Showing 114001 words to 117000 words out of 142169 words

Chapter 39 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

468

bata samu ba. Dole sai a wanda aka yi anan bangaren Ummah ta daukar musu ita da Babangidan ta wuce sashenta dashi. Shi kanshi dai ranar ya ji dadin halin sukuni da farinciki data yini dashi.

*

Washegari suka dauki hanya ita da Mami da kuma Farida. Hanya suka dauka dodar a cikin motar da Babangida din ya bada a kaisu, Rav4 dinshi ja. Ya hadasu da amintaccen direbanshi, Mr. Hassan Bayareben kasar Ilorin, an cika musu bayan mota da akwatu guda da Ummah din ta bada a kaiwa amarya, da kuma tarkacen tsaraba da za a kaiwa yan uwa.
Nadiya kuma ta cika musu mota da kayan tabe-tabe, motsi kadan ta ciro lemun Teem ta bincire hancin, bata ajiyewa sai ta ga babu komi sai robar.

Farida barcinta take sha cikin kwanciyar hankali, tafiya suke yi a cikin mota kamar dai ba ma a cikin mota suke ba, babu bumps na titi, basa ko jin kwarzaben kan hanya da titi sabida sun samu kosasshiyar mota.
Mami ke kallonta tana dan murmushi ganin halin da take ciki, tace, "ba zaki daure ki ci wani abu ba Nadiya? Ga nama nan Babangida ya hadomu dashi kala-kala, ga kuma snacks da ke kika yi da kanki, amma ki ki duka ki buge da shan lemu?"
Ta dan turo baki, "ba na jin yunwar ne wallahi Mami. Ni tunanin cin nama ma yanzu tayar min da zuciya yake yi wallahi. Wannan lemun ne kadai nake jin dadinshi."
Mami ta yada kai gefe guda, tace, "ai shikenan. Idan kinji kina son wani abu dai ki fada da wuri, sai mu tsaya a duba ko a hanya ne."
Tace, "to."

Suna tafe Mami tana janta da hira cikin hikima ta manya da kwarewa irin ta likitoci therapists da suka kware a harkar bin kwakkwafin magana da zance.
Mr. Hassan ya dage yana gudanar da aikinshi cikin kwarewa da iyawa, a gefe guda kuma he's very alert ga duk abinda ke faruwa akan hanyar. Saboda bayan lasisin tuki da yake dashi, Dan sa????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
nda ne na farin kaya da aka yi musu training na musamman. Ba yaren hausa yake ji ba sosai, hakan ya ba Nadiya damar sakin jiki suna magana ita da Mami.

Abun nan daya dake damunta ta kasa gane mishi shine take yiwa Mami korafi akai. Don bayan ita bata san wa zata fuskanta da zance makamancin wannan ba.

Sai Mami din ta mata murmushi, tace mata, "kin cika tsoro ne Nadiya, shi yasa!"
Ta kalleta da mamaki, tace, "tsoron me kuma Mami?"

Mami ta gyara zama sosai tana kallonta, tace, "watakila kema baki san da hakan ba, amma a can karkashin zuciyarki tsorone yake hanaki sakewa da maigidanki. Amma kada ki damu, hakan yana yawan faruwa a cikin mata da dama. Akwai mata da yawa da zaki ga yawan yarda da suka yi da mazajensu, ita ce take hobbasawa kuma ta dadada musu rayuwar aure. Ta bangarenki zata iya yiwuwa akwai wani abu tare da Babangida da kila ke a karan kanki baki dauki hakan wata hujja ba, amma kuma unconsciously zuciyarki ta dauki hakan a matsayin wani abu na kare kanta. Kila kina tsoron idan kin sakar mishi jiki watarana zai rabu dake ne, watakila zuciyarki na rada miki ai baya sonki dari-bisa-dari, silly excuses dai iri-iri wadanda basu da kai ma balle kafafu. Abune dake faruwa damu psychologically. Ke da kanki zaki zauna ki nutsu, ki tambayi zuciyarki me kike tsoro? Ki lalubo amsar da kanki. Idan ta magancewa ce ke kadai, sai ki maganceta. Ko ku zauna ke da shi, talk about duk wani insecurity dake addabarki. Idan kinyi hakan, zaki samu mafita in shaa Allah. Sannan kofata a bude take kullum, ko da ace bana nan, zaki iya tuntubata a kodayaushe Nadiya. I'll be glad to help!"

Nadiya tayi shiru tana saurarenta sosai da sosai. Akwai kamshin gaskiya sosai a cikin kalaman Mami. Ta mata godiya, sai kuma ta yada kai kan kujera ta hau barci.

Barci tayi sosai a cikin motar nan har tayi mamakin hakan, don ita ba ma'abociyar yin barcin mota bace. Ga shi tafiyar tasu tayi sauri sosai wannan karon.
Sun shiga Maiduguri wasu masallatan ana kiran sallar la'asar. Kai tsaye gidan da aka sauki Hajiya Ummah wancan lolacin aka wuce da su. Suka samu dafifin yan uwa ana jiransu.
Tarba suka samu sosai da karramawa. Suka yi wanka suka yi sallah, Anty Lima tana ta mata shakiyancin wai me take ci ne ta canza kala da kamanni, ko dai canza musu ita aka yi ne? Tayi banza ta kyaleta tayi ta gama abinta, don gajiyar da tayi da zazzabin dake kadata ma kadai sun isheta. Da kyar ta iya zama ta kira Habibun ta sanar dashi sun sauka lafiya, ta kira Ummah da su Mama suma suka gaisa. Ta kashe wayar ta lalubi gado ta zube har da su rufa.

Anty Lima ta shiga ta sameta cikin wannan halin. Sai ta ajiye kwanukan abinci data kai mata, ta yi kanta da sauri tana tambayarta lafiya? Jin yadda jikinta ya dauki zafi yasa ta fita da sauri ta kira Mami. Tana dubata tace ba wani abu bane, gajiyar tafiya ce kawai. Aka samo paracetamol da ibuprofen ta bata tace ta sha amma ta dan fara cin wani abu.
Ga abinci nan varieties Anty Lima ta shigar mata da su, musamman dashishi da taushen gyada da ya ji naman kaji zako-zako da man shanu da tasan tana cin shi sosai, amma ta kasa ci. Hasalima cewa tayi warin man shanu yana so ya sanyata amai.

Ta janye kwanon daga gabanta tana danne dariyar dake ciyota, tace, "ai ce min zaki yi kawai junior Habibu ne yake tambayarki, har kike nema ki tayar min da hankali!"
Ta watsa mata idanu cikin harara, "a'ah, abinda ya fi junior mantawa kika yi! Ni gajiyar tafiya ce kawai ta sanyani hakan ba wani abu ba!"
Anty Lima tace, "haba yarinya, ai wallahi kici gaba da denying, amma ni tuni na gama harbo jirginki. Baki ga irin murmushi da kallon da Mami take ta yi miki bane ba wai sanda tana dubaki?"

Dan tsaki ta ja, "kin ji da shi dai ko menene. Idan akwai nono ko yoghurt a dama min fura ko tukudi ni dai."
Tayi saluting dinta, "an gama ranki ya dade! Ai fura da tukudi yau sai kin gaji da su!"
Ta fita da sauri sai ga ta dawo babu jimawa, hannu rike da tasa an dama fura ta sha nono mai kyau. Ta gyara zama da kyau ta sha, ta kora da maganin kafin ta koma ta kwanta.
Cikin dan kankanin lokaci zazzabin ya sauka, sai gata ta tashi an cigaba da bidiri da ita.

Da dare suka wuce gidan Anty Hauwa ita da amarya tunda a can take ita da abokanta, suka bar Mami a can.

Wata sabuwar tarar suka samu a can gidan Anty Hauwa. Ita dai suna zuwa da kyar ta iya shiryawa a tsaitsaye, ta bi lafiyar gado ta kwanta ko karfe tara bata gama rufawa ba.

Ta tashi da Asubahi ta tarar da missed calls din Babangidan bila adadin. Don haka ta kirashi suka gaisa. Fadi mata yake yana karawa, shi already gidan ya gama mishi fadi da bata nan, anya ba dawowa zata yi ba ko kuma shi ya biyo ta ba? Ta dinga mishi dariya tana cewa 'ashe da ya zama bita zai-zai?!'
Yace, "ai baki ga bita zai-zai ba sai kin dawo na hanaki zuwa ko nan da can na shekara sannan zaki tabbatar!"
Tayi dariya sosai har ta gode Allah.

Anty Lima tana zaune tana saurarenta tana ta sakin murmushi abinta, har suka yi sallama da shi. Ta kalleta kasa-kasa cike da alamun tsokana, tace, "su yar ware ana cewa ba a so, ba za ayi ba, yau kuma ga ki kece kike i love you I miss you?! Lallai in da ranka ka sha kallo!"
Tayi dan murmushi kawai, tace, "oho miki dai. Ni ki daina tuno min lokacin kan ta waye don Allah!"
Anty Lima kuwa me zata yi ba dariya ba?

A washegarin ranar aka fara gudanar da shagulgulan bikin Anty Lima wanda ya matukar kayatar ya kuma burge.
Sai dai tunda aka fara bikin Nadiya ba zata ce ga takamaiman abinda ke faruwa ba, don kuwa cikin barci take sosai da sosai. Yanzu bata da lokacin komi sai barci, koda yaushe za ka sameta to barci take yi, abin har ya fara damunta kuma. Don kuwa tunda ake events na bikin sau daya taje wajen sisters evening, ta dawo da ciwon kai sosai da sosai har sai daya haddasa mata zazzabi. Don haka Anty Hauwa tace mata ta hakura da zuwa kawai, ta dinga zama a gida tunda ga dangi nan suna ta shiga da fita abinsu, idan taji barci kuma ta gyara kwanciya ta kwanta abinta.

Ga abinci har yanzu bata iya cin komi, sai fura da kankana kullum da lemu mai tsami. Amma biredi wannan in dai zata hadiya sai ta tanadi lemun tsami a kusa da ita. Wannan da kuma rashin ganin bakonta na wannan watan ya sanya ta fara tunanin anya?

A haka dai ta lallaba aka cinye satin nan guda tas ana ta biki kamar ba za a kare ba. Washegarin ranar da aka daura aure, suka dauki amarya aka kaita Garin Kano. A can iyayen mijinta ke zaune, amma harkokinshi sun ma fi karfi a California. Don haka akwai yiwuwar can zata bishi da zama.

Sun kaita gidanta dake can Hotoro G.R.A. Gidanta hadadde ma shaa Allah, ya sha duk wani abu da ake bukatar samu a gida.
Suka wayi gari ita da yan'uwansu anan ana ta son barka. Wasu sun juya tun a ranar, wasu kuma sai washegari. Ita da Mami suma duk a ranar zasu juya Kaduna don kuwa gogan yana can yana jira. Don shi tun a jiya ya sanya ran zuwansu.

Da yamma suka shirya zasu tafi yadda zasu yi shigar dare. Don haka wajajen karfe goma na safe, suka fita Ita da Mami suka yiwa gidan Anty Jamilah tsinke. Ta taresu da murnarta, ita da Rabi'ah suna ta yabon irin kyawun da tayi da cika data kara. Ita dai tana ta musu murmushi kawai.

Zuwa can suka yi musu sallama, Anty Jamilah ta hadasu da turaruka da kayan shafa masu kyau. Ita da Mami din har sun dinke kamar wasu tsofin abokai. Suka yi mata sallama tana musu alkawarin in shaa Allah itama kwanan nan zata shiga Kaduna din.

Akan hanyarsu ta komawa tace su dan tsaya a shoprite, akwai spices da take son saya wadanda bata dasu a gida.
Suka shiga ita da Mami, hannunta rike da hannun Farida. Ita Mami kai tsaye sashen kayan snacks da tarkacen su biskit ta wuce. Ita kuma ta wuce wajen spices da seasonings, ta debi iya wadanda zata iya. Sai ta koma bangaren kayan sanyi zata daukarwa Farida Ice cream.

Ta kai hannu zata dauki Mint n Choco na Robofob, ita kuma budurwar ta kai hannu zata dauki fanice. Hannun nasu ya hadu waje daya, suka kalli juna a lokaci daya da niyar ba juna juna hakuri. Sai kalmar ban hakurin nata ta makale a bakinta. Cikin tsananin mamaki ta bi bayan yarinyar da take juyawa da kallo, ranta yana kiyasta mata wani abu.
Kasa jurewa tayi, ta bi bayan yarinyar da sauri tana mata magana cikin alamun rikicewa.


46.



Yarinyar ta juya tana kallonta cikin alamun mamaki. Sai Nadiya ta ja tunga a gabanta tana sauke numfashi daya bayan daya.
Tace mata, "don Allah kiyi hakuri na tsayar dake baiwar Allah, tambayarki ce nake so inyi!"
Ta gyara tsayuwarta tana kallonta, "to, Allah Yasa na sani!"

Tayi shiru tana kara kallonta, a ranta addu'a take tana karawa, Allah Ubangiji Yasa zarginta ya zama gaskiya. Idan ta daga ido ta kalli yarinyar sai taga kamar Maryam ko Anty Haulatu ko Yaya AbdulHadi take gani. Haka duka 'ya'yan Mama suke, duk ita suke daukowa a kamanni kamar an tsaga kara an karya. In ka dauke Nazifi da kuma diyarta data rasu, wadannan Abbansu suka dauko a kamanni.

Ta daga baki murya na karkarwa, tace mata, "don Allah, ba wai tambayar rainin hankali bace ba, amma ko kin san Ardo Usmanu? A can Wuro Yanka? Ko Jafe?"
Yarinyar ta kalleta cikin mamaki, tace, "Ardo dai namu? Kakana ne ai, kuma shi Jafe din da kike fadi Babana kenan!"
Kawai sai Nadiya ta rungumota jikinta, ta saki wani irin kuka cikin tsananin farincik mai dauke da tu'ajjibi da murna da mamakin wannan iko na Allah.
Yarinyar nan sai tayi tsaye ta sankame tana kallonta tana zare ido.

Haka Mami ta samesu cikin wannan hali. Da kyar ta samu ta janye Nadiya daga jikinta, suka samu suka biya kudin abubuwan da suka siya. Suka fita farfajiyar wajen, hannunta jimke cikin na wannan yarinya da tace sunanta Zainab. Idan abinda take hasashe hakane, ita din diyar Yayan Mama ne da take yawan basu labari, Yaya Jafe, wanda lokacin da aka daura auranta ma baya gari. Idan kuwa hakane, ashe tsaye take da dangin Mama da suka jima suna nema da addu'ar Allah Ya bayyanasu.

Kuka tace sosai, take ce mata, "matsayin diya nake a wajen kanwar Jafe din, Zuwai-Juwairah. Wadda suka rabu da danginta a can Wuro Yanka din tun tana yar yarinyarta, anyi neman duniya har yau bamu samu wani bayani ko kadan daga garesu ba. Yanzu har mun dawo gefe muna ta addu'a kawai da fatan Allah Yasa muna da rabon ganawa da su."

Zainab itama sai ta hau share hawaye, tace mata, "kwarai kuwa, Babanmu yana yawan bamu labarin wata kanwarshi da kullum yake cewa mu dinga mishi addu'ar Allah Ya kaddara saduwarsu. Saboda ita ne ya nemi wajen zama anan Kano shi da danginshi, suka daina yawo. Kusan kullum sai yayi mana zancenta, da yadda yake dana sani da nadamar rashin kasancewarshi a wajen a lokacin da ta bar gari!"

Nadiya ta kara fashewa da kukan dadi da murna. Da kyar Mami ta lallasheta suka shiga mota, sai ga su sun koma gidan Anty Jamilah bagatatan.
Ita kanta ba karamar murna tayi ba da jin dadin wannan labari. Nan da nan ta dauki waya ta kira Yaya AbdulHadi ta sanar dashi. Abinda yace mata shine su yi hakuri kar su sanar da Mama, gashi nan zuwa a yau ba sai gobe ba.

Don haka ta dauki makullin mota suka tafi gidan su Zainab har ita.
Kafin zuwan nasu Zainab har ta kira gidansu ta sanar dasu abinda ke faruwa. Don haka zuwa lokacin da Anty Jamilah ta tura hancin motarta cikin gidan Alhaji Ja'afar Usman dake cikin unguwar Gwammaja, a kofar gidan suka sameshi shi da Iyalinshi suna tsammaninsu.

Nan suka rankaya cikin gidan, aka zauna a falo ana maida bayanan abubuwan da suka faru.

Anan gidan suka yini har karasowar Yaya AbdulHadi shi da Nazifi can da yammaci, Allah Ya taimakesu sun samu jirgi mai tahowa daga Lagos zuwa Kano a wannan ranar. Da so suka yi a ranar su tafi Kaduna, amma Alhaji Ja'afar yace su daurewa gobe saboda tafiyar dare bata da dadi. A daddafe suka kai washegari.

Ga basu sanar da Mama halin da ake ciki ba, ga Nadiya bata yiwa Babangida bayanin abinda ke faruwa ba. Ta dai tura mishi text din cewa yayi hakuri sai gobe zasu dawo saboda wani abu na gaggawa daya taso.
Kaikayin baki ya isheta, tunda assalatu ita har ta gama shirinta. Sai data kira Mama tace mata ta shirya suna tafe da manyan baki a yau.

Suna gama kari suka nufi gidan Alhaji Ja'afar. Yaya AbdulHadi da Nazifi a hotel suka kwana, don duk da tayin da Anty Jamilah ta mishi na yaje ya kwana a can gidanta cewa yayi a'ah. Suka samesu suma sun gama shirinsu shi da Iyalanshi, matar shi daya tun ta lalle. Suna da 'ya'ya bakwai, wasu sunyi aure. Zainab da kaninta Ma'aruf sune a gaban iyayen yanzu, akwai Yayanta Fahad yana BUK, sauran kuma matane duka suna gidajen aurensu.

Motoci biyu suka dauka, wadda su Nadiya suka je da ita Nadiya din ce da Mami da Nazifi da Farida. Yayinda ta Alhaji Ja'afar kuma shine da Iyalinshi da Yaya AbdulHadi.
Kasancewar tafiyar safe suka yi, sai nan da nan gasu a cikin Kaduna kafin karfe goma ta rufa.

Mama tana zaune a tsakar gida bayan sun gama sallamar yara yan makaranta tana kokarin hada kayan wanki Maryam da Amina su yi in sun dawo makaranta. Sai jin sallamar Nadiya tayi a saman ka, ta dago da mamaki sai tayi turus ganin Yaya AbdulHadi yana binta a baya.

Tace, "dannan! Nadiya! Sannunku. Ku ne da sassafen nan?!"
Nadiya ta tafi ta rungumota cikin murna, tace, "Mama ki shirya da kyau, yau tafe muke da bakin arziki!"
Kafin Mama ta gama tantance abinda ke faruwa, Nadiya ta fara yiwa mutanen gidan shelar cewa su kimtsa baki zasu shiga.

Sai jin sallama tayi da muryar da ko mutuwa tayi ta dawo, ba zata taba mantata ba. Girma da yawan shekarun da suka dauka ba a tare ba ba zasu sanya ta manta da wannan halittar da ke gabanta ba. Tafiya tayi ta sume gabadaya. Suka rufu kanta ana yayyafa mata ruwa har ta samu ta farfado. Kawai sai ta saki wani irin kuka daya matukar karyar da zuciyar mutanen wajen, su ma suka fara sharar hawaye. Lallai dan'uwa ba wasa ba, babu kuma wanda zai taba iya cike maka wannan gurbin nashi har abada.

Ta kama hannun Yayanta Jafe ta rike, cewa taje yi, "ashe dama kana raye? Ashe zan sake ganinka a rayuwata? Ashe dama kaima zaka iya yin fatali da ni a cikin rayuwarka, ka manta da ni? Nayi zaton ko su Dada sun sallamani saboda abinda na musu kai ba zaka cireni daga ahalinka ba!"

Ya kai hannu yana share hawayen fuskarshi, yace, "kiyi hakuri kanwata, amma ko da iyayenmu sun yayeki, ni ba zan taba yayeki ba. Dawowa kawai nayi na tarar da labarin wai an miki aure kin bar Wuro Yanka. Nayi neman duniya amma ban sameki ba. Saboda ke ne ma gabadaya na nemi rassa na zauna a Kano, na koma Wuro Yanka ko zan sake samun labarinki bayan yan shekaru, aka ce min tabbas kin je, amma rashin sanin inda muke ne yasa basu baki takamaimiyar amsa ba. Na bar musu lambar waya da inda nake zaune a Kano ko Allah zai sa watarana ki koma su fada miki, amma har yau babu wani labari. Kiyi hakuri kinji? Yau gashi Allah Ya hadamu cikin ikonSa ai."

Ranar dai gida ya cika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login