Showing 120001 words to 123000 words out of 142169 words

Chapter 41 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

720

wani wanda ya kalli wannan shiri.

Mutane da dama kuma sai bayan wannan shirin sannan suka san cewa Habibu din matanshi biyu. Nan da nan kuma sai mutane suka fara raba kafa. Nadiya ta fara samun kira daga manyan mutane da manyan women leaders da aides, wadanda yawancinsu ma na bangaren Shukurah dinne suke zamewa suna komawa wajenta.
Ita kuma sai take kaffa-kaffa da kowa, musamman masu kai mata gulmar Shukurah da yadda take wulakantasu da musu iko da kudi. Ita kuma da taji ka fara wannan maganganun sai tayi gaggawar katseka, tace maka kawai kuyi maganar data kaika, idan kuma wannan ce kadai to kayi hakuri kawai ka tafi.

Sauran abubuwan da Shukurah tayi fushi ta tafi bata karasa ba sai suka koma hannunta. Su da kansu women leaders din suka tara mata taron karawa juna sani da manya-manyan mata yan siyasa da suka jima ana fafatawa dasu a wannan harkar, aka yi zaman anan cikin gidan. A nan ne tasu taje daya da matar Gwamnan Kano Haj. Badariyya Kamal, wanda suke sa ran zai yi tazarce a wannan karon. Suka yi musayar lambar waya da ita akan cewa za su cigaba da zumunci, kuma idan Nadiya din tana da wani bukata ko tambaya na daban, zata iya tuntubarta.

Da za su yi sallama da ita bayan taron ya watse, ta rakata ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
har gaban motarta inda securities dinta ke jiranta, take fada mata cewa, Shukurah ta jima tana tura mata takardar son ta bata damar ganinta amma tana ki, tace mata, "kina da wasu qualities na musamman da ake son matar shugaba su kasance dashi. You are sincere, sannan duk wani magana da zaki yi kina da interest na talakawa da son kyautatawa kasarki, don haka keep it up Nadiya, muna tare dake in shaa Allah!" Tayi mata godiya sosai da sosai.

A cikin satin Mami tayi musu sallama ta juya Jordan. Ta musu alkawarin idan zabe ya zo nan da watanni hudu, za ta dawo da izinin Allah domin tayi zabe kamar yadda kasa take bawa duk wani danta dake rayuwa a wata kasa ta daban wannan dama.

Ta tafi din ba da jimawa ba aka yi bikin bude Madam Zarahs Arena. Wanda ta dauki bakuncin manya-manyan kasa da dama da kusoshi na Gwamnati. Aka yi bikin taro aka gama lafiya, Madam ta fara gudanar da aikinta. Sai ta fara dakatar da sauran ayyukanta da take yi a sauran wajaje, saboda tana so wajen ya amsu ya kuma ginu a garin Kaduna cikin dan kankanin lokaci. Nan gaba kadan idan ta samu yadda take so, zata bude musu manyan rassa a garin Maiduguri da Abuja.

Ta bangaren Habibu ma cikin ikon Allah sun fara rounding up kamfen dinsu, duk inda zasu shiga sun shiga, suna kuma ganin nasara da cigaba. Saura kuma ya rage suyi ta addu'a da jiran zuwan lokacin zabe.
Zaman daya samu ya sanya ya kara daukar duk kulawarshi da nutsuwarshi ya maida akan Nadiya da abinda ke cikinta. Laulayin nata ya lafa kwana biyu, tana kuma iya cin abinci yanzu sosai. Don haka jikinta yana ta kara murmurewa gwanin sha'awa.


48.




Shukurah ta hau dokin zuciya kwarai da gaske bayan fadan da Ummah tayi mata. Ta dauki makullin mota ta tafi gidansu kai tsaye ba tare da wani tunani ba.
Dama can gidansu gidane na sangartattun yara wadanda gata ya yiwa yawa. Mahaifiyarsu macece da bata son ganin laifin yaranta ko kankani, shi yasa tun tashinsu basu ganin kan kowa da gashi. Babu kuma wanda ya isa dasu balle ya ce zai sanya musu kara yace kada su tsallaka.
Mahaifinsu ba mazauni bane, shi yasa ba wani rawa yake takawa a cikin rayuwar tasu ba duk da cewa dai yana kokarin tsawatar musu shi ba kamar mahaifiyarsu ba.

Tana fadawa Mommynsu abinda ya faru, itama ta hau zubda nata fadan da zagi, wai Hajiya Ummah ta ci mata mutunci tunda har ta zagar mata diya.
Ta kuma ce mata ta wuce daki tayi zamanta, Hajiya Ummah din zata je ta sameta har inda take. A takamarsu su dukan, irin rawar da Shukurah take takawa ga kamfen dinsu, ga mahaifinsu shima dake bada nashi taimakon ta bangaren kamfen din Habibun, ai gani suke yi sun fi karfin wulakanci a wajen Hajiya Ummah.
Don haka koda Ummah ta kirata kan batun Shukurah, sai ta rufe idanu ta dinga zazzaga mata masifa, tace mata Shukurah ba zata koma ba har sai Habibun yaje da kanshi, itama kuma Ummah din sai ta ba Shukurah hakuri na muzantata da tayi a gaban Nadiya.

Ummah tayi murmushi sosai kamar tana gabanta, tace mata, "Hajiya Talatu, kiran da kika ga nayi ba wai don ina tsoron barin Shukurah gidannan bane kamar yadda kuke tunani, saboda naga alamun tana ganin kamar idan babu ita din ba zamu iya rayuwa bane ko kuma ba zamu samu nasarar zabe bane? Bayan kuma ba haka bane, ita kanta ta san da hakan, yaudarar kanta kawai take yi. Na kirane a matsayina na babba, wadda na dauki Shukurah tamkar diyata. Kwarai na yi mata fada saboda ta aikata ba daidai ba, don haka babu zancen bada hakuri a cikin wannan magana. Maigidanta kuma da kuke son gani, in fada miki gaskiya ma da na ce mishi ta taho gida cewa yayi umma-ta-gaida-assha. Don haka ki mata fada ki kuma kara da mata nasiha, ta dawo dakinta tunda nan ne marufar asirin kowace mace. Ta kama mijinta da abokiyar zamanta ta rike, su cigaba da zaman rufawa juna asiri. Ita rayuwa ai yar hakuri ce, zaman aure ma ya gaji haka kuma. Duk lokacin data shirya dawowa ina maraba da ita Hajiya. A gaida maigidan!"
Ummah ta kashe waya ta bar Hajiya Talatu da waya a hannu cike da mamaki.

Ta cewa Shukurah tunda hakane, ta kara mike kafa kawai ta cigaba da zama anan. Tana da tabbacin Hajiya Ummah da kanta zata kwaso kafa tazo bikonta. Ta kuma bi kalaman mahaifiyarta ta zauna a kansu daram, ta kara mike kafa tana jiran Habibun ko Ummah.

Sai dai me? Har ta kwashe sati biyu babu alamun wani zai je yayi bikonta. Zaman gidan ya fara takurata. Don kuwa dama dai can duk rayuwar bogi ce ake yi a gidan. Mahaifinsu yana da kudi babu laifi sai dai bashi da sakarwa iyalinshi kudi. Shi idan ya aurar da yarinya ma to ficika bata kara hadaki da shi sai in ta kama dole. Yayunta kowa na gidan aurenta, ba wata tsayayyar sana'a ba suke yi ko aiki duk kame-kame ne kamar dai ita. To gwanda ita din ta fisu fantamawa da budi na gidan aure. Don kuwa babu laifi Habibu ya tsaye mata sosai da sosai, yana kokarin sauke hakkinta dake kanshi, haka ko kudin kashewa zai bata yana kokarin bata masu dan kauri.
Rashin godiyar Allah ne ya sanya har take bi ta hanyar mayar da auratayyarsu tana karbar wani abu a hannunshi tunda dai babu ta inda ya rageta. To itama wannan din tun fara zancen aurensu da Nadiya ya fita harkarta, tunda ya samu wadda tasan hakkinshi da iya sauke nauyin dake kanta ta wannan bangaren meye na shi na biya?

Yawace-yawacen kamfen data fara ne ta fara zarar wasu yan kudade daga nan, tasan kuma Hajiya Ummah tasan da hakan amma bata taba mata maganar ba koda wasa.

Sauran kudaden da suka rage mata a cikin akwunt dinta ta cirosu, da Mamansu ta gani ta lallaba ta karbe rabi a hannunta. Ta kuma koma suka sake cinye na wajen Shukurah din da ita.
Da suka kare sai ta koma gefe kuma ta zuba mata idanu.

Cikin sati na uku da zamanta a gidan idanunta suka fara raina fata. Musamman ganin yadda mutane suka karkata hankalinsu ga Nadiya gabadaya, ake neman a manta da ita.
Sai gata ta fara kiran wayar mutanenta data tattara, tuni su kuwa da suka nufi wani Sarkin da suka fahimci dai bata da wata fawa yanzu. Wadanda suka samu wajen zama a wajen Nadiya da Hajiya Ummah suka zauna, wadanda basu samu ba kuwa sai suka canza sheka.

Cikinta ya duri ruwa sosai, tsoro ya dabaibayeta. Babban abin takaicin shine duk cikin Yayunta aka rasa wadda zata iya tallafa mata da wani abu, bayan kuma a da kullum cikin bani-bani suke daga su har Mommyn tasu.
Ga Daddynsu tunda taje gidan ma sau biyu suka hadu, yana ta yawace-yawacen daya saba shima don bai cika zaman gida ba.
Yana ganinta a gidan da safe ya tambayeta me taje yi gidan? Mommynsu ita ta dinga mishi bayanin abubuwan da suka faru, bayan ta hada karya da gaskiya. Ya gama saurarenta tsaf, ya kalli Shukurah yace, "gida dai ba zan hanaki zama a ciki ba, amma ki sani, you are on your own!"
Ya dauki kan wayoyinshi ya fita abinshi.

Gani na biyu data mishi magana ta mishi akan ya taimaka ya bata kudi tana son sayan kayan bukatu, kamar dama can jiranta yake yi. Ya rufe ido ya mata cin mutunci sosai. Ya rantse ya kuma maya, kwandalarshi ba zata shiga hannunta ba. Shi yace tayi yaji? To shi wallahi ko mijinta mutuwa yayi abin Allah Ya kiyaye, ta dawo gida, sai dai ita da uwar da ta daure mata wani gu su dinga ciyar da ita amma ba da shi ba. Ya kara da cewa ta gode ma da take samun ci da sha mana.

Ya fita yana baza babbar riga Mommy ta bi bayanshi da sauri tana kara mishi tunin kudin da yayi alkawarin bata jiya. Suma da kyar ya lalubo ya mika mata su yana mata mitar ta fa dameshi da bani-bani.

Ta koma falon tana kallon kudaden a wulakance. Shukurah na rakube a gefe tana kallonta, tace, "Mommy bani dubu goma a ciki mana?!"
Ta zaro ido har tana hadawa da dafe kirji, "wace irin dubu goma Shukurah? Dududu dubu ashirin ce fa ya bani a cikin dubu hamsin. Ni wannan da zan miki lissafin abubuwan da zanyi da ita ma da wallahi duk inda kudi suke sai kin nemo min kin cika min su."
Ta wuce dakinta tana cigaba da mitarta.
Sai Shukurah ta rufe fuska da tafin hannu tana jin kamar ta kwala ihu.

Duk yadda taso daurewa ta cije, kasawa tayi. Sai gata bayan kwana biyu tana neman Habibu a waya, ta yi ta kira tana shiga tayi kara amma bai taba dagawa ba. Daga baya ma idan ta kira sai taji a kashe.
Ta sake rufe ido wannan karon ta kira Ummah. Wadda ta daga a kiran farko, suka gaisa da ita kamar babu wani abu dake faruwa. Har tana tambayarta ya Mommynsu da Daddy? Take ma bata labarin ai Daddyn nasu a gidanta ma yayi karin safe dazu, suna tare har wajen Azzuhur saboda wasu filayenta da yake son saya.

Sai kawai ta barkewa Ummah da kuka. An ce fadan da yafi karfinka ka maidashi wasa. Sai a lokacin Shukurah ta fahimci ashe bata da wayo ko kadan. Shi wanda take takamar dole ne su Ummah su nemeta saboda shi, gashi can yana cigaba da zuwa inda suke ba tare da sun ma sani ba. Da alama kuma ko zancenta ma kila bai taba yiwa Ummahn ba. Wata zuciyar tace mata to zancen me zai mata? Shi a wajenshi ai ko yanzu kasuwa ta tashi to dankoli ya gama cin riba. Ko kun rabu da Habibu yanzu ai ba shi da asara, saboda yasan da taimakon daya yiwa su Ummah, in dai sun samu mulki ko kina nan ko ba kya nan ai dolene su rama mishi.
Anan ta fahimci cewa ashe ita duk tutiyar banza da wofi take yi. Don kuwa ba ita ta ke yiwa Ummah alfarma ba, su suke mata. Dama dai masu magana ai sun ce wuya makarantar kare.

Jin kukan da take yi tana karawa yasa Ummah ta fara tambayarta lafiya? Amma ta kasa magana, sai hakuri da take bata kawai.
Ummah tayi murmushi a hankali, tace mata, "har kin karaya ne tun yanzu Shukurah? Ai nayi tunanin ma watakila sai mun shekare a hakan kafin ki fahimci duniya da yadda take?"
Ita dai bata iya cewa komi ba sai shiru da tayi tana jan hanci da shessheka.
Ummah tace mata, "ban yi fushi dake ba Shukurah, haka ma mijinki baya fushi dake. Kuma kamar yadda na fada miki ne tun wancan karon, kofarmu a bude take idan kin shirya dawowa." Ta kashe wayar.

Amma duk da haka din sai ta yakice maganar komawa. Ta cigaba da lallabawa a haka, tana fatan Allah Yasa Ummah taji tausayinta taje tace su tafi. Amma abin ai da kunya, ta kamo kafa ta taho kuma ta koma babu wanda yaje biko?

Ta cinye wata fiye da daya tas a haka. Gabadaya watan nan har wani canzawa tayi, fuska ta fara mata kurzunu-kurzunu da dabbare-dabbare.
Ta ture kwanon abinci data gama ci tana hararar kwanon kamar shine mai laifi, "yanzu saboda Allah gida kamar wannan ace wai ba za a yi abinci da nama ba ko kifi? In babu su ko vegetables a dinga zubawa mana. Ni dai gaskiya ban saba da cima irin wannan ba!"

Ta fadawa Mommy hakan tana turo baki cike da shagwaba. Hajiya Talatu ta kalleta baki a bude, "to, gori ne nan kike min ko me? Ai kin dai fi ni sanin cewa mahaifinku bai cin nama balle kifi, don haka ba zai kawo ba. In kina so ki sa kudinki ki saya mana? Da kike mana gorin kuma baki saba da wannan cimar ba, ina ba ni ce nace ki baro gidanki ki zo ki nan ki kwarzabeni ba ko?"

Ta kalli mahaifiyar mamaki kwance akan fuskarta. Amma tsabar mamakin ma ya hanata cewa komi. Kawai sai ta tashi tsam daga kan dinning din, tace, "wallahi babu wani Daddy baya cin nama, kawai mako ne yasa yace bai ci don kada ya kawo shi nan!"
Ta haura da gudu dakinta na da inda ta sauka ganin Mommy din tana shirin wartota. Gyale kawai ta dauka da makullin mota ta fita. Mommy din tana kicin, sai jin tashin motarta tayi.

Kai tsaye gidan matar babban Yayansu Anty Hadiza ta yiwa tsinke. Ma'aikaciyar asibiti ce ita. Duk cikin yayunta daga ita sai Yaya Buhari ne kadai suka nuna jin haushinsu na rashin karbar ban hakurin da Ummah ta yiwa Mommy. Suka kuma fadawa Shukurah din itama bata kyauta ba, ba kuma haka ake yi ba.
Amma da yake a lokacin kanta rawa yake yi, sai ce musu tayi ba sonta suke yi ba shi yasa.
Amma ko a yanzu da halin data shiga, Yaya Buhari ne kadai mai taimaka mata da wani abu.

Anty Hadiza ta kama baki ganin yadda Shukurah din ta koma, duk ta wani birkice. Tana ganinta kuma sai ta saki kuka, ta dinga rera shi Anty Hadiza na bata hakuri har tayi shiru.
Tace, "Anty Hadiza na tuba, don Allah ki maidani gidan Habib wallahi na dauki darasina!"

Sai tayi dan murmushi, ai dama tasan ranar yau na zuwa. Amma maimakon ta zauna tuna mata baya da ce mata ai dama na fada miki, sai ta samu ta kara lallashinta. Ta zubo mata abinci shinkafa da miya ta ji kaji, ga wani romon na kayan ciki da ta dafa shi da sinadarai na gyara jikin ya mace. Sai zama tayi a gefe baki dage tana kallon yadda Shukurah take kai lomar abincin nan hannu baka hannu kwarya.

Ta gama cin abincin tayi gyatsa tana kallonta, "wallahi rabon da in ci nama tunda na bar gidan Habibu!"
Anty Hadiza dai wannan lokacin ta kasa daurewa, sai ta saki dariyar data jima tana dannewa. Shukurah ta jingina da kujera tana kallonta har ta gama, tace, "don Allah ba tashin-tashina zamu yi ba, ni dai yanzu ki taimaka ki fada min abinda zan yi in gyara wannan laifi da na tafka!"

Anty Hadiza ta zaunar da ita a ranar tayi mata nasiha da fada sosai irin wanda bata taba yi ba, don Shukurah bata taba bata damar hakan ba. Amma da taga yau ta zauna kuma tana sauraronta sai data juye mata duk wani abu dake ranta. Ta bata shawarar tayi hakuri ta zauna da abokiyar zamanta lafiya, uwar miji kuma ta riketa da mutunci don kuwa babu namijin da zai kyale matarshi ta raina mishi uwa matukar dai yasan inda ke mishi ciwo.
Maganganu dai masu dama da tsayi wadanda rabinsu tana yinsu ne a lokacin da take taimaka mata tana kimtsawa. Har zancen yadda take hana miji hakkinshi na aure da kuma neman ya mata wani abu kafin ya kusanceta sai data mata, ta kuma nuna mata hakan babu kyau.

Ta shiryata cikin wata shadda ruwan gwaiduwar kwai mai kyau, suka dauki hanya a motarta sai gidan Habibu.
Hajiya Ummah sai jin sallamarsu tayi kamar daga sama.

Anty Hadiza ita ta kai Shukurah har gaban Hajiya Ummah ta kuma bata hakuri kan duk abubuwan da Shukurah din tayi. Tace ita dama bata riketa ba, amma irin wadannan halaye data tsira ba zasu karbu bane a wannan gida. Ta amsa cewa tayi laifi kuma zata daina da yardar Allah, kafin Anty Hadiza ta rakata dakinta.

Da dare Ummah ta sake hadasu waje daya ta musu fada da nasiha sosai game da zamantakewa. Bayan sun tafi ta sake jimawa da Habibun tana kara gayar dashi muhimmancin tsayar da adalci a tsakanin iyali. Don yadda taga yayi biris da Shukurah din baya ma nuna alamun yaji dadin dawowarta gidan sam. Tasan ba karamin jan aiki bane a gabanshi.

Ranar Nadiya tayi kwanan rungumar filo. Duk da cewa ita da kanta ta dinga so ya dawo da Shukurah din da kuma kwatanta yadda ba zata bari wani abu ya dameta ba idan ta dawo din, amma ina, ta gaza. Wannan lokaci da suka kasance a tare da babu abinda yake rabasu, sunyi wani irin sabone mai wuyar fassarawa. Don haka ita dai ranar barci sai barawo yayi awon gaba da ita.


49.



Sun hadu da Shukurah din washegari a bangaren Hajiya Ummah. Ta sameta ita kadai a kan dinning, sai ta ja kujera a daya gefen ta zauna, tace mata, "Ina kwana?"
Ba don tayi tunanin za ta amsa ba. Ga mamakinta kuma sai taga ta amsa mata din.
Bata nuna mamakin hakan ba, sai kawai ta janyo kwano ta fara zuba farfesun naman kan sa da ya sha taruhu da daddawa yana ta tashin kamshi mai dadi. Ta fara cin abinta a nutse. Wayarta ce a hannunta tana chatting da Aramide

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login