Showing 138001 words to 141000 words out of 142169 words

Chapter 47 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

452

da tayi bayan data dawo gida Najeriya bayan ta shafe watanni biyu a Makkah, ta baro Ummah a can wadda itama tace cikin watan da zai kama zata dawo, shine ta sayar da Arena dinta tare kuma da neman lasisin mayar da ita can Maiduguri.
Haka ta sayar da kadarorinta da dama dake nan Jos da Kaduna, domin Maiduguri take da niyar komawa da zama gabadaya. Don kuwa Ummah tace mata galantoyi da yawo barkatai ba nata bane ba yanzu????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  , musamman da yake babu aure a kanta. Ita 'ya mace a duk inda take da halin da ta tsinci kanta, miji shine mutuncinta. Idan kuwa babu shi to yan'uwanta ne da iyaye.
Komawarta Maiduguri din kuma ba ita kadai ya yiwa dadi ba, har yan uwa da dangi sun fita jindadin hakan. Don kuwa wajen shakatawar data gina wanda yafi na can Kaduna girma da tsaruwa ma, ta dauki yaran dangi da dama ta basu aiki a can, har ma da wadanda matakin karatunsu bai kai ba.
Haka gidauniyoyinta da suka yi sanyi saboda ganin ta samu abinda take so a hannun mutane, suka cigaba da aiki babu kakkautawa anan Maiduguri din da kewaye.


55.


Watanni shida ne bayan wannan, abubuwa duk sun lafa suna kuma tafiya cikin tsarinsu da yardar Ubangiji.
A cikin wannan satin ta yaye yan biyunta. Ummah ta aika Hindatu, -wata matashiyar yarinya jikar kawunta Tasi'u da ta roki alfarmar a bata ita riko bayan data dawo kasar da zama.- Taje ta amshi yaran aka kaiwa Ummah din don ta yayesu.

A cikin satin kuma aka gayyacesu wajen mashahurin taron da matan Gwamnoni na Nigeria suka saba hadawa a duk shekara, don karawa junansu sani da ba juna shawara akan abubuwa da suka cabe musu a game da mulkin nasu. Daga karshe kuma suna bada awards na abubuwa da dama a taron. An gayyaci Nadiya da Shukurah duka, sai Nadiya din ce ta samu zuwa, saboda Shukurah bata jin dadi sosai. Laulayi take fama dashi ba mai sauki ba, ko ruwa ta hadiya sai ta dawo dashi. Don haka bata samu damar zuwa ba.

Ita kadai ta tafi sai security dinta daya, tayi masauki a Gibson hotel inda duk aka yi musu masauki ita da sauran masu zuwa.
Washegarin ranar da taje aka yi taron, an kuma bata award din wadda ta fi kwarewa akan aikinta da kuma tallafawa marasa karfi. Yayinda Shukurah aka bata award din wadda tafi kowa iya shiga mai kyau da tsara kwalliya.

Anyi taron cikin dadin rai da raha, aka kammala. Wasu tun a ranar suka juya gida, ita kam sai ta kara kwana biyu anan saboda tana so ta ga Her Excellency kafin ta juya gida. Tayi magana da PA dinta tace sai nan da kwana biyu sannan zata iya ganinta.

Suka fito daga dakin taron suna yin sallama da junansu, hankalinta yana kan wayarta suna magana da abokiyar aikinta lokacin da aka bude mata bayan bakar range Rover dinta ta shiga.
Sam bata kula da mutum a gefenta ba sai da kamshin turarenshi ya fara shiga hancinta sannan. Ta juya da sauri sosai, sai idanunta cikin nashi
Mamaki yasa ta kasa iya cewa komi sai bakinta data hangame. Tace "yaushe ka zo nan?!"
Cikin tsananin mamakin ganinshi a wajen. Don kuwa ko mintuna talatin da suka wuce sunyi waya da shi, ya tayata murnar award din da aka bata, amma kuma koda wasa bai fada mata cewa yana Abuja ba. Abinda bata sani ba shine tun a safiyar ranar yaje can, za su yi wani zama da yan majalissu a ranar da yamma.

Direba ya ja mota suka fara tafiya, yayinda ya juya ya kalleta yana kasheta da murmushinshi, "ai anan ma nayi lunch dina."
Ta dan turo baki, "shine kuma ko ka fada min?"
Kasa daurewa yayi ya jata cikin jikinshi yana sumbatar gefen kumatunta, ta fara kokarin janyewa saboda kaucewa idanun direba da security dake gaban motar wadanda suke kamar ba ma a cikin motar suke ba, amma shi kuma ya ki bata damar hakan.
Yace, "to menene amfanin sanar dake din ni da nake so inyi surprising dinki?"
Sai bata ce mishi komi ba, ta janye jikinta daga nashi da kyar ta koma ta zauna tana kallon hanyar inda suke nufa.

Direba ya shigar da motar farfajiyar hotel din Fraser Suites dake nan Garki, security ya bude mishi murfin bangarenshi ya fita. Ana kokarin bude mata daya bangaren, ya dakatar da shi tare da bude mata da kanshi. Ta fita daga cikin motar hannunta sarke cikin nashi, bin shi take yi cike da alamun tambaya. Musamman da taga kai tsaye ya wuce da su ciki, sun shige elevator tayi sama da su.
Tace mishi, "ina da masaukin da aka kama min fa."
Yace, "na sani, na kuma sanya an dauko miki kayanki daga can saboda zamu zauna anan din na dan lokaci mai tsayi ne."

Suka fita daga cikin yar motar, suka taka har zuwa kofar dakin da yayi masauki ya bude musu kofar suka shiga suite din.
Babban dakine sosai, komi kyal-kyal gwanin kyau yana ta tashin tattausan kamshi mai dadi.

Kai tsaye bandaki ya shige ya dauro alwala, ya fito ya sameta a tsaye a wajen daya barta tana kallonshi da mamaki. Yace, "zan fita masallaci, daga can kuma wajen meeting zamu shiga ina tunanin sai bayan Magriba sannan zan dawo. Idan kina bukatar wani abu zaki iya kiran room service sai su kawo miki."
Bai bari ta ce wani abu ba, ya duka yana bata peck a baki kafin ya fita da sauri.
Sai ta bishi da kallo, kafin kuma ta dan girgiza kai tana sakin murmushi. Ta fada toilet itama don dauro alwala.

A daren ranar ya iskota zaune akan kujera dake tsakiyar falon, ta gama shirin barci amma laptop ce a gabanta tana aikin dannawa furiously, hankalinta kacokam akan abinda take yi.

Ya tsaya a gaban mirror yana taje sumar kanshi, yana satar kallonta ta cikin madubin. Yayen da tayi har ta fara mayar da jikinta, duk da cewa dai dama can ba wani rama tayi ba, amma duk da haka sai data dan fada da kuma duhu da fatarta tayi. Shayarwar yara biyu ai ba wasa ba. Amma yanzu gashi nan har wani sheki take yi na musamman, jikin nan ko'ina bul-bul. Musamman kugunta daya kara budewa yayi daram. A yadda take zaune dinnan ta dan duka, cikin riga da wando na barci marassa nauyi, surarta ta fita yadda yakamata.
Ya dan lumshe idanu yana girgiza kai kafin ya ci gaba da shirin shi. Har ya gama sanya farar singileti da wando sweat pant ruwan madara, ya bi jikinshi da turaruka ya fesa, Nadiya bata san me yake yi ba.

Ya wuce kai tsaye ya dauke laptop din gabanta, yayi saving aikin da take yi tare da kasheta. Haka ya dauki wayarta ya kashe, duk tana zaune tana kallonshi.
Ganin kallon alamun tambaya da take jefa mishi yasa yace mata, "daga yau har zuwa ranar da zamu bar dakin nan, ban yarda da daukar waya ko laptop ba. Kai ko maganar aiki ban yarda ba wadda bata shafi rayuwarmu ba (personally)."

Tayi dan murmushi tare da langabar da kanta gefe, "to Alanguburo (ranka ya dade) ya kake so inyi da tarin ayyukan dake gabana ne kuma?"
Yace, "ban sani ba Nadiya, ni dai kawai abinda na sani shine yanzu lokacina ne, ban kuma yarda wani abu ya gifta min a tsakani ba. Finally na sameki ke kadai din ki, babu laulayin ciki, babu rainon ciki, babu na yara, sannan babu zancen aiki da na mutane da marassa lafiya da sauransu, don haka sai na fanshe duk wadancan kwanakin da yan biyuna da aiki ya dinga hanani cin amarcina da kyau!"
Tayi dariya sosai, "ashe kace nan da wata daya ma ba zamu bar nan ba? Don kuwa ni dai nasan lokutan da yawa!"
Yace, "babu matsala ai, we can rectify that, my love."
Ya sungumeta ya nufi gado da ita yana manna mata wata gigitacciyar sumba, wadda ke fita tun daga karkashin ranshi, tana kuma fada mata irin tsananin kewarta da yayi. Ga su dai a gida daya, su kwana su tashi a waje daya a wasu ranakun, but this, wannan na daban ne. Su kadai ne, babu aiki, babu kiran waya ta ujila, babu yara da sau tari suke katsesu a al'amuransu ko kuma su raba dare dasu a zaune. Yanzun su kadai ne, ya kuma samu Nadiya din yadda yake son samunta, pliant, loveable, da kaunar nan tata mai kashe jiki da sanyaya zuciya wadda a wajenta kadai yake samu.
Cin amarci wane lokacin da tana amarya? Wannan ai honeymoon ne mai lasisi suka sha wanda babu kamarshi a tarihin rayuwarsu.
Satinsu guda anan, fita idan ba ta kama dole ba to babu inda suke zuwa. Itama tun bayan zamansu da Her Excellency bata kara fita waje ba, sai dai sau tari idan ta gaji da zaman dakin su fita nan kasa wajen shakatawa su zagaya su huta, ko kuma su je wajen cin abinci su ci maimakon a kai musu har daki.

Anan ta samo wani cikin. Allah Ya taimaketa dai wannan bashi da tsarabe-tsarabe irin na yan biyu, don haka har cikin nata ma ya girma ya fito ba kowa yasan da shi ba.


*****

*EPILOGUE*

SHEKARU GOMA A GABA!


Rayuwa ta mika musu bakidayansu, ta kuma yi musu albarka fiye da tunaninsu. Hajiya Nadiya Auwal, mata ga Alhaji Habib Abdullahi Makama, toshon Gwamnan Jahar Kaduna.
Ya rike wannan mukami har sau biyu, don kuwa tazarce yayi wanda Talakawa da al'ummar Jahar Kaduna suka mara mishi baya har ma fiye da lokacin farko daya fita takara. Haka kuma anyi ittifakin cewa kaf a tarihin Jahar Kaduna ba a taba ganin jajirtaccen Gwamna ba kamar shi.

Mutane da dama sun so ya sake neman kujerar Shugaban Kasa, amma yace a'ah, wanda yayi ma a baya Allah Ya sanya albarka. Yanzu kam yana son karkata hankalinshi ga iyalinshi ne kawai.

Nadiya a halin yanzu marikiyar Masters ce, tana aiki da wata Private University anan Kaduna din inda take koyar da Home Management. 'Ya'yanta shida, Yan biyu yanzu shekarunsu sha daya, Juwairah yar kimanin shekaru takwas da yan watanni, bayan ita akwai wasu yan biyun duka maza, Hassan da Hussaini, shekarunsu biyar. Sai Fatima (Maamah) itace autarta shekarunta uku.
Shukurah kuma Yayanta uku, Muhsin, Mus'ab da kuma Ruqayyatu. Ita Shukurah din yanzu tana aikine da hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa.

Kawunansu a hade yake sosai, haka ma yayansu sun taso cikin kauna da girmama juna da kuma iyayensu, don kuwa a lokuta da dama ma baka iya bambance dan wannan dakin da na wancan.

Shekaru uku da suka wuce su Mami suka dawo Najeriya da zama gabadaya ita da iyalanta. A kuma cikin shekarar ne aka yi auren Safiya da Fu'ad, dama can Nadiya ta jima tana zargin akwai wani abu a tsakanin yaran, don haka bata yi mamakin jin zancen ba. Suka sha biki sosai da sosai kamar babu gobe, Safiya ta tare a gidanta dake nan Kaduna. Ba a gina mata asibitinta na kashin kanta ba bayan ta kammala karatunta, amma kuma tana aiki da wani babban asibitin kudi anan Kaduna din, sannan kuma tana zuwa asibitin Gwamnati lokaci zuwa lokaci. Diyarta daya a halin yanzu.

Alhaji Habib yanzu babban dan kasuwa ne, wanda yake safarar jewellies, kayan ado na maza da mata har ma da furnitures daga sassa na duniya daban-daban. Shagunanshi suna da manyan rassa a jahohi daban-daban a cikin Najeriya, nan Kaduna, da Maiduguri, Abuja, Kano har ma da Lagos.
Ita kanta Nadiya tana da babban wajen cin abinci mallakinta, wanda yayi shura ya kuma yi fice a cikin Kaduna kwarai da gaske. Don kuwa wajene wanda yake tafiya da zamani sosai da sosai, haka ba a abincin nan kasarmu Najeriya kadai suka tsaya ba, suna lekawa har kasashen ketare suna yin irin girke-girkensu.
Haka kuma, ita din yanzu tana rike da gidauniya har guda biyu ta tallafawa mata da marayu tata ta kashin kanta.

Aikin Hajji ya kwashi iyalan nashi suka je gabaki dayansu banda yan kananun, su a wajen Ummah aka barosu.
Ranar da suka dawo, a gidan Hajiya Ummah suka yi masauki gabaki dayansu. Aka yi musu tarba mai kyau, abinci iri-iri, babu irin wanda ba a dafa ba.
Suka hau kan babban dinning table wanda ya daukesu gabadayansu tsaf, har da sauran kujeru ma. Kowa ya zuba abinda yake son ci, babu abinda ke tashi a wajen sai tashin sautin muryoyinsu kawai suna ta hira cike da nishadi da kauna irin ta yan'uwantaka.

Nadiya ta harari Khairiyya wadda ta dauke sauran soyayyen kifi guda daya daya rage akan farantin Mus'ab, ta kuma kaishi baki ta taune tana gaggaba mishi dariya.
Tace, "wai don Allah me yasa kin cika tsokana ne Khairiyya? Ba na hanaki cin kayan kannenki ba?"
Ta turo baki tana cewa cike da shagwaba, "To Mommy na ga ya zauna yin tsentseni ne, yanzu wannan sai kiga har mu tashi daga nan bai gama cin abincin ba. Ni kuma ina so in ci ne."
Tace, "to amma ai ba haka ake yi ba ko? Sai ki tambayeshi kiji idan ba ci zai yi ba kafin ki dauka. So kike yi ya miki bore ke kuma kice zaki nuna seniority ki ci zalinshi ko?"
Ammar ya katseta, yace, "Mommy da ma kin daina shiga tsakanin wadannan yaran wallahi. Yanzun nan zasu baki kunya a bainar jama'a. Kin gama tare mishi fada yanzu, yanzu kuma zaki gansu sun hade kawuna suna shan hannu da dariya abinsu."

Shukurah tace, "ai ni dama tuni na gama fita daga cikin harkokin yarannan da kike ganina. Ni ai tun ranar nan da suka gama yace min zani a kasuwa ita da shi, nace to anyi babu kari. Shi yasa bana taba ce musu komi idan suna abinsu."
Wajen suka dauki dariya sosai da sosai.
Ummah kallonsu take yi, a cikin ranta wani irin farincikine irin wanda bata taba jinshi a rayuwarta sai in tana cikin wannan zuriya.

Ba ita ta haifi Habib ba, don haka 'ya'yanshi ba jikokinta bane na jini. To amma kuma so da kauna da shakuwa dake tsakaninta da su, sun ma fi na wadanda suka hada jini din. Komi yaran suka dauko, kaji sun ce granny, granny. Duk da cewa itama Yakumbo din suna sonta akwai kuma shakuwa a tsakaninsu sosai, to amma fa bata kamo kafar shakuwarsu da Ummah ba ko kadan.

Sai zuwa dare sannan ya hada kan matanshi suka wuce gida. Su kadai suka tafi, don Ummah tace a bar mata yaran su zauna tare da ita har su koma hutu. Saboda tana so ne ma a cikin satin su je su kaiwa Yakumbo ziyara a Makarfi koda ta yini daya ne ko kwana.

*

Bayan an kwana biyu, sun gama hutawa da kuma karbar baki yan sannu da zuwa, ta fita a yammacin ranar Alhamis zuwa gidansu.
Ruwa aka gama yi babu jimawa, garin yayi luf gwanin sha'awa. Ta fita a cikin silver Jaguar F-Pace sport car dinta, sabuwar mota ce wadda bata jima da siya ba.
Allah Ya buwaye mata, sai gashi ta wayi gari rayuwarta tayi kyawun data fi karfin abubuwa da dama a cikin rayuwa. A halin yanzu ita da kanta bata san iya adadin kadara da kudade data mallaka ba, wanda kuma duka cikin buwaya ta Ubangiji nata ne, mallakinta, ba tare da wani ya taimaka mata da asin kwabo ba.

Ita take tuka kanta a hankali, cikin jin dadi da ni'imar da ruwan sama din ta saukar mata. Gidansu ta yiwa tsinke, bikin Amina da Fatima ke tunkarosu a cikin wannan watan. Ita Maryam an jima da yin aurenta, ta samu miji a cikin yan'uwan Mama, a yanzu haka tana can Kano da zama ita da yayanta.

Ta yi horn a bakin gate din gidan, yaran gidan suka dinga rige-rigen bude mata kofa. Ta danna hancin motarta farfajiyar gidan ta shiga, ta kashe motar tare da fita a hankali tana gyara gyalen data rataya a kanta.
Ta tsaya a jikin motarta tana karewa gidan kallo, shine dai gidan da suka tashi, aka kuma rainesu a ciki. Wanda a shekarun baya kadan suka sayi sauran gidaje dake makwabtaka dasu, aka sake rushe tsohon aka yi sabon gini na zamani. Lantana tuni ta jima da barin gidan itama. Saboda bayan wasu yan lokuta, tace ita ba zata iya wannan rayuwar ba, ta nemi saki shi kuma ya sallameta.
Aka warewa matan dakunansu, shima Abban haka aka ware mishi nashi bangaren daban, ta yadda zai dinga cin karenshi babu babbaka ba tare da wani ya jiyo shi ba balle yasan wainar da yake toyawa. Irin rayuwar da taso ace ta rayu a cikinta kenan, irin wannan tsarin tayi burin ace shine a gidan a lokacin da take nan.

Saboda idan ta zauna ta duba baya da kyau, sai taga cewa raini mai yawa daya shiga tsakaninta da matan mahaifinta ba komi bane ya assasa hakan ba face mu'amalarsu da take ji da duk wani sirri daya kamata ace nasu ne su kadai, wadanda bai kamata wani kunne yaji ba face su. Shi yasa ta rainasu, bata sonsu, bata girmamasu, shi kanshi Abban nasu sai da rainin ya so shiga tsakaninsu ai.
Bata son kannenta na baya su dandana irin wannan rayuwar data dandana a baya, shi yasa ta bada shawarar ayi haka din. Musamman da bayan yan shekaru da yawan shan magunguna da yake sha, ya samu lafiyarshi garas duk da cewa dai har lokacin babu tabbacin zai sake iya haihuwa.
Bayan wannan kuma haka suka samu shago babba aka zuba mishi yadika da shaddodi na maza inda ya fara gudanar da sana'arshi, duk sunyi hakan ne saboda zaman hakanan din bashi da dadi musamman ga mutum mai iyali irinshi.

Ta nisa a nutse, kafin ta taka a hankali akan takalminta mai matsakaicin tsayi na Chanel da mahadin jakarta data sanya kan wayoyinta da sauran abubuwan da zata bukata a ciki.

Ta shiga bangaren Salame da a halin yanzu da ita da Mama suke amsa sunan Hajiyoyi. Ita da su Yaya AbdulHadi da su Anty Jamilah suka biya musu aikin Hajji a wata shekara, suka je su duka suka sauke farali.

Ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon, suka gaisa da ita cikin girmama juna. Haka diyan Salame din da kuma na Lantana data bari a gidan bayan tafiyarta, suka dabaibaye Nadiya din suna gaidata, ta dinga amsawa da fara'arta tana tanbayarsu game da karatunsu. Su dukansu sun girma Tubarkallah, hankali ya ratsasu, haka kuma kowannensu karatunshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login