Showing 1 words to 3000 words out of 167047 words

Chapter 1 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
   💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Book 2

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim



       Page 1


...nan da nan hankalin  ma'aikatan dake fitowa yayi kansu duk suka tsaya suna kallon ikon allah yayinda zukatansu ya cika da mamakin DG  m.malik "dan Allah ku taimakeni saceni yake qoqarin yi karku bari ya saceni dan Allah  "maryama ta fad'a cikin tsananin kad'uwa ,duk yadda taso ta kwace hannunta daga cikin nashi ta kasa dan ba qaramin riko yayiwa hannunta ba ,abinda yasa mutanen dake tsaye suna kallonsu basu taimaka mata ba kuwa shine basu ta'ba gani DG m.malik ya kula wata  mace  dake cikin ma'aikatan ba bare har  hannunsa ya kai gareta ba sai yau ,dan haka suka kawo Idanu suka zuba suna kallon sarautar allah domin dai sun tabbatar akwai wata matsalar da tashi aikata hakan ."


hankalin maryama ya sake tashi fiyye da tunanin mai karatu ,kai tsaye wani office ya nufa daita ya tura ya kofar office din  ya shiga daita sai alokacin ta saki qara mai sauti tana sake neman agajin mutane kafin ta qara wani sautin taga ya bud'e wani d'akin acikin office din wanda yake ajiye zanenta ,turus tayi tsaye tana bin d'akin da kallo yayinda zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri ,numfashi kawai tayi ta saukewa sakamakon tafiyar saurin da tayi yayinda kwakwaluwar kanta ta shiga yamutsawa sakamakon abinda idanunta suka ci karo dashi ."

gabadaya d'akin hotunan zanenta ne da mai gidansa yake zanawa a duk lokacin da yayi mafarkinta kallon d'akin kawai ta cigaba yi hankalinta na qara tashi "ya kalleta sosai ya kalli zanen hotunan dake manne da bango
ya qara tabbatarwa kanshi  ita ce, muryarsa na rawa ya soma magana "ki taimakawa rayuwata ki biyoni zuwa wajen mai gidana"
"wani kallon tsoro tayi masa tana ja da baya jikinta na wani irin rawa dan a yanzu tsoro ya shigeta matuka sakamakon ganin zanen fuskarta ."


"Mai gidana ya dade yana nemaki ,mai gidana ya mutu a soyayyarki ,mai gidana yana matukar sonki so kuma na hakika ,dan allah ki auren shi idan ba haka ba zai iya rasa ransa akanki matukar kika yi kuskuren butulcewa aurensa dan ba qaramin so yake miki ba ,akanki zai iya komai ya qara maganar yana qoqarin kamo hannuta akaro na biyu" muje na kaiki wajensa .."wallahi mutuwa zai yi  idan ya rasaki ."



saurin ja da baya tayi agigice tana girgiza masa kanta cike da matsanancin tashin hankali , yanayin bugun zuciyarta kuwa sai ya baka mamaki"dan Allah ki fahimceni bazan ta'ba cutar dake ba wallahi kawai gidansa zan kaiki ya ga abinda ya dauki shekara da shekaru yana mafarki ,ina kaiki zan kama gabana wallahi kinji na rantse bazamu cutar dake ba ,mai gidana yana qaunarki zai iya mutuwa idan har bai sameki ba "kallon taba'b'be  dakiki mara hankali take masa daga tsayen da take acikin d'akin kafin daga bisani muryarta na rawa tace " a she kuwa zai mutu tun wa'adin mutuwarsa bai kusantosa ba ."


"kai kuma hakika ka shiga d'imuwa ko nace ka haukace da har ka amincewa zuciyarka da rudin daka shiga ,kai yanzu a ganinka nice nan ?"ta fad'a cikin tsananin tashin hankali dan tabbass zanen fuskarta ne har ma da yanayin tsarin jikinta sai dai a nata tunanin wata ce dabam mai irin surarta amman ba itace bace aka zana ,dan daman kuma ance mutane biyu biyu allah yake halitta a duniya wata killa ma aljanace tazo masa da siffarta a mafarki dan babu abinda aljanu basa yi dan haka bata ga dalilin da zai sa ta amince wa kanta cewar  itace ba bayan mafarki ne ita a yanzu ma wani sabon tsoro da tashin hankali ya sake lullu'beta ."

Jikinta na rawa ta cigaba da magana " idan hauka kake yi kayi maza ka dawo cikin hankalinka?idan kuwa dimuwa ce ta sameka akan mafarkin mai gidanka kayi hanzarin dawowa cikin haiyacinka, dan bani bace wannan ,banza sha sha dakiki kawai dabba wanda bai san kima da darajar mace ba ,kawai akan wani zanen banza zaka jawo mutun zuwa nan alhalin mutane na kallonmu ,ni yanzu babu abinda zance maka sai allah ya isa hannuna daka ta'ba da zubar min da mutunci da kayi  tana gama fad'ar haka ta juya zata bar d'akin taji ya biyota yana qoqarin rikota dan bazai yarda ta gudar masa ba , duk runtsi duk wuya sai ya kaita wajen mai gidansa ai kuwa tana juyo ta dauke shi da maruka  biyu ajere ji kake tass tass !!! ."

Nan da nan ya shiga ganin double acikin kwayar idanunshi saboda wani irin hasken daya gilma a cikinsu tsayawa yayi cak dafe da kuncinsa bazai iya tuna lokacin daya sha mari haka ba , a fusace ta shiga nunasa da yatsan hannuta tana huci tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta sannan tace "karka sake gangancin kai wannan banzar hannun naka jikina ,jikina mai daraja ne tayi maganar cike da zafin rai da kunar zuciya , jiki a sanyaye ya zube k'asa bisa gwiwowinsa a gabanta yana rokonta da sauri ta fito daga office din tare da murda key ta rufeshi aciki ,ta fito gabadaya zuciyarta na wani irin rawa ganin idanun mutane akanta zuciyarta ce ta karye sai hawaye sharrrr  tasan wani kallo mutane suke mata ,wata killa ma suyi tunanin yayi wani abu daita ne ."


Cike da tashin hankali ta soma d'aga kafafunta cikin sauri kamar zata tashi sama
Kallo daya zaka mata ka fahimci bata cikin natsuwa da kwanciyar hankalinta, tana fitowa bakin get din ma'aikatan bata sha wahala ba ta samu mota ta fad'a cikin tashin hankali sai da motar ta tashi sannan ta tuna da wata aba subai'a sun yi tafiya mai dan nisa ta sauka a oshodi under bridge, tana tafiya hawaye na bin kuncinta ,ai har abada bazata sake dawowa wannan ma'aikatar da sunan aiki ba, duk yadda zata dojewa zuwa zatayi sai dai a maye gurbinta da wata ."


tafiya kadan tayi ta qaraso inda zata shiga mota mai zuwa agege allah ya taimaketa mutun daya yayi saura motar ta cika ta fad'a da sauri suka wuce wani sanyayyen ajiyar zuciya ta sauke dan sai alokacin ta d'an samu natsuwa ta sauka a capito road ta d'auki titin unguwarsu sai dai har lokacin bata daina jin mummunar fad'uwar gaba ba adalilin zanen halittarta data gani ,ahankali ta shiga gidansu tana shiga idanunta ya sauka akan umma data fito da wata qawarta ladin na amadu umma na ganin maryama ta saki fuska tana murmushi  tace   "kar dai sai yanzu kika dawo?".

Maryama ta fesar da numfashi tace "wallahi umma sai yanzu na dawo" tô sannu da zuwa amman dai yau kin jima gsky " yau muyi busy ne a wajen aiki gashi yau har apapa aka watsamu sannu da gida ".sannu da zuwa maryama  ya aiki ta sake maimaita wa akaro na biyu ?"alhamd mun godewa allah mun dai kusan qarewa mu huta."

" ina wani hutu tunda ga aiki a gabanki Allah dai yasa mu dace kina qarewa ki samu aiki"
"Ameen ummah na gode allah ya bar girma ." Ladi na amadu tayi shiru tana kallon maryama , ta d'an rusuna ta gaisheta ta wuce su zuwa bangaren su "kamar maryama ko ?inji cewar ladi" Eh! itace "kai girman dan mutu ba wahala kalli yadda ta girma ,wallahi kam ta girma Kmr fa jiya jiya aka haifeta "ai shine mamakin da nake gata ta girma masha allah har ta kai ga bautar kasa kun tsaida mata miji ne ".?

"Masu neman auren suna  zuwa sai dai da zarar anyi magana mai karfi sai su gudu amman dai yanzu ta samu wanda bazai gudu ba ,d'an aminin abban sadam Ke sonta kuma da gaske aurenta zai yi "kash ."! ladi ta fada cike da damuwa ,umma ta kalleta a natse tana cewa "ya naga kin yi wani iri ko akwai wanda zaki nemawa aurenta ne ?ladi ta girgiza kai tana cewa "ko daya wad'an nan ya'yan nawa da duk suka zama abinda suka zama dama lafiyayyu né basu saka rayuwarsu a shaye shaye ba ai sai kayi masu kamu dan naga yarinyar  natsuwa ."


"Sosai kuwa maryama akwai natsuwa su kuma allah ya shirya mana su "Ameen ya hayyu ya qayuyum "amman me yasa zaku bawa wani ?bazaki tsaya an bawa d'ana sadam ba ?a gsky sunyi matukar dacewa da juna "wannan sarkin shiriritan ni kaina nayi masa shaawar auren yarinyar amman ganin gashi gata na dauka shima zai wa kanshi shaawar aurenta amman sai naga shi sam bama maganar aurene a gabansa ba ,amman da zaku had'asu da sai kun fi samun saukin hada kayan aure tuwona maina ba wani abun kirki zaku kashe ba "umma  tai murmushi tana cewa "wato auren arha kuke nema ?ladi ta gyad'a mata kai alamun eh !
"ai kuwa sai dai kuyi gaba dan maryama kam sai wanda aljihunsa zai yi kuka" ahankali suka cigaba da takawa suna tautaunawa a tsakaninsu."

Aunty na fitowa daga daki ta iske maryama tana zaune tana hawaye da hanzari ta qaraso wajenta tana tmbyrta "Ke lafiya me kike ma kuka ?"wani matsanancin kuka ya sake zoma maryama hakan yasa hankalin aunty ya sake tashi "wai me ya faru ne kike kuka haka ? rarrashinta ta soma yi a tunaninta ko mutanen gidansu suka ta'bota daga dawowarta da kyar ta samu tayi shiru ".

"Bari na kawo miki abinci kila kina jin yunwa ta mike ta kawo mata abinci da ruwa sai dai ruwa kawai maryama ta iya sha nan taji zuciyarta tayi sanyi "wai meke faruwa ko abinci kin kasa ci cikin natsuwa ta fad'awa aunty duk abinda ya faru daita yau a wajen aiki "shiru aunty tayi tana dubanta a tsanake kafin ahankali ta soma mgn "zanen mai kama dake princess?."

ta gyada mata kai alamun "eh! "to shine zaki daga hankalinki akanshi ? aunty ai ni bama zanen bane tashin hankalina ba  kamar yadda hankalin mutumin ya tashi matuka ,wai shi sai ya kai ni wajen mai gidansa wallahi aunty yau Allah ne kawai ya taimakeni da sai dai wata bani ba ,wama ya sani ko masu satar mutane ko masu shan jini haka kawai yaje ya saceni su zuke min jini ."

."aunty tayi murmushi tace "masu satar mutane da shan jini ne zaa basu office acikin babbar maikata haka? wata killa dai maigidansa mai kama dake yake mafarki kawai shine kuka yi aran gama dashi Ke kuma kika tsorata" maryama tayi murmushi wallahi nayi matukar tsorata dan bazan qara zuwa aiki wannan maakatan ba "baki da zabi princess dole idan an sake buqatarki kije ke dai kawai ki dinga addua kafin ki bar gidan nan "wallahi aunty ina yi ban ta'ba barin gidan nan batare da nayi addua ba ."


"To shikenan Allah ya qara tsarewa yanzu dai karki saka damuwar wannan abun a ranki har kizo ki rame dan yanzu ma duk kin canza kin rame ba kamar kwanakin baya ba dama ya lafiyar kura" murmushi maryama tayi" allah aunty ba wani rama da nayi ina after dad ? na fita da safe bangansa ba gashi na dawo ma banji motsinsa ba da alamun ya baya gida ?"bai jima da fita ba "bana son ina gida baya nan duk sai gidan yayi min wani iri gida ya dawo kamar gidan mutuwa"ni kuma nafi son shi haka bakina ya huta kwakwaluwata ta huta dan duk abinda akayi akan idonsa bai masa ba sai ya tanka shiyasa idan ya fita sai naji kwanciyar hankali haka sukai ta hira har Maryama ta wastsake daga damuwar da take ciki ."


Shi kuwa bangaren m.malik cikin dauki ya shiga neman layin mai gidansa, daman abinda yasa tun farko bai nemesa ba so yayi yayi masa suprice sai dai kawai ya gansa daita  ,duk da ya rasata yau amman sai da yayi dariyar farinciki ,  lallai mai gidansa dan bawa ne shi da mahaukaci ma ya daukeshi a she dai mafarkinsa zai zama gaskiya ko
babu komai a yanzu sun tabbatar ita din gsky ce kuma dole su basu nemanta "ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun office din hankalinsa yaji ya dan fara tashi sakamakon abinda computer sadawar ke fad'a masa number a kashe take ."


cigaba yayi da kiran numbobinsa sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off "oh my goodness wai me yasa ya kashe wayoyinsa?wani yaronsa ya kira ya budesa yana fitowa  direbansa ya taso cike da girmamawa yana qoqarin ya bude masa mazauninsa ya mika masa hannu alamun ya bashi keyn motarsa "yalla'bai ka bari na kai mana "ya fadi haka ne saboda ganin yanayin da yake ciki kai kawai ya gyada masa ya shiga gidan baya direba yaja suka wuce "ina muka nufa yalla'bai?"


"Babana esatate zaka kai ni direba ya d'auki hanya, duk bayn second sai ya kira layin a kashe a karshe dai ya yanke shawarar turawa ATA sako kamar haka "Slm sir Please call me sir I have gist for you." tafiya kadan sukayi suka kawo bakin tafkeken get din
gidansa ,sai dai kash basu samesa ba dan tun daga bakin get aka sheida masu baya nan "shiru yayi yana tunanin jiya ne fa aka d'aura masa aure kuma ya kamata ace ya tare da amaryarsa "kenan baa nan ya tare da matarsa ba ?yayi wa kanshi tmbyr ."

Ko da yake mutun mai tarin arziki haka ai yana da gida bilaadadin duk kusan yasan rabin gidajensa sai dai bai san wanda zai nufa ba ahalin yanzu dole yana bukatar yayi waya dashi kafin ya nufi kowanne daga ciki ,cike da tashin hankali ya bawa direbansa umarnin su wuce zuwa apapa gra yasan dai dole mahaifiyarsa ko cikin yan'uwansa zasu san inda yake tafiya kad'an sukayi suka hadu da wani matsiyacin go slow tsaki m.malik yaja yana dafe kanshi."

Bangaren  ata kuwa yana can kwance shame shame ya sha whiskey Kmr yadda ya saba yayi mankas yana ta sharar bacci a kasan d'akinsa wannan dalilin né yasa m malik yaji  gabadaya wayoyinsa  akashe dan sai daya kashe wayoyinsa sannan yayi mankas,hakan bai sa m malik ya hakura ba duk wucewar mintuna sai ya kiran layin mai gidansa amsar daya ake bashi ,ganin har zuwa wannan lokacin bai samesa ba yasa yayi qoqarin kira salim ko suna tare dashi shi kuma kiran na shiga baya dauka haka zalika number hisham ."

Wanda a wannan lokacin m.b ,salim ,yaya Ibrahim amar kai har ma da hisham suna tsaye akan ATA cikin tsananin damuwa ,hisham ya fito da wayarsa ya duba number m. malik ya gani bai dauka ba dan nan take ya fahimci magana yake son yi da ATA ya sake kallonsa yadda ATA din Ke kwance wani iri tamkar mara rai ya maida wayarsa cikin aljihu gabdayansu zukatansu cike yake da tashin hankali halin da yake ciki tunanin kawai hisham yake me zai faru idan mami tasan halin da yake ciki dan shi bai san iya kwanakin daya dauka yana shan giya ba sai yau da mb ya kira salim suna tare salim din ne ma ya takura masa yazo ."

wayarsa ta sake ringin ya fito dashi ya duba still m malik ne dan haka ya sakata a silet ya sake maidata aljihunsa "ku kama min shi mu daurashi akan bed inji cewar mb daya kai hannunsa jikinsa yana zubar da hawaye "he don't want to loose him at all ,shi bai san ma soayyar mafarkinsa ya kai haka ba wallahi duk tunaninsa da zarar an daura aurensa shikenan komai ya zama tarihi agaresa a she komai zai yi worst ne atare dashi wani irin tausayin abokinsa ne ya lullesa ".

"Me Ke damun tunanin adam ne ?he's so much in love with his dream ,what will happen idan bai sameta ba? "zan iya mutuwa for real." salim yaji sautin muryarsa cikin maye yana bashi amsa da haka "farincikina na ganta I just love her with all my heart "gbdy suka suke numfashi suka daurashi akan katifa ya kwanta sharaf yana sauke wani wahallalen numfashi "yanzu me zamuyi mu raba rayuwarsa da wannan damuwar ?" yaya Ibrahim ya fad'a "yana dubansu."

Amar ya numfasa yace "ni dai idan son samu ne a rabashi da auren nan na maryam yaji da matsala daya "idan kuma ita yarinyar mafarkinsa ba gsky bace fa ?inji cewar hisham, kawai mu tayashi da addua, yanzu bari mu sheidawa mami halin da'ake ciki saboda idan ya farka karta bari wani ya shigo inda yake ko shi ya fita zuwa koina a tsareshi zuwa na wani lokaci adai samu wanda zai zauan tare dashi da zai dinga kula dashi kamar zai fi "mb ya fad'a yana dauke hawayensa ni bansan wake zuwa siyo masa giya ba dan dai da kanshi bazai iya zuwa ba wallahi muddin naga mai siyo masa giya sai naci uban kowa waye ya qarasa mgnr yana naushin iska ."


"kun fa san halinsa, kunsan halin taurin kanshi babu wanda zai hanashi abinda ya ga dama inji cewar hisham "duk da haka dai a samu mutun biyu zuwa uku su tsaya tare dashi wannna karon bai isa ba matsawar bazai daina shan giya ba ya zama dole mu dauki mataki akanshi haba nifa na fara tunanin aljana ce yarinyar mafarkinsa duk suka zuba masa ido " to idan ba haka ba  kamar adam me zai tsaya batawa kanshi lokaci akan wani mafarki diya ko ta uban waye ai zai samu, kawai   aljanna  da yake gani nata salon kenan  ,amamn da yarda allah qarshenta yazo sai muyi 'bata 'bata daita da ayoyin Allah yanzu dai bari na kira mami "inji cewar yaya Ibrahim ."


Mami kam dake cikin mutanen da suka zo mata biki suna ta'ba hira acikin damuwa take dan duk wanda ya kalleta yaga yadda take abubuwanta yasan tana cikin damuwa mai tsanani sam sam ma babu kuzari ajikinta kawai she's thinking of abubuwa daywa abu biyu yafi damunta rayuwar adamcy bata san yadda zatayi dashi ba, ga kuma ta uwar maryam da kawayenta suna buqatar amarya ta tare a gidanta kafin su wuce ga ango baya cikin natsuwar da zasu tare,yanzun ma da take zaune addua take allah ya saukowa danta tilo da kwanciyar hanakali da natsuwar zuciya."

tana cikin wannan halin wayarta ya fara ringim ta dauka ta duba "sunan yaya Ibrahim ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login