Showing 150001 words to 153000 words out of 167047 words

Chapter 51 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

rashinsa zai wa ciwo a bayana yake to na barwa Allah kada wanda ya sake dawo min da hannun agogo baya kuje na sallameku bana son ganinku, yadda baku qaunar maryama nima wallahi a yanzu bana qaunarku daga yau na yanke duk wata halaka daku ." da sauri aunty salma ta qaraso ta durkushe gaban ummah ta rike qafafuwan umma da duka hannuwanta ta soma girgiza mata kai kamar wata kadangariya tana kuka tana bata hakuri "dan girman allah aunty kiyi hakuri  bazamu sake cewa komai akan lamarin mutuwar sadam da gadonsa ba ki yafe mu dan Allah wallahi sai yanzu nake jin nadamar abinda nayi in sha allahu bazan sake ba tabbas maryama tamkar diyarmu ce Allah ya huci zuciyarki wallahi bazamu sake ba ."



gwalalo idanu aunty hasana da baba gali sukai suna kallon  makirci irin na aunty salma ,sam basu ta'ba tunanin zata aikata haka ba "lallai ta cika babba makira ta qarshe "kiyi hakuri dan Allah aunty ta sake  fad'a tana mai sakar ma umma qafafun ta kamo hannunta numfashi umma ta sauke da karfi sannan ta samu waje ta zauna akan kujera tana runtse idanunta tare da dafe goshinta" sigina aunty salma tayiwa baba gali da aunty hassana alamun suma suce wani abu ai kuwa nan da nan suka matso kusa da umma suna mata magiya da ban hakuri "shikenan komai ya wuce allah ya yafe muna gabadaya amman dai kusani maryama bata cancanci haka daga gareku ba ,maryama a yanzu tafi bukatar kulawa da tausayawa da soyayya tattare da rarrashi daga gareku tun daga farkon rayuwarta baku qaunaceta ba wallahi kuji tsoron allah na rashin rike zumunci tsakani da Allah da kukayi ,wani abun mutane sunayi ne dan ganin ido wani dan zumunci zasu fake suci amana mussaman zumuncin wannan zamani amman ku babu wanda kukayi aciki kona ganin idon ma bakuyi ba bare bayan ido amman wallahi kusani zumunci a duniya wajibi ne duk kuma wanda bai yisa a duniya ba zai yisa a lahira alahirar ma acikin wutan jahannama ta fad'a tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta ".


"wannan tabbas haka ne allah ya shireyar damu gaba daya allah kuma ya bamu ikon sadar da zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba "baba gali ya fad'a yana mai  cike da nuna tausayawa ga maryama wacce hawaye biyu biyu ke bin kuncinta yace "diyata maryama Kiyi hakuri kinji in sha allahu kuka da damuwarki sunzo qarshe domin a yanzu a shirye nike dana baki duk wata kulawa da uba zai bawa diyar cikinsa ."da sauri maryama ta d'ago kwayar idanunta da suka jeme ta tsurawa baba gali cike da mamakin jin furucinsa  aunty salma  tayi tsigil tace "ki daina mamaki jin abinda babanki ya fad'a ,daa na shiga zuciyar mutun a ga abinda yake ciki da mun bude miki zukatanmu a yau kinga irin tarin nadamar da mukayi a yanzu babu wacce muke son gani cikin farinciki kamarki ki yafe mana duk da bamu dace da a yafe mana ba saboda abubuwan da muka dauki tsawon shekaru muna yi miki "in a slow voice maryama tace "babu aunty salma komai na wuce na yafe maku ." murmushin bakinciki suka sakar mata kafin ahankali suka shiga wata hirar allah sarki umma har ga allah ta hakura domin ta d'auka nadamar gasky sukai ,ta sake dasu sosai tayita masu nasiha kuma  duk akan zumunci ne bayan kamar mintuna shabiyar d'aya byn d'aya sukai wa umma sallama suka  fice suka bar umma da maryama .


"Umma nah !"
maryama ta kira sunanta cikin sanyin murya "na'am maryama kina bukatar wani abu ne ?bana bukatar komai umma ,ina dai jin dadi ne tare da godewa allah daya   bani ke amatsayin uwata kuma uwar mijina , ya  allah ka bani ikon kyautata ma umma nah   ,ya Allah ka bani ikon yi mata biyayya, ya Allah ka dawo mana da yaya sadam cikin koshin lafiya ka azurtamu da samun zuria masu albarka dashi ,ya Allah kasa mu kasance  har a aljannatul firdausi atare "ameen maryama ina alfahari dake, nima haka umma ina sonki "baki kai wa ni ba  maryama sonki ajinina  yake maryama, allah ya za'ba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki,Allah ya bamu ikon cinye jarabawar mu ,ahankali suka dinga kwantarwa da zukantansu hankali har suka samu natsuwa sai dai da zarar ka d'aura idanunka akansu zaka fahimci zallar tashin hankali da damuwar da suke "ummah ina jin kauri "bari naje na duba ina ganin abincin da auntynki hasana ta daura ne yake kauri  ."a'a umma Kiyi zamanki bari naje"uhm uhm maryama  bana son kina damun kanki "a'a ummah nah sai dai muje tare ta fad'a tare da mikewa ta tsaya kusa da ummah, umma tayi murmushi a tare suka nufi hanyar kitchen."


*******

tsaye nuzlah take ajikin wondo d'akinta tana zubar da hawayen nadama  a yanzu damuwa tayiwa zuciyarta mummunar kamu  dan ko abinci bata ci tunaninta kaf ya tafi ne akan son sanin matsayinta a wajen yaya hisham ,shin zai aureta ne ko kuma zai zillewa aurenta ne ?kanta yayi mugun kullewa mafuta kawai take nema "idan har bai aureta ba tayi biyu babu kenan bata ga auren ata bata ga nashi auren idan kuwa haka ne ta cuci kanta da kanta tana cikin wannan halin ta  hango shigowar motar yaya hisham din cikin haraban estate dinsu da sauri ta  saki labalen ta qarasa gaban mirrow ta soma gyara fuskarta ta d'auki bakin mayafin abayar da take sanye dashi tayi rolling kanta ta feshe ilahirin jikinta da turare ta fito cikin sauri wanda alokacin har sun samu waje sunyi parking din motarsu sun fito suna taku yaya hisham na rike da jakar nana hauwa'u yayinda nana hauwa'u take takawa da kyar saboda cikinta ya tsufa ."da  sauri nuzla take daga kafafunwanta lokacin data qaraso daf dasu ta kira sunansa "yaya hisham!" cak suka tsaya a tare shi da nana hauwa'u sai dai ita bata juyo ba dan tasan muryar wacce  ,muryar nuzla a raunane tace "yaya hisham ina son muyi magana da kai "jin haka yasa nana hauwa'u ta  daidaita natsuwarta tare da danne zuciyarta da kishin mijinta ba dan komai ba sai dan ta qara kankaro wa kanta mutunci a idanunsa domin ba komai ake magana akai ba hakan yana zubar da martabar mace a idanun mijinta sai dai wani irin bugawa zuciyarta keyi da karfin gaske saboda tsananin kishin mijinta ."



ahankali ta cigaba da d'aka qafafuwanta domin basu dama  hakan yasa yaya hisham  ya juya bayansa  tare da zubawa nuzla ido yana kallonta a tsanake " duk ta rame ta d'ashe kamar wacce tayi shekara babu lafiya ko wacce babu jini ajikinta "idan na kiraka baka d'aga kirana yaya hisham laifin me nayi maka ?tayi maganar cike da rauni ,yayinda hawaye suka cika kwarnin idanunta" ban ta'ba expecting haka daga gareka ba well duk a ajiye wannan maganar ya batun aurenmu dan naga kamar yanzu ka fara canza raayinka akaina ?"Eh tô nuzla kamar haka ne dan a yanzu dai gsky bana jin wannan abu zai kasance a tsakaninmu "me yasa yaya hisham ?ta tambayesa  tana mai kamo hannunsa cikin tsananin tashin hankali "babu wani dalili kawai matata ta isheni daman can giyar soyayyarki ce ta hanani gane quality's dinta a yanzu kuma idanuna sun bud'e na fahimci duk duniya babu salahar mace kamar nana hauwa'u mace ce mai hakuri mai biyayya mai kyautatawa mai kawaici bazan iya had'ata da wata mace ba ita kad'ai ta isheni na qarasa rayuwata ,na godewa allah na godewa mahaifiyata da tayi silar da nana hauwa'u ta zamo mata agareni "dan girman allah yaya hisham kayi hakuri ka aureni nima zanyi maka duk abinda ka lissafa "bazaki iya ba nuzla bazaki iya hakurin da nana hauwa'u take dani ba "saboda me ?murmshin takaici yaya hisham yayi yana girgiza mata kai "kayi tunani akaina yaya hisham karka hukuntani akan laifin da nayi maka wallahi sharrin sheidan ne  ,ita soyayya fahimtar juna ne kuma tun farko bamu fahimci junanmu dake ba shiyasa muka samu matsala,ina sonki baki sona zuciyarki na kan wanina wanda ke a karon kanki Kinsan bazaki ta'ba samunsa  ba "yanzu nake qara jin wannan nadamar da dana sanin abubuwan da nayi maka dan girman allah kayi hakuri wallahi har da sharrin sheidan ".



" babu wani sharrin sheidan nuzla kisa aranki babu qaddarar aure a tsakaninmu ne ana gobe fa daurin aurenmu kika gudu kika barni da tarin damuwa Kiyi hakuri kawai haka Allah ya qaddaro miki sheidan bai isa ya raba abinda allah ya hada ba saboda shi Allah daya hadani da nana hauwa'u yasan abinda yasa ya rabamu ya hadani daita ,a yanzu soyayyar dake tsakanina da nana hauwa'u babu dalilin da zai sa na ita had'ata da wata ina sonta da dukanin rayuwata kasa cewa komai nuzla tayi dan gabad'aya ta lura hankalinsa naga matarsa wacce take can ta rasa yadda zatayi ta shiga cikin parlour'n mami dan zuciyarta wani irin dokawa take da karfin gaske wanda hakan ya haifarwa d'an cikin hantsilawa."
da nana hauwa'u tayi niyyar tura kofar parlour'n mami sai taji ta kasa tsoro take ji zuciyarta na cike da tsoron bari mijinta a hannun nuzla da tayi shi kansa yaya hisham din bai mata adalci ba daya cigaba da tsayuwa da nuzla ai ko babu komai ya kamata yaji kunyarta sannan ya nunawa nuzla tana da matsayi ko yaya ne agurinsa amman saboda bai dauketa da daraja ba yana kallonta ta wuce ya cigaba da tsayuwa daita runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharrr sun biyo kuncinta ."


da kyar dafe da qirjinta dake faman luguden bugu dum dum ta tura kofar ta shiga allah ya taimaketa bata iske kowa acikin parlour'n ba numfashi ta sauke wani zufa na karyo mata a saman goshinta da karan hancinta zagaye parlour'n ta shiga yi zuciyarta na tafarfasa tana cikin wannan halin taji sautin sanyayyiyar muryarsa kasa juyowa tayi ta kallesa dan zuwa lokaci hawaye sun qara cika idanuwanta "baby nah!"tana jinsa amman ta kasa juyowa ta kallesa dan bata son yaga rauninta "baby nah kukan me kikeyi diriricewa tayi tana qoqarin maida hawayenta "zo gareni !qoqarin juyowa take amman kukan da take yasa ta kasa  sai numfashi da take fixgowa tana fitarwa da kyar "please baby nah maman abar qaunata ."still bata juyo ba ta cigaba da tsayuwa tana jan numfashi ahankali ya qarasa ya tsaya abayanta ya had'eta da qirjinsa ya daura hannunsa daya akan cikinta yana shafawa yana shakar kamshin turaren jikinta kusan second goma suna tsaye haka tunani tayi kar wani yazo ya samesu haka yasa ta zare jikinta kwayar idanunsa ya tsura mata yana jin yadda soayyarta ke sake huda zuciyarsa ."


Ahankali ya riko tafin hannunta yayi taku biyu ya zaunar daita akan kujera mai zaman mutun daya ya dawo gabanta ya durkusa a gabanta tamkar mai neman gafara tare da kafeta da kwayar idanunshi yana kallonta yana nazarin yanayinta ahankali ta kawar da fuskarta gefe tana qoqarin sake danne damuwarta numfashi ya sauke da karfi tare da tsarke hannunshi cikin nata ya dawo da fuskarta garesa  "am sorry baby !ya fad'a yana murza tafin hannuta cikin nashi" me kayi ?naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana sake damke hannunta cikin nashi sannan ya motsa labbansa "na haifar miki da damuwa "wani irin damuwa kuma ?ni babu wata damuwa daka haifar min?na haifar miki da damuwa mana nayi silar saka zuciyarki shiga qunci na tsaya na saurari nuzla alhalin ban nemi izini daga gareki ba nasan dole zakiji babu dadi aranki dan Allah kiyi hakuri ki yafe min ."murmushin tayi wanda yafi kuka ciwo "dan Allah ka daina fad'ar haka banaso meye aciki dan ka kula nuzla ?karfa ka manta ni matarka ce nuzla kuma yaruwarmu ce gabad'aya kana da damar aurenta ma ba kulata ba ,karka manta na baka wannan damar idan har yanzu kana raayin aurenta kofa a bud'e take bazan haramta halal din da Allah ya halallta ba sai ma nayi maku fatan alkhairi ta fad'a tana kallonsa shima ita yake kallo yana sake hango damuwa daga gareta ,"


gabad'aya fuskarta ta sauya hankalinta a matukar tashe take maganar da take amman kaji abinda ta fad'a dan karta haifar da damuwa atsakaninsu "ni dai Kiyi hakuri bazan sake kulata ba yau ma na tsaya na kawo qarshen komai ne a tsakaninmu sautin muryarta ne ya katse masa magana "tashi ka zauna please kar qafafuwanka sunyi ciwo ka daina damun kanka dan baka min laifin kome ba tana gama fadar haka ta mike da kyar tana cewa "bari na shiga dakin mami yanzu zan fito ta soma daga kafarta da kyar bayanta yabi da kallo yana mamakin hali irin nata da duka matan duniya haka suke kamar matarsa da baa samu wata damuwa a gidan aure ba komai nata dabam ne yasan tana da tsananin kishi akansa amman yanayin kishinta na daban ne kuma yana burgesa dan sau tari idan ya kira tana d'auka zata ce "an gaishe da mijin nuzla da nana hauwa'u tun abun na masa dadi har yazo ya fara jin zafin abun dan tun yana amsawa yazo baya amsawa sai dai kawar da maganar ya shigo da wata ,mata mu sani wannan d'abia ta nana hauwa'u d'abia ce mai kyau mu dinga kawar da idanunmu da hankulanmu akan mazajen mu ,mu basu dama kada mu saka ido dayawa akan lamuran su most especially akan mata domin Allah ya halatta zuciyar maza da son mata dayawa yayinda zuciyar mata take son nmj kawai mu san irin salon kishin da zamuyi idan kayi mijinka kawaici tabbas zai dinga jin kunyar aikata wasu abubuwan."



"Tun dazu nake binka akan maganar sultana Adamcy  fa sam sam yaki yarda ya dauketa aiki akarkashinsa amman kaki kayi komai akai aunty abida ta cigaba da bin yaya ibrahim abaya tana masa magna amman bai ce mata komai ba "yanzu shikenan babu abinda zaka iya yi akai ?ta fad'a adaidai lokacin da suka tsaya suna fuskantar juna "na rasa meke damun taunainki kina yi kamar baki san halinsa ba tsawon shekaru kina cikin gidan nan kuma babu abinda baki sani akansa ba , kinsan yadda halinsa yake "haka ne nasan komai amman ni nasan yadda zanyi wanda shi kansa bazai ta'ba tunanin zan iya aikatawa ba ai tunda har nayi niyyar sultana ta auri adamcy kamr anyi auren nan an gama muddin ina raye "wannan shine dalilinki naso ta kasance kusa dashi ?ta gyada masa kai alamun "eh! "kina tunanin Adam zai amince da wannan hadin naki ?" ka tsaya kasa ido kaga ikon allah muddin ina raye sai ya aureta "numfashi ya sauke "gsky da kin canza shawara kina kallon yarinyar da mahaifiyarsa ma tayi masa umarni ya aura da kyar ya yarda yayi mata biyayya a qarshe ma sai daya saketa bare wata sultana can ,dama baa acikin family's dinmu take ba ".


"kai dai ka  tsaya kasa ido kayi kallon abinda zanyi tunda shi har yanzu bai fahimci menene dalilin da yasa nake son sultana ta kasance a kusa dashi ba dan haka zanyi komai akai tunda kaima har yanzu kana bada umarni a kafani kamar yadda yake bayarwa ko..."dan allah malama ki bar wannan shirmen naki tun wuri ki dawo hankalinki idan ba haka ba zaki aikata katoton kuskuren da zai jawo miki matsala tabbas  ina da iko akan kafanin adalili mahaifina kuma shima mahaifina nawa a koda yaushe cikin bin bayan adamcy yake akan komai he always supporting Adam nayi imani ko wannan tsarin daya kawo baba babba yasan da komai dan haka a matsayina na mijinki zan baki umarnin ki cire hannunki ki fita cikin lamarinsa idan ba hk ba duk abinda yabi yo baya babu ruwana ya qarasa mgnr yana nunata da dan yatsansa sannan ya kama gabansa shiru tayi tana kallon bayansa tana ystsina fuska ."


Maryama zaune a kusa da mahaifiyarta cikin halin damuwar data tsinci kanta, kullum qoqarin raba kanta da tunani take amman ta kasa domin da zarar ta runtsa idanunta yaya sadam dinta take ganin cikin tashi hankali  yanzu hk ma jan hankali mahaifiyarta take mata "ki fahimceni princess wannan matsalar gabadaya ta shafemu ko nace na fiki shiga cikin damuwa da tashin hankali mai tsananin akan mutuwar  sadam amman me zamuyi daya wuce hakuri mu barwa allah komai hatta mahaifiyarsa ta hakura ta barwa allah mai yasa Ke bazaki hakura ba "nasan akwai ciwo sosai amman ki dauka haka taki qaddarar take bawa kuma bai isa ya canzawa kansa qaddararsa ba ,bamu sani ba ko wani mijin Allah zai kawo cikin kankanin lokaci yasa wannna lamarin ya faru "numfashi maryama ta sauke mai hade da saitin kuka" dan allah kiyi hakuri ki daina fad'a min haka babu wani aure da zanyi na gama aure har abada ."ta jingina bayanta da abun gado ta daga idanunta sama hawaye na zubo mata "you better eat enough with all this cry cry ..."bazan iya cin komai ba aunty ."



"Common bude baki na baki abinci kinji my princess wasu sabbin hawaye ne ya zubo akan kuncin maryam ta dube mahaifiyarta gabadaya ta fita haiyacinta adalilin damuwar data sameta " aunty kin cikin abinci ne ?banci ba ina son sai naga kinci ne taya zan iya cin abinci alhalin princess dina tana kwance kwana uku kenan bata sakawa cikinta komai ba ,maryama ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta dauki karbi spoon din hannun mumcy ta dibi abinci ta kai bakinta "kici abinci sannan naci batai mutsu ba ta bude mata baki ta kai lomar abinci bakin mahaifiyarta, bata kai ga cire spoon din ba aunty ta dibo abinci da hannu ta kai bakin maryama."
Maryama na hawaye mahaifiyarta hawaye aunty tana matukar tausayawa kanta da rayuwar yayanta "ina rokon allah yayi min sausauci domin zunubina yake shafar yayata da basu baji basu gani ba wasu hawaye masu ciwo ne masu zafi sukai zuba a idanunta "in sha allahu zan koma ga dangina zan rokesu gafara "dan allah Allah ki daina damun kanki nima na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login