Showing 39001 words to 42000 words out of 142169 words

Chapter 14 - Nadiya Book 1 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

448

bata sani ba, kai ina! Ba zai yiwu ba. Amma kuma idan ta duba ta wani bangaren taga alamun ita kanta Madam din ta fi bukatar ayi da Safiya, sai taji dan sanyi a cikin ranta.
Tunda idan ba da Safiya take so ayi ba, me yasa zata yi karyar Safiyar ce take girkin da ake kaiwa Hajiya Umma?

Da dai taga barcin ba zuwa zai yi ba, sai ta tashi kawai ta dauro alwala ta fuskanci alkibla.
Ranar rayuka uku kwana suka yi basu runtsa ba. Ita tana fata da buri da addu'ar Allah Ya tsallakar da ita wannan ibtila'i da yake kokarin tunkarota. Wata tana addu'ar Allah Ya mallaka mata Habibullahi Makama. Shi kuma yana addu'ar Allah Ya mallaka mishi daya daga cikinsu.


&&&&&&

Washegari ta shiga dangi don yin sallama dasu. Tunda safe data tashi ta hade yan komatsanta waje daya, Anty Lima ta bata jaka mai fadi ta sanya sauran kayanta da basu shige cikin akwatu ba a ciki.
Itama Anty Limar kayanta ta hade saboda a ranar zata koma gida.
Suka yi sallama da Madam tun da safe din saboda tasan ba lallai su kara haduwa ba. Madam din bata mata maganar komi ba game da abinda ke faruwa, don haka itama bata ce mata komi din ba. Har kudin mota ta tura mata ta account, Nadiya tayi godiya.
Da zasu rabu da Safiya ta dan mata wa'azi da hannunka mai sanda game da rayuwar duniya. Musamman yanzu da take shirin shiga cikin turawa ta zauna a cikinsu. Nadiya tasan abin na Safiya sai abinda ya karu don kuwa ba raguwa zai yi ba.

Sai can yamma ta dire a gidan Dada, tunda data gama zagayen wadanda zata zagayawa zuwa fitowar masallaci, sai ta dire a gidan Anty Hauwa. Itama da zata taho haka ta hadata da atamfofi har kala biyu manya da takalma, Nadiya ta mata godiya sosai.

Kafin karfe tara na dare tuni ta gama shirin kwanciya. Tana cikin yin shafa'i da wutiri taji wayarta tana kara. Da tayi sallama sai ta dauki wayar da niyar bin bayan mai kira, sai taga Madam ce. Data kira bata dauka ba sai ta kyaleta har ta katse, tana katsewa din kuma sai gashi ta dawo da kiran. Don haka ta daga.

Suka gaisa kamar yadda suka saba, har tana tambayarta ko har ta kwanta ne? Tace mata a'ah, shafa'i ne tayi da wutiri. Madam tace, "Habib, dan gidan Hajiya Umma gobe zai koma can Kadunan, ita kuma sai ta kara kwana biyu kafin ta koma. To shine nace mata ke ma ai gobe zaki koma, sai tace to ki shirya idan zasu tafi sai su wuce dake."

Tayi saurin girgiza kai kamar tana ganinta, tace, "Mommy, na fa riga na gama shirin komi da komi, kuma ni fitar wuri zan yi gaskiya saboda da wuri nake so in isa gida!"

Madam tace, "to ke in banda abinki tafiya a motor gida bai linka na haya ba sau dubun dubata? Kuma ai zaki ma fi isa gida da wuri."
Tasan sarai Madam din ta fita gaskiya, amma kuma tafiyar ce bata son yi dasu kwata-kwata. Ta sake daga baki da niyar nunawa Madam tsarinta fa bai yi ba, tace, "to ai kinga ba saninshi nayi ba, kuma shima hakan take. Kinga kuwa tafiyar tamu ba lallai tayi dai-dai ba. Sai inga kawai gwanda kowa yayi tafiyarshi ko?"

Madam tace, "sai ku san juna ta dalilin haka ai. Ki shirya da wuri, wajen karfe takwas zasu zo su daukeki."
Ta katse wayar ba tare data bari Nadiya ta sake cewa wani abu ba.

Ta ajiye wayar yaraf! akan cinyarta jiki a matukar sanyaye. Gabadaya wadannan abubuwa dake faruwa ta kasa fahimtarsu. Ta rasa ta yaya zata fahimcesu. Ya za ayi ita dake kokarin nesanta kanta da abu kuma a dinga kokarin kusantata dashi? Yanzu da zancen aure yake lilo a tsakaninsu, gani take kamar idan ta rabu dashi hakan zai iya zama gaskiya.

Don haka kafin ta kwanta, ta riga ta gama yankewa kanta shawarar abinda zai faru kawai.
Asubahin farko, ta gangara akwatunta ta fito. Ta bugawa Dada kofa, ta bude ta fito da tasbaha a hannunta alamun lazumi take yi.
Ta kalleta da mamaki, tace, "Nadiya, sammako kika bugo kuma? Nayi tunanin zaki bari garin ya gama wayewa?"

Tace, "ai Dada saboda yanayin hanya shi yasa, gwara in fita da wuri din zai fi."
Dada ta yi mata fatan alkhairi sosai. Maigadin gidan ya fita ya samo mata abin hawa ta loda kayanta a kai ta hau, sai tasha.

Sai dai zuwan nasu tashar sai suka tarar da jira. Dole ta shiga mota ta zauna bayan ta biya kudi, aka hau jiran fasinjoji.
Suna nan zaune har bakwai ta kusa rufawa, gabadaya ta fara kagara da zaman jira.
Sai taji wayarta tana kara. Data duba ta ga lamba ce babu suna sai ta mayar ta cikin jaka ta ajiye. Bata cika kin daga sabuwar lamba ba, amma dai wannan lambar ji tayi hankalinta bai kwanta da ita ba, don haka ta ki dagawa.

Aka yi ta kira tana kin dagawa har sai da aka ajiye mata missed calls kusan guda hudu, daga karshe dai ta daga cikin nuna alamun gajiyawa.
Ta kara wayar a kunne, tace, "wai waye ne?"

Shi kuma mai kiran ya tareta da tambayar, "Nadiya kina ina ne?!"

Sai da taji zuciyarta na canza bugawa, amma ta danne zuciyartata. Duk da ta fahimci mai tambayar kuma sai ta mayar mishi da wata tambayar, "waye ne wai?"
Daga can ya fara bata amsar tambayar tata, "kina ina...?"
Kafin ya karasa kuma sai taji yace, "got you!"

Kafin kuma ta ankare kawai taga mutum a tsakiyar kanta.
Ya tsaya ta gefen da take yana kallonta ta cikin bakin gilashi daya rufe fuskarshi da shi, wai ya hau yi mata alamun ta fita daga motar.
Ta kuwa danna mishi harara ta juya kanta gefe guda. Wannan bakar masifa har ina! Ta gudu din ma bata tsira ba sai an dauki hanya an biyota har tasha sai kace wadda tayi sata? Tafiya ko? To ba zata hau motar ba sai taga yadda za ayi da ita.

Ganin ba fitar zata yi ba sai ya koma ga direba, bata san me suke cewa ba, bayan yan mintuna sai taga ana fitar mata da akwatu daga mota. Ta juya tana kallonsu cike da mamakin wannan karfin hali. Da taga dai da gaske fitar da kaya suke yi, sai ta tashi ta fita daga motar, tana tambayar direba lafiya kuma?

Direba ya kalleta, yace, "yata, kiyi hakuri kin ji? Komi na rayuwa fa hakuri ake yi da shi kinji? Ki daure ki taushi zuciyarki ki bi mijinki. Don bai shirya da wuri ba sai kawai ki ce zaki tafi ki bi motar haya? Dama ana haka ne? Yanzu dai tunda gashi ya shirya din, kuma kinga motar ma har yanzu ko rabin cika bata yi ba, ki daure ki bishi din. Allah Ya kiyaye muku hanya!"

Wallahi tsabar mamaki sai ta ma kasa daga baki tayi magana, sai cira idanu data dinga yi a tsakaninsu.
Ta kalleshi, rannan nata idan yayi dubu a bace, tace, "wai wacece matarka?"

Yayi wani murmushin tura haushi, "ga ki nan a tsaye kina kallona!"

Ta jinjina kai kamar wata tsohuwar kadangaruwa tana kwafa, ta juya ta kalli yaron mota dake kokarin daukar kayanta, tace mishi, "Malam ajiye min kayana!"
Babu musu ya ajiyesu ya tsaya yana raba kallo tsakanin ita da Habibu din.

Ta kama akwatinta taja, ta kalli Habib, tace, "kaje ka nemi inda matarka take amma ba Nadiya ba. Tafiya kuma ba zan yi da kai din ba, ka kama hanyarka ka tafi salin alin!"

Ya daga kafada, "ke dai zaki zo mu tafi salin alin saboda kinga lokaci yana kara ja. Don haka tun kafin dare yayi mana, ki zo mu tafi kafin in ciccibeki daga ke har kayan naki wallahi!"

Wata irin dariya ta kwace mata mai cike da takaici da bacin rai. Bata ma iya ce mishi komi ba kawai ta juya zata tafi. Motar ma ta fasa hawa. Gwanda ta tafi wani wajen, kai ta gwammace ta tafi a kafa akan ta bi bayan mutumin nan su tafi tare.

Kamar wani wanda yake jira, ya tattare hannun rigarshi tsakaninshi da Allah har da dan dukawa wai zai dauketa. Taga dai tsakaninshi da Allah daukar nata zai yi a tsakiyar tasha, ga mutane sun zubo musu ido suna kallo.
Sai tayi saurin dakatar dashi, tace, "tsaya, tsaya! Zan tafi da kafafuna!"

Yayi murmushin samun nasara, ya kama akwatinta har da karamar jakar hannunta don ma kada tayi yunkurin tserewa ta barshi da kayan sanyawa. A yadda ya fara karantarta yasan zata aikata fiye da haka ma.
Ya nuna mata hanya, "yauwa, muje!"
Haka ya sanyata a gaba kamar wata diyarshi, suka tafi. Direba yana tambayar kudin motarta fa data biya? Ya juya ya kalli wata tsohuwa dake cikin motar yace a biya mata kudin mota dasu.
Haka suka bar tashar nan tsohuwa na ta kwarara musu addu'ar Allah kiyaye, Allah Ya tsare. Shi kuwa direba ya dage yana karawa Nadiya nasihar a kara hakuri, zaman aure dan hakuri ne. Ji take kamar daga Habibu din har direban ta kamasu tayi ta hade musu kawuna.

Suna fita daga tashar suka samu lafiyayyar bakar Jaguar tana jiransu. Da kanshi ya bude booth ya sanya kayanta a ciki.
Ya dawo har lokacin jakarta tana hannunshi, ya bude mata gidan baya. Taja tsaki, ta harareshi, ta murguda bakin, taga shi dai ko a jikinshi wai an tsikari kakkausa. Sai ta kara jan wani tsakin ta shiga. Ya maida kofar ya rufe, ya zagaya daya gefen shima ya shiga ya zauna.

Sai da yaga direba ya tashi mota sun dauki hanya, ya kuma tabbatar ya dantse kofofi, sannan ne ya mika mata jakarta da wayarta take ta faman ruri.

Ta warci jakar kamar fada, shi kuwa yayi wata irin siririyar dariya data kara bata mata rai.
Ta ciro wayar ta ga Anty Lima ce take kiran nata. Tayi-tayi ta daga kiran wayar taki motsawa. Abin tun faduwar da tayi take bata matsala, wani lokaci sai screen din yaki dannuwa. Tunanin idan ta koma gida ta hade yan canjin hannunta ta canza waya take yi.

Ganin wayar ba daguwa zata yi ba, da takaici ya cikata sai kawai ta kasheta ta jefa cikin jaka.

17.


Tunda suka dauki hanya bata iya ce mishi komi ba, kanta a gefe daya don ma kada yayi gigin tunanin janta da hira.
Hakan bai dameshi ba ko kadan, haka yayi ta yunkurin janta da hirar kuwa ta hanyar watsa mata tambayoyi daban-daban, amma duka tayi biris dashi. Don kanshi ya hakura ya hau kiraye-kiraye da dage-dagen waya.

Basu sarara da tafiya ba sai da suka shiga Damaturu, ya yiwa direba magana akan su tsaya a gidan abinci.
Suka tsaya a wata restaurant mai kyau, ya bude kofar ya fita kafin ya kalleta yace, "ki fito muje mu nemi abin karyawa ko?"
Ta kalleshi a kaikaice tace, "nagode!"
Shi kuwa bai kara ce mata komi ba suka fita shi da direban suka shiga gidan abincin.

Ta kwantar da kanta a jikin kujera tana binsu da kallo har suka shige. Yunwar take ji sosai, cikinta sai kugi yake, amma saboda tsabar taurin rai ta kasa tashi ta bi bayansu. Sai ma rufe idanu da tayi wani wahalallen barci yayi awon gaba da ita.

Bata san lokacin da suka dauka a ciki ba, sai da taji an bude motar an shigo sannan ta dan farka. Data duba lokaci sai taga sun dauki kusan mintuna talatin.
Ta gyara zama a hankali tana kara gyara zamanta.
Yana zama direba ya tashi mota suka kara daukar hanya. Ya mika mata leda madaidaiciya, ganin bata amsa ba yasa ya dora mata ita akan cinyarta.

Tayi biris da ita na dan lokaci. Kamshin dake fita daga ledar yana shiga hancinta yasa yunwar dake nanikarta ta kara tasowa, don dama daren jiya ba wani abin kirki ta ci ba.
Ta daga ledar tana zaro kayan ciki a hankali kamar wata mai tsoron dagawar, ta fara zaro samosa, meatpie, danginsu spring rolls da lemuka guda biyu na exotic, har da karin tarkacen cakuletin dairy milk da alewar bounty. Ta tabe baki kamar ba wani abin arziki ya mata ba.

Ta fara cin kayan a hankali tana korawa da lemu, kafin kace me ta kusa cinye komi. Sauran da suka rage ta dukunkune su a cikin leda, ta kara kwantar da kanta a jikin kujera ta koma wani barcin.
Wannan kam yayi nisa sosai. Jifa-jifa dai ta kan farka ta duba inda suke da kuma lokaci kafin ta koma, bata tashi daga barcin sosai ba sai da suka shiga Kano. Nan ma sai da suka tsaya ne a wani masallaci na matafiya sannan.
Su duka suka fita, su suka wuce bangaren maza, ita kuma ta wuce na mata.

Daga nan suka sake daukar hanya. Tafiya lumi-lumi gwanin dadi, sai gashi ana kiraye-kirayen la'asar suka shiga cikin Kaduna.

Babu wata kwakkwarar magana data hadasu har a lokacin.
Ya juya ya kalleta yana ce mata, "a ina zamu ajiyeki?"

Tace mishi, "idan mun je Kawo kawai ku ajiyeni, zan karasa da kaina!"

Ya sake kallonta fuska a dan gintse, "tambayarki nake inda zamu ajiyeki."
Ta turo baki kamar zata ce wani abu, sai kuma ta canza shawara. Ta fada mishi unguwar da zasu sauketa.

Da taimakon kwatancen da take yiwa direban sai gasu har a kofar gidansu.
Yana yin parking, ta bude murfin motar ta fita kamar wadda ake mintsina a cikin motar.

Direba ya fita ya bude booth ya fitar mata da kayanta. Sai ga yaran gidan sun fito aka hau murnar ganinta da kuma fadan wanda zai daukar mata kaya.
Bai fita daga motar ba, sai gilashin motar na bangarenshi daya bude, ya dan zura kanshi waje yana mata magana, "baki ji ba!"

Yi tayi kamar ba zata juya din ba, sai kuma ta juya tana kallonshi, fuskar nan idan ka ganta kamar wadda tayi tuntube da kashi.
Wata jaka yake mika mata irin gift bag dinnan ruwan hoda, tayi tsaye kawai tana kallonshi babu alamun zata matsa ma balle ta amsa. Sai ya yafici Fatima, ita kuwa ta ruga da gudunta taje har da dukawa tana gaida shi. Ya mika mata jakar yace mata, "rikewa Antynki wannan ko?!"
Ta kuwa sanya hannu biyu ta amsa, kafin ma Nadiya tace mata wani abu har ta falla cikin gidan da gudu.

Shi kuwa ya kalleta, ya sakar mata murmushi, ya rufe gilashin mota direba ya ja suka yi gaba.

Tayi tsaye a kofar gidan tana bin motar da kallo har ta wuce. Mamakin wannan al'amari take yi, karfin halin mutumin ai har ya wuce misali.
Ita abin gabadaya ya fara daure mata kai. Wannan shisshigi da ake mata ya fara shigar mata hanci da kudundune fa. Tayi kwafa ta wuce cikin gidan itama, a ranta tana fadin zata taka mishi birki matukar ya kara hada hanya da ita.

Tana shiga gidan ta kula da canjin da aka samu. Ita gabadaya ta ma manta da zancen amaryar Abbansu zata tare, sai da ta ci karo da bakuwar fuska a zaune akan dan dandamalin dakin Mama da farantim shinkafa a gabanta tana aikin tsinta.

Su Salame da Lantana kuma suna kofar dakin Salame din wanda yake fuskantar na Mama, sun baza tabarma akai suna ta zubda ruwan habaici.

Data musu sallama sai taga sun watsa mata kallon banza, suka kara da harara da tsaki. Don haka ta dauke kanta daga garesu, ta karasa kofar dakin Mama da take a tsaye, kai tsaye ta rungumeta cike da kewa da jindadin ganinta.

Bayan sun gama gaishe-gaishensu, amarya ta juya tana mata sannu da hanya.
Ta kare mata kallo cike da mamaki. Da ake cewa amaryar ta Babansu yarinya ce, bata yarda ba sai data ganta da idanunta sannan.
Yarinya ce danya shataf, da kyar idan ta haura sha takwas. Amma wai a hakan ma aurenta ne na biyu.

Ta amsa mata a nutse, kafin ta karasa cikin dakin.
Ta shige can cikin dakin Mama ta watsa ruwa don bata tunanin zata iya shiga na tsakar gida. Data fito ta sanya doguwar riga ta jan material marar nauyi, tayi sallah.
Kafin ta gama har Maryam ta kai mata danwake, da alama shi suka yi a gidan da rana. An yanka mishi albasa da tumatiri da latas, ta zauna ta ci sosai da sosai ta kora da ruwan sanyi.

Ta jona wayarta a caji, kafin ta fita wajensu Mama da suka koma kofar kicin yanzu ita da amarya. Amarya na jajjagen kayan miya a turmi, Mama kuma tana kokarin dora tukunya akan wuta.
Nan ta zauna suna hirarrakinsu tana tayasu da wani aikin har aka yi Magriba.
Ta fahimci amaryar ta Abban nasu babu laifi tana da hankalinta, kuma bata da rawar kai. Gashi tana girmama Mama sosai, don hatta da ita kanta Nadiya din bata kiran sunanta kai tsaye, sai dai tace Antyn yara. A ranta take tunanin wata kila ita za ayi zaman mutumci da ita.

Har ta gama shirin kwanciyarta, sunyi waya da su Dada da Anty Lima har da Anty Hauwa. Data kira Madam bata dauka ba sai ta tura mata sakon cewa ta isa gida lafiya, itama Safiya sai data kirata suka gaisa.

Idanunta suka sauka akan jakar da aka bata dazu, wadda ta dorata akan TV stand, bata kuma kara bi ta kanta ba sai a lokacin.
Ta so ta kyaleta tayi ta zama anan, amma curiosity ya hanata. Ta tashi ta dauki jakar, ta koma ta zauna tare da fara zaro abubuwan dake ciki.

Ta zaro idanu cikin tsananin kaduwa da mamaki, zuciyarta na duka ganin gyallelen kwalin wayar Samsung a ciki. Ta hau kwale kwalin wayar har ta ci karo da ita, taga da gaske dai wayar ce ba wasa ko tsokana ba. A bayan kwalin an lika karamar post it card an rubuta, 'fansar wayar da na lalata miki. Fatan za ki karba' a turance.
Ta kama baki cike da mamaki, kafin kuma ta janyo sauran abinda ke ciki. Kwalayen turaruka ne masu kyau kusan kala hudu, da Borneo Oud, Oud Violet, Nishane, Amouage, Thomas de Monaco Raw Gold. Su kuma a jiki an rubuta 'to a fellow perfume lover'

Ta tabe baki kamar yana gabanta. Ta rasa ta yadda aka yi cikin dan kankanin lokaci har ya fahimci tana da son kamshi. Da alama dai yana da kula, 'da kuma sa ido ba!' Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata hakan.
Ta zauna na tsayin lokaci anan tana tunanin abinda ya kamata da sake-sake. Daga karshe dai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login