting dinshi emotionally, sai kaga yaro ya kasa yin abokai, ya zama socially inept.

Suna cikin yin hirar wannan sai ga mai aiki taje kiran Ammar din inji Hajiya Ummah. Nadiya ta dan bata fuska cikin rashin jin dadin hakan, shima Ammar din ga dukkan alamu bai ji dadin kiran ba. Amma bai yi musu ba ya tashi ya bi bayan mai aikin.

Ta bisu da kallo cike da taraddadi. Ba tun yau ba ta fahimci kokari ake yi a janye yaron daga jikinta, a hanasu mu'amala.
Yanzu haka kiri-kiri hirar da suke zama su yi da bitar karatu da suke yi an soketa saboda da sun zauna ne, zaka ga yar aiki a saman kansu, 'Hajiya tace lokacin kwanciya barcin Ammar yayi' ko 'Hajiya tace Ammar yaje tana son ganinshi'
Ita dai ta kasa fahimta dalili da manufar yin hakan. Idan Ummah ta rabata da Ammar ribar me zata ci ne? Saboda me?

Wadannan tunane-tunane da take yi sai taji ranta ya fara baci. Al'amarin nasu ya fara kaita bango kuma. Tun zuwanta gidan bata ga wani abu marar kyau ko na assha da tayi ba, amma kuma duk da hakan kullum yadda ake treating dinta kenan. Kamar wata wadda ta aikata wani gagar??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????umin laifi.
Zuciyarta take tambayarta, to haka zata cigaba da zama ne? Ana takata duk yadda ake so, alhalin babu wani takamaiman dalili?

Abu daya Nadiya ta rike akida a cikin ranta, shine, hukunci kowane irine zata iya dauka matukar tana da laifi a cikinshi. Tana kuma yiwa mutum uziri idan taga yana hukuntata din.
A inda kuma tasan bata da kuskure kuma taga ana hukuntata, nan ne fa bata iya dauka. Don kuwa ko sama da kasa zata hade, ba zata dauki laifin wani ta kakaba a kanta ba. Ko ta karbi hukunci akan abinda bata aikata ba.

Shi yasa zaman gidansu ya wahalar da ita kwarai. Saboda a can, da gangan ake tsokanarta kuma daga baya azo a lakana mata laifin da ba nata ba. Ita kuma ga rashin iya daukar laifin da ba nata ba, ga rashin iya bada hakuri shima a laifin da bata aikata ba.

Ganin tunanikan nata suna neman jefata cikin wani yanayin na daban sai kawai ta dauki waya ta kira su Mama.
Abba ya dawo daga aikin Hajji lafiya. Gida ya cika dankam da mutane yan sannu da zuwa, kwana biyu da dawowar tashi amma har yanzu gidan da sauran yan sannu da zuwa basu tafi ba. Maryam ta hadasu da shi ta sake yi mishi sannu da zuwa, kafin ta kirata ta vedio call ta hadata da kowa da kowa dake gidan suka gaisa suka kuma ga juna.
Lallai da ake cewa lokaci babu abinda ya bari. A yan watannin baya har alwashi take sha iri-iri, akan cewa idan har ta samu damar barin gidan wannan, da ba don su Mama ba da sai ta shekare bata waiwayesu ba. Sai gashi a yau, babu abinda take so kamar ta bude idanu ta tsinci kanta a tsakiyar gidansu da dandazon yara da matan gidan.

Da zasu yi sallama ta cewa Maryam ta samu su ware rana ita da yaran gidan su je suyi mata yini kafin ta fara zuwa makaranta. Sun rubuta jamb cikin ikon Allah ta cinye. Yanzu Post utme zata yi sai kuma jiran admission.
Ta mata alkawarin in shaa Allah za tayi hakan, sai suka yi sallama daga nan.

Ta karashe yinin ranar cikin kiraye-kirayen waya da gaisawa da yan'uwa, da Anty Lima suka yi waya ta karshe. Ta ajiye wayar kan center table a nutse, ta koma ta zauna tana bin wayar da kallo.
Rabon da suyi waya da Maigidan yau kwana biyu kenan. Ta kira shi har sau biyu, amma tarin uzirirrika sun hanashi iya daga wayar. Balle ya samu damar dawo mata da kiran. Don haka itama sai bata sanyawa ranta lallai-lallai sai ya daga wayar ba, ta koma gefe abinta. Shawara take yi da canki-cankar ko ta sake kiranshi ne? Daga karshe dai ta tashi taje tayi sallar la'asar.
Ta karashe yinin ranar akan abin sallah tana karatun Al Qur'ani da yin lazumi. Kasancewar karshen sa'ar ranar Juma'ah lokacine mai tsananin falala, Nadiya bata bari ya kufce mata ba tare da tayi addu'o'i ba.

Cikin kwanaki biyun da suka biyo baya ta fara fahimtar kamar Hajiya Ummah bata jin dadin jikinta.
Ta fara lura da rashin cin abinci da take yi yanzu, sannan ta rage yawan yin zirga-zirga kamar yadda ta saba. Yanwancin lokuta zaka sameta ne a kwance ko a shingide, ga shi cikin dan lokacin har ta fara rama a fuskarta. Ubangidan ya dawo ranar Asabar da yamma a gurguje, ya sake juyawa ranar Lahdi tunda safe, don haka Nadiya bata tunanin ya kula da halin da Ummah din take ciki.

Ita kuma bata son shisshigi da tura kanta inda ba a yinta, ko don gudun kada a gwasaleta. Don haka ta rasa confidence din tambayar Ummah din ko bata da lafiya? Amma ta damu kwarai da gaske a cikin ranta.

Ranar Litinin ta tashi da azumi a bakinta kamar yadda ta saba. Ya jima da fada mata matsayarshi akan azuminta na nafila, yace ba zai hanata samun lada ba da neman yardar Allah. Amma dai bai amince mata da yin azumi ba ranar da take dashi, don kuwa bai yi mata alkawarin zai kauda kanshi daga gareta ba. Amma duk da cewa ranar girkinta ne, sai ta tashi da azuminta tunda dai ai baya gari.

Tayi sallama bangaren Ummah din da misalin karfe goma da rabi na safe, falon babu kowa sai TV da take ta aiki.
Tayi kokarin hayawa sama don su gaisa da Ummah, sai ta ganta tana kokarin saukowa.

A hankali take tako steps din tana sauka kamar marar laka. Daga yanayin tafiyar tata kadai ma zaka san cewa lallai bata da cikakkiyar lafiya. A kullum tafiyarta cike take da isa da takama mai dauke da wata irin haiba. Hajiya Ummah bata tafiyar salo-salo, kodayaushe zaka ji tana tafiya ne cike da sassarfa, mai dauke da nutsuwa da kuma alamun karfi. Amma yau duk babu wadannan a tattare da ita.

Data sauko, Nadiya ta tareta a tsakiyar falo tana gaisheta, ta amsa mata cikin yar karamar murya. Sai ta tsinci muryarta na tashi a cikin falon, tana furta, "Ummah ko ba kya jin dadi ne?"
Ba tare data gama tauna hakan a cikin ranta ba.

Tace mata, "lafiya lau" kawai, ta wuce kan dinning.
Ita kuma ta koma kan kujera ta zauna tana jan tasbahar hannunta cikin yin zikiri tana ambaton Allah. Lokaci zuwa lokaci kuma tana satar kallon Ummah data hada shayi baki ta sha. Ta ture kofin ta tashi, taje ta wuce Nadiya zata sake hawa sama.

Sai ga Hajiya Shukurah ta fado falon kamar wadda aka jefo. Ta ci kwalliya cikin doguwar riga ta leshi, don kyau kam tayi shi har ta gaji. Gashin nan an tamkeshi a keya da yake babu laifi tana da yalwar sumar kai, an daura kallabi a samanshi yadda ya fito da kyau. Dan gyalen nan ta yafo shi a kafadarta yadda kasan wata budurwace. Ita dai tasan ko Maryam ba zata yafa wannan dan gyalen ba.

Ganin Ummah tana kokarin hawa sama yasa ta karasa da dan saurinta tana kiranta, "Ummah! Ummah!!"
Sai ta juya tana kallonta a nutse. Ta ja tunga a gabanta kafin tace, "Ummah ina bukatar wasu kudine yanzu-yanzu, saboda abubuwan da muka saya jiya na kayan masarufi basu isa ba don haka dole yau sai mun kara sayen wasu."

Ta daga baki da kyar tace, "ki yiwa Zakari magana Shukurah."
Shukurah tace, "ok! Sannan jiya na fara miki maganar wata women leader da nake zargin fa kamar tana cin duga-duginmu ne. Ina bincike a kanta ne don in tabbatar, amma akwai yiwuwar tare take da kungiyar adawa, don naji daga bakin mutane da dama suna cewa bata aikin komai sai na zaginmu da yi mana batanci. Ina so ne idan har hakan ta faru, ki barta a hannuna. Don kuwa wallahi sai na sanyata yin dana sanin abinda tayi mana!"

Magana take ta zubawa, hankalinta ko bai kai ga yadda Ummah din take layi bane daga tsaye? Idanunta na budewa da kyar suna kara komawa su rufe. Nadiya tayi wuf ta tashi da sauri, nufinta ta karasa wajen ta fadawa Shukurah tayi hakuri da zancen wannan tukun, sai Ummah din ta samu zama ta huta.
Tana karasawa wajen, Ummah tana silalewa zata fadi, Nadiya tayi azamar tareta, suka tafi su duka suka fadi a kasan tiles din wajen. Allah Ya taimaka duk basu yi wata buguwa ba, amma dai da alamun Ummah ko dai ta suma, ko kuma tana kan hanya.

Tayi gaggawar tallabota tana kallon Shukurah da tayi tsaye cikin kidemewa tana kallonsu ta rasa me za tayi. Tace, "me kike jira ne?! Ki kira mana likita ko ki kama min ita mu kaita asibiti!"

Sannan ne ta zaro waya a jaka da sauri ta dannawa likitan gidan kira. Aka yi sa'a yana kusa dasu. Don haka yace ta bashi mintuna goma gashi nan.

Kafin zuwan nashi Nadiya ta sanyata a gaba tana yi mata firfitu da tofa mata duk addu'ar da taje bakinta. Shukurah tayi tsaye a kansu tana kaiwa da kawowa, lokaci zuwa lokaci ta kan kai dubanta da latsetsiyar agogo dake daure a tsintsiyar hannunta. A gefe daya kuma ga kiran waya da ake ta jera mata amma ta ki dagawa.

Cikin abinda bai gaza mintuna goman daya ambata ba kuwa sai gashi, ya shiga hannu rike da first aid kit. Ya dukufa a kanta yana aikinshi, sai gashi cikin dan kankanin lokaci ya samu kanta. Ta bude idanu tarr tana kallonsu, numfashinta dake hawa da sauka da sauri ya dawo ya daidaita. Sannan ne da taimakon Nadiya suka samu suka haura sama da ita zuwa dakinta. Inda anan ne ya hau dubata da kyau. Ya manna mata drip din ruwa da wasu allurai, sai gashi nan da nan ta yi barci.

Ya juya yana yiwa su Nadiya din bayani da suka yi cirko-cirko suna kallonshi kamar wasu zakaru,
"hawan jininta ne ya motsa, sai alamu na mura data kamata. Akwai sauran tests da zan je inyi yanzu, zan dauki jininta saboda akwai wasu abubuwa da nake tunani amma ba zan tabbatar ba har sai nayi mata test. Ta ci wani abu ne?"
Nadiya tace, "ehh, ta sha kofin shayi daya yanzu babu jimawa."

Yace, "Ok! Zan je inyi mata sauran test din zan dawo zuwa anjima, sai a kula sosai da ita kafin in dawo please. Ga magunguna na rubuta yanzu zan bada a kawosu, don haka idan ta farka a tabbata ta ci wani abun mai dan ruwa-ruwa, marar tsami kuma da yaji. Sannan a kiyaye yi mata amfani da gishiri a abinci. Allah Ya sauwake!"
Ya dauki sample din jinin nata tare da yi mata fatan samun lafiya kafin ya hada kan yan kayanshi ya wuce.

Nadiya ta bi Ummah da kallo ranta duk a jagule cike da tausayin yadda lokaci daya ta yi wani fiyat da ita.
Shukurah kuma ta mike tana makala wayarta a kunne, ta cewa Nadiya, "yauwa ni bari inje wajen taron da zamu je saboda ga mutane can sunyi gangami suna jirana."
Ta bita da kallo kamar tace, 'taron ba zai yi hakuri ba zuwa na wani lokaci ko kuma ki sanya wani ya wakilceki ba?' amma sai ta yiwa bakinta fada, ta bita da kallo kawai tana jinjina kai. Ta juya ta fita daga dakin tana magana da Zakari akan kudaden da take bukata a tura mata yanzu-yanzu.

Babu jimawa da fitarta aka kai magungunan da likita yace za a kai. Da yake kowanne da prescription dinshi a jiki, sai ta zauna ta dubasu a nutse. Ruwan da ake zubawa a hankali yake tafiya, don haka karewarshi ba yanzu ba.
Sai ta kara gyara dakin, kafin ta sauka kasa a nutse ta shiga kicin.

Lailah da sauran masu tayata aiki har sun nabba'a a falo zasu fara aikin abincin rana, sai ta fada musu yau kada suyi abinci da yawa a gidan saboda ba lallai a bukace shi ba.

Ta bude firiza ta fara ciro abubuwan da zata bukata na girki, ta kunna gas ta hau aiki.
Farfesun talo-talo tayi, ta dafeshi ya dahu luguf, ta wadatashi da kayan kamshi da yar daddawa saboda ta fahimci Ummah din tana son farfesu da daddawa. Sai ta fere irish potato shima tayi fatenshi. Ta zuba kayan lambu irinsu alayyahu, green beans, peas da danginsu kabeji a ciki. Ta kuma hada mata kunun gyada yadda take so.
Data gama ta sauye komi a cikin kwanuka masu kyau, ta jerasu a karamin trolley na abinci, ta garashi ta koma sama.

Ta samu ruwan ya kusa karewa, don haka ta dauro alwala ta nufi yin sallar Azzuhur. Tana gamawa ta cire mata ruwan tunda dai babu laifi ta iya wannan aikin.
Ta cigaba da zama anan dakin zaune akan sallaya da casbaharta tana lazumi har lokaci mai tsayi, Ummah din ta farka daga dogon barcin daya dauketa.

Sai ta karasa wajenta da sauri, tana jera mata sannu cike da kulawa da tausasawa. Kallonta take yi kamar Mama ce take a kwance a lokacin, saboda haka damuwarta ta kasa boyuwa.
Ta taimaka mata ta tashi zaune tare da jingina mata filo a bayanta yadda zata ji dadin zama. Sai ta gara trolley dinnan gabanta tana fada ga abubuwan data dafa saboda likita yace a bata abu mai dan ruwa idan ta farka, wanne zata ci?
Tace ta fara bata kunu. Ta zuba mata shi a kofi mai dan yawa, ta mika mata ta amsa tana sha a hankali. Sai ta janyo bowl ta zubo farfesun nan shima ta mika mata, ta amshi kofin kunun da ta sha rabi.

Ta girgiza kai, "bari haka nan Nadiya, na koshi."
Sai ta dan marairaice, tace, "Ummah kiyi hakuri ko kadan ne ki dan sha haka nan. Naga magungunan da aka rubuta fa suna da karfi, idan kika ce zaki dinga shan su hakanan kuma babu abinci sai kiga suna daukarki!"

Tace, "zuciyata ce take tashi ai sosai, ji nake kamar zanyi amai."
Sai tace, "to bari in zo."
Ta sauka kasa da sauri, ta shige kicin ta samu danyar citta ta bare bayanta ta markada a blender nan da nan, ta matse lemon tsami a juicer ta hadesu waje daya ta tace ta juye a cikin wani madaidaicin jug na glass, ta zuba zuma da kankara ta motsa da kyau ta koma sama din.

Tace mata, "ga wannan juice din, idan kina sha in shaa Allah zai rage miki tashin zuciyar."
Ta sake mika mata bowl din, wannan karon ta amsa babu musu ta fara ci, ita kuma ta tsiyaya mata lemun a kofi ta ajiye mata. Tana cin farfesun tana korawa da lemun, sai nan da nan ta cinyeshi duka. Nadiya taji dadi sosai, ta dauko magungunan tana balla tana bata tana sha da ruwa har ta gama sha duka. Ta kwashi yan mintuna a zaunen kafin Nadiya ta shawarceta data koma ta kwanta saboda alamun gajiya daya fara bayyana a jikinta. Sai tace mata bari ta fara lallabawa tayi sallah tukun.

Ta taimaka mata har zuwa bayi ta dauro alwala, ta shimfida mata abin sallah tayi daga zaune. Sannan ne ta koma ta kwanta. Babu jimawa barci ya sake daukarta.

Sam-sam ta manta da wata aba wai ita waya data baro a jikin caji a bangarenta da zata fito, balle tayi tunanin sanar da Babangidan halin da Ummah take ciki.
Tana kokarin janye kayayyakin abincin ne taji an turo kofa, wannan unique kamshin nashi ya fara bazowa cikin dakin kafin ya shigo gabadayanshi cikin farar kaftan, kanshi babu hula.


37.


Ta juya tana kallonshi a nutse, shi kam kai tsaye gefen gadon Hajiya Ummah ya wuce ya zauna. Ya kama hannunta ya ninke a cikin hannuwanshi damuwar shi karara tana bayyana.
Sai ta dan kara tausasa muryarta tana mai yi mishi sannu da zuwa, ya amsa a tausashe yana kara kallonta cikin wani yanayi na daban.
"Lafiya lau Nadiya, ya mai jikin?"
A hakan sai taji dan dadi a ranta, ya alakantata da Ummah har yana tambayarta jikinta. Lallai zuciya da bure-bure. Sai ta samu kanta da dan murmusawa ba tare da yasan dalilin hakan ba, tace, "jiki da sauki Alhamdulillah. An cire mata drip din yanzu babu jimawa, kuma ta ci abinci ta sha magani har ma tayi sallah kafin ta kwanta din."
Ya jinjina kai, "ok, sannunki da kokari. Nima likitan ne ya kira ni yake fada min halin da ake ciki. Luckily bamu yi nisa da Kadunar ba sosai."

Ya kara mayar da hankalinshi ga Ummah din dai, ita kuma sai ta fara gara trolley din da tayi niyar fita dashi.
Ya dakatar da ita ta hanyar cewa, "akwai sauran abincin ne?"
Tace mishi, "eh, akwai."
Ya kuwa gyara zama yana kallonta, "to zubo min ki gani."
Da alama dai yunwa ce ya kwaso ba karama ba.
Ta juye mishi duka sauran abincin ta ajiye mishi. Sai ta sauka kasa ta mayar da kayan kicin. Kafin ta gama abinda zata yi ta koma saman, tuni har ya gama cinyewa tas. Ta kalleshi da dan mamaki a ranta da kuma tausayi. Bata dai ce mishi komi ba sai kwanukan data kwashe.
Tace mishi zata je falon sama ta dan shingida haka nan kafin lokacin la'asar yayi. Idan Ummah din ta farka yayi mata magana. Ta juya ta fita da kwanukan hannunta. Gajiya da rashin barci da kuzari har sun fara tambayarta, ko don ta jima bata yi azumin ba? Sai kawai ta ajiye kwanukan anan sama, ta samu doguwar kujera mai laushi ta kwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login