Showing 18001 words to 21000 words out of 142169 words

Chapter 7 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

441

tayar da gininshi.

Zance na gaskiya Auwalu akwai tsilla-tsilla, don kuwa babban dalilin da yasa yafi yin kaurin suna wajen abokan huldarshi shine yadda babu ruwanshi da bambance tsakanin aiki mai kyau ko marar kyau, in dai zai samu kudi, to shi fa babu abinda ba zai iya yi ba. Har mata yake dauka ya kaiwa mutanen nashi su biya shi. Harka irin wannan kuwa tafe take da rufewar ido da zuciya, kafin kace me kuwa, ya fada harkar bin mata ruwa tsundum. Mutum ne marar mafadi, babu wanda ya isa ya sanyashi abinda bai yi niyya ba sai dai mahaifiyarshi da a lokuta da dama ita ce take da wannan fadar. To itama ba kullum ba, harkar bin mata dai babu irin fada da nasiha da bata yi mishi ba, daga baya dai sai data dawo ta dinga binshi da addu'a kawai.

Cikin yawace-yawacen da suke yi ne Allah Ya kaisu wani kauyen Wuro-Yanka a can cikin Yola. Mazauna garin Fulanine usul, sai dai mafi yawancinsu fulanin yawo ne, watau wadanda basu da takamaiman gari ko wajen zama. Idan sun je waje ya musu, zasu zauna na iya adadin wasu kwanaki ko shekaru, daga nan kuma su kara gaba.
Anan Allah Ya hadashi da Juwairah. Bafulatana ce danya shataf, idan ka ganta kyawunta kamar wata diyar Aljanu. Allah Ya sanya musu kaunar juna kamar me, sai dai iyayenta suka ce ba zata auri bare ba. Babu ta inda bai bi musu ba amma suka ki, daga karshe dai ya zugeta suka je Dagacin garin ya daura musu aure da yaga iyayen kudin da Auwalu ya zube mishi. Iyayenta na jin haka suka ce aikuwa haihata-haihata ita dasu, sun yafeta har abada.

Nan fa idanunta suka raina fata, don kuwa cikin dadin bakin da yayi mata har da cewa in dai aka dauro musu auren to kuwa dole ma iyayenta su amince, sai kuma akasin hakan ya faru.
Ya kara kalallameta da wani dadin bakin, yace mata ai fushi suka yi da ita, amma zasu sauko. Don haka ta basu dan lokaci, daga baya zasu hakura.
Giyar kauna da dadin bakin Auwalu, da yake gwanine ta wannan bangaren, ta kwasheta, ta biye mishi ta bi bayanshi kamar yadda yace zuwa gidanshi daya gina a Kaduna.

Mahaifiyarshi Inna Deluwa sai ganinshi tayi da bafulatanar mata sama-ta-ka.
Da yake tana zaunene a nata gidan na daban, dan tsamurmurin wajene da marigayi maigidanta ya bar mata gado ita da Auwalun.
A gidan nata ya sauka da amaryarshi, wadda ta kasa ko motsin kirki saboda tsabar kunya data lullubeta.

Daya gama mata bayanin abinda ya faru, idanu kawai ta zuba mishi ta kasa cewa komi. Ji tayi kamar ta kama shi tayi ta hada kanshi da bango ko Allah Yasa ta huce takaicin maganar da Auwal yake daukar mata.
Ta kara kallon budurwar, yarinya ce danya shataf, bata tunanin zata haura shekaru sha biyar. To shima ba wani girma yayi ba, duka-dukanshi a lokacin ba zai haura ashirin da biyar ba, rigima ce kawai irin tashi.

Taga dai idan tace ma fada zata mishi bata baki ne, don kuwa abinda ya faru ya riga ya auku dai, sai dai fatan Allah tsare gaba. Watakila kuma hakan zai iya zame mishi sanadin shiryuwarshi da daina bibiyar matan da yake yi. Ga amaryar tashi da take a takure, tana tsoron tayi mishi fadan a gabanta taga kamar kila bata yi na'am da ita ba.
Don haka ta rufe zancen fada. Ta gyara mata mazauni tare da tashi nan-da-nan ta tayar da sanwa ta dafa musu abinci.

Zuwa bayan isha'i sun gama hutawa, sun ci sun koshi. Ya tashi tafiya bayan ya dawo sallah, ya nemi amaryarshi da taje su tafi gida. Inna Deluwa tayi kicin-kicin da rai tana kallonshi, tace, "wane gidan?"

Fir! Ta ki ya tafi da ita ko'ina tace har sai yayi mata garar kayan dakI sannan. Rai cune ba don yaso ba haka ya tafi.
Shi yasa har a yau da take ba a raye ba, Mama bata taba ganin suruka irin Inna Deluwa ba. Don kuwa ta mata halaccin da ba a taba yi mata ba. Ita ta tsaya tsayin daka sai da Auwalu ya mata jeren daki tsaf kafin ta tare, ita kuma tayi mata gara irin wadda uwa take yi. Duk kuma wanda ya tambayi dangin Juwairah zata ce diyar 'yan'uwanta ce dake Adamawa. Da haka sai ya zamana 'yan'uwanta sune suka dawo 'yan'uwan Juwairah din.

Ita dinma kuma da yake bata da hayaniya da kwaramniya, gata mace mai kawaici da hakuri, sai tasu ta kusan zuwa daya da mutane.

Ko lokacin data haihu ta haifi danta namiji AbdulHadi, haka Inna Deluwa ta sake daukarta ta maidata gidanta wanka. Ta kuma yi mata duk wata al'ada da uwa take yiwa yar ta idan ta haihu. Lokacin shekarunsu biyu da yan watanni da aure.

A kuma wannan zaman jegon ne komi ya sauya a zamanta da Auwal. Gabadaya sai ya bi ya canza mata, wulakanci iri-iri babu wanda baya yi mata ita da danta, ashe wata yar kyakkyawar budurwa ce ya kyalla ido ya hango.
Tana komawa gidanshi ko wata biyar cikakke bata yi ba, ya dankaro mata amarya ya kai.

Sai a wadannan lokutan ne Auwalu yake bambance mata tsakanin aya da tsakuwa, don kuwa yadda ya rufe ido ya dinga nuna kamar ita da babu duk daya a wajenshi abin babu kyan gani.
Inna Deluwa tayi fadan, tayi nasihar, tayi ban bakin, akan ya tuna yadda yaje ya rabota da danginta ya kawota cikin nashi dangin da bata sani ba, kuma duk ta dalilinshi. Daya daga baki sai yace ai ita tayi radin kanta ba tursasata yayi ba. Wannan maganar ta matukar bakantawa Juwairah rai, tayi mata zafi sosai.

Amaryar tashi ko wata shida bata yi ba suka rabu. Kuma kafin a rufa watanni biyu ya sake yin wani auren. Nan da nan sai ya zamana wani idon mata. Mace duk inda ya kyalla idanu ya ganta to shi dai kawai ya aureta. Wanda abin takaicin daya samu abinda yake so a wajenta sai kuma wulakanci ya fara biyowa baya wanda kafin kace me sai a zo a rabu.

Ana cikin wannan yanayin sai ga amaryarshi ta biyu ta kai mishi dan jinjirin data haifa a gidansu wanda shima ba karamin rikici aka ci da Auwalun ba kafin ya kai ga sayen abin yanka. Abinda aka kayyade mishi kuma na maijegon da jinjirin ba kaiwa yake yi ba, don haka tana yayeshi ta kai mishi kayanshi.

Ana kaiwa kuma ya ba Juwairah shi yace ta hada da nata ta kula dashi, nan ne ita kuma tace ba zata yi ba. Ba zata kula da dan da bata haifa ba. Da wanda ta haifa ma ya ta kare?
Anan kuwa suka yi tashin hankalin da basu taba yi ba har ya kai ga mata gorin dangi, daga baya ma yace ta tafi wajensu duk da bai furta mata saki ba.

Bata yi shawara da kowa ba ta tattara yan kudadenta ta dauki danta, asubahin farko ta bar garin.
Sai dai abin ban tsoron shine da taje Adamawa bata samu yan'uwanta ba. A can ake ce mata ai sun fi shekara da barin garin kuma babu wanda yasan inda suka tafi kuma babu wanda ya bar mata sakon inda zata samesu koda taje nemansu daga baya.

Nan fa ake yinta. Idanunta suka raina fata data fahimci cewa bata da wata madafa ko mafita. Gidan Dagacin garin ta zauna na yan kwanaki tana tunanin mafita da tunanin abinda yakamata tayi a daidai wannan lokaci.

A kwanakinta na uku da zuwa garin ne Dagacin ya nemeta da zancen ya kamata fa tasan inda dare yayi mata, saboda shima dawainiyar dake kanshi da iyalinshi ta mishi yawa, gata kuma da danta yana kulawa dasu suma.
Ta kasa ce mishi komi sai idanu data dinga binshi dasu cikin tsananin mamaki da tu'ajjibin yadda dan'adam kan iya canza hali daga mumini zuwa dan iska. Kodayake, a wancan lokacin ai kudi ya gani, a wannan karon kuwa da ita ce take ci mishi kudin dole yayi mata wannan dibar albarka.
Ta iya daga baki da kyar ta ce mishi to ta gode da dawainiyar da yayi da ita. Ta kuma kara da cewa kuma Allah Yayi mata sakayyar abinda suka aikata mata. Idan har sun shiga hakkinta, to bata yafe ba.

Ta tashi daga gabanshi ta barshi yana mata ihun shi bai ga alkaba'in daya aikata mata ba tunda dai ai da kanta ta amince a daura mata auren da wanda iyayenta basu yarda ba, ba wani ya tursasata ba. Ta kwashi yan komatsanta tayi sallama da matanshi ta tunkari tashar mota.

Rasa inda zata nufa tayi, a iyaka tunani da tayi, ba zata iya cewa ga asalin iyayenta ba. Daga ina suke, ina suke nufa, ba zata iya fada ba.
Dai-daikun garuruwa kadai zata iya tunawa inda suka zauna, saboda duk inda suka je ba wani zama suke yi na azo a gani ba. Wuro yanka yana daya daga cikin garin da suka jima a cikinshi. Tasan ko tace zata shiga duniya neman danginta yana dai-dai da cewa tayi damarar neman jaki mai kaho, wanda yake abu mai kamar da wuya gurguwa da auren nesa. To amma ina zata nufa kenan?

Ta biya kudin motar Kano ta shiga. Aka yi ta tafiya kamar ba za a kare ba, sai can talatainin dare sannan suka isa.
Ta tsaya a cikin tashar tana kalle-kalle don kuwa ba tasan ina zata nufa ba daga nan.
Ga AbdulHadi yana ta tsala mata kuka, gajiya da yunwa su duka sun lullubesu.
Yan canjin daya rage mata ba wasu masu kauri bane. Ta matsa wajen wata mata dake sayar da abinci. Da alama ma ranar abincin kwantai ya mata don kuwa tashar ba wasu mutane bane da yawa. Ta bada aka sanya mata dafadukan shinkafa, ta kara da kunun gyada ta matsa gefe ta zauna tana ci hannu baka hannu kwarya, don kuwa tun karin safe da tayi babu abinda ya kara shiga cikinta, tana yi tana mikawa AbdulHadi shima yana ci.

Da suka gama ta lallabashi yayi barci, ta samu waje tayi alwala sannan ta shiga biyan bashin sallolinta.

Data kula da wannan mata mai abinci dai rumfa take da ita a kusa da tashar, kuma anan take kwana, sai ta matsa ta sameta da hawayenta a ido ta roki data taimaka mata ta kwana a wajenta. Ta mata karyar ai ganin gida taje, kuma sai ta yanke shawarar ta koma gida kafin adadin data dauka ya cika, kuma abin bata taba zuwa ko'ina ita kadai ba tare da maigidanta ba, shine dare yayi mata kuma tana tsoron yin tafiyar dare ko kuma kwanan tasha ita kadai.
Matar ta tausaya mata kwarai, don haka ta mata. alfarmar ta kwana din.

Kafin safiyar ta gama yankewa kanta shawarar daukar hakuri ta koma gidan Auwal tunda bata da wani zabi wanda yafi wannan.

Gari yana wayewa kuwa ta yiwa matar nan sallama da godiya, ta shiga mota suka dumfari Kaduna.

Inna Deluwa sai ganinta tayi da tsakiyar rana kamar wadda aka jefo. Tayi salati ta sanar da Ubangiji. Ta kamata ta rungume cikin murna. Daga ita har Auwalun sun shiga cikin tashin hankali da damuwa kwarai da gaske. Don kuwa duk iskancin da yake yi, yana sonta kawai giyar mata da kudice take kwasarshi tana sa wa yana mata wulakanci.

Tafiyarta kuma ita ta kara tabbatar mishi da hakan. Shi yasa hankalinshi ya dagu yayi sama, gashi lokacin waya bata zagaya ko'ina ba, to ko da wayar ma wa suka sani da zasu tuntuba? Shi yasa suka mayar da hankali wajen addu'a kawai.

Kafin a sanar dashi dawowar tata yaje har sunyi wanka, Inna Deluwa ta hada miyar kuka da tuwon dawa da Juwairah din ta sameta tana tukawa ta kai mata ta ci tayi nak, sun kwanta ita da Abdul din sun hau barcin gajiya.
Sai gashi ragajab-ragajab kamar wani amale yana ta baza uwar babbar riga ko daga ina yake? Ganin suna barci sai yayi turus daga bakin kofa yana zabga fara'a yana tambayar Inna Deluwa da yaushe suka dawo? Ta amsa mishi ciki-ciki don kuwa har lokacin cikin fushi dashi take.

Zuwa dare ta sake hadasu ta musu sasanci da kara tausar Juwairah din. Ta amince da cewa zata riki da, amma fa ya daina mata gorin dangi. Ya amsa da saurinshi yace ya daina.
Da haka dai suka tattara suka koma gidansu, ta rike Hannafi da AbdulHadi ta rika kamar dukansu ita ta haifesu. Shima kuma Auwalun yayi mugun sanyi ya shiga taitayinshi, sai tattalinta yake yi.
Cikin lokaci kankani sai gata da wani cikin. Ya kuma nuna matukar farincikinshi da jin haka.

Ashe ba tare da sanin kowa ba, ya hadu da Barira, mahaifiyarsu Jamila. Lokacin itace ma Vice Principal a FGGC Munjibir, kuma haifaffiyar garin Kano ce a unguwar Galadanchi.
Ya je raka wani Ubangidanshi ganin diyarshi da take karatu a makarantar suka hadu da ita, jininsu ya hadu da ita. Kuma cikin dan kankanin lokaci zancen aure ya shiga tsakaninsu. Ya gundura mata karyar ai bashi da aure sun rabu da matarshi.
Aka yi aure ta tare abinta kasancewar kuma zawara ce, ta taba aure amma bata taba haihuwa ba sai abin yaje musu da rashin hayaniya.

Shikenan duk karshen sati yana tafe kan hanyar Kano, ya cewa Juwairah din ai wani aiki ne na musamman yake kaishi gidan Gwamnatin Kano, ita kuma ta hau kai ta zauna daram.

Kusan a tattare suka haihu su biyun, ita Juwairah ta haifi 'ya mace, Barira kuma ta haifi danta namiji.

9.
Diyar da Juwairah ta haifa bata dade ba ta koma sakamakon matsananciyar rashin lafiyar data yi. Suka yi jimami na dan lokaci suka hakura suka maidawa Allah lamarinshi.

Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka. Auwalu kuma ya cigaba da aure-aurenshi. Juwairah tun tana jin haushi da tashin hankalinta har ta gaji ta hakurewa kanta. Tunda abin dadin matan basu cika zama ba. Abin takaicin shine da yawancinsu suke maida mishi 'ya'yanshi da zarar sun rabu. Don ma tun bayan Saminu bai kara kai mata da ba sai dai wajen Inna Deluwa yake kaiwa. Don kuwa a lokacin daya zaunar da ita yake bata labarin yana da wata matar a Kano har suna da 'ya'ya biyu da ita, akwai wasu yaran biyu a hannun Inna din. Itama kuma da wata diyar wadda ta sake haifa tana shayarwa.
Cikin ikon Allah kuma sai taji kwata-kwata hankalinta bai tashi ba sam. Ta tabe mishi baki tace to 'Allah raya!'
Ta tashi ta bar mishi wajen. Shi kanshi sai da yayi mamakin hakan.

A cikin wannan kwaramniya kwatsam sai Allah Ya hadashi da Fatima Zahra. Sun je can Maidugurin lokacin ana ruguntsumin siyasa kuwa.

Tun bayan da karayar arziki ta samu Lamin, gabadaya komi ya cukurkude ya rikice, abubuwa duk sun tsaya musu cak.
Lokacin Hauwau tayi aurenta, Allah Ya hadata da wani mutum magidanci ya nuna yana da sha'awar aurenta kuma yayi alkawarin tsaye mata tayi karatu har ta gama. Babu bata lokaci kuwa aka daura aure ta tare a gidanta. Anan Maidugurin suke da zama saboda mijin nata Lakcara ne yana koyarwa a Jami'ar Maiduguri.
Yasir shi kuma cikin ikon Allah ya samu scholarship a Bangladesh ya tafi.

Ita kuma Zarah ta samu ta gama karatun sakandaren da kyar babu zancen cigaba da wani don kuwa a lokacin ta abincin ci ma ake yi karewa.

Fatima Zahra wata irin yarinyace mai tsananin son abun duniya. Tana da son hutu da watayawa, kuma zata yi duk abinda zai kai mata yan kudade komi kankantarsu kuwa. Tana kuma da kutse-kutse da tura kanta wajen masu hannu da shuni. Duk da dai yawanci su masu mu'amala da ita kyawunta ne yake dibarsu suke so suyi kawance da ita.

Kawancen ne ma ya hadata da wata diyar wani hamshakin mai kudi, wanda yake na hannun damar Gwamnan da ya ci takara a wancan lokacin. Kuma so take yi ta samu dama, ta rokeshi akan ya taimaka ya hadata da wani Kaninshi dake zaune a Kano kuma babban darakta domin harkar fim take so ta fara.

Daga farko so tayi Lamin ya hadata da mutanen da shi ya sani tunda har lokacin suna dan yin hulda da wasu manyan mutanen. Shi kuwa yayi tsalle ya dire yace ba a gidanshi ba, ya kuma fada ya kara nanata mata, matukar ta shiga harkar film to haihata-haihata shi da ita, sun rabu kenan.

Ita kuwa wata kawarsu ce ta tsole mata idanu. Tana tsakiyar karatun sakandare ta ajiye ta tafi harkar film. Kuma cikin ikon Allah da yake taje da kafar dama, sai gashi cikin abinda bai gaza shekara guda ba har tayi suna tayi arziki. Don taji ance ma har motar tukawa ke gareta. Yadda kuma abokanta suke zugata da kara nuna mata baiwar kyan da Allah Ya mata, suna fada mata Fadilar da ko rabin kyanta bata yi ba ta samu wannan daukaka ina ga ita? Sai kanta yake kara huruwa suna kara mata karfin gwiwa. Wannan dalili yasa ta nemi yin kawance da Karimah ta kuma samu damar shiga jikinta da iyayenta.

A cewarta, ko basu yi mata hanyar shiga film ba, zasu mata hanyar haduwa da wani babban wanda shi zai iya yi mata hanyar.
Nan da nan kuwa dai gashi ta riga ta zama kamar yar gida, ya zamana duk wasu shirye-shiryen abubuwa da ake yi na walimar da mahaifin Karimah ya hadawa sabon Gwamna da ita ake yi. Don hatta ranar da Gwamna da iyalanshi suka tare a gidan Gwamnati da ita aka je. Anan kuma suka hadu da Auwalu wanda shi kuma Gwamnan abokin Ubangidanshi ne na kut-da-kut.

Duk wani namiji dake cikin gidan wannan a lokacin Zahra ta tafi da imaninshi. Kuma kowa a shirye yake da tace zata aureshi a daura musu aure.
Cikin ikon Allah sai hankalinta yafi karkata ga Auwalu. Don kuwa akwai shi da iya tsara zance, ga kuma naci da rashin zuciya in dai akan macen da yake so ne. Ga shi ya rufe ido ya dinga mata barin kudi ba ji ba gani.
Duk wulakancin data dinga mishi ko a jikinshi bai dinga nunawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login