Showing 21001 words to 24000 words out of 142169 words

Chapter 8 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

440

ba, sai ma salo da dabaru na sace zuciya daya dinga je mata dasu iri-iri.

Har dai ya tashi komawa Kaduna bata bashi wata gamsasshiyar amsa ba amma bai karaya ba. Don kuwa ko wata guda cikakke bai yi ba ya sake koma mata tafiya ta musamman
Anan suka daidaita da ita. Ya galla mata karyar matarshi daya da danshi daya amma sun rabu da matar shi kuma dan yana wajen mahaifiyarshi.
Ya kuma nuna mata yana da irin makudan kudaden nan, don yana ma gab da shiga siyasa. Jin haka sai tayi caraf tace ta amince.

Nan da nan sai ga magana tayi karfi, abin mamakin har aka yi aka gama abokan ango ne ke ta kaiwa da kawowa babu danginshi ko daya. Amma barin kudin da suke musu yasa babu wanda yayi gigin cewa ba haka ba.
Allah kadai yasan iyaka adadin kudin da Auwalu ya kashewa Zarah. Zai iya cewa tunda yake bai taba kashewa mace rabin abinda ya kashe mata ba, har Juwairah din kuwa. To amma da yake so ya rufe mishi ido, ko a jikinshi.

Ta bangaren iyayenta ma kuma da dangi sun yi iyaka bakin kokarinsu sun mata duk abinda ya dace.
Ranar daurin aure kwatsam sai ga dirar Ummulkhairi diyar marigayi Alhaji Kachalla gidan.

Wasu jibga-jibgan motoci kosassu kamar ana ciyar dasu suka yi mata rakiya, sai ga bodyguards na take mata baya.
Kai tsaye kuma gidan bikin ta yiwa dirar mikiya babu wanda ta nema a cikin dangi.

Nan da nan sai murna ta hadu gida biyu, aka taru ana ta murna ana mata sannu da zuwa da nan-nan da ita kamar a dauketa a goya a baya.
Ta yini guda cur cikin dangi ana ta hira da ita da raha gwanin dadi. Zuwa yamma ta tashi tafiya don tace ba zata kwana a nan ba, an riga anyi mata masauki a masarautar Borno, kuma idan gari ya waye ba zata biyo ba daga can zata wuce.
Ta yiwa yan uwa kyauta ta kudade masu yawa, suna ta mamaki da godiya baki ya kasa rufuwa, amma aka rasa wanda zai tambayeta inda ta samu wadannan kudade. Tana da aure ko bata? Wani hali take ciki? Duk babu wanda ya mata wannan tambayar.

Sai da zata tafi dinne ta bukaci ganin Lamin. Duk a zaton mutane kyautar bajinta shima zata mishi kamar yadda ta musu. Suka shiga uwar daka suka rufe.
Shiru-shiru suka jima a ciki, me suka ce, me suka tattauna? Allah kadai ya sani. Zuwa can bayan lokaci mai tsayi ta fito, tayi waje kai tsaye ta shige mota aka ja suka tafi.

Sai ga Lamin ya fito daga daki yana ta zabga zufa kamar wanda aka watsawa ruwa, idanu sun rine sunyi jawur sai kace wanda yayi kuka. Mutane suka dinga binshi da tambayar lafiya? Amma babu amsa.
A haka dai aka lallaba washegari aka tafi kai amarya dakinta. Kalilan daga cikin danginta sune masu yin rakiyar. In ka debe Hauwau sai wata Yayar Babarta, Iya Lantu sai kuwa kanwar Lamin din Harira, sai maza guda biyu.

Suka je suka dawo da daddadan labarin diyarsu tayi goshi. Don kuwa irin gidan da aka kaita da kayan alatun da aka zuba mata, ko diyar wani hamshakin mai kudin sai haka.

Ana ta wannan murna da yiwa juna san barka, watarana Lamin ya fita kawai sai ganinshi aka yi ya fadi, barin jiki ya shanye. Aka kwasa hankali tashe aka yi asibiti dashi. Bayan dogon bincike dai likita ya tabbatar da cewa damuwa ce tayi mishi yawa, jininshi ya hau da yawa. Kuma babu abinda zasu iya yi akai sai dai kawai a rubuta magungunan da za a dinga bashi, sai kuma yayi kokari ya rage yawan damuwa.
Haka aka kwasheshi aka koma gida aka hau jinya.

Amarya mutanen Kaduna, tana can tana ta shan amarcinta bama ta san kalar wainar da suke toyawa ba. Soyayya ake zubawa kamar ba gobe, yadda kasan su hadiye juna ita da Auwalu tsabar so. Yace mata yana aiki a Kano, don haka kwana biyu yake yi anan ya tafi wajen aikinshi yayi kwana biyu. Bata kuma taba tambayar wani aiki bane yake yi wanda har ranar karshen sati sai yaje. Ita dai tunda ya ajiye mata duk abinda take bukata shikenan. Ga talbijin dinta da bidiyo, ya sayo mata kaset-kaset sai wanda ta zaba, kwana take yi ta yini kallo babu abinda ya dameta.

Abinda dai yake ci mata tuwo a kwarya shine yadda har ta tasar ma cinye wata daya a gidan babu wani dangi nashi data ga ya taka kafa yaje inda suke.

Shi kuwa dama tunda auren ya gabato, ya sanarwa da Inna Deluwa da Juwairah zai yi aure. Juwairah ta yada kai gefe guda tace 'Allah bada zaman lafiya!' don kuwa ita abin ya riga ya zame mata jiki yanzu.
Inna Deluwa ce ta dinga kallonshi kamar wani wanda ya samu matsalar kwalwa, musamman da ya karkace kai ya hau bata labarin ai ba a gida daya zai hadasu da Juwairah ba. Saboda ita din yarinya ce, wadda ta tashi a gidan hutu bai kamata ya dauketa ya kaita gaban kishiya ba da hayaniyar yara.

Inna Deluwa tace, "wallahi kai dai anyi mutumin banza Auwalu! Har kana da bakin dagawa kacewa Juwairah wai ba zaka hadata da kishiya ba saboda yarinya ce kuma gidan hutu ta tashi? To ahir dinka wallahi! Aure ba zan hanaka ba, kaje kayi tayi matsalarka ce, 'ya'yane kayi ta tarawa kowa da uwarshi, daga baya kai abin zai dawo yana ciwa tuwo a kwarya. Amma wai raba kan mata wannan shine ban yarda dashi ba sam! Ka kawota nan kamar yadda ka kawo wadanda suka fita. Wannan ita ce magana!"
Ta tashi ta barshi anan.

Amma duk da haka bai ji maganarta ba, sai yayi kunnen uwar shegu da ita ya cigaba da bidirinshi. Wannan dalili yasa koda aka kawo amarya da yace su je su ga daki basu je ba.

Dama Inna din a shake take dashi. Bata taba sanin yana da wata matar ba a Kano sai a wannan dan takin kafin aurenshi da Zahra din. Rana daya sai mata ta musu sallama a gida da yaranta biyu mace da namiji, don namijin ma da alama ya haura shekara goma macen kuma zata yi takwas.

Ta amshesu da hannu bibiyu, ta basu wajen zama ta kai musu ruwa suka sha. Bayan sun gama hutawa sai take tambayarsu ko daga ina?
Budar bakin mata sai ce mata tayi ai matar Auwalu ce.
Tace 'wace mata kuma yar nan?'
Ta sake ce mata, 'matar Auwalu dai dake zaune a Kano?!'

Inna tayi salati da salallami, taji kamar ta dora hannu aka ta dinga kwala ihu. Sai suka hau kallon-kallo ita da mata da yara, Inna ta rasa abin cewa. Don kuwa iyaka rikicewa tayi.
Tana cikin wannan yanayi sai ga Juwairah ta shiga gidan hannu rike da kwanukan abinci data dafa zata kaiwa Inna din.

Inna tace, "yauwa diyar nan, zo kiji min wani lamari! Wai matar Auwalu ce tazo daga Kano!"

Ga mamakinta sai taga Juwairah din ko dar bata yi ba. Ta zauna a gefenta tace, "to! Kwarai kuwa ya taba fada min cewa yayi aure a Kano matar har ta haihu. Lallai shekara kwana ga mai yawan rai! Kinga yara sun girma tubarkallah!!"

Inna tace, "yanzu kin san da hakan shine baki taba fada min ba?"
Ita kuma mata kallonsu take yi cike da mamaki, ta kasa boyewa dai ta daga baki ta tambayesu, "wai ko kanwar Auwalu ce wannan?"

Juwairah sai tayi dan murmushi kawai, bata yi mamaki ba da Auwalun bai sanar da ita yana da mata ba sam. A halayen Auwalu ai kalilan ne bata sani ba.

Inna ta kada baki tace, "kanwar ina? Matarshi dai. Ai ita ce matarshi ta lalle!"
Ta dinga kallonta da mamaki zane akan fuskarta. Don kuwa ko ba a fada ba to ta girmi Juwairah din nesa ba kusa ba.

Tana nan sai ga Auwalun ya shigo bararam-bararam, karin hula a gefen kunne. Kafafunshi furtutu kamar wanda aka tono daga rami. Yana ganin wadda ke zaune a tsakar gidan sai yayi turus, ya hau share zufa.
Ita kuwa wani murmushin takaici tayi, ta kalli Inna tace, "dama Inna ba wani abu bane ya kawoni face in zo in nuna miki yan jikokinki ki gansu. Tunda shi Uban nasu yaki sadasu da ku balle ku san juna!"

Inna ta hau gyada kai, "kwarai kuwa yar nan, kinyi kyan kai! Kin kyauta sosai wallahi, Allah Ya shi albarka!"
Ta kama hannun yaran tana kokarin jan su da hira. A gefe guda kuma aka dinga kallon-kallo tsakanin Auwalu da Juwairah da Barira dake ta watsa mishi wani kaskantaccen kallo.

Zuwa can kuma ganin ya coge a bakin kofa yana ta muzurai ya kasa cewa komi yasa ta tashi tsaye ta kama hannun yara, ta cewa Inna, "to Inna zamu koma. Dama zuwa muka yi mu ga gida, ku ganmu mu ganku muma. Amma in Allah Ya yarda zamu dinga zagayowa ana gaisawa."

Inna ta rasa abin dauka ta basu, sai yan abubuwan tabawa da ba a rasa tsofi dasu ta basu. Suka yi sallama ta kama hannun yaranta suka wuce.
Da suka je gaban Auwalu, ta watsa mishi wani mummunan kallo taja tsaki ta zagayeshi ta wuce.

Kamar wanda aka dankare a tsaye, har suka fita ya kasa yin wani motsin kirki. Inna ta kalleshi tana girgiza kai, tace, "ban san me kake so ka zama ba Auwalu, amma wannan dai ba hali bane na kwarai wallahi. Allah Ya shiryeka Ya dawo da kai kan hanya." Ta tashi ta shige uwar daka.
Juwairah ma kuwa bata ce mishi komi ba ta tashi ta hau yan ayyuka a tsakar gidan don ma kada ya nemeta da wata magana. Ya gaji da tsayuwarshi ya lallaba ya fita.
Washegari asubahin fari ya yiwa Kano tsinke. Sai dai duk yadda yaso ya shawo kan Barira ta riga tayi fushi sosai. Ta ma ki bashi fuskar yin magana. A takaice dai ba a yi sati ba sai daya rubuta mata takardar saki. 'Ya'ya kuma tace ba zata bashi ba ya kai mata su gidanshi. Daya so nuna mata jan ido sai ta mishi duniyanci itama, ta nuna mishi akan wannan maganar zasu iya zuwa har kotun koli don kuwa ba zata yarda ba. Idan kuma ya matsa to wallahi zata iya sanyawa a batar mata dashi.
A haka dai suka yi sasanci, da cewar zai dinga aika musu duk abinda zai iya duk karshen wata. Ya koma ya sanar dasu Inna wannan labari. Duk da basu ji dadin hakan ba, sai suka yi addu'ar Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi.

To kuma sai gashi ko wata ba a rufa da yin wannan zance ba ya kara babbako wani zancen auren a Maiduguri. Kuma yake zancen ba zai hadasu gida daya da Juwairah ba. Abin daya konawa Inna rai kenan.

10.

Sai ta wayar Auwalu suka samu daga can Maidugurin aka kira Zahra aka sanar da ita halin da ake ciki, hankalinta yayi kololuwar tashi, babu bata lokaci ta tafi Maiduguri. Lokacin watansu daya da yan satika da yin auren.
Halin data sameshi ya matukar tayar mata da hankali kwarai. Yana nan a kwance sai dai a kwantar a tayar, baya 'Uhm' baya 'uhm uhm!' sai dai ya bi mutane da kallo. Gabadayan Iyalinshi babu mai nutsuwa a tattare da shi.

A sati biyun da tayi anan babu wani canji da aka samu na azo a gani. Takurawar da Auwalu yayi akan ta koma gida da kuma yadda Dada Iyani itama take mata korafin ta koma dakinta hakanan, yasa ta hakura ta tafi din ba don ranta ya so ba.
Ta koma suka cigaba da gudanar da soyayyarsu ita da Auwalu, lokaci zuwa lokaci kuma tana kiran gida su gaisa ta kuma ji yadda jikin Lamin yake.

Ana nan sai ta fara laulaye-laulayen ciki. Hankalin Auwalu kacokam sai ya koma kanta kamar a kanta aka fara mishi haihuwa. Kulawa da dadi na duniya babu wanda bai jiyar da ita ba. Kai gabadaya ma sai daya kwashe fiye da wata daya bai je wajen aikin nashi a Kano ba. Tsakaninshi da Juwairah da 'ya'yan dake gabanta sai dai ya leka a tsaitsaye ya bata abinda ya sawwaka na cefane ita da Inna Deluwa, ya kara gaba. Ita kam tuni ta dawo daga rakiyarshi, tun tana fadan abinda yake kai musu na cefane din baya isarsu, har dai tayi hakuri ta sallama. Allah Ya taimaketa tana sana'o'inta iri-iri, ba a zaune take ba. Don haka ko da wani abu da ake bukata ita take yiwa kanta. Don kuwa ko su Saminu da AbdulHadi da kaninsu Tanimu dan wata Bafulatana daya aura ta kai mishi dan bayan sun rabu, ya daukesu ya kai almajirci can Jama'are bai kuma kara bi ta kansu ba sai in sun je gidan ya gansu, ita take dawainiya dasu. Duk sanda za a kira a nemi wani abu, mawuyaci ne ya dauka ya bada sai ita ce mai badawa. Daga karshe ma ta roki Malamin nasu daya sanyasu a makarantar boko, kuma ita take musu bukatun makarantar tunda ta gwamnati ce. Bata ma tunanin yasan da zancen suna makarantar, idan kuwa ya sani to bai taba fada mata ba.
Ita fa gabadaya komi nashi ya fita a kanta sam. Kawai dai tana zaune dashi ne don bata da wani zabi wanda yafi haka.

A kwana a tashi, Zahra ta fara warwarewa daga laulayin da take yi. Jikinta yayi kyau yayi luwai hankalinta a kwance yake, bata da wata matsala sai ta rashin lafiyar mahaifinta da kullum jikinshi ke kara hautsinewa.
Da take ta samu Auwalun ya bata jacen wayar salular hannunshi. Wani lokaci da suka je taron nadin sarautar wani hakimi da aka yi a Zaria, aka ba manya-manyan na hannun damar Gwamna kyautar salulolin a kwalinsu, ciki har da Auwalun. Ta samu da wayo da kissa ya bata tsohuwar tashi ya hada mata sabon layi, don haka kusan kullum akan waya take tana gaisawa da yan'uwa.

Cikin ikon Allah cikinta ya shiga watanshi na shida, aka aika musu da mummunan sakon rasuwar Alhaji Lamin a wata safiyar ranar Talata. Tashin hankali wanda ba a sa mishi rana! Suka kwasa gabadaya har Auwalun suka tafi Maiduguri.
Rasuwar tashi ta girgiza iyalinshi da ma al'umma da dama, duk da cewa ya dade yana jinya amma dai babu wanda yake bashi rasuwa. To dama rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah ai, idan kuma Yaso kaje gareShi, ko da ciwo ko babu sai kaje.

Aka yi zaman makoki aka watse, aka bar Iyani da zaman takaba. Itama Zahra satinta uku ta koma. Duk da cewa taso ta yi zamanta anan har ta haihu don ta dinga debewa Iyani kewa, amma Auwalu ya nuna sam bai yarda da wannan zancen ba. Don haka ta tattara ba don rai yaso ba ta tafi.
Zancen rabon gado kuwa babu shi, don kuwa babu wani abu daya bari sai ma bashi da kudaden mutane dake kanshi. Don haka ne ma aka yanke shawarar a sayar da gidan da suke ciki tunda yana da girma sosai, sai a samu madaidaici a saya, in yaso sauran kudaden sai ayi biyan bashin dasu.

Zahra ta koma Kaduna da niyar su sake sabunta kauna da soyayyar da aka jima ana cin bashinta. Sai dai abin sai yaje mata ba a yadda tayi tsammani ba. Don kuwa a bakin mutanen unguwa ta dinga jin wai Auwalunta aure zai kara, kuma ma bayan hakan, wai yana da wata matar, da tarin 'ya'ya wadanda ba ma matar dake zaune a gidan nashi bace ta haifa, wadanda sauran matanshi ne na baya suke haifa mishi.

Kai tsaye tace karya suke yi. Don kuwa kwata-kwata hankalinta ya kasa daukar hakan. Ta kasa yarda da hakan. Gani take yi idan ta yarda zata iya hadiyar zuciya ta mutu.
Allah Yayi ta da wani irin kishi wanda ita kanta ba zata iya kwatanta shi balle wani mutum ya iya fahimta. Ita ko a gidansu tsakaninta da 'yan'uwanta kishinsu take yi idan taga iyayen sun basu kulawa fiye da wadda suke bata. To ina ga kishiyar da take hada miji da ita?
Yarjejeniya suka yi da Auwalu tun farko, ya mata alkawarin ba zai taba yin aure ba. Matukar tana raye kuma a gidanshi, babu shi babu wata matar har abada. Ire-iren alkawurran da yake yi mata kenan har a bayan aurensu. Ita kuma ta yarda dashi dari bisa dari, don kuwa bai taba bata wata kofa da zata yi zarginshi ba.

Da taga dai maganganun sun yi yawa, sai ta mishi maganar. Kai tsaye kuma ya karyata, ya fitittike ya dinga fadan karya da gaskiya, wai shi ashe duk kokarin da yake yi a kanta bata gani, zarginshi ma take yi, har tana iya yarda da zancen mutane yan zauna gari banza da dama su abinda suka iya kenan su dinga shiga tsakanin ma'aurata don su rusa musu farincikinsu? Da wannan maganganu dai ya dan kwantar mata da hankali maganar ta wuce na dan lokaci.

Ranar nan dai tace su kaita gidan amaryar da suke cewa zata aur???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i Auwalu, ta gani da idonta, idan kuma karya suke yi, ko kuma sabani ne aka samu, wani Auwalun daban ake magana ba nata ba, sai taji.
Suka shirya da yamma tace mishi dubiya zata je, tinkis-tinkis suka samu abin hawa suka yiwa unguwar Rigasa tsinke.

Suna zuwa layin da yarinyar take ma tayi kyakkyawan gani, don kuwa mashin din Auwalun ne a fake a kofar gidansu yarinyar, shi kuwa yana a tsaye ya jingina da mashin din, yarinyar a gabanshi suna hira. Da alama ma wata hirar yake mata ta nishadi data bata kunya, don kuwa tasa hannune a fuskarta ta rufe tana dariya shima yana yi.

Yadda kasan wadda wuta ta daukewa haka ta ji, ta kasa tsayuwa waje guda sai data jingina da bango sannan.
Wannnan duk bai isheta ba. Bayan ta dawo cikin hayyacinta ta gama daidaituwa, kuma sai ta bukaci da su rakata gidan nashi. Su kuwa dama da yake abinda suke so kenan, sai suka kara mikar hanya. Lokacin har ya ma kara fente gidan don kuwa a yadda ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login